Showing 159001 words to 162000 words out of 363280 words

Chapter 54 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1370

da gasken gaske..... Wata irin zuciya da idan tana so tana so.....idan bataso bataso,zuciyar da zata iya sadaukarwa da abinda takeso komai data mallaka.....ta zamewa abinda take qauna kariya daga dukkan wata iska ko kuma guguwa.

"Wanne iyalin kake magana akai fu'ad?,iyalin da nice silar wanzuwarsu a rayuwarka?.....ko kuma iyalin da babu wata kima ko martaba a tattare dasu?.....ko kuma ni da aka tsinceni daga ayarin tafiya aka wofantar dani saboda kun nunawa duniya bani da wata daraja a wajenku?,ni din ba kowa bace a wajenku?". Wani ciwon kai dukka maganganunta sukaso tasar masa lokaci daya,ya sanya tafin hannunsa ya dafe goshinsa yana murzashi a hankali tare da lalubo me ya kamata yace mata?,gefe guda kalmar IYALIN DA BASU DA WATA KIMA KO MARTABA tana masa zillo cikin kwanya.
"AKWAI WANI ABU A LULLUBE" yaji wani saqo na zuciyarsa yana gaya masa. Idan har maamah ta aura masa sabreen ne saboda ta yarda da tarbiyyarta kaman yadda tace da farko......me ya kawo wannan maganar a kanta a yanzu?. Bayajin akwai wani abu qwaya daya da zai iya tunawa wanda ya taba hadasu koda cikakkiyar magana bare yayi tunanin akwai abinda ta taba yi mata.

"Fareeda ta taso qafa da qafa.......ta sameni har muhallina......ta girmamani matarka ta tabamin haka?,fareeda tabar qasarta ta biyoka har inda kake,bata da kowa batasan kowa ba saboda tana sonka.......me matarka ta taba yi me kama da wannan?". Kanshi yaji ya sake qullewa......a yau din duka me ya kawo maganganu akan sabreen?,me yahau kan maamah duka akan sabreen din?.

"Ina me baka umarni a matsayina na uwar data haifeka.......nan da kwanaki goma zan bar qasar nan......ba wani jirgi da zanbi,ba wanda zaizo ya daukeni....kai da kanka nakeso kazo ka daukeni ka kuma kawoni Maldives......ka kuma soke barinku qasar ka daidaitashi da nawa barin har sai na kammala uzurina sannan mu tafi......daga qarshe ina me baka umarni kaje kaga fareeda......ka kuma marabceta kaman yadda kowanne baqo yake marabtar baqonsa......wannan umarni na ne indai nice na haifeka" Daga haka ta yanke kiran ba tare data jira cewarsa ba.

Shima wayar ya sauke daga kunnensa yana kallonta,kafin ya sakata a tafin hannunsa yana dan dokata kadan kadan. Kallonsa farouq yayi kafin ya aje dubansa ga wayar hannunsa. Ya fahimci wadda tayi kiran ya kuma ji wani abun da take cewa saboda magana take da qarfi da kuma fushi.

A abinda yake lisssfawa zaiwa fareeda kowanne ya debo sai yaga yayi masa kadan. A hankali maganganun maamah din sai yaji kamar suna tafiya da farincikinsa suna son rushe duk wata walwala daya samu.

Idanunsa ya bude kan farouq yana hadiye kowanne bacin rai da maamah ta sanya masa da rudanin saqon daya shigo wayarsa a dazun.

"Ina jinka......kaman magana kakeso muyi ko?" Yace da farouq. Idanu yadan zubawa fu'ad din,sai yaji tausayinsa yana kamashi. Kowacce ni'ima da baiwa ta rayuwa Allah yayi masa......amma ya rasa UWA TA GARI. Ya sake yarda tabbas rayuwa jarabawa ce,hakanan kowanne dan adam akwai inda tashi jarabawar take,ba wanda yake samun jin dadin duniya dari bisa dari.

