Showing 279001 words to 282000 words out of 363280 words

Chapter 94 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1379

KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ce=??,na muku tallan turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loser=??=??,confirmed=?L?
"Saboda kai ne muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka tsoma a bahon turare.

"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa kanta tsakanin dukiyar fulaninta.

"Name?" Ta tambaya tana murmushi.

"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar.

Tafukan hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin daga ina ta fito?.

"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni.

Idanunshi cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.

"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage hannuwansa sama.

Hannunta ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi.

"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin wani nau'i na rahamarsa"

"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi yana sake jin ta masa kima sosai.

"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa.

"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta.

"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye lafiyarka"

"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.

"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi.

"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma ya shiga uku.

Tsaf ya janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to tabbas yana da ladan koyi dashi.

Cikin wasu sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga wata qasar,suka sauka qasa tare.

Bayan kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya qayyumu).

Ganin ta langabe masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta.

"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace

"Muffin.......nawa name?"

"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana kama hannunta.

"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza.

"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.

Kyawawan akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki.

Wasu irin sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya ware a ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a sama.

"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai ya tura sauran boxes din

"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.

Tana shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.

"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a. Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci gaba da aikinsa.


&Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah maisharif babaghana .

Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne.

"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata

"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.

"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.

Wannan karon qaramar dariya ta saki.

"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.

"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"

"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.

"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da riba biyu.

_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_

_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_>?y?


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX


139


*_WEDDING VIBES_*

*_KANO & MAIDUGURI_*

Idan aka ambaci umar farouq kibiya,wani mutum ne me wasu irin halaye nagartattu,iya mu'amala da mutane da kuma Tarin abokai,duk da kusan kowanne aboki da zai shigo rayuwarsa yana qoqarin tantance cancantar wanzuwarka a rayuwarsa.

Bikin ya karade kafofin sadarwa masu yawa,ya kuma shiga jerin sahun bukunkunan da kowa yayi amanna zai bada wani irin salo me qayatarwa,duk da ba wani abu me yawa aka tsara za'ayi ba.

Tun lahadi ya yiwa maiduguri tsinke ta jirgin jadda wings,yayin da ya saukewa fuad saboda yanayin hannunsa. Su ahsan da sauran abokansu sune suka zame masa groomsmen.

Duka komai dasa hannun fuad aka kammalashi da wani irin dattako da nuna tsantsar 'yan uwantaka,sunyi fuad din zai taho ranar zaman ajo sai kuma da farouq ya sanya ya masa alqawarin zaije har gurin,saboda yasan halinsa,tun asali dama shi bameson ire iren wadannan abubuwan bane.

&A nutse suke takowa zuwa farfajiyan da motocin da zasu masa rakiya zuwa airport daga can su zarce Maiduguri. Hannunsa sarqafe cikin nata,kwana biyu din da zaiyi sai yake jin kamar wanda zaiyi shekara biyu ne. Ita kanta duk sai takejin kamar ta sake masa kuka,kewarsa takeji tun bai tafi ya barta ba,duk da takan ji dama dama idan ta tuna in ya tafin itama zata wuce gidan anni don shirye shiryen biki,wanda idan an dauko fannah an kawota nan din,walima za'ayi gagaruma guda daya da anni ta shirya,zasuyi yini randa za'a sauka da fannah,walimar kuma washegari ce,to amma ita din a yanzun ta zama kamar auntyn amaren gaba daya da angwayen. Tuna su huda na tare da itan yana rage mata wani kadaicin,duk kuwa da cewa ba wanda ya isa ya cike wannan gurbin nasa.

Baiko kulaa ko damu da mutane a wajen ba,ya ajiye mata tattausan kiss a goshinta bayan duka sallamar da akayi a ciki.

"Saina dawo?,ki kulamin da kanki sosai,if possible ki dawo gida ki kwana,banaso na tuna cewa baki dakinki kinji please" Kai kawai ta iya gyada masa,don idan tace zatayi magana kuka ne zai qwace mata.

Har ya fara takawa zuwa motar da Jordan ya bude masa ta jawo yatunsa,ya dawo da baya yana kallonta da narkakkun idanunsa.

"Yadai?.....ko na fasa ne?" Kai ta maqale sannan ta girgizashi.

"BB ne fa......idan banda BB dinne ba wanda zan bawa aronka....."

"Nima banda ina kishin a kallemin ke.....banda ina tattalin 'ya'yana ba abinda zai sanya na tafi na barki"

"To amma...." Ta fada tana turo baki ba tare data qarasa magana ba. Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana kallonta,ya mata alama daka akan ta fada.

"Banason ka kalli kowacce mace please...." Tayi maganan tana juya masa baya alamun kunyarsa takeji. Qaramar dariya ya qwace masa,yasa hannu.ya juyo da ita yana fadin.

"Say it mana.....Louder please!,with all your might" Ya furta yana mata sassauqar runguma ta baya,yadda ta nuna kishin na faranta masa kaman farincikin na neman masa yawa.

Kai tsaye ta juyo ganin abun na masa dadi,ta saka idonta cikin nasan tana dubansa.

