Showing 99001 words to 102000 words out of 363280 words

Chapter 34 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1449

dake ajiye a gefe sannna ya daga hade da sallama.

"Barka da yamma" Ya dora da fada yana lumshe idanunsa saboda yadda kansa yake sarawa.

"Barka kadai......kana office ne?,inason ganinka idan kun tashi,akwai muhimmiyar magana da zamuyi da kai,sannan akwai baqi da sukeson ganinka" Ta fada kanta tsaye. Yatsun hannunsa da baya riqe da wayar ya cusa cikin sumarsa,yanajin yadda ta jero buqatunta kai tsaye ba tare da neman jin uzuri ba.....ya ya wuni?,akwai damuwa?,yana da lafiya ko babu?. Baisan sai yaushe wannan dabi'ar tata na damuwarta itace kadai damuwa zata sauya ba.....baisan sai yaushe zata damu da damuwar wani ba ta aje tata damuwar da son kan a gefe ba.

"Bana company na dawo gida....."

"Okay,to ya za'a yi kenan?,don duk yadda za'ayi inason ganinka lallai lallai a yau din,ko meye kakeyi ka katseshi kazo ka sameni" Ta sake fadi da dukka sautin da zai gaya masa da gaske take.

Jaririyar ajiyar zuciya ya sauke yana cire yatsunsa daga sumar tasa

"Ciwon kai nake maamah.......amma zansha magani na kwanta zuwa anjima zan shigo" Ya fada da raunanniyar murya,yana jin har qasan ransa ya rasa wani part me girma a rayuwarsa,yanajin ya rasa wani abu me matuqar muhimmanci a rayuwarsa. Duk da yana da anni,yana da farouq,yana da saddiq da musaddiq,amma lokuta da dama yana jin kamar shi kadai ne.....yanajin kamar shi kadai yake rayuwa a duniyar,wani irin maraici da kadaici yana mamayarsa.

"Allah ya kaimu,kada kayi dare da yawa Allah ya sawwaqe" Ta hade maganar duka lokaci guda.

Ya jima idanunsa saman wayar yana kallonta,zuciyarsa na tuna masa abubuwa da dama ciki harda abbansu. Tun asali shike damuwa kuma shike kasa bacci idan dayansu baida lafiya,koda ciwon baikai ya kawo ba. Tun da can ita din bame damuwa da lamuransu bace,tafi damuwa da duk hanyar da zata maida taro ta koma sisi.

Sai daya bushe tas bai sani ba kafin ya miqe yana isa ga walk-in closet dinsa,boxer kawai ya zura bayan ya mulke jikinsa da cream dinsa,ya kuma shafe j?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ikinsa da turarukansa,sai ya koma gefen gado ya zauna bayan ya balli wasu tabs na saukar da ciwon kai ya sha,ya dauki remote guda uku,daya ya zuge duka labulayen dakin dashi,daya ya kashe hasken duka fitilun dakin banda ta gefen gadon,dayan kuma ya saisaita sanyin ac din yadda zai daidai da yanayin da yake ciki.

Cikin duvet ya shiga ya duqunqune yana lumshe idanunsa gami da sauke nannauyan numfashi,ya lumshe idanunsa yana son fatattakar kowanne tunani da lissafe lissafe ko zai samu brain dinsa tadan huce.

Ana kiraye kirayen sallar magariba ya farka daga gajeran baccin daya daukeshi,yaji dadi sosai a jikinsa,sai ya wuce toilet yayi tsarki ya daura alwala. Masallaci ya wuce kai tsaye,akayi magariba da ishai duka dashi,sannan ya dawo ya shirya cikin tattausar exclusive Morocco ta maza me zuwa hade da wandonta. Kalar royal blue ce,sai akayi mata ado da gold zare daga wuyanta hannu aljihu qasan wandon da tsagar gefe da gefe na rigar. Wata zagayyar hula ya dora saman kansa ruwan gold din,wanda yawanci yankin larabawa su sukafi ta'ammali da ita,take farin bafullatanin nan muhammadu jikan jadda ya fito da wani irin kyau da zai wahala ka kalleshi sau daya ka kauda idanu
(Niko nace uhmmmm,kaman kuwa yasan zance akazo yi gurinsa=??).