Murmushi farouq ya sakar masa,sai yaji bazai iya kowacce magana dashi a irin wannan yanayin ba,don haka ya sauya akalar zancan yana yin murya qasa qasa

"Wai yaya akayi wannan gingimarin ta iya hawa saman keke?,karaya nawa keken ya samu?,duk da ni shaida ne akan yadda keken ya kusa komawa akwala sabod......" Naushi yakai masa cikin sa'a ya daki iska. Ya fahimci lallai da gaske farouq so yake ya maidashi birin wasanshi. Gefe farouq ya koma yana dariya,can qasan ransa yana jin dadin hararar da fu'ad yake watsa masa,yasan tabbas ko bai nasarar gusar da baqincikinsa ba zai rage masa wani abu.

"Wallahi ka iya bakinka akan iyali na......kada ka yarda mu saka qafar wando daya dakai" Yayi maganar yana nunashi da yatsansa.

Ido farouq ya zaro yana daga hannuwansa sama

"Ya salam.....kace me?,iyalinka?,unbelievable.....wazai tayani jin wannan kalmar.......sabreen won the battle" Qaramin dutse ya dauka zai jefeshi ya kwasa da sassarfa ya wuce cikin gida yana cewa

"Wallahi ta haukatashi......ya zama madoki" Tilas dariya ta subuce saman labbansa. Sai da farouq ya bacewa ganinsa sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa. Kai tsaye ya kira jordan sukayi magana ta wasu mintuna sannan ya kashe,ya kalli agogonsa yana lissafin awannin da suka rage su kaishi gurin target dinsa.

&K'arfe takwas na dare agogon Maldives ya gama shiryawa cikin wasu lafiyayyun trouser da t.shirt. ta fidda sigarsa sosai da wani sassanyan kyau ke tsayawa a zuciyar dukkanin 'ya macen data Kalleshi. Wani irin mutum ne da zai wahala ka kalleshi ka kauda kai,koda baka furta komai a kanshi ba amma zai tsaye maka a zuciyarka da idanuwanka. Jikinsa yabi ya feshe da turarukansa,sannan ya sanya sau ciki a qafarsa,ya dauki wayarsa da maqulli ya nufi qofar fita daga dakin.

Dukkaninsu suna dining area suna cin dinner. Kusan tunda suka iso garin tare suke cin abincin safe dana dare,na rana ne kowa da tsarin cin abincinsa bai yuwu suci lokaci guda. Ire iren wadannan abubuwan sune suke qarawa iyalan anni hadin kai qaunar juna shaquwa tare da fahimtar juna.

A kanta idanunsa suka fara sauka,wani irin abu ya tsarga masa tun daga kwanyarsa har zuwa tafin qafarsa. Tun jiya bai sake sanyata a idanunsa ba,suna dakin annin ita da amna. Bazaice ga abinda sukeyi ba,amma lokaci lokaci yana jin muryar amnan da motsinsu,ita kanta amnan bata sake fitowa ba. Ita da amna suna seat din kusa da juna,kaman magana suke qasa qasa,baka iya ji saboda musaddiq da saddiq da suka cika gurin da musunsu da bai gane ma akan meye suke musun ba.

Kaman wadda aka umarta,nata fararen idanun da a kwanakin yaga kaman sun qara girma ta daga ta watsa masa cikin rashin sanin shi dinne ya is wajen. Qwayoyin idanunsu suka gauraye da wani irin mabanbantan feeling. Da sauri ta janye qwayar idonta yayin da nata kallon a gareshi ya zame masa kamar wani irin dafi daya sabbabba mutuwar dukkan wasu gabbai a jikinsa. Tsigar jikinsa ta zuba sanda ta soma motsa wadannan siraran lips din nata tana tauna Chip's din dake gabanta. Bazai taba manta abinda yaji daga kowanne sashe na jikinsa ba a ranar farko daya soma tsotsar tausasan lips dinta ba......wani mahaukacin saqo da suka aike masa da baisan inda zai iya adana yawansu a kwanyarsa ba. Yanzun da take juyasu tana tauna sai ya zamana tamkar tsokanarsa takeyi haka yakeji tana aika saqo kowanne sassa na jikinsa.

