Showing 354001 words to 357000 words out of 363280 words

Chapter 119 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1374

daga zuciyarta.

Ta samu daman zama da amaren nadra da haneefa har kusan sha daya na dare,don shima sun kebe dasu musaddiq suna tasu tattaunawar,har suka kammala ya dawo ta parlor din.

Daga tsaye yake dubanta da lumsassun idanunsa,hannayensa cikin aljihun rigarsa.

"Madame.....baa kammala bane?".

"Saura kadan hamma" Agogo ya kalla sannan ya sauke dubansa.

"Kubar addan nan ta huta mana.....da safe sai a qarasa" Dariya nadra da haneefa suka saki suna miqewa gami da tattare kayan da take dubawa,haneefa tace

"Hamma babu ruwanmu fa,tun dazu mukace mata xamu qarasa gobe tace yau xaa gama.....saida safe" Ta shilla da dan qaramin gudunta tana bin bayan nadra da tuni ita ta fece.

Ta dawo da idanunta daga kan haneefa tana murmushin wai auta itace yau da aure?,saiji tayi kawai anyi sama da ita.

Wutsil wutsil ta fara yi da santala santalan qafafunta kamar qaramar yarinya.

"Hamma......please mana,kada wani ya ganmu mana?".

"Who cares?" Tunda taji ya fadi haka tasan zai wahala ya sauketa idan ba fita sukayi ba,don haka ta kwantar da kanta saman qirjin da duk duniya yafi mata ko ina dadi da samun cikakkiyar nutsuwa.

&Kwanaki uku kacal da dawowarta aka fara bikinsu nadra din,iya events din data fada din kusan haka aka yisu. Saidai fa tun ranar bridal shower fu'ad din bai sake barinta taje komai ba,saboda wani irin sassanyan kyau da tayi me daukan hankali cikin wata butter color gown ita da iffa da tayi order dinta tun daga Egypt,tana yawo kuma da tag din bride sister daya sake bata ranshi. Lallaba kayanta kawai takeyi,tasan halinsa sarai a kanta baida sauqi,ta samu ta saukeshi ta kuma kiyaye dukka dokokinsa har aka gama bikin lafiya. Saidai ko bayan bikin still mitar bridal shower day din ya dinga mata,saida ta samu ta bashi wani zazzafan dare guda daya sannan ta wanke kanta.


*_GRADUATION DAY_*
*@KING ABDUL'AZEE INTERNATIONAL SCHOOL*


Triplet din 'yan qasa nigeria kuma haifaffun qasar madeenatul munawwara......wasu irin yara ne da sunansu dasu kansu sukayi fice cikin makaranta dama wajenta. Bawai don kawai farinjinin 'yan uku ba.....aah hatta da kaifin basira da Allah ya zuba musu,matsanancin nutsuwa da sanin ya kamata.....inda daga qarshe kuma suka zama dalibai madiya hazaqa da qoqari cikin daliban da makarantar ta fitar.

Sanda makarantar ta tasosu ta tsaidasu saman stage tana wassafa kyawun dabi'u da hazaqar yaran sai sabreen ta kasa daurewa,ta kifa fuskarta tsakanin tafukan hannayenta tana jin wani irin alfahari da yaran da kuma qaunarsu tana ratsata.......wani irin farinciki da batasan yadda zata misaltashi ba na kyauta da baiwar yaran da Allah yayi mata,wanda a yanzun haka cikin amsa kuwwa ake sanar da kowa cewa su din cikakkun 'yan qasa ne.....gwamantin saudiyya kuma sun dauki nauyin komai da komai nasu saboda girmamawa da jin dadin yadda suka zauna da kowa cikin makarantar dama qasar lafiya.

Da qyar ta iya isa tsakiyar yaran nata don karba musu kyaututtukan karramawa da suka samu,duk da jikinta a lullube yake kirif,baka ganin komai nata sai zagayayyar fuskarta,amma duk da haka wasu sun cika da mamakin cewa itace mamansu. Tun tana iya amsa har gifts din sukafi qarfinta saida jadda dake sanye cikin wata rantsatsiyar shadda ya tako da sanyin nan nasa da nutsuwarsa ya tallafeta da wasu kayayyakin.

