Showing 318001 words to 321000 words out of 363280 words

Chapter 107 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1413

jinjina,kuma tun daga wannan lokacin bata sake bari ya mata gyara akan duk yadda yakeso ta kasance ba.

Bata tashi bude idanunta ba sai a gaban wani gida,wani irin qawataccen gida daya fusgi hankalinta tun a waje. Ya bude mata motar ta fito,suka zagayo a tare,sai yayi tsaye gaban gidan yana zura hannunsa a aljihun rigarsa ya fiddo key.

"Wannan gidan na siyeshi ne da sunan yarana......mallakinsu ne halak malak cikin wannan garin na madeena,ya Allah ka shaida" Yayi maganar yana damqa maqullin a hannun sabreen.

"Bude mana" Ya furta yana sakin murmushi. Sanda take budewa dukka hannunta rawa yake,idan tace bata taba ji ko ganin matar data samu tsananin soyayyar miji ba irinta batayi qarya ba.

"Kawo nan raguwa ce ke wani lokacin" Ya fada yana tsokanarta sanda ya bude gidan.

Da bismillah da kuma sallama suka sanya qafafunsu. Tun a parlor na farko tasan sun shigo aljannar duniya ne kawai,wani irin gida me cike da tsari da nutsuwa ta daban.

Tiryan tiryan yake nuna mata kowanne sashe na gidan har zuwa sanda sukazo kan daya cikin bedrooms biyar da gidan yake dasu.

Murmushi ya sakar mata yana mata nuni data bude dakin,ta maida masa sannan a hankali ta saka hannu ta murda handle din ta tura.

"Wow......ya subhanallah" Ta fadi tana ware idanunta da kyau. Wani irin lafiyayyen dakin yara ne dake dauke da wasu irin designers gadaje masu dan karen kyau. Komai na dakin an shiryashi da wani irin hikima da tsari me tafiyar da hankali. Komai na dakin guda ukune tabbacin ana welcoming yara uku kenan. Curtain rug da duk wani furniture na dakin abun kallo ne.

Bango zuwa bango na dakin dauke yake da frames masu rubutattun ayoyin qur'ani na tsari kala kala,sunayen annabi da sunayen Allah.

Daga cikin dakin akwai wata qofa,banda tasan cikin gida suke ba abinda zai hana ta kira da dakin baby shop. Komai akwai a ciki,babu ce kawai. Tarkacen kayayyaki Cots,baby bassinet,portable cribs kala kala. Kayan sawa kuwa cikin wasu irin kwalaye na alfarma suke me dauke da wani tambari na musamman da zai tabbatar maka musamman aka yosu. Tun idanunta na iya fahimta har ta daina gane wasu kayan ma,don wasu abubuwan ko sanin mene ne batayi ba ballantana amfaninsu. Idan tace babu ce kawai babu cikin abinda ya shafi tarkacen jarirai sabuwar haihuwa batayi qarya ba,tun daga nan ta sallama,ta yadda lallai 'YA'YAN GATA zasu shigo duniya.

Fuskarta kawai ta rufe da tafukan hannunta kuka yanaso ya qwace mata,komai tana kallonsa ne kamar a mafarki ba a zahirin rayuwa ba,sai ya jawota ya sanyata cikin jikinsa yana bubbuga bayanta.

"Wanne irin so kake musu haka hamma?"

"Beyond imagination sabreen.......ina dreaming gina big family duniyata.......inaso nayita tara yara nayita tara yara,wadanda zasu zamemin sanyin idaniya" Ya furta yana hadiye wani abu. Shuru kawai tayi tana sauraren bugun zuciyarsa,ta wani bangaren kuma zuciyarta ta cika da tarin addu'o'i da fatan samun rayyayun 'ya'ya masu albarka.


& *_LOKACI TAMKAR TAKOBI YAKE_*



Kamar yadda yayi mata alqawari ya cikashi,kwanaki biyu rak suka sauka a makka ta sauke umrarta a ranar. Tayi matuqar qoqari shi kansa ya yaba,duk da nauyin da cikinta yayi amma tayi addu'o'i sosai tayi ibada a kwana biyu kacal da sukayi. Ranar da suke sanyan rai zasu dawo sai ga uban 'ya'yan BB farouq da amarya fannah.