Clogs ya sanya gold color,ya feshe jikinsa da mayen turarensan nan dake saurin kama zuciya.

Key ya laluba a ma'ajiyarsu ya dauki spare key din daya daga cikin motocinsa. Yau din da kansa yake sha'awar yin driving,abinda ya jima rabonsa da yayi. Yanason ya shaqi fresh air dinnan shi kadai ba tare da wani a gefensa ba wai da sunan yana kare lafiyarsa ba.

Ta kammale komai a daki kaman yadda ta saba duk dare,wanda idan ta shiga kuma ita da fitowa koda hallway ne sai kuma da safe. Tun wancan ranar ta sake jin ta tsani dukka wani abu da zai sake hadasu ko ya hada alaqarta dashi. Idan ta tuna tambayarsa din kuma takanji wani mugun haushinsa na sake mamayarta,tana jin a sannan me yasa bata amsa masa da eh wajen wani naje ba?.

Sai data zauna tsaf sannan ta duba night stand fridge dinta babu ruwa ko qwaya daya a ciki. Baida girma fridge din,don haka kadan kadan take saka ruwan saboda gorar zata cika waje. Miqewa tayi tana yamutsa fuska,ta dauki Indonesian hijab dinta navy blue ta zura wanda ya haskata matuqa,ya kuma fidda lallausar sumar dake kwance gaban goshinta. Harta miqe ta dauki wayar huda da zuwa yanzun tayi nisa da amfani da ita,tayi playing drama din da take kalla daga inda take,a haka ta fita rabin hankalinta yana kan wayar.

Wannan dalilin ya sanya bataji saukowarsa ba daga stairs din saboda lallausan clogs din dake qafarsa baya bada sauti ko kadan,duk kuwa da cewa da dan sassarfa yake saukowar yana gaggawar isa ga mota,so yake yaje ya dawo da wuri akwai ayyukan da bai samu daman yi ba dazu,yanaso ko cikin daki ya ragesu.

Stairs din ya danyi kwana kadan wanda sai kazo rabi sannan zaka hangi wanda ke fitowa daga farkon hallway din,kaman shima......sai daya zo rabi sannan ya ganta. Idanunsa suka sauka saman fuskarta data fita fes cikin tsakiyar hijabin kalar luxury Morocco din jikinsa. Hasken dake fitowa daga cikin wayar ya haske fararen idanunta dake sheqi kamar an diga mai. Bai fasa saukowa ba kaman yadda taci gaba da takawa idanunta kafe akan wayar,har sai da cikin jikinta taji kamar ta iso qofar da zata sadata da parlor din.

Daga kan da zatayi ta tsinceta dab dashi sanda yake stair din qarshe. Sai ta juya a hankali da zummar yi masa yadda ta saba wato komawa don ta kubcewa hada numfashi dashi.

55


_Daga abu hurairah RA yace,manzan Allah S A W yace: "ku kashe baqaqe guda biyu koda kuna cikin sallah; MACIJI DA KUNAMA_




Taku biyu kacal tayi ya cimmata,ya kuma sanya hannunsa ya dawo da ita baya,sai gata tsaye cak a gabansa kaman ba inda ta matsa. Idanunta tsakiyar nasa idanun da suka qaa girma kadan saboda ciwon kan dazu,yayin da hucin numfashinsa ya dinga fita cakude da qamshin turaren jikinsa yana kaiwa ga hancinsa.

"Wanne kalan dodo ne ko abun tsoro a jikina da kike gani?" Ya jefa mata tambayar a zafafe yana ware mata idanunsa. Ja baya tayi niyyar yi da sauri saboda yadda ta dan tsorata kadan da yadda idanun nasa suka qara girma,ga wani shimfidadden kwarjini dake fita daga cikinsu ya daki zuciyarta lokaci guda ya kuma ninka gudu da bugun zuciyartata.

