Showing 291001 words to 294000 words out of 363280 words

Chapter 98 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1375

nan da azahar gidan ya zamana daga mu sai mu,na tabbata ku kudai kukasan abun.....daga haka banaso labarin ya qara gaba"

"In sha Allah yallabai za'ayi duk yadda kace" Ta fada cikin girmamawa.

Yana shirin haurawa saman yaji muryar farouq,waiwayawa kawai yayi ya kalleshi yana amsa sallamar saiya juya yana haurawa saman. Hankalinsa duka yana kan anni,don haka ita ya fara gani a sanda ya bayyana a parlor din saman.

Kallo daya tak yayi mata yaga wata irin rama ta bayyana saman fuskarta,daga daren jiya zuwa yau?,idan kuma abun ya shallake haka kuma fa?,fu'ad ya tambayi kansa da kansa hankalinsa a tashe.

Sauke dubansa ya sakeyi ga huda,wadda ke cure waje daya taci kuka har ta soma jin ba dadi,saddiq na zaune kusa da ita,da alama qarfin gwiwar lallashinta yake neman tattarawa kuma bai samu hakan ba.

Musaddiq kuwa yana zaune kaman zane,ramarsa har taso wuce ta annin da wani taqi na musamman.

Kallon da yayi musu dukkaninsu a lokaci daya sai yaji zuciyarsa na nufin karyewa kaman yadda ta anni ta karye. Ganinsu sun biyun sai takejin dukka qarfinta ya tattara a nan....kaman sune duk wani hope nata a yanzun.

Fu'ad ne ya lura da yadda jikinta ya soma rawa,ya qarasa da sassarfa ya riqeta yana zaunar da ita. Komawa yayi gabanta ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa.

"Kece qarfin mu anni.....don Allah ki sake bamu wannan qwarin gwiwar koda karo na qarshe ne....koda shine alfarmar qarshe da zaki mana mu 'ya'yanki". Duk yadda taso tsare hawayenta sai daya zarto,saidai tayi qoqarin saurin daukeshi,banda su farouq da fu'ad din ba wanda ya gani.

"Allah shine qarfinmu muhammadu.....shine kuma zai tsaya mana" Ta fada tana tattaro jaririyar dauriyar data rage mata. Saidai shigowar abba a daidai lokacin ya sanya qwarin gwiwar nata ya sulale yabi ruwa,don nufarsa tayi hawaye yana tsinke mata,fu'ad ya yiwa saddiq alama daya sauko da huda ya juya yana sauka da sassarfa.

*_BAYAN MINTI TALATIN_*

Dukkaninsu suna falon daya dauki shuru bayan gama tattaunawarsu akan al'amarin.

"Nayi alqawarin muddin ina numfashi......tsakanin yau da gobe.....idan yayi tsanani zuwa jibi,tabbas da ikon Allah,da kuma girman zatinsa amna zata dawo cikin ahalinta.....inason kowa a cikinku ya ajiyemin wayarsa.....BB harda kai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?,kubar security code dinku akai basai kun cire ba.....abu na biyu kowa inaso ya sanya ido akan motsinsa,da motsin duk wani mutum da yake mu'amala dashi komai qanqantarta.....anni ki saka taki wayar a ciki.....abba zanyi connecting kowanne kira da wayata basai ka bayar da taka ba.....but kowanne saqo ko.kiran duk da nayi connecting ka kula sosai yayin dagawa......zamuyi aiki da team dina na kwana biyu zuwa uku in sha Allah" Yadda yace din duka hakan akayi,har zai fita ya dubi huda.

"Bani taki wayar" Saboda wani tunani da yayi. Throughout yau bayason yau sabreen tasan komai ko taji komai,idam ta yuwu ma har zuwa sanda zaa kammala abun,saidai yasan abune me wahalan gaske,karbe wayar hudan zai rage shigarta tashin hankali.

Wunin ranar gaba daya bai zauna ba,dukkaninsu shi da farouq dinma,zirga zirga ce kawai ake yinta a sirrance. Hankalinsa dukka yana kan wayoyin daya karba,wai ko zaiga wani baquwar number ya shigo,saidai ko gilmawar saqo bai gani ba.

Zuwa yammaci saqo da kiran sabreen ya cika masa waya,sai daya idar da sallar la'asar ya ciro wayar sannan ya tuna tunda ya fita a gida bai kirata ba. Da sauri ya maida kiran nasa zuwa ga wayarta,bugu daya ta dauka,muryarta duk tayi wani laushi sosai.

"Am so sorry my world.....ayimin afuwa,munyi busy yau sabgogi sun riqe muffin sosai".