Ranar wata rana ce da bazata gushe ba a zukatansu,cike da tarihin da bazai kankaru ba cikin rayuwarsu.

Already sun tsara ana kammala taron zasu koma makka su sauke umra gaba dayansu,saboda nuna godiyarsu ga Allah da kuma sake roqon ubangiji ingantacciyar rayuwa me dorewa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


*_NACE BA......._*>??????
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*=??=??

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*=?G? wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
____________________________
*_PLEASE FOLLOW MY TIKTOK PAGE_*=?G? https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1
__________________________



175



A maimakon jirgi a babbar lafiyayyar mota suka taho zuwa makka. Wata irin tafiya ce ta iyali me dadin gaske,hirrraki da labarai duka sun cika motar dake dauke da JADDA FAMILY.

Saidai duk da hakan daga can seat din baya ita da fu'ad ne zaune,tadan dora kanta saman kafadarsa tana jin kasala da wani saqe saqe da cikinta yayi mata wanda batasan Meye dalili ba.

A fili kuwa hotunan graduation din take kalla daya bayan daya. Duk inda zata wuce fu'ad da yaran sai tayi zooming ta kallesu sosai,tana jin kaman ba yaranta ba,kaman wani imagination ne a cikin duniyar mafarki ma,har sai da fa'ad daketa sauraron shirmen yaran daga gaban motar yana murmushi kadan kadan ya ankara da ita.

"Kina mamaki ne?" Kai ta daga ta kalleshi sannan ta maida saman kafadarsa.

"Ina mamaki mana hamma......yau sabreen da kowa ke mata kallon KARUWA da yara irin wannan?,sabreen din da kowa ya gaza janta a jiki yaji meye damuwarta,meye kuma uzurinta yau ita keda yarannan?......sabreen din da tafi kowacce yarinya nutsuwa da hankali saboda ita din rainon ummee ce yau ta zama haka meye sila?,ba hujja ba dalili sai yanke hukunci babu bincike". Bata tsaya jin ta bakinsa ba ta dora.

"Alhaji ahmad me citta shine asalin sunan mahaifina,wanda ya shahara da sana'ar saida citta kanunfari da sauran kayan da suka danganci wannan da wasunsu ma daga qasar larabawa ake shigo musu dasu. Abbana ya auri ummeena ne a sanda yake da matan aure biyu da yara mata goma sha biyar,ummena ce ta uku,mace me tsananin haquri da kawaicin daya sanyata taci nasarar zama da sauran matan abbana,wanda cikin su take da babbar abokiyr adawa wato bibo,wadda ita ummee ke bi. Abban mu ya tsaya sosai a kanmu,shanmu cinmu tarbiyya da iliminmu,don har yanzu tasirin dagewarsa ce a jikina na ilimin dana samu daga private school daya sakamu me tsada,tun daga matakin free nursery har secondry,duk da cewa ina js 3 abbanmu ya koma ga Allah,ummenmu itace ta jajirce naci gaba da wannan makarantar har na shiga ss3 second semester,a lokacinne Allah yayi mata rasuwa,a lokacinne asirinmu ya tonu,maraici kuma ya afko.mana gadan gadan,ummenmu ba 'yar qasar nan bace,don haka bamu da kowa a kusa damu da zai tallafemu. Sh momma sunso tafiya damu amma kawu ya saka kuka,wai ya za'a tafi da zuri'ar ahmadu yana raye?,shi yayi alqawarin kula damu kaman yadda abbanmu ya kula da rayuwarsa. Abbanmu ne ya riqeshi bayan rasuwar iyayensu tun auren abban ma na fari,bai kuma qyale kawu ba sai daya aurar dashi ya hadashi da jari yana saka ran wasu halayensa da bayaso zuwa sannan kawun ya dainasu. Da wannan yaqinin suka barmu hannunsa,ashe kuma lokaci lokaci suna masa aike da sunanmu,amma ko labari bai taba bamu ba bare muga abinda suka kawo.