Hannunsa qwaya daya ya sanya yasake dawo da ita gabansa yana sake bude mata girman dukkanin idanunsa.

"Ki nunan abinda ke baki tsoro a jikina nace!" Ya fada da dan tsawar takaicin abinda takeyi masan. Shi tun farko mutum me dan kai tsaye,koda laifi kayi masa yafison ka fuskanceshi kai tsaye.....haka koda matsala kake dashi yafiso ka tunkareshi kai tsaye ku warwareta.

So take ta maida masa me zafi ko zata fanshe abinda ya gaya mata ranar nan,amma sai ta lalubi kwanyarta da bakinta tsaf ta rasa komai kamar an mata sata.

Ringing din wayarsa ne ya sanyashi maida dubansa ga wayar. Kusan a tare idanunsu suka kai kai,kuma daga shi din har ita sunga sunan da yake rubuce a kai FAREEDA KHALED MUSTPHA.

Maida dubanta tayi ga fuskarsa ba tare da tasan dalilin hakan ba,sai kawai ta zabi ta zille ta tsakanin qofar ragon da yayi mata,saidai kuma tana motsawa kamar hankalinsa yana maqale ne a jikinta ya daga kai ya watsa mata idanunsa bayan ya maida wayar aljihu ya sakeyin kicin kicin da fuska.

"Daga yau duk ranar da kika qara ganina kika koma kaman kinga dodo saina biki har cikin dakin na zaneki tas ciki da baya". Maganar tayi mata banbarakwai,kamar wata nadra ko haneefa?,wannan mamakin ya bayyanata tsakiyar qwayar idanunta da baisan me yasa yake yawan sanya nasa idanun a cikinsu ba duk sanda magana irin haka ta hadasu.

"Kina mamaki ne?,ko kina ganin kin wuce duka?,ki gwada koda gobe ne ki gani.....and,daga yau kada ki sake ganina baki gaidani ba......tunda ko banza ana ci dake ai ko?,koda ban baki abinda wadancan suke bakin ba" Ya qarashe maganar yana sakar mata hanya.

Cikin qasa da second uku ruwan hawaye ya tararwa idanunta,ya za'ayi ya qara mata ciwo akan wancan ciwon,tana jin lallai yau ta barshi ya tafi haka yaci bulus din da ba'a taba cinta a kanta ba

"Ka daina burga kaman kana da abun bayarwar.......ni bana buqatar ragowar su fareeda tunda akwai masu fresh......." Cak maganar ta tsaye mata a maqoshi sanda yayi wani irin waiwayowa daidai sanda yake dab da zarcewa falon. Batasan ta juya ba har ta soma tafiya zuwa dakinta ba sai da taji tana taka lallausan carpet din dake shimfide daga tsakiyar wajen.

Dif wuta ta dauke masa,zuciyarsa ta shiga raya masa nau'ikan hukunci mafi tsauri daya dace yayi mata. Saidai kiran wayarsa ya sake katse masa duk wani hanzari,ya duba kiran a fusace yana tunanin fareeda ce,amma ganin maamah ya sanyashi tattare duk wani bala'i daya taso masa ya hadiyeshi,sannan ya daga wayar yace da ita a taqaice

"On my way"

"To ka hanzarta" Maamah ta fadi tana jin dadin yana hanya bawai yaqi amsa kiran nata bane.

Kai ya jijjiga yana takawa a hankali yana ficewa,saidai a ransa yaci alwashin dole ya ajiye mata abun tunawar da bazai sake fadin magana ta maida masa ba. Duka duka shekarunta nawa amma sanadin aure raini yana neman shiga tsakani?". Ya fada qasan ranshi sanda yake tayar da motar.