"Your eyes belong to me,don't look at any other women please,na maka alqawari a karan kaina.....my gaze is fixed on you alone,bana ganin kowai sai jadda na" Ta fada tana rungume Hannayensa". Sulalewa yayi sai gashi saman gwiwarsa a gabanta,abinda ya sanyata zaro ido ta fara kallon mutanen dake wajen.

Dukka guards nashi sun juya bayansu,ba wani guda daya da yake kallonsu,saima kaman katanga da sukayi musu ta yadda ba wani a farfajiyan gidan da zai ganin ainihin abinda ke faruwa.

"Karki damu,My men are extremely competent" Yana kaiwa nan ya kamo yatsuntsa masu kyau da taushi. Kafin yace komai wayarsa ta dauki tsuwwa,yadan yamutsa fuska yana cirota a aljihunsa. CP ahmad nuhu ne,don haka ya daga kai tsaye ya sanya a kunnensa.

Cikin ban girma suka gaisa,kafin ya soma gabatar masa da bayanai.

"Sir dukkaninsu a yanzu sunyi taushin da kowanne bayanai muke buqatar tatsa daga wajensu zamu sameshi in sha Allah,don yanzu haka bibo da zuwaira ma mun samu dukkanin bayanan da muke da buqata,ban sani ba ko zamu iya aike maka ta email?"

"Good job sir.....thank you,basai ka turo ba,don yanzu haka mun fara hidimar bikin dan uwana.....but zuwa Monday dukka zamu zauna dasu,akwai yiwuwar wanda za'a sallama a cikinsu.....thank you sir"

"Okay sir.....in sha Allah" Cp din ya fada suna sallama cikin farinciki da mutuntawar yadda dukiyar FU'AD din bata sanya yana musu kallon na qasa dashi ba. Ya basu dukkan wani girmamawa da dama na gudanar da ayyukansu.

Kashe wayar yayi duka ya sanya a aljihu don kada wani ya katse masa shauqinsa,sannna ya sake riqo tausasan tafin hannunta da har yanzu yake jiyo wannan sassanyan qamshin na jiya (incense by kabo daughter+234 803 211 9803 Da gaske turarenta kwana yake a jiki,kama gida kuma da wuri yake,khumrorinta dukka na dabanne bare akai ga turarenta).


"Ni muhammad FU'AD jadda,an halicci ruhi Zuciyata dama gangar jikina gaba daya saboda ameenatu sabreen........har abada gangar jikina da zuciyata sun haramta ga wata diya mace ba ita ba......mata gaba dayansu wallahi wallahi kallon maza nake musu 'yan uwana,daga kanki an gama haifar wata diya mace har abada,amana daya ce......kuma kin sameta,bana canza magana,bana sauya alqawari" . Tasha jin ana cewa maza basu da magana daya.....ta gani da idanunta yadda maza suke zama wasu ababen tsoro game da mata,amma a yanzun saita samu kanta da amanna da maganganunsa.

Tana tsaye har dukka motocinsu suka bar harabar gidan,sai ta juya ta koma a hankali tana jin kaman ita kadai ce ta rage a duniya. Bata dauki lokaci ba itama sai kawai ta shirya,ta yiwa securities din daya bar mata magana suka shirya motoci ta fice zuwa gidan anni.

Ta samu amare sunata wani glowing kaman wadanda anni ta dauka ta jefa cikin engine aka sauyo mata da wasu,duk da dama daga amna har huda kyan fata garesu.

"Aah,mrs saddiq and musaddiq" Sabreen ta fada cikin salon tsokana. Abun mamaki wai yau ita suke kunya,kowacce sai ta sadda kai,saidai kuma yanayin amna data gani kaman ba yadda ta saba ganinta ba.

Duk da akwai surukuta sosai tsakaninta da anni,amma ta dan sake wasu abubuwan da ba zasu zamto zaqewa ba ta shiga anyi da ita. Lefen data gani wajen anni akwati ashirin da hudu na huda ashirin da hudu na amna,guda biyu arba'in da takwas kenan. Daki daban anni ta saka ta shiga tana nuna mata wasu designers akwatunan guda sha biyu samfurin shekara mai zuwa,wanda akayi lunching nasu a dubai cikin satinnan. Ita tsoro ne ma ya kamata da anni take gaya mata wai nata ne,ya ilahi ina zatakai wadannan?,kada ya jawo mata baki fa na jama'a.

A daren suna video call take jeranta masa kalaman godiya,kalaman da suka sake kashe masa jiki da zuciyarsa,yaji kaman zai narke saman sofa din da yake kwance akai.

"Sabrrrr" Ya kirayeta,wanda kiran kawai ya gaya mata yanayin da yake ciki.

"Anya ba gobe zan taho ba?,anya duniyata?". Dariya ta qyalqyale masa dashi tana tsokanarsa.

"So kake BB da fannah suce nice na hanaka?,kayi haquri please,awa arba'in da takwas ne kawai".

"Allah ka bani juriya" Ya fada yan lumshe ido,yana jin wata kewarta tako ina,tattausan skin dinta me qamshi laushi da santsi.

&Randa FU'AD ya sauka ranar fanna tayi bridal dinta,baije ba farouq ma bai matsa ba tunda yasan bame son


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login