....... Tom ko bayan mutuwar abba kowacce mace ita ta koma hidimar kanta da kanta,to yanzun da bamu da uwa sai ya zamana ba wanda ya damu damu,ba wanda yake dubamu,ba wanda yake damuwa da munci bamu ci ba,munsha ko bamu sha ba,mun tashi lafiya?,waye baida lafiyar?,dukka ba wanda ya saka hakan a tsarinsa. Da farko na dauka abun na wasa ne,na dauka zasuji qanmu,saina fara nema mana abinci daga dakunansu kafin na fahimci ba wanda zai iya cida mu,don da zagi nake fita a dakin da qyama da tsangwama,daga bisani dole na koma roqarwa su huda a maqota,donni ban damu naci ba,muddin sukaci shikenan tawa me sauqi ce,zan iya kwana uku ma banci komai ba,saidai nasha baqin ruwa na kwanta. Sannu a hankali suma maqotan suka fara hanani,sai ya zamana mun qarasa galabaicewa,ciwon yunwa yanason kama huda da haneefa da bata gama sanin ma me ake ba idan yunwar taji ba. Ba wanka ba wanki don ba wanda zai bamu sabulu,saidai da yake ummenmu ta saba mana da tsafta hakanan mukeyi da zallar ruwa.

Maqociyarmu kuma qawa ga bibo ita ta fara bani shawara.

"Kina da kyau sosai sabreen,kaf gidanku ba yaro me kyanki.....me zai hana ki tallata hajar jikinki?,wallahi abinci ma saikun bawa wani" A ranar hankalina yayi mugun tashi,mukayi uwaka ubaka da ita,kaf kimarta ta zube a ido na,ita kuma ta kamani tamin shegen duka akan na mata sata kuma na mata rashin kunya. Ba wanda ya damu yaji ba'asi saboda basa sonmu bamu da gata,saima tayata da bibo tayi,haka nayi kwana uku kwance ina zazzabi ba magani a dole na warke. Sanda naga yunwa na neman rayuwarmu saina fara da tambayar alhaji baqo,aboki na kusa ga mahaifinmu wanda nake kyautata zaton zai iya taimaka mana" Shuru tayi tana hadiyar wani abu me ciwo.


"Saidai abun mamaki abinda kuma ko yau na tuna yakemin ciwo,ya nemi yaci amanar amintaka,ya nemi na bashi mutuncina yaci gaba da ciyar damu duka. A nan ne naci masa mutunci saboda mamakin daya bani,kamar yadda mukayi da waccar matar shima duka yayimin ya hadamin da sharri,abu na farko daya fara qeqasarmin da zuciya,na fahimci kaman ba wanda zaiji tausayinmu a unguwar,binda yasa na kasa mantawa ko yafewa,na koma na kunna masa gobara a dakinsa data jaza masa asara me yawa,ya gano nice,yace zai kaini ga 'yan sanda,na gaya masa ina da shaidar cewa muddin ya aikata haka ni kuma nizan babbake gidansa duka da 'ya'yansa da matansa,abinda ya sakashi haqura kenan,tun daga ranar idan na ganshi sai tsaki habaici da tsartar da yawu,sai duka ya tsargi kansa yana tsoro kada na tona masa asiri,sai ya koma kaman sirikina. Daga nan saina fara yawon nema mana abinci,duk da ba cikin kyakkyawar kama nake ba,amma duk wanda ya ganni ringidi ringidi zai jani ya kaini gun cin abinci a zubamin,saina juyewa su huda a leda,sukance ki cinye,indai kin bamu hadin kai lallai abinci saikin ture. Mutun na farko daya fara nunan me hakan yake nufi na samu na gudu ina zaginsa,akayi na biyu na uku na hudu na biyar shida har goma,duk wanda yaga bazai samu abinda yakeso ba saiya qwace abincinsa. Maza da yawa haka muka dinga yi,abinda ya sake dasamin duniya ba imani.....babu me taimako don Allah sai don wani abu na daban,dana fahimci haka saina fara tunanin ta yadda zan amfana da kudadensu ba tare da mutuncina ya tabu ba.