"Hamma na dauka ka manta dani ne yau?,yau Walmar anni,ga lokaci yana shirin kufcemin,na gama shiryawa ban sameka ba,kasan bazan fita ba kuma bada izininka ba,still kowa a gidan na kira number dinsa bai daga ba,hadda huda ma,lafiya kuwa hamma?". Yadda tayi maganar ya tabbatar jikinta ya soma raya mata akwai matsala,muryarta tayi wani laushi.

"Na saka an tsaida walimar nan sabrrr...zazzabi ne ya saukarwa anni,kinsan kuma tana da asthma.....so kiyi zamanki a gida.....i will tray my best naga na dawo gida da wuri". Dan jim tayi kadan kafin tace.

"Anya baka boyemin wani abun hamma?,ko wani abunne ya samu annin?". Murmushi ya saki me dan sauti na qarfin hali.

"Ba komai my world.....karki damu.....ki kulamin da kanki,ki gaidamin yarana". Ya fadi yana katse kiran.

Lamo kawai tayi saman gadon zuciyarta na wani bugawa,bugun sam ba daidai take jinsa ba,hakan yana sake bata tabbacin akwai abinda yake tafiya ba daidai ba.

Tayi juyi saman gadon har batasan adadinsa ba,a nan sallar magariba ta sameta taje ta bada ita,tayi isha'i ta sake dawowa ta kwanta.

Indai ciwon anni baiyi tsanani ba ai ya kamata ace ta samu koda mutum daya ya daga kiranta,bawai kowa ta kira wayarsa zata yita ringing bai daga ba.....ciki harda fuad din kansa.

Sanda tara na dare yayi sai taji hankalinta ya soma tashi,kiransa ne ya bata relief dan kadan.

"Am sorry....on my way dear,karkiyi kewata da yawa". Maganan da sukayi kenan a taqaice.

Yana ajiye kirannata wayar farouq ta dauki ruri. Da hanzarinsa ya ajiye tasa wayar y kuma daga wayar farouq din yana kallon screen din.

Baquwar number ce da babu ita a jerin lambobin kan wayar,baiyi jinkiri ba yayi hanzarin hada abinda zai hada ya kuma daga kiran.

"Farouqu hamza kibiya haka ne?"

"Shine" Fuad ya furta kansa tsaye yana fatan hirar tayi tsahon da yakeso.

"Yauwa......mune wadanda muka dauki qanwarka amna a jiya........saidai kafin mu tattauna komai daku muna buqatar kudi naira billon goma". Idonsa ya lumshe ya sake budesu,wani fushi yana taso masa yana lullube zuciyarsa. Ashar yakeso ya fara sake musu a matakin farko,to amma kuma har yanzu ba'azo gurin ba.

"Ba matsala.....zamu saka muku......amma idan munyi hakan zaku sakar mana qanwa salin alin?".

"Me yuwuwa....duk da bamu keda wannan hukuncin ba,wanda keda ikon fadin a saki ko a kashe daban.....wannan din ladan aikinmu ne muke buqata daga gareku". Bakinsa yaji yana motsi,amma sai yayi qoqarin danne zuciyarsa.

"Zamu biya mun amince......ku fadi inda za'a saka kudin".

" Zamu saka" Ya fada yana datse kiran.

"Oh shirt" Fu'ad ya fada yana dukan seat din motar. Qiris ya rage mintunan su cika.....baici nasara ba......

Bayajin wannan daren yana da nutsuwar gyangyadi ko bacci komai qanqantarsa.....maganar kisa suke fa idan ta kama?. Baiko jira Jordan ya gama tsaida motar ba ya bude ya dira daga ciki yayi cikin gidan.

Baiko tsaya tantance wanda yake parlor din ba ya ketashi ya wuce hallway,wannan qofar dake a kulle kullum ya danna ya budeta yana kutsa kansa ciki.

Ajiyayyen gurinsa ne dake dauke da tarin na'urori,ba kuma kasafai ya fiya shiga wajen ba sai ta baci ko kuma yana da babban aiki irin haka.

Gaba daya qwayayen ya kunna ya kuma kunna kowacce na'ura ya saitata kan aiki,ba dadewa komai ya daidaita,ya fidda gaba daya wayoyin ya zubesu ya riqe ta farouq a hannunsa yana kwafe numbers din zuwa allon screen din dake gabansa.

Tiryan tiryan ya soma kurdawa cikin bincikensa,saidai kaman yadda ya zata komai ya tsaya daidai iya mintuna daya kashe kiran.

"Ya salam" Ya fadi yana jin wani zafi da fusata.

"Da gaske dai wani abu ya faru" Muryar sabreen ta ratsa kunnensa. Da sauri.ya daga kai yana dubanta. Tana tsaye daga bakin qofa,sanye da night wear baby pink masu daukan idanu masu hawa biyu,gashinta ta sakeshi saman kafadarta,yayin da jaririn cikinta ya bayyana sosai ta cikin rigar kasancewar ta lafe mata sosai a jikinta.