Da wani irin speed yake jan motar,wanda dama sabonshi ne gudu a mota,ba tun yau ba ba kowa ke iya shiga mota ba indai shine zai tuqa. Idonsa ya lumshe yana tuna abinda tace masan,sai wani sashe na zuciyarsa ke gaya masa.....zai wahala cikakkiyar budurwa me kunya ta iya fadin hakan.....ita kuwa bata cikin kowanne sahu,dom haka idan ta fadi sama da haka ma fuad kada kayi mamaki.....kowa yasai rariya yasan zata zubda ruwa.

Har ya isa gidan maamah wannan kalmar ta kasa fita a ranshi

"Ragowar su farida....kamar ma kana da abun bayarwar" Har cikin ransa ya gamsu ta rainashi,sai ya samu Kansa da kallon Kansa a side mirror,yana tuna dararen da yake kashewa a tsaye ba tare daya isa ya kwanta ba bare ya samu cikakken bacci saboda tsananin yadda ya kame kanshi. Da wannan bacin ran,da kuma tunanin hukunci mafi tsananin daya kamata ya dauka ya isa parlor din maamah.

Mamaki na gasken gaske ya cikashi lokacin da yayi sallama ya tsinci fareeda cikin masu amsa masa sallamar tasa. Tana zaune hankali kwance saman sofa din parlor din. Sanye take da riga da wandon Palazzo daya bude sosai daga qasa. Rigar me gajeran hanny ta lafe a jikinta ta kamar yadda Palazzo din ya fidda shape din hips din ta zuwa qugunta. Bandana ce kawai saman kanta,hannunta riqe da wayarta.

Kallo daya tak ya mata ya dauke kansa kai kace bai taba sanin wata halitta a duniya me ire iren kama da ita ba. Qasan maqoshinsa kuwa kawai kaiwa da kawowa maqogoronsa yakeyi,adams apple dinsa yana motsi daga sama zuwa qasa,ya taka a nutse kuma kai tsaye ya wuce gaban maamah din a ladabce.

Tunda yayi sallamar ya shigo taji gaba daya an tsinke duk wata jijiya daka iya baiwa dan adam kuzari daga jikinta. Tunda take haukan son fuad bata taba tunanin haduwarsa da kyansa ya zarta yadda ta gagganshi bama sai yanzu data ganshi cikin shigar mutanen Morocco,wanda nan Nigeria zaka ga suna kama da tufafin da sarakuna ke sanyawa musamman idan suna ganawa da baqi cikin gida. Numfashinta cak yaso tsayawa,muhammad fuad ya wuce yadda take hangensa a nesa,a take taji tabbas zata iya sadaukar da komai data mallaka don ta samu fuad din a matsayin mijin aure
(Anya....fuad din fa me tsada ne......amma muje zuwa,tunda kin kama maamah wataqila kina da rabo).

Kusan duka gaisuwar da sukayi shida maamah da gajeriyar gabatarwar da maamah tayi masa bata ji ba

"Baquwar taka ce muhammadu.......ina me umartarka ka saurareta ka kuma fahimceta.....duk wanda yayo tattaki qafa da qafa ya taho gareka saboda yana sonka ba qaramin masoyi bane,idan Allah yaso kuma matarka ce" Ta fadi maganan qarshe tana yunqurawa ta miqe.

Daga kai yayi yana duban maamah sanda take jifan fareeda da murmushi,da salo kuma na bada goyon baya take cewa

"Gashinan fareeda,bari na shiga na fito kafin ku gama"

_idan Allah yaso kuma matarka ce_ yaji amsa kuwwar maganarta ta qarshe tana nanata kanta cikin kunnuwansa. Maganar sai taso ta masa kama da maganar data masa daidai sanda ta tilastashi auren waccar yarinyar.......me yake shirin faruwa?.ya tambayi kansa.

"It will never happened" Ya fada yana qaryata komai da zuciyarsa ke qiyasta masa zai iya faruwa.