.....salis shine mutum na farko dana fara gwada hakan a kansa,na saka masa maganin bacci a lemo,na kuma debi kudade masu yawa na gudu. Wannan kudin su suka fara canza rayuwata,na siya mana abinci me yawa,suturu da komai na fara kwalliya muka fita daga qazanta.

Da bincike salis yasa aka samoni,aka kamani,kamun da dashi bibo tayi amfani ta fara bugamin tambari da batamin suna,tunda tana baqinciki kwana biyu muna cikin abinci da duk kayan wadata na rayuwa,saita saka idon lallai sai tasan inda na samo,saiga case din salis.

Sanda ake tuhumata na kasa bada amsa,na tsinci dai wata murya tana cewa.

"Ku saketa fa,nine shaida bata da laifi,ya cinye kudinsa ne kawai zai laqabawa wata" Wani matashin dan sanda ne ya fadi haka. Wannan shine jib,silar haduwarmu kenan,mayen computer na gaske da salis da yake kawunsa yaqi taimaka masa da registration a shekarar qarshe da yake ciki saboda rashin kirki,wannan ya sanyashi rasa damar karatunsa,da cuku cuku ya samu aikin dan sanda da qaramin albashin da bai wuce ladan ganin ido ba.

Haduwarmu uku da jib magana ta hadamu. Shima maraya ne,banda wanda nake gayawa damuwata amma ganin kirkinsa da yadda da nayi da nutsuwarsa a ranar mukayi dogon hira dashi.

"Basa taimako Don Allah,ni shaida ne.....amma idan basu taimakemu don Allah ba,zamu diba ta qarfi da yaji" Da taimakonsa muka soma gudanar da plan dinmu,ranar farko na fadi,aka biyo sawunmu,Allah ya hadamu da busari ya daukoni kyauta,wanda tun daga ranar ya zama dan adaidaita sahuna,daga baya bayan uban gidansa ya qwace abun hawansa,na hada dukka kudina na siya masa wata,sanadin haka kwananmu biyu ha abinci,saboda shi dinma marayanne,kuma shike daukan nauyin tsohuwar mamarsa wadda shi kadai Allah ya bata a duniya"

"Sannu a hankai aikinmu ya dinga tafiya daidai,indai zan fita sai nayi nasara,ina yin nasara ina gane cewa maza babu Allahba ransu,wasu mazan sukan daukaki matan bariki su wulaqabta iyalinsu,wasu mazan kuma saidai ki bada jikinki su baki kudi,don haka mukayi tsare tsaren da duk wayonka bani zuwa gurin da kakeso,saidai na sameka a guri public mu qarqareta a nan,na zare kudin ta hanyar taimakon jib dake sarrafa na'uarar,daga ranar kuma ba zaka sake jina ko ganina ba,bazan sake kuma zuwa duk wani guri da muka t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????aba haduwa dakai ba. Nasha samun barazana amma Allah ya kiyeyeni,ban taba yarda ko farcena wani namiji ya tabamin ba duk kuwa iya wayonka,wanda ni nasan hatsari na saka kaina me girma,ba wayona ko dabarata bane kuma ya qwaceni ba,zuciyata akwai Allah ya duba.

Duk namijin da zan hadu dashi ina fara karantarsa,adadin son matanka da fasiqancinka.....adadin barnar da zaka gani a dukiyarka......akwai nutsasun maza daidaiku dakeson aurena da tun tafiyar farko nake zamesu daga gareni saboda basu cancanci na cutar dasu ba,amma kuma bani da wani nufin aure kai ko sha'awa ma baya bani.....mazanma dukkaninsu haushi suke ban,saina sallamesu salin alin duk iya nacinsu kuwa.