Dukkaninsu sunyi wani irin kyau shi da fannah din,sunyi bundum abinsu gwanin sha'awa. Yayi mamakin saurin qarasowarsa,don dai kawai ya gaya masa saura kwana biyar ayi CS din sabreen baiyi zaton zai taho da wuri haka ba.

"Dole muzo mu yiwa adda addu'a,sannan so nake a matsayina na uban 'ya'ya na riga kowa daukarsu" Murmushi fu'ad yayi,yana jin wannan qaunar har cikin jininsa,farouq na dabanne a rayuwarsa.

Su suka tsaidasu suma saida suka sauke tasu umarar,sannan suka tattara suka wuce madeena.

A kwanakin sosai sabreen taji dadin zuwan fannah,ta qarfafa mata gwiwa sosai ta kuma bata shawarwari a matsayinta na wadda bangaren ta karanta. Akwai fargaba kadan da takeji,amma tana dannewa saboda fu'ad din. Dukka tunaninsa da hankalinsa yana kanta,burinsa na duniya gaba daya ya tattara a kanta da abinda yake cikinta. Ta san ko yaya ne sai damuwar ta tabashi,shi yasa taketa qoqarin nuna komai normal ne.

Ranar da zasu wuce asibiti da azahar,ko kara fu'ad qin yiwa fannah yayi,ya hanata hada kayan tafiyar,sai list data musu ya zage da kanshi ya hada komai.

"Zo mu tafi daki abunmu.....muje na baki labari me dadi" Farouq ya fada yana janye fannarshi.

"A dawo lafiya......Allah ya bada lada" Fu'ad yabi farouq dashi ba tare daya kalleshi ba,don idan kaga yadda yayi maganar zaka dauka badashi yake ba.

Qaramar dariya sabreen tayi,kominsu yana burgeta,tsakanin farouq da fu'ad ba wanda ya isa ya shiga,idan ka shiga ma zaka fice da qafafunka don kunya zasu baka.

Ba'a wuce awa daya ba ya dawo ya janye dude dinshi,can ta hangosu suna qus qus kafin ya juya ya fice. Idanunta ta lumshe,tana jin wani sanyi qasan ranta,koda ta mutu wajen aikin,fu'ad yabi bayanta,tayi imani da Allah muddin farouq yana raye yaransu ba zasu tashi a maraici ba,yaransu ba zasu wulaqanta ba,yaransu ba zasu fuskanci kalar rayuwar da ita da abbensu sukayi a duniya ba.

Sallamarsu anni kawai sukaji,anni huda da saddiq. Mamaki ya kama sabreen har ta gaza daurewa,ta taka a hankali ta isa ga anni,sai annin ta rungumeta tana mata sannu,lamarin da ya sanya sabreen din sakin kukan da batasan meye dalili ba.

158




Hannu anni ta dora saman bayannata tana shafawa a hankali gami da fadin

"Ya isa haka mana.....kukan na mene ummmm sabreen?,habba addarsu.......bakya gani duka qannen naki suna kallonki?" Annin ta fada cikin murmushi. Kunya kadan ta kama sabreen,saita boye fuskarta saman kafadar annin tana murmushi.

Qarfe takwas na dare suka shirya suka wuce asibitin bisa jagorancin tuqin BB farouq,wanda a yau yake jin kansa kamar yafi kowanne mutum farinciki a duniya. Shi yake driving din fu'ad yana gefansa,a haka suka qarasa asibitin.

An shirya mata lafiyayyen daki kafin isowarsu wanda aka zuba komai da zai sakasu su jisu comfortable sosai.

Sosai qwalla ta cika idanunta sanda ta bude qofar dakin,wanda aka tsarashi da gadajen jarirai har guda uku,gadajen da taji zuciyarta na bugawa,yaran zasu hau?,ko gawarsu ce zata hau?,zata bude ido ta gansu su duka ukun akai?,ko kuma za'a rasa wani ko ita a rasata?,dukka wannan Allah shi ya barwa kansa sani.