Fitowarsa ya sassauta tashin muryar saddiq da musaddiq din,kowa ya maida hankalinsa jikinsa,kasancewar sunsanshi mutum ne da baison ire iren musunnan nasa. Yakance

"Shashanci ne wannan,kuna da abubuwan yi da yawa a gabanku cikin rayuwarku,shi ya kamata ku fuskata" Sau tari musaddiq yakanyi dariya idan bai wajen

"Shifa hamma ya dauka kowa irinsa ne.....ba baki nayi mana ba,amma ba zamu iya achieving abinda yayi achieving ba.....we are doing the best,amma ba zamuyi kaman nasa ba". Kujerar dake opposite dintata ya zauna,sam table din baida fadi sosai,wannan yana iya sawa idan ka zura jiki da yawa gwiwarka ta iya taba ta abokin zamanka.

Zamansa a wajen sai taji kaman gaba daya ya cika wajen.....kwarjininsa da qamshin sassanyan turarensa gaba daya ya gauraye wajen. Nauyin idanuwansa takeji har tsakiyar kanta,abinda bata taba ji ba a kansa tsahon tarayyarsu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_

_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_




84


"Barka da fitowa hamma" Amna ta fada wadda sun hadu yau kusan sau uku sun riga da sun gaisa already.

"Lovey dovey.....barka da dare" Ya fada cikin wani irin aji kaman me qididdige adadin kalamansa na ranar. Murmurshi amna ta saki qasa qasa.

"Hamma.....kada ka saka adda sabreen taji kishi fa.....sunan nan for now ya kamata ace nata ne". Daga shi har ita nauyi maganan ya musu musamman da anni ke a wajen,wadda tayi burus kaman bataji ba tana qarasa shan black tea dinta. Amnan ya kalla sannan a dabarance ya saci kallon sabreen din. Bayajin akwai wani suna daya cancanci ya kirata dashi......har yanzun duk sunan daya bata sai yaji tafi gaban wannan sunan. Daidai lokacin tana jefawa amna harara da fararen qwayar idanunta ne,wani irin kyau yaga ta sakeyi masa,tsigar jikinsa yaji ta zuba sosai har sai daya lumshe idonsa.

"Ka maida hankalinka fa.....aiki zaka fita kayi" Wani sashe na zuciyarsa ya gaya masa ganin tana neman dagula dukkanin lissafinsa.

"Yi serving hammanku takwarata" Anni data kammala shan tea din ta yiwa sabreen magana. Hakan ya masifar yi masa dadi,sai ya ajiye mug din daya dauko da farko yayi relaxing bayansa jikin kujera yana jin jikinsa yana sake mutuwa gaba daya....wani irin feeling yana taso masa yana sake kashe masa duk wani kuzari nasa.

Sai data ji gabanta ya fadi da anni ta fadi haka,amma dole ta ajiye fork din hannunta ta miqe,fork din yabi da kallo,gaba daya ya gama karantarta,bata qaunar abinci ko kusa ko alama....bayajin zai iya bari taci gaba da hakan,dole ta dinga cin abinci me inganci tana qoshi,bayajin indai zata dinga zama ba abincin kirki zata iya dauke lalurarsa yadda yakeso. Shi kansa wani lokaci yana tsoron kansa,tun a lokacin da yake shi kadai ma.....shi da kansa yasan yana da buqatar mace me juriya kafin ya samu abinda yakeso. Faruwar abunnan kuma ya tabbatar masa sa zarginsa,bai taba kawowa ma zata iya dauke buqatarsa.....duk da abinda ya farun yasan akwai aikin gaggawa da kuma rashin sabo a tattare da ita,amma yasan cewa lallai akwai aiki a gabansa,dole sai ya horar da ita yadda zata dace da muradi da tsarinsa.

Kwata kwata ya mance ya samu farouq a wajen,ya shagala wajen qare mata kallo ta qasan idanunsa. Zaka dauka sam ba ita yake kallo ba,amma kowanne motsi da zatayi idanunshi suna kanta sanda take zuba masa abincin. A cikin qaramin hijab take,amma shi ba hijab yake gani ba,wannan kyakkyawar surar tata yake gani,kyakkyawar surar da yakejin koda zata shekara a yana ganinta zallarta bazai gaji ba......kyakkyawar surar data kusa qwace kowanne tunani tasa,ta kusa sanyashi manta waye muhammad jadda gaba daya. Wani sashe na zuciyarsa dake danqare da mahaukacin kishinta ya soma masa zafi,gani yakeyi musaddiq saddiq da farouq dake zaune a wajen suma suna iya ganin abinda yake gani.....yana jin kamar duka suma qare mata kallo sukeyi.

