Showing 78001 words to 81000 words out of 363280 words

Chapter 27 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1420

jiki da kuma kaffa kaffa da ita.

"Indai surutun haneefa ne saika gaji dashi......ni kuma magana nakeso nayi dakai,next time idan kazo sai kuyi hirar" Ta fada tana dan hade rai gami da gyara zama.

Sake dubanta yayi a karo na biyu,abubuwa biyu suka hade masa waje guda. Har yanzu dabi'ar nan tata tarashin son yara tana nan?,banbanci qarara me kuma fadin gaske na farko tsakaninta da anni. Indai haka ne yara uku ne cikin gidanma kenan?,akwai daya a cikin daki?. Me ya kaita dauko yara har uku?,ita da basu dameta ba?. Meye abun damuwa don yana hira da yarinya qarama?.

Agogonsa ya kalla,sai ya maida dubansa ga fuskarta.

"Ba damuwa ai,yau muna da enough time sama da kullum". Kafin ya sake cewa wani abu haneefa tace

" Zaka kaini naga adda sabreen?......don Allah hamma kada kace aah" Ta fada tana narke murya. Maganar taja hankalin huda dake saman dining,itama saita ajiye spoon din abincin da takeci ta maido hankalinta kansu.

Gumin dake tsatsatsafowa maamah din ya sake yawaita,da sauri kamar ana tankadata tace

"Aah fa haneefa......ni da kaina mukayi zan kaiku haka ne?".

"Eh amma har yanzu baki kaimu ba maamah,shi kuma hamma ma daga can yake ko?" Ta maida tambayar kansa. Kansa ya gyada a nutse yana karantarta.

"Maamah ki barshi ya kaimu ko anjima ne,in yaso saimu dawo da kanmu" Huda itama ta saka baki,don da gaske sunyi tsananin kewar sabreen din.

Sanda ta waiwaya da nufin yiwa huda din magana sai maganar fu'ad ta dakatar da komai.

"Jeki dauki hularki kuzo muje nasa a ajiyeku" Yayi maganar kansa tsaye,maganar data daki tsakiyar kan maamah da wani irin ba zata.

Har ga Allah kanshi tsaye ya fada kuma hankalinsa kwance,kawai dai a cikin zuciyarsa ya dade da rashin aminta da kowanne motsi na maamah din. Bashi da gamsuwa akan abubuwa da yawa sa suka shafeta,shi yasa a kusan komai idanu da zuciyarsa suna akai.

Cikin qasa da minti uku sai gasu kowacce da mayafinta. Dab da zasu fita daga falon ta kirayi sunan huda da yanayin da tunda hudan tazo gidan bata taba gani cikin muryarta ko sautinta ba. Fuskarta a dinke ba fara'ar nan da suke kwana suke tashi da ganinta akan fuskarsu

"Kada ku wuce ko ina,daga can ko dawo gida,zanwa driver magana zai biyo bayanku,karku wuce awa daya......." Idanu huda tadan zuba mata,sai kuma kawai ta gyada kai mamakin sauyawar maman tana kamata. Tasha musu alqawarin fa zata kaisu.......sai kuma daga baya tace ai wani uzuri ne ya taso sai bayan wani lokaci,duk da ta lura akwai permanent driver a gidan da yake zaune baya aikin komai.

Yana zaune daga cikin motar saidai qafafunsa suna a waje ba'akai ga rufe masa murfin ba suka fito. Yadan daga kai ya kallesu,dukkaninsu suna kama da ita saidai qaramar ta fisu daukan kamanni sosai da ita. Mamaki kadan yana dan kamashi na ganin banbanci muraran tsakaninsu. Dukkansu da alama suna da sauqin hali da kuma tarbiyya sosai,don ba wanda ya gaidashi a tsaye a cikinsu saida suka rusuna

"Ta fita zakka kenan" Ya gayawa kansa da kansa yana sauko qafafunsa qasa ya fito waje.

"Abdulgaffar" Ya kirayi shugaban tawagar tsaron nasa,ya matso da gaggawa yana rusunawa

"A cire mota daya a sakasu a kaisu gida" Ya bada umarni hankalinsa yana kan kiran fareeda dake shigo masa. Kaman yadda baya gajiya da qin dagawa hakanan itama bata gajiya da kiran nasa,yaja wani dogon tsaki yana komawa motar,ranshi yana tsananin baci da kalar wannan kiran nata da dukkanin numbers dinsa,kamar wadda batasan abinda ya dace ba,baisan ma ya akayi take da dukka numbers din nasa ba.

"Soulmate" Sunan da tayi kiransa dashi kenan da wani irin salo na kashe murya da jan ra'ayi.

"Why?.....ke bakya gajiya da kira ne?,it's so annoying.....please don't do it again.....stop it" Ya fada da sautin bacin rai a muryarsa.

"Haba ka fahimceni mana" Ta sake fada da hanzari cikin tsoron kada ya katse mata wayar..... Kada ya ajiye wayar bayan ta samu dama ya daga wayar bayan dukka wahalar da tasha

"Na fahimci me?....ke bakya ganewa cewa macace ke?,ke ya kamata abi bawai kibi ba?.....kina mantawa mace da kamun kai aka Santa?.....". Da sauri take girgiza kai

"Indai a kanka ne bani da wadannan qualities din....."

"Okay....then karki sake kirana....." Yaja qaramin tsaki yana yanke kiran hadi da jan dogon tsaki yana wurga wayar gefe.

Gaba daya soyayya tana sake tona masa kanta a matsayin wani abu da yafi komai zama matsala da takura a rayuwa,shi yasa bazai bari ta kunno rayuwarshi yanzu ba har sai sanda ya shirya ya kuma kebe mata lokaci nayin nata.

Idanunshi akan motar BMW din da aka sanyasu a ciki,sai da yaga fitarsu a gidan sannan yayi musu umarni suka tashi motocin suna fita suma daga layin.

Sauke labulen window din da yake bata daman ganin farfajiyar gidan tayi cikin wata irin matsananciyar fargaba da kuma tashin hankali. Gaba daya kowacce idea tata ta kunce,ta rasa wanne zaren tunani zata kamo?.

Wacce irin baqar rana ce yau?,wanne tsautsayi ne qaddara ya sanyata lokacin shigowarsa ya kubce mata har ta saki yaran haka?. Idanunta ta mayar saman agogo......sai a sannan ta lura,yau ya sabawa lokacin shigowar tasa ne,ya shigo da wuri ba kaman yadda ya saba ba,sai tasa hannu tana sharbe gumin fuskarta da tafin hannunta.

Da dan hanzari ta taka da kanta tana fita farfajiyar gidan tana qwalawa mansir kira,kiran daya sanyashi sakin duk abinda yakeyi ya qaraso babu shiri.

"Ka fito da mota,kabi bayan motar jadda diamond zuwa gidan muhammadu......akwai yara da sukaje gaida matar gidan,suna shiga minti goma kacal ka aika su taso ka dawomin dasu......mansir?,idan ka kuskura aka samu akasi baka maidominsu akan kari ba to ka kuka da kanka......ban yarda ku biya ko ina ba......ban kuma yarda ka ajesu ako ina ba" Ta fada tana zare idanu tanaji a jikinta tamkar wani abu zai faru.

"In sha Allahu ba zaa samu ko daya daga ciki ba" Daga haka saita juya tana komawa ciki.

Kasa zama tayi ko a cikinma,a jikinta takejin kamar akwai wani abu da ba daidai ba

"Ki kira zuwaira kisa ta kula miki da motsinsu" Wani sashe na zuciyarta ya bata shawara.

Bibbiyu ta dinga hada stairs din tana haurawa samanta,cikin lokaci qanqani ta isa dakinta,ta zauna gefan gado tana daukan wayarta dake saman drawer ta fara kiran zuwairan.

Saidai kash!,kiran farko aka shaida mata kwata kwata wayar a kashe take,ta sake gwadawa cikin rashin gamsuwa da bayanin farko na na'urar......still sukace mata yana a kashe,ta sake dai gwadawa a karo na uku,nan dinma amsar dukka daya ce,saita ajiye wayar a gefanta tana jan wani matsiyacin tsaki

44

_Daga hassan dan sumra R A yace,daga manzan Allah S A W yace:Duk macen da waliyyai biyu suka aurar da ita ga maza mabanbanta a lokaci guda,to ita din mallakin na farkon ce(wanda aka fara daura mata aure dashi)_



"Tur da halinki zuwaira,Allah wadai da halinki" Ta fada tana cika tana batsewa,har cikin ranta tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta tafi gidan da kanta. To amma kuma idan tayi duba ga wasu abubuwa,hakan bame yiwuwa bane,dole taci gaba da zama tana gwada kiran akai akai,yayi da idanunta ya ta'allaqa akan agogo tana qidanye da mintunan fitarsu daga gidan.

Daga qarshe ta sare kan samun xuwaira,to amma dole tana da buqatar kiran wani da zame zame mata garkuwa a can gidan

"Laila" Zuciyarta ta tunasar da ita.

"Yauwa" Ta fada da madaukakin zumudi,ta soma lalubar number wayar lailan.

Duk da safiya ce amma ta kusan awa guda da rabi a gidan nasu. Cikin asalin dakin da yake shine mallakinta,saman gadon sun qule ita da mahaifiyarta hajja harira wadda ta tsareta da idanu bayan ta gama zayyane mata karonsu da fu'ad na qarshe.

Sai da tayi kaman ba zata daina kallon nata ba kafin taja wani tsaki tana dauke dubanta daga kanta.

"To wai meye ma amfanin zamanki a gidan laila?,kada ki zama albasa mana wadda batayi halin ruwa ba?,na kaiki gidan badon kin rasa wajen zama ci sha ko sutura ko kuma gata cikin naku gidan ba.....na kaiki ne saboda ki karanci komai.....ki haddace komai ki kuma bi kowanne taku da motsi na kowa a gidan kafin mu fara gabatar da namu shirin koda kuwa.mariya batayi nasara ba......nasarar mariya ko faduwarta ba damuwata bane.....hasalima inda zata fadi hakan shine daidai a tare dani......kinsan me?" Kai laila ta girgiza tana jin faduwar gaba da kiran sunan maamah da akayi.

"Nasarata itace ya kamata ta fara samuwa......nasarata ita ya kamata ta fara wanzuwa kafin ta mariya........ni ya kamata na fara samun fu'ad na mallaka miki shi......muddin mariya ta rigamu samun fu'ad to ba shakka dukkan wata nasara da muka sanya rai a kanta zata iya zuwa mana da tsauraran hanyoyi da matakai......shan kai nake da buqata mu yiwa mariya laila.....donme kikaje kika kwanta kina bacci?,waye ya gaya miki nasara na zuwa ta sameka har inda kaka?,bakisan fita ake a nemota ba?!" Tayi maganar da alamun qunan rai a cikin muryarta,hatta