Sukam gaba daya tsarin dakin ya burgesu,sunbar anni a gida saboda yanayin tafiya da zaman jirgi,don haka har huda da fannah suka samu sakewa abinsu. Huda kam kaman taso tafi kowa gaza boye farincikinta,idan triplet sukazo zanyi kaza......ni zanyi kaza.....ni zanyi kaza,har tana dariyar sai ta riga haneefa da nadra daukansu.

"Idan kika kira kika tsokanesu fa zan iya daukanki mu koma salin alin.....musamman kika saka mana haneefa auta kuka" Saddiq ya fada qasa qasa yana jifanta da wani irin kallo da kana gani kasan na shauqin soyayya ne.

Kukan shagwaba ta saki masa,Allah yasa fu'ad a lokacin ya fita magana da likita. Kunya ta kama sabreen,sai dauke kai tayi tana ajiye kayan kunyarta,sai yanzu ta fahimci haka sukeyi ashe suma?,kuma ko yanxun ba fasawa akayi ba. Fu'ad din baya gane kowa baya jin maganan kowa bare ya fahimta a sanda suke tare da ita.

Tana jinsu ta gama,ya lallashi abarsa,koda ta dawo kusa da sabreen harara ta balla mata.

"Ke bakijin kunya ne?,wannan tabarar da kikeyi ko haneefa sai haka". Dariya sosai ta ballewa hudan,tadan matsa baya kadan.

"Adda.....bamayin komai fa a kanku keda hamma......adda kinsan kuwa yadda kuke komawa keda hamma?.....wallahi idanunku ma narkewa suke su juye idan kuns tare,har wani laushi jikinku yakeyi baki taba lura ba?" Daquwa sabreen ta watsawa huda da sauri.

"Qaniyarki huda.....kakarki ce ni?"

"Barta ta fadi fa......sister gaskiya ta fada,Allah na tuba waye yayi yaku?,har yanzu gani nake BB bai kamoku ba,in kuna wani abun sai inga tabbas mu dukka 'yan koyo ne" Cewar fannah tana dariya bayan ta gama duba bayanan asibitin da yadda zasu gudanar mata da aikin. Kai kawai sabreen ta girgiza,bata iya ce musu komai ba don bata da abun cewar. A fakaice take bin huda da kallo,ranta fari tas tana godewa Allah,tana tuna shekarun baya......tana tuna nasir,wanda tabbas inda yakai ga cimma gaci qila yanzun huda ba'a wannan matsayin take ba. Yadda ta mori miji haka tayi imani huda ta mora,ta lura da yadda hudan ke qara mulmulewa abinta,jikinta kuma ya bata juna biyu ne,fadi ne kawai basuyi ba saboda kunya,uwa uba kuma sai Allah yayi mata baiwar juna biyu maras laulayi sam sam sam,kawai dai ya sakata mugun cin da ya sanya taketa qiba. Amna ce tayi fama da laulayi,yanxunma dai daya girma sai a hankali,abinka da auta shagwaba ga quruciya,duk da shekarunsu kusan daya da huda amma rainon ma ba daya bane,amna bata saba da wahala ba,huda kuwa ta daku da wuya iya wuya,qilan ma shi yasa yazo mata ba'a wani kayan wahala ba,duk da cewa asali halitta halitta ne.

Aikam zancansu dutse,don sanda fu'ad yake shigowa dakin duka kasa zama suyi,kowa yaja matarsa,daga qarshe ma sallama sukayi musu akan gobe zasu dako sammako don ayi aikin a gabansu.

A hanya suke gulmarsa,fannah tace.

"Kasan Allah mine......nasha gulman dude dinka,nakance wadda ta aureshi zata wahala,miskilancinsa yayi yawa,duk yadda kuke dashi sau daya ya taba rakoka zance,koda yaxo ma sai naga magana wahala take masa,nace wannan ina za'ayi walwala a gidansa?,ashe expert ne......Shahrukhan ne" Dariya sukayi gaba dayansu. Huda ta karba itama.