"Gyara kintsi yallabai.....anni fa na wajen nan kada a tafka abun kunya" Cikin kunnuwansa ya tsinci muryar farouq yana fada. Cikin dakiya ya gyara zamansa yana basarwa,abinda ya kusan sawa farouq ya fashe da dariya.

"Shi yasa ake cewa bawa yaji tsoron Allahnsa koda yaushe" Farouq ya kuma fada sama sama. Tunu fuad ya gama karantar abinda yake fada,so amma yanzun baida energy din kulashi. Hannu yasa don karbar mug din da take miqo masa,cikin dabara ya hade da zara zara yatunta da suka ja hankalinsa sosai,ya kuma motsa hannun nasa yana lullube bayan hannunta da tafin hannunsa.

"Thank you" Ya fada da wani irin sauti can qasan maqoshinsa yana karbar mug din.

Kaman an yarfa mata ruwan sanyi haka taji sanda dumin tafin hannunsa yake ratsa kowacce jijiya ta jikinta,ta koma ta zauna tana jin cikin ta duka ya gama cushewa ta qoshi da chips din,sai ta koma juya cokalin kawai.

Tana jin hirarrakinsu amma ita din ta gaza cewa komai,kaman yadda shima ta fahimci jifa jifa yake cewa wani abu. Kanta da idanunta cikin plate din,ta gagara daga idanunta saboda yadda takejin kowanne motsi nata ita yake kallo,ranta ya dinga baci kadan kadan,wannan wanne irin kallon wuce qa'ida ne?. Ta aje kallo a muhallin mazan bariki,wanda yawancinsu suna amfani da wannan hanyar idan sunso dilmiyar dake su afakaki komarsu.....wannan dalilin ya sanya da wurwuri take qarawa namijin da ya fiya kallon wuta. Amma wannan karon nasa kallon sai taji ya banbanta da nasu,don nashi kashe mata jiki yakeyi,ya kuma aza mata wani kwarjininsa sosai da har yake hanata sakewa.

Tsoro sosai taji sanda taji ana lalubar tafin hannunta ta qasan kujerar. Ta fidda idanu waje tanason fahimtar waye,saidai ya bata haske ta hanyar cewa.

"Miqo min tissue paper dincan please" Da wani narkakkiyar murya. Kallonsa tayi ya kashe mata ido daya,ta janye dubanta da sauri tana tura masa tissue din,ya dauka ya aje gefe yana ci gaba da cin abincinsa tabbacin ba amfani zaiyi da ita ba kenan.

Tana ji tana kuma gani yaci gaba da murxa tafin hannun nata ta qasan table din,lallausan tafin hannunsa yana saukar mata da wata irin kasala da kuma tsoro,bai bata dama ba ballantana ta miqe ta nesanta kanta dashi,ba kuma zata iya nunawa kowa abinda yake faruwa ba.

"Amman adda.....you look familiar,tun randa kuka iso Maldives naji kaman na taba ganin face dinki......kin taba zuwa asibitin SAMHG?" Musaddiq ya shigo da maganar cikin hirarsu. Duban musaddiq tayi tana qoqarin daidaita yanayinta kada wani ya fahimci akwai abinda ke faruwa under the table.

"Eh......kaman sau daya ba......na taba kai wata....." Zancanta kuma sai ya katse,ta maida dubanta kan fuskar anni. Duk tsahon watannin da kwanakin sai yanzu fuskar ta dawo mata fes cikin kanta. Matar nan data fadi wajen sallah asma dinta taso tashi.

"Exactly anni itace..." Ya fada yana sakin murmushi sosai gami da ture abincin gabansa.