Duk da yanayin da yake ciki na tashin hankali hakan bai hanashi hango kyawunta ba......hakan bai hanashi ganin wani kwantaccen kyau daga gareta ba.

"Listen sab....."

"Karka rufemin hamma.....na roqeka" Ta fada jikinta da muryarta dukka suna rawa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*




144


"Is alright......zo ki zauna" Ya fada yana tashi da kansa,ya kuma tarbota yaja mata kujera ya zaunar da ita.

Ta bashi dukkanin wata nutsuwa da hankalinta tana kallonshi.

"Kiyimin alqawari ba zaki daga hankalinki ba....."

"Nayi hamma.....nayi". Kai ya jinjina,ya sake riqe hannunta sosai yana duban tsakiyar qwayar idanunta.

"Amna ce tadan bace jiya,amma yanzun haka ina kan gano inda take"

"Amna ta bata ko kuma an saceta?,wanne ne daidai a ciki?". Ta tambayeshi tana jin wata kaduwa tana kama ilahirin gabbanta.

Juya maganar tata yakeyi a ransa,ya sake kallonta yana ganin yadda ta kafeshi da ido kaman me tuhumarsa da aikata hakan.

" Kowanne za iya zama daidai....."

"Bazai zama ba.....inaji a jikina dauke amna akayi intentionally.....wallahil azeem" Tana kaiwa nan saita rushe masa da kuka gaba daya.

Rudewa yayi,gaba daya kukanta ya dauke masa nutsuwa.

"Bamuyi haka dake ba sabreen.......karki cutarmin da yara please" Ya fadi yana hade hannayensa guri guda gami da sanya nata hannuwan cikin nasan=?O?.

"Me yasa zaka boyemin hamma?......sai idan ta mutu sannan zaka gayamin?,ina huda?"

"She's safe" Ya bata tabbaci. Kai ta girgiza,sam hankalinta bai kwanta ba.

"She's not safe tunda aka dauki amna.....nadra haneefa dukkansu suna cikin barazana"

"Like how?" Ya fadi yana dubanta da tarin tambaya gami da zama sosai a gabanta sabanin tsugunnon dazu.

Tambayarsa ta dawo da ita cikin hayyacinta. A hankali ta sassauta sautin kukan nata. Zato bai zama gaskiya ba.....zatonta kuma a yanzu baida hujja ko dalili sai qwqwaran zargi,tana gudun ta furta abinda idan yaje ya dawo zai zama ba gaskiya bane,da wanne ido zataci gaba da kallonsa?..

"Kina da wani masaniya ko hasashe ne?" Kai ta girgiza

"Babu....but duk wanda ya shiga ya dauki amna....nadra dasu huda ba zasu gagareshi ba"

"A tsukinnan indai ba aljani ba,banajin akwai wani dan adam daya isa ya keta tsaron da gidan yake dashi ya dauki amna.....ina kyautata zaton fita tayi.....zan binciki duk wani CCT footages na gida.....naci alwashin amna ba zata kwana uku ba cikin iyalinta ba". Wani irin abu taji yana yawo da ita,ya jima yana qoqarin daidaita mata nutsuwarta,amma kuma hakan bai hanata kwanan kuka ba,bisa sharadin itama gobe ba zata zauna a gidan ba,ya kaita gidan anni.....anni bata cancani fuskantar wannan tashin hankalin ita daya ba.

&Taku biyu tayi ta sake juyowa tana komawa bakin window din. Sake riqe wayar tayi sosai a kunnenta tana jin wani farinciki yana yawo da ita,jinta take tamkar a saman gajimare. Karon farko data fara kasancewa cikin sa'a a rayuwarta,karon farko data aiwatar da wani aiki da yazo mata da nasara ba a karon farko ba sai wannan.

"Komai kakeso zaka sameshi tunda har ka cikamin muradin raina,iya wannan nasarar daka tabbatarmin ta isheni farinciki......wannan yarinyar dake hannunku kadara ce.....kadara ce me girman gaske,kada kuyi wasa da ita har sai kun samu abinda kuke nema"

"Na sani hajiya,daga adadin abinda muka fara tambaya kuma muka samu tabbacin samunsu nasan munyi babban kamu,munyi kuma babban aikin da zamu fita daga talauci har abada".

"Qwarai da gaske" Ta fada tana jinjina kai.

"Ina yarinyar take?" Ta buqata ganin amna,ba bata lokaci ya juya kiran video call ya kuma haska masa amnar.

Tana ya she tun sanda suka sheqa mata abun bata dawo hayyacinta ba. Baki ta tabe

"Wai wannan abarce zata cakuda jinina da nasu?....kuci gaba da aliyarta.....tabbas sai na sanya sunyi nadamar hada hanya dani da kuma sanina koda sau daya ne a rayuwarsu" Ta fadi tana dauke idonta daga kallon amna.

Kiran ta katse tana sake murmusawa,idanunta kan farfajiyar gidanta.

"Wannan wasan zaiyi dadin kallo.....zan samu farinciki matuqa idan naje idanuna suka ganemin jigatar da ahalin alhj hamza sukayi tsakanin jiya shekaran jiya da yau" Ta fadi a ranta,sai kawai ta fada wanka.

A nutse ta shirya cikin qasaitaccen lace,lace ne na alfarma da ita kanta a jininta tasan ba qananun kudade fu'ad ya sanya ya siya mata shi ba.

Laluba ma'ajiyar sarqunanta tayi,duka gold sun qare sai fashions masu tsada. Su ta sauko ta zuba tsakanin hannuwanta wuyanta da kuma kunnenta,ta bade jikinta da turare,ta kuma dauko tsadajjen mayafinta mahadin lace din ta yafa.

Tunda tazo gidan taga yadda anni da musaddiq ke a birkice idanunta basu huta da zubda hawaye ba,ba iyasu ba.....hatta saddiq dimma da hudan gaba daya. Sak gidan ya koma musu kaman gidan makoki,sauqin abun daya duk an sallami kowanne baqo ba tare da an bari ya fahimci komai ba.

Duk yadda anni keji daga qarshe ita ta koma lallashin sabreen,wani irin abu takeji daya kasa tsarga mata,qaqqarfan zato da zargi maras iyaka dake mata kai kawo,wanda tayi imanin wannan karon komai ya kawo qarshe muddin ya tabbata abinda take zato dinne.

Cikin isa da izza take takawa zuwa ainihin babbar qofar parlor din. Iska take zuqa sosai d'ai d'ai tana fesarwa. A yau jin kanta dama duniyarta sabuwa takeyi,a haka ta isa qofar falon annin ta turata ta shiga tana rangada sallama da muryarta data fita fes.

Sabreen ce mutum ta farko data fara daga idanunta ta kalleta,fes ta zube mata kallonta sanda maamah din ke takowa zuwa cikin parlor din.

Kasa motsa bakinta tayi bare ta amsa mata sallamar,sai idanunta da suka zuzzurma saboda kuka data kafeta dasu.

Anni wadda ke zaune saman abun sallah bayan ta idar ce ta daga idanunta tana amsa sallamar.

A mamakance anni take duban maamah dake takowa parlor din,ci gaba da dubanta anni takeyi haka kawai tana jin wani yanayi daban yana shigarta game da maamahn.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX




146



Murmushi ta saki tana sake takowa da wani irin qarfi da conference,laushin da take gani iya idanuwansu da fuskokinsu wani nishadi yake bata.

"Barkanku da wannan lokaci" Maamah ta fadi tana yiwa kanta da kanta wajen zama gami da harde qafafunta guri guda.

Idanu anni ta sake binta dashi,tana so tace mata ta tashi ta fita idan ba alkhairi tazo dashi ba,tana so tace mata ta fita salin alin bata buqatar dogon magana,tanaso ta gaya mata ta nesanta fuskarta daga garesu muddin ba zaman lafiya ya shigo da ita ba......saidai kuma shi wanda bai sonka,ba'a ko yaushe ba,ba kuma a kowanne lokaci bane kake bashi daman da zai fahimci wani yanayi da kake ciki na matsatsi ko tashin hankali ba.

"Mun yini lafiya ameenatu?,ya taro kuma ya tashi?" Maamah tayi maganar data bawa anni mamaki sosai.

"Lafiya alhmdlh" Anni ta furta tana tsareta da idanu. Wannan sauyawar yanayin daga Mariya baiyi mata ba,wannan sanyin da nuna kirkin gaisuwar bai gamsheta ba sam sam.

"To ai haka akeso,yayi kyau....Allah ya maimaita.....nace ba fada me ya kawo gaba ameena?,ina cewa duk tsiya dai nice mahaifiyar musaddiq,har abada kuma tuwo sunansa tuwo,babu me canza masa suna......ace an tashi bikin d'ana na ciki na amma bani da masaniya?,haba ameena,son kan naki ai yayi yawa,ko a 'yan Allah ya sanya alkhairi ai nazo ko?". Idanu anni ta dauke tana maidawa wani guri. Ko daya bata tsinci wani abu me ma'ana a cikin zantukan maamah ba,hasalima ciwon kai kawai zasu qara mata ba wani abu ba.

"Yanzunma bata baci ba.....baki kuma makara ba" Annin kawai tace da maamah.

Wani murmushi maamah ta saki tana dan doka hannunta saman kujera,a nutse sabreen ta sake kai dubanta wajen tana aje wata qatuwar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login