"Hi......ka ganni har gida?,yanzu ka yarda garin masoyi baya nisa ko?" Ta fada tana sakar masa murmushi,murmushin nata dake daidai da diban garwashin wuta ta watsa masa.

Wannan bai dameta ba,yanayin fuskarsa duka bata sakashi a mizanin damuwa ba.......zai gata ta zame tana saukowa qasa. Ta qaraso dab dashi tayi Zaman raquma tana dubansa

"Please Muhammed kada kayi rejecting dina.....na maka alqawarin zame maka duk kalar matar da kakeso kake buri" Ta furta da tsananin narkewa.

"Stop it please......ke me yasa baki nemawa kanki martaba mutunci da kima?". Ya fada bayan ya daga mata hannu ya dakatar da ita daga maganan farko launin idanunsa sun fara sauyawa saboda bacin rai.

A rikice ta girgiza kai ganin yana juye mata zuw wannan fuad din me wahalar samu.....wannan fu'ad din me tsananin tsauri

"Mutunci martaba da kima duka susha zamansu muddin zan samu muhammad fuad". Shuru ya ratsa qarshen maganarta,ya xuba mata ido yana sansano alamu alamun hauka tattare da ita,sai ya matsar da fuskarsa kusa da tata kadan,da wani sauti can qasa wanda tsanantar bacin rai da kuma sarawar da kansa yayi ya dawo da ciwonsa sabo fil ya tilas masa maganar a haka yace

"Gashi shi kuma muhammad fu'ad din saida wadannan abubuwan ake samunsa......." Daga haka ya miqe tsam da zafin nama,sai gata ta miqe tare dashi cikin tsoro da fargabar kada yaqi tsayawa ya saurareta duk da kuwa ta dangana da mahaifiyarsa.

"Umarni nake baki......ki tattara kayanki kibar gidan nan,kada na dawo jibi na sameki,don gobe ma tayimin kadan,bazan iya shaqar iska a wajen da kika dade a cikinsa ba". Yana kaiwa qarshe ya juya da zafin nama me gauraye da fushi ya soma fita.

Ta dauka zata jure saita kasa,ta bishi a baya da gudu gudu tana kiran sunanss,saidai ko ta kanta baibi ba,ya bude motarsa ya shige ya kunna ya tasheta da wani irin qarfi ya fusgeta yana fita a gidan,don ko sanda ta qaraso sawayen motar kawai ta samu,saita zube a wajen tana qwala kiran sunansa,abinda kunnuwan maamah suka jiye mata kenan,ta fara saukowa da sassarfa daga sama.

Baisan yadda yakai kanshi gida ba saboda tashin hankali da tsananin ciwon kan daya saukar masa,shidai yaji daya daga cikin security nasa na cewa yabar motar daga nan zai qarasa shigo da ita ya gyara parking din.

"Sai yaushe maamah zata canza?,sai yaushe zata zama cikakkiyar uwa?,sai yaushe zata zabi girma da mutunci sama da kudi?,sai yaushe?,sai yaushe?".

Kusan wannan shine abinda ya sanyashi kwana ya kuma tashi da ciwon kan daya hanashi fita,ya kuma kashe dukka wayoyinsa don baya qaunar ya nemi wani ko shi a nemeshi.




*_WASHEGARI__*

*_BAQIN DARE_*

*_MUHAMMAD JADDA RESIDENT_*


*10:45 NA DARE*

Tunda ta fara kallon film din hankalinta bai kwanta ba sai yau da taga qarshensa. Duk da cewa ya bata mata lokaci sosai,don sai a yanzun sha daya saura na dare ta kammala......amma kuma ya haifar mata da wani irin nishadi a zuciyarta,nishadin da duk idan ta tuna yadda rayuwar stars din ta kasance a ciki sai taji ta saki dan murmushi kadan. Sam ita din ba ma'abociyar kallo bace......wannan shine film na farko data fara kara full kuma wai korean series.

Idanunta ta lumshe tana shaqar iskar dake kadawa sosai take kuma yiwa kanta hanya ta windows din


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login