"Anni ya akayi kika samota?.....wannan data dinga mana masifa saboda mun barki ba kowa a wajenki.....wannan dinnan dataqi bayyana kanta bare ki gode mata,bayan ta dawo miki da jakanki ba'a dauki komai a ciki ba". Maganganun musaddiq suma sanyashi daga kai daga abincin da yakeci yana maidawa kan fuskarta gami da matse yatsunta softly cikin nasa,yanason yaji qarin bayani,yanason samun tabbacin da gaske ita ta taba cetar anninsu?. Anni da mamakin duniya ya isheta ta ware hannunta tana sakin qaramar dariyar farinciki

"Ban sani ba musaddiq......hammanku zaka tambaya.....duk da shima nasan bai sani ba,tunda bai santa ba" Ta qarashe maganar tana kamo hannun sabreen ta riqe cikin nata

"Yau kuwa zan miki godiyar da nayita so nayi miki ban samu dama ba.......sai gashi cikin hikimar ubangiji wadda ta ceci raina ta zama mata ga yaro na......dame zan saka miki sabreen?". Numfashi taja sosai kaman numfashinta zai qwace mata saboda yadda ta qasan table din fuad din ke mata wani irin salo tsakiyar tafukan hannayenta. Ta kasa fadin komai,sai muryar anni data sake ratsowa.

"Komai zan miki ban saka miki ba takwara.....lallai kinyimin abinda bazan iya saka miki dashi ba.....wallet dina babu ko sisi da aka taba a ciki,kaman yadda wayata ta dawo lafiya lau.....ubangiji ya jiqan magabatanki ya kyautata makwancinsu.....na gode na gode sosai". Murmushin jin nauyin annin ta saki tana yin qasa da kanta.

"Ba komai anni......idan har kana da hali dole ka taimaki wanda yake buqatar taimakon nan,da jikinka koda kudinka". Kai take jinjinawa tare da sake qaunar sabreen din,qasan ranta kuma tana tsara wanne abu zata mallakawa sabreen madadin kirkinta gareta?. Hirar yadda abun ya faru a ranar aka fara maidawa,kadan kadan yana kallon fuskarta yana cin abincin,kallon dake qara bashi qwarin gwiwar cin abincin. Duk wani hirar abun da sukeyi sai yakejin kamar suna qara mata gurbi ne da muhalli cikin rayuwarsa.

"Ashe ta mallaki wannan dabi'ar me kyau?" Ya tambayi kansa yana tuna kiran wayar anni daya dinga yi a wancan lokacin.

"Dama can me tsiwa ce.....dama can bata da tsoro" Ya fada qasan ransa yana tuna yadda ta daga wayanshi har sukaso yin fada.

Tana kallonsa ya gama laqai laqai dinsa,abincin da zaici cikin minti ashirin sai daya jashi talatin da biyar,kafin ya gama duk ta jiqe da gumi,tayi saurin miqewa tana cewa

"Bari nayi fitsari" Sanda ta samu ya cire hannunsa a nata.

"Karki yadda da tsarin yin nesa dani......bazan lamunta ba" Ya fada mata qasa qasa sanda take giftashi. Numfashi kawai ta dinga saukarwa cikin bandakin tana jin bacin ransa,haka kurum zai fara zame mata takura ya hanata sakewa?.

Wucewarta yasa yaji cin abincinsa ya qare,ya dan ture plate din yana miqewa.

"Anni zanje Vaadhoo......but bazan jima ba". Maganansa ya daki kunnenta sanda ta murda qofar dakin anni zata shige. Bata fasa shiga din ba,duk da tayi kaman ta tsaya ta kuma waiwaya ta kalleshi.

" Vadhoo kuma?,wajen wa?" Ta tambayi kanta tana zama gefan gadonsu zuciyarta na tuna mata abinda ya faru na qarshe a wajen a waccan ranar.......ranar data bashi dama ya bude wata qofa da ba tashi ba....qofar da bata tanadawa kowa ita ba. Kusan minti uku tayi zaune a wajen,bata shiga bandakin ba bata kuma san me take tunawa ba. Wani mugun tsaki taja,hankalinta yana dawowa jikinta

"Ko ina ma zaije menene naki a ciki?" Ta tambayi kanta da kanta sannna ta miqe da confidence tana shiga bandakin don rage fitsarin da taji mararta ta tara.

Sanda Jordan ke bude masa murfin motar yaji amna na kiransa. Sai daya shiga ya zauna yabar qafafunsa a waje sannan ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login