Showing 90001 words to 93000 words out of 363280 words

Chapter 31 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1426

Kai ya jinjina yana motsa system din dake saman cinyarsa

"Na gani......aiki ne me bala'in hatsari da dukkaninmu zamu jefa rayuwarmu cikin hatsari........amma kuma,ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba.......let's try it......idan mukayi winning...." Sai ya saki murmushi yana rufe system din

"Zamu kasance mutane mafi sa'ar zuwa duniya" Ya qarasa maganar yana dukan bayan kujerar dake a gabansa. Iya nasarar da yayi musu hasashe ta saka mashkur qyaqyacewa da dariya

"Inaso naji dandanonta.....inaso naji ya take.....bansan adadin mafarkin da nayi a kanta,ban taba sanya kwadayina akan wata 'ya mace ba tunda na fara sanin 'ya'ya mata....wannan macen ta zullemin bansan ya take ba sai a kanta,dole ta fahimci wannan kuskuren data aikata!" Ya fada da qwarin gwiwa qwarai da gaske,yana jin ya zaqu da komai ya tabbata.

"Bazan iya dogon jira ba Mike.......ka shirya komai tsakanin kwanakin nan biyu" Daga hakan sai kawai ya qarawa motar wuta sosai suna gaggawar ficewa daga layin.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

50


_Daga ibn juhaim bin haris RA(wannan sunan sahabin annabi ne=??),yace:Manzan Allah S A W yace "da me wucewa ta gaban me sallah yasan abinda yake kansa na sabo,tabbas da ya tsaya(ya jira me sallahn ya gama)tsahon gwargwadon shekara arba'in shine yafi masa alkhairi akan ya wuce ta gabansa_

_Bukhari da muslim ne suka rawaito_



50


&Daure da babban towel ta fito daga wanka,qaramin tana tsane doguwar sassalka sumarta dake a jiqe sharkaf da ruwa,alamu dake bada tabbacin wankesa tayi. Idanunta a lullumshe tana jin kalan nauyin da yayi mata saboda kukan da tasha a jiya. Duk da nauyin da zuciyarta tayi mata amma ta wani fannin sai take jinta sawai kamar wani nannauyan dutse dake danne da ita ne ya sauka. Tun daga jiyan data tabbatar ta miqasu hannun da bata haufi akan zasu cutu ko wani abu maras kyau zai samu riskarsu.

Tana daga gaban madubin,kadan kadan tana hangen yadda iska take kada labulayen dakin,wata sassanyar iska me dadi kadan kadan tana ratsowa cikin dakin. Lumshe ido ta sakeyi sanda ta gama gyara gashinta ta matseshi cikin ponytail holder bayan ta lanqwasa jelarsa me tsaho sosai,fuskarta ta fito sosai,sai ta sake lumshe manyan idanunta da suka rusuna sosai. Zuciyarta ciwo takeyi idan ta tuna da tuhumar da yayi mata jiyan,tana jin wani zafi cikin qirjinta duk sanda kalmar

"Wajen wa kika je?" Ta dawo mata a kunnenta

"Me kikayi?" Tana sake sakata jin zuciyarta na matsew a qirjinta.

Vibration din da taji daga gefanta shi ya ware zaren tunanin dake qulluwa cikin kanta. Maida dubanta tayi wajen,wayar huda data karba ce wadda ta sakawa charge tun da asuba,bayan wayar ta cika kuma sai ta kunna kanta da kanta kamar yadda tsarin wayar yake.

Sunan MAAMAH data gani ya isheta bayanin wacece,wani matsiyacin tsaki taja tana janye idanunta daga kan wayar,sannan ta juya tana wucewa closet dinta don neman kayan da zata saka.

Idan ta tuna abinda d'anta da ita sukayi mata,sai taji kanta ya cika da shawarwarin hanyoyin da zata dauki mummunar fansa a kansu kafin ta tattare tabar rayuwarsu. Duk da cewa nashi me sauqi ne,don baiyi yunqurin taba mata kowa nata ba,saidai ya taba mata zuciyarta da munanan kalmomin da koda tayi nesa da rayuwarsa bata jin zata iya mancesu.