"To ai har yanzu adda fannah....." Harara fanna ta aika mata.

"Nifa ba fulbe bace.....ki daina kirana da addan nin.....bayinmu fulani ke amfani dashi" Dariya ta sake sosai.

"Adda kin riga fa kin shigo cikinmu,kema kin zama bafulatana daga yau......" Jujjuya kai fannah tayi alamun ya zata iya?,anfi qarfinta.

"Ko yanzun ba boss yake,yanzu fitowarmu daya shigo yana taku yana shan qamshi in ke baquwa ce ba zakice haka yake ba.....amma yana isa gurin matarsa ya koma wani mutum na daban" Huda tace tana dariya abinta. Da irin wannan hirar ta qawatacciyar soyyarsu suka qarasa gida.


*WELCOME TO THE WORLD*

*_The jadda's triplet_*
*_a bundle of joy_*
*_three little miracles_*


Idanunta tsakiyar nashi,ta kasa banbance tsakanin ita dashi waye yafi wani fargaba,waye yafi wani tsoro?,waye yafi wani shiga yanayi na zaquwa da kuma shauqin ganin yaran da har a sannan basusan wanne jinsi bane?.

Cikin tsararren dakin aiwatar da tiyatar,kwance saman gadon wanda likitoci ke kewaye da ita. Aikinsu suke daga qasanta,sun saki koren labule daga saman cikin nata zuwa kanta bata tare dasu......amma muhamma fu'ad jadda.....rauninta kuma qarfinta yana tare da ita.

Yana zaune daga saman kan nata saman kujerar da tsahonta yakai daidai kanta,sanye yake da wasu kayan green color shima da irin hular dake kawunan likitocin. Hannunsa cikin nata hannun,ya sarqafe yatsunsu guri guda,idanun kowannensu cikin na dan uwansu.

Qur'ani yake karanta mata qasa qasa,cikin wani irin daddadan sauti daya sanya hatta da likitocin sauraronsa babu shiri,idan kaji sunyi magana ya kama ne. Sosai takejin wani nutsuwa yana saukar mata,idanunta kan labbansa dake motsawa cikin gwanancewa da qwarewa cikin karatun qur'ani me girma.

Daidai sanda yakai kan ayar qarshe ta cikin suratu yaseen

"Innama amruhu iza arada shai'an an yaqula lahu kun fayakun,fasubhanallazi bayadihi malakuti kulli shai'in wa'ilaihi turja'un". Sound din kukan baby na farko shine ya biyo bayan saukar nashi muryar.

Sake sarqewa idanuwansu sukayi cikin na juna,zukatansu na wani irin bugawa da wani irin madaukakin farinciki.

"Second baby" Muryar likitar ya baqunci kunnensu da kuma wani sabon kukan jaririn.

"Third one" Suka fadi sanda sabreen din ta sauke wani nishi saboda fitar yaron daga cikinta da ya sanya qirjinta fadawa sosai.(wannan wani irin yanayi ne da kowacce uwa da aka taba yiwa CS ta sanshi,wani ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yanayi ne da bakya taba mantashi,ya Allah ka taimaki duk wasu uwaye musulmi,wanda CS ya zame musu abu na ko yaushe yayin haihuwa ya rabbi ka basu da sauqi,ka tsallakar dasu dukka wani hadari da wata wahala dake cikinsa,masu haihuwa da kansu don isar annabin rahama ka basu naquda me sauqi,masu neman haihuwa ya Allah don hasken fuskar manzan Allah ka azurtasu da ita,ka basu masu albarka wanda zasu iya dasu ameen).

(A wannan gabar nima nake barar addu'arku da bakunanku masu albarka=??,Allah ya azurtani da twins ko triplet nima=?O?
A lokacin fu'ad ji yake kaman bazai iya jira su zagayo da yaran su nuna musu su ba,duk da yasan definitely zasuyi hakan. Bai jima da sauke tunanin ba kuwa mutum uku suka daga musu yaran yadda mahaifiyarsu ta haifesu suna tambayar sabreen meye gender dinsu.