Yadda nake shiga me kyau nake fita da yadda duk wata buqata nake sauke mana ita ba tare da anga ina sana'ar komai ba sai bacin suna yahau kaina......yayin da shaidar zur dasu bibo ke qarawa 'yan waje ya sake basu qwarin gwiwar yadda da komai a kaina,ban damu sosai ba sai dana qara hankali,amma damuwata ta dadu qwarai sanda naga suna qoqarin brainwashing ma su hud akan qazafin karuwanci da zina.

Kudi suka fara shigowa har suka fara fin qarfin buqatuna,sai a sannan na lura akwai tarin marayu a unguwanni daban daban,mabuqata marayu da iyayensun harma da marasa qarfi......saina saka marayu guda hamsin nauyin su saman kaina,duk wani abu da zan samu kuma kasonsu yafi nawa yawa,a haka na dinga kula dasu da nawa qannen......har xuwa sanda na hadu da mika'il komai kuma ya faru" Ta qarasa maganar tana sanya gefan mayafinta tana share qwallar data jiqa mata fuska.

"Ki yafemin......ki yafemin sabreen don girman Allah......ku tayani roqar anni ta yafemin" Muryar maamah data sauka musu a baza wadda ta saka sabreen sake sakin kuka.

Ashe dama akwai rana irin wannan da zatazo?. Sautin kukan ya taso anni tana dubawa ko cikin yaranne suke rigima,saidai sanda ta kawo qarshen motar taga sabreen ce saita zauna a wata kujerar tana shirin tambaya,amma yadda maamah ta riqe hannunta gam cikin nata ya tsoratata ya kuma bata mamaki.

"Ameenatu ki yafemin........ki yafemin,iya abinda zan iya cewa daku kenan....kunyimin halaccin da bazan iya biyanku ba amma baqar zuciya da shaidan gaba daya sun sanya idanuna rufewa,kin yafemin don girman zatin Allah ta yadda idan na tashi mutuwa zan mutu cikin salama". Sosai qirjin fu'ad yayi nauyi saidai wani farinciki kebantacce yana dawainiya dashi. Har yanzu ya daina jin sautin kukanta na daren jiya,sanda ta sanyasu a gaba shida musaddiq akan su yafe mata. Wani irin kuka dake dauke da zallar nadama cikin ido murya da kuma lafazinta. Daga shi har musaddiq ba wanda baiyi kuka ba......wani hukuncin Allah da lamari na uwa kuma.......cikin awanni biyu kacal da sukayi zaune da ita tana qoqarin basu labarin komai da hardaddiyar muryar ta,saiga zukatansu dukka sunyi wani irin sawai. Basu bar dakinba saida tayi bacci tsakanin qafafunsa shida musaddiq,wanda ko bayan sun fito a dakin shi da musaddiq din ganin komai suke kaman mafarki,sai suka samu kansu da rungume junansu. Fu'ad ke lallashin musaddiq

"Ba abinda yafi qarfin addu'a......ba wani lamari da yafi qarfin Allah,alhamdulillah da Allah ya qaddara mata shiriya tunda sauran damarta" Wadannan kalaman su suka tsagaita kukan musaddiq.

"Anni ki roqamin hamza ma......na cutar da mutane da yawa ta fuskoki da dama......amma yanzu kune nake gani kune tare dani ku kuka rage.....ku yafemin naji dana sauran mutane.....hajja da laila dukkaninsu babu su bare na nema yafiya a garesu........fareeda ta haukace bata da cikakken hankalin da zamu yafewa juna nida ita".

"Allah ya yafe mana gaba daya" Cewar sabreen qwallar farinciki na fita a idanunta.

"Allah ya tabbatar damu kan hanya madaidaiciya.....Allah ya kyautata qarshemu" Anni ta qara da wannan tana goge Qwallar farinciki da Allah ya qaddarawa maamah shiriya bata mutu da haqquna ba saina wadanda suka rigata gidan gaskiya.

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login