Har zuwa yanzu da take wannan tunanin ta rasa wanne kalar abu ya kamata ta yiwa maamah?. Abu daya tayi ittifaqi akai shine......tabbas zata banbance mata tsakanin aya da tsakuwa......zata kuma shayar da ita mafi girman mamaki.

Tabbas inda tana da ra'ayin d'anta......lallai da zata mallakeshi a gaban idanunta ne,mallakar da babu boka babu malam.......mallaka ta ruwan sanyin da sai ta gwammace bata sanyata a shirmen shirinta ba.

Har ta ciro kayan ta dawo ta shirya cikin Palazzo da blouse data kasance cif cif jikinta don bata buqatar kaya masu nauyi kiran bai daina shigowa ba,ta kammala ta feshe jikinta da turare . Scarf ta sanyawa kanta sannan ta taka a hankali tana isa inda wayar take sanda take dab da tsinkewa.

Stool taja ta zauna bayan ta daga kiran ta sakashi a handfree ta kuma ajiye saman mirror table din tana tattara hankalinta akai.

"Dawa nake magana?" Abinda ya fara fita kenan daga bakin maamah da wani yanayi na zaquwa da son jin wayar a hannun wa take?. Idonta ta lumshe sannan ta bude

"Gaggawar ta meye?,kina tunanin wayar huda zata kasance a hannun wani qato ne?,ko a hannun wata sabanin halastacciyar 'yar uwarta data shirya sadaukar da tata rayuwar saboda tasu?". Maganar ta kama zuciyar maamah sosai,ta kuma saukar mata da matsananciyar fargabar data bata tabbacin KOMAI YA QARE saidai a sake sabon zubi da lale.

"Naga alamar hakan......kin kuma yi qoqarin sadaukar da rayuwarki ma 'yan uwanki.....ni shaida ce,amma inaso kisan wani abu guda.......kina wasa da baqin kumurcin maciji ne daya shirya dukka dafinsa da xummar harbi ga duk wanda yabi ta hanyarsa" Wani dan murmushi ta sakarwa maamah din tana murza hannuwanta,har yanzu tana jin bata gama dawowa ainihin sabreen dinta ta asali ba......amma kuma da alama komai yana bisa hanyar saituwa

"Shi wannan macijin.....idan har yayi sake halittar data fishi sanin kogon da yake kwana yake kuma tunqaho dashi.......tabbas akwai yiwuwar a cimmasa har inda yake......a kuma sanyashi ya yanke wannan kan dake dauke da dafin da kansa da kansa ba tare da yasan hakan ta faru ba....."

"Ke dakata qaramar alhaki!" Maamah ta furta bayan dukkan haqurinta ya gaza da yadda yarinyar dake qarqashin igiyar auren d'anta ke iya maida mata magana me zafi haka kanta tsaye......ba shayi ba fargaba,yarinyar da a haife dukka cikin 'ya'yanta ba sa'anta.

"Shshshsh....." Sabreen ta fada tana dora yatsanta akan lips tamkar maamah na zaune a gabanta.

"Meye na saurin fusata haka?.....ina cewa abun baiyi zafi har haka ba?" Ta furta da alamun murmushi cikin muryarta.

"Yaro man kaza......yaro baisan wuta ba sai ya taka..."

"Your royal highness......har yanzu bansan meye dalilin wadannan zafafan kiraye kirayen ba da safennan". Iya maqura a rainin hankali maamah tana jin sabreen tayi mata shi,ta dinga qoqarin tausa kanta da daidaita kanta kada yarinyar ta tunzurata furta abinda batayi niyya ba.

"Yaro yaro ne.......sabreena......kina da masaniyar cewa nice na tsugunna na haifi fuad?" Dan murmusawa tayi kadan sannan tace

"Haka naji labari!"

"Amma kina da yaqinin ni na daukoki ko kawoki cikin gidan na maidaki sunan matarsa?.......idan naso qasa da awa biyu rak! Zaki rasa wannan damar?" . Qaramar dariya ta saki ma maamah din,ta gyara zamanta sosai tana kallon kanta a madubi. A yau hirar nishadi take bata a maimakon razani da take samu a kwanakin baya da suka shude.