"Boys" Ta fada muryar ta na rawa da wani irin narkewar zuciya. Shikam kasa magana fu'ad yayi,sai sake damqe hannunta da yayi cikin nasa,ya maido idonsa cikin nata yana dubanta da wani kasantaccen shauqi.

"Thanks hamma......na gode sosai hamma......inama ummeena tana raye?,ka bata jikoki da jinsin da har ta mutu ake mata gorin bata haifa ba.......ka bani wata kyauta da bazan taba iya mancewa da ita ba". Hannu ya dora saman lips dinta yana fadin.

" Shshshsh.....ki huta my world......ki huta duniyata" Ya aza hannunsa saman kanta yana shafa mata a hankali. Bayaso taci gaba da magana,don ya tabbatar muddin zataci gaba din to tabbas zata karya masa zuciya ne,zuciyarsa a kusa take da sakin kukan farincikin da a yau bayajin yana da nutsuwa idan bai dangana da masallacin ma'aiki ya miqa godiyarsa ba.

Yana iya hangen yaran bayan an gama tsaftacesu an kuma shiryasu cikin kayan jarirai,kowannensu ya cika kayansa,kaman ba jiriri ba,abinda yake bashi mamaki yadda cikin duniyarshi ya dauki manyan yara kaman haka,yana hangensu suns wutsil wutsil,yana jin shauqinsu daga nan inda yake zaune,amma kuma bazai iya sakin hannunta ya barta yaje wajensu ba. Tana ankare da hakan,saita saki tattausan murmushi ta kuma matsa hannunsa,wanda hakan ya jawo da hankalinsa kanta

"Tashi kaje hamma....tashi kaje wajensu" Kai ya girgiza mata yana sakin murmushi,qwalla cike da qwayar idanunsa.

"Bazan iya motsawa daga inda duniyata take ba....until you feel okay"

"Am okay hamma.....am okay" Ta bashi assurance,amma sai ya maqale kafadarshi yaqi tashi.

Cikin minti arba'in gaba daya aka kammala gyarata tsaf ita da yaran,sannan aka tura gadonta zuwa dakin da zata huta.

Tsaiwa nurses din kawai sukayi da yaran suna dariyan ganin drama din da akeyi tsakaninsu BB farouq huda anni saddiq harda fannah ma. Shidai abba Alhaji hamza kibiya da isowarsa kenan asibitin baya yaja ya tsaya yana dariya,don baisan shi kansa ya zaiyi musu ba,kowa so yake shi za'a fara bawa,wannan ya sanya kawai suka zarce wajen Alhaji hamza suka miqa masa daya,sauran biyun wuka sanya masa su kan cinyarsa.

"Shikenan sun raba rigima ko?" Abba ya fada yana dariya gami da zube idanunsa akan yaran.

159


"Ma sha Allah,tabarakarrahman.......alhamdulillah.....alhamdulillah" Abban ya maimaita yana jin wani qaunar yaran sabuwa fil tana taso masa. Har ransa yakejin alfahari da samun yaran,har cikin jininsa yake jinsu tamkar amna ko farouq ne ya haifesu,wani irin rahama yaji kaman ta sauka a family din nasa,samun qananun yara har qwaya uku a lokaci daya,a sanda suke kewan yara qananu din. Baisan wani abu da yakeso yake kuma matuqar alfahari dashi ba irin iyalin nasa......irin family din nasa ba,wani baiwa da kyautar ahali Allah yayi masa,badon yafi kowa wayo ko dabara ba.

Addu'a sosai abban ya dinga musu a sarari a bayyane,su anni suna amsa masa da ameen,duk kuwa da cewa kowa ya qagu abban ya gama ganin yaran ya basu su.

Na hannun nasa da suka ce masa shine babba ya juya,yayi masa kiran sallah a dama,sannan yayi kasa iqama a hagu,bai ambatar masa sunansa ba,don shi din ba mutum bane me yawan kutse ga al'amarin yaran sa ba,muddin basu sabawa al'ada ko addini ba yana barin kowa ya zabi abinda yakeso ne.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login