"Kina zaton kina da wani makami da zaki iya fiddani daga gidan yaron naki?........kiyi haquri da abinda zance......amma ko shaidan a yanzu bai isa ya fiddani daga gidan yaron naki da kike tutiya ba........bana son danki ko kadan bazan kuma taba sonshi ba......amma yadda kika sakoni cikin rayuwarku......kika maidani matarsa da qarfin qwanji dana kudi.......to haka fitata daga gidansa da rayuwarku zata kasande bisa zabin kaina a kuma duk sanda nayi niyya......so kibi a hankali,bawai sonshi nake ba.....infact ma baiyimin ba.......amma bazan fita daga rayuwarku ba har sai sanda nayi niyya"

"Qarya kike....baki isa ba!"

"Dama bance na isa ba......amma zan gwada saiki tayani tabbatarwa...."

"Kina kirawa kanki ruwa!,zaki iya rasa rayuwarki ta dalilin haka fa!"

"Bari na fara raba naki d'an da rayuwarsa tukunna ki fara ganin kalar wannan baqin cikin kafin ki aiwatar a kaina......zan shayar dashi ruwan guba a ruwan shayinsa na yanzu a maimakon tsubbace tsubbacenki....." Tana kaiwa nan ta kashe kiran tana ma kashe wayar gaba daya.

Murmushi ta dinga yiwa kanta a madubi,hirar ta sanya mata nishadi sosai,ko ba komai ta dasa mata tsoro da fargici tabbas na mintunan data ambata.

Da gasken haka shine ya faru. Wani irin gumi ya fara tsatstsafowa maamah da wani irin kalar tashin hankali. Zuwa yanzu bata da tabbas akan yarinyar.......tana ji a jikinta zata iya aikata komai da tace din. Kasa zama tayi,jikinta yana rawa ta soma lalubar layin fu'ad tanason gargadarsa akan ya kaucewa komai da zai fito a yanzu daga hannun yarinyar.

Kira kusan goma tayi masa a jere saidai ba wanda ya daga,abinda ya sake tsananta tashin hankalinta kenan,ta dinga duban agogo tana qirga mitunan da yarinyar ta kwasa mata.

Daidai lokacin ma shi ya jima a office. Ayyukane da yawa a gabansa da suka hade masa saboda jiya bai samu yin komai ba a office din yayi baqi da suka tsaidashi har zuwa dare.

Daga jiyan zuwa yau komai zaiyi yana yinsa ne cikin wani irin fushi da zafin ran da hatta saddiq ya fahimci akwai abinda ke damunsa,kuma tabbas ranshi a bace yake.


Ture file din gabansa yayi yana jan wani mugun tsaki. A duk sanda ya tuna ko abun ya fado masa a rai sai yaji wani mugun bacin rai yana lullubeshi. Tashi yayi daga kan ainihin kujerarsa yana takawa a nutse,yasa hannunsa yana sassauta tie din dake wuyansa cikin wani irin yanayi da yakejin kamar numfashin da yake shaqa yana masa kadan.

"Why i cares so much?" Ya motsa labbansa yana furtawa da wani irin zafi. Ba kasafai yake sanya kulawarsa ko damuwarsa akan komai ba sai abinda yake da muhimmanci a rayuwarsa. Ya tabbatar a karan kansa she's nothing to him amma me yasa abun yake masa zafi

"Igiyar aurena" Abinda yake da tabbacin shine dalilin tsaiwar abun a ransa. Sai daya sassauta tie din hade da belt din suspenders din jikinsa,sannan ya jsa ga dispenser dinsa ya tsiyayi ruwan sanyi ya rage sanyinsa ta hanyar zuba ruwan zafi kadan akai,sannan ya koma saman recliner chair din dake gefe wadda aka ajeta don gajeran hutu irin wannan ya zauna akai.

Kadan ya samu sassauci sanda yasha ruwan,ya dire cup din idanunsa suna sauka kan wayarsa dake haske. Da farko ya share yana tsammanin fareeda ce data zama kaman wata mahaukaciya. Kusan kullum cikin canza layin da zata kirashi dashi gudun kada yaqi dauka. Layinsa nada wani tsari na hana baqin numbers shigo masa amma nata kiran ya tsallake wannan shingen bai kuma san dalili ba. Sabanin mamakinsa sai yaga maamah.

Baya iya qin daga wayarta komai runtsi,duk da daga ita har anni zai wahala su kirashi a irin wannan lokacin,sai ya jawo wayar ya daga yana sanyata a kunnensa.

"Kana ina?" Abinda ta fara tambaya kenan tana qoqarin daidaita muryarta

"Ina office.....wani abu ya faru?" Ya tambayeta a mamakance

"Daga yau wannan yarinyar......." Sai kuma ta dakata saboda wani qaqqarfan gargadi da aka watso mata daga can qasan zuciyarta. Dan jim tayi shima sai yaci gaba da sauraronta baice komai ba

"Shikenan,ka kula dai da kyau" Ta yanke tunaninsu su duka biyun da fadin haka.

Wani haushi ya cikata bayan ta aje wayar,ita yarinyar zatayi wa wasa da tunani irin wannan?,tabbas idan har ta bari yarinyar ta qara kwanaki uku a gidanma.......bata amsa sunan mariya ba.

*_to masu karatu......me maamah zatayi da zai saka auren sabreen qarewa cikin kwanaki uku?.....wanne qwarin gwiwa ko tabbaci sabreen ke dashi wanda yasa taci alwashi ko shaidan bai isa ya kashe mata aure ba?.....muje zuwa jama'a,WANNAN ALQALAMIN NA HUGUMA ZAZZAFA NE_*



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

51


_Daga sumrah dan jundub RA,yace manzon Allah S A W ya kasance yana nemawa mumunai maza da mata gafara a kowacce juma'a_

_harda ni dake da kikazo a wannan zamanin kin shiga ciki,LALLAI HASARA DA TABEWA TA TABBATA GA DUK RUHIN DA BAISON ANNABI,ALLAH KA DAUKI RUYUKANMU RUHINMU YANA CIKE DA MATSANANCIN SONSA S A W_




Sai data fara lalubar number da take da muradin yin magana da ita sannan zuciyarta taci gaba da kwabar data fara mata.

"Da kinason gayawa fu'ad me?,ya saki yarinyar?,kada ya amince da ita?,kada yaci abun hannunta?,bayan ke kika aura masa ita?,ke kika bashi tabbaci akan ingancinta da kuma cancantar aurensa da ita?,bayan ko sati biyu ba'ayi ba ke dindai ke kika kafa masa sharadin ya bata kulawarsa?,ya sota?,ya jata a jikinsa?,kinason dabawa kanki wuqa?,kinason sanya wani zargin saman zargin dake kansa naki?".


Wannan tunanin ya sakata sakin ajiyar zuciyar tana kiran number da tazo kai,a gefe guda tana mamakin abinda ya hana hajja nemanta ko zuwa gurinta ko tuntubarta akan matsalar da ta shaida mata jiya,TABBACIN DUKKAMIN MAGANGANUN LAILA BA QARYA KO SHAKKA AKAI KENAN. Sai taja qwafa tana gyada kai

"Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha" Ta furta a bayyane,daidai sanda taji an murda qofar dakin an shigo laila ta bayyana.


Da kallo tabi lailan har zuwa sanda ta qaraso gabanta. Ta durqusa saman gwiwoyinta wani abu da bata taba yiwa maamah shi ba duk da matsayinta na qawar mahaifiyarta shekara da shekaru.

"Ina kwana maamah" Ta furta cikin tsantsar ladabi har bata iya hada idanunta da nata.

Kai ta daga ta kalleta,dukka wani bayanin plan nasu da lailan tayi mata jiya sai ya shiga dawo mata kanta tar tamkar a lokacin take labarta mata. Wani bacin rai da radadin da wanda akaci amana keji ya taso mata,sai ta maida kanta ga waya kawai tana tura masa saqo. Sai data tabbatar saqon ya shiga sannan ta kalli laila,wadda kafin lokacin duk wani kalar tashin hankali laila ta shigeshi. Tana jin kamar ta dora hannunta aka ta yita zunduma ihu,iya yadda maamah taqi amsa mata gaisuwa ya sanyata cikin firgicin kodai wani laifi tayi mata?. A yanzu a rayuwa bata jin akwai wani abu da zai daga mata hankali sama da taga fushin maamah.....ko kuma tayi wani abu da zai saba umarninta.

"Lafiya qalau....." Amsa matan kawai da tayi ya sanyata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ba wani abu tayi daya bata mata rai ba.

"Na shiga dakinki naga basu shareba.....na gyara miki,saiki duba idan akwai abinda baiyi ba ki gayan a sake gyara mikin". A nutse take qarewa laila kallo,ji take a ranta inama ace fu'ad ne haka a gabanta yake wannan bayanin bawai laila ba?,inama ace aikinta ya fada daidai?,i yanzu da batasan wanne irin farinciki take ciki ba.....lallai da zata kasance wata halitta mafi farinciki a fadin duniya,ta qarasa wannan tunanin tana runtse idanunta gami da budesu.

"Basai na duba ba,saidai anjima kafin na kwanta ki sake"

"To ba matsala.....waida so nake naje wajen hajja.....jiya muna magana bamu gama ba kika kirani" Kai ta girgiza,duk da tanason sake samun information,don tayi imanin duk abinda zasu tattauna tamkar a gabanta za'a yishi,to amma kuma tana buqatar ta kammala da aikin sabreen tukunna......tabbas komai da zai biyo baya me sauqi ne.

"Ki kirata ki gaya mata nace ba yau ba,zan duba gobe na gani idan ya dace kije goben" Ta fada kanta tsaye tana ci gaba da riqon wayarta cikin jiran tsammanin shigowar kiran hanzari nan da kowanne lokaci.

Sanda laila ke gayawa hajja saqon maamah kai tsaye murmushi ta saki bayan sun gama wayar tana jinjina kai

"Mariya!.....Mariya,zan miki babban karatun da gogewarsa sai a cikin kabarinki,a sanda qasusuwan mowacce halitta ta jikinki ta gauraye da qasa,kin bani qofofi masu yawan gaske ba tare da kin sani ba.....zan shiga ta kowacce qofa......na fita ta kowacce qofa.....na shiga kuma cikin rigarki na dimauta duniyarki......sannan na hana muradinki da mafarkinki su zama gaskiya" Abinda ta fada kenan tana qurawa wayarta idanu dake aje tana ta burarin nemon taimakon a daga kiran daya shigo.

Tun safen har azahar zuwa la'asar da tayi dukka cikin dakon shigowar kiransa take. Sai bayan la'asar din liqis cikin ba zata daya daga cikin masu aikinta suka shaida mata tana da baqo me suna hanzari.

"Ki rakoshi can cikin setting room,kada a barshi a waje" Ta fada cikin doki da zumudi,ta miqe tana daukan dankwalinta ta maida kanta,har ranta tana jin mafita tana tunkaro ta.

Fitowarta ya sanya hanzari sauke qafafunsa da suke dore daya saman daya. Sanye cikin baqar shiga,wandon jeans da shirt dukka baqaqe,sai baqar hular Ascot cap daya jawota tadan rufe fuskarsa kadan.

"Barka da fitowa" Yayi maganar yana miqa mata nannadaddun takardun dake hannunsa,sai ta fasa zama ta sanya hannu ta karba sannan ta zauna dasu ta soma budewa tana cewa

"Aiki dakai akwai jan kudi.....amma kuma akwai hanzari kamar yadda sunanka yake" Ta fadi a nutse tana bin list na sunayen da kallo da kuma hotunan.

Sai data gama qare musu kallo tas sannan ta kaudasu daga fuskarta tana kallonsa

"Kin gansu hajjaju?" Ya rigata fada,sai ta gyada kai ranta yana yin fari.

"Kayi qoqari sosai hanzari.....amma waye kake ganin ya dace mu dauka?" Ta fadi maganar tana sake kallon list din. Matsowa gaba yayi kadan ya miqa mata hannunsa yana cewa

"Kawo nan ki gani" Ba musu ta miqa masa,ya aza takardar saman teburin dake tsakaninsu yana binsu da yatsa daya bayan daya,kafin daga bisani hannunsa ya tsaya daidai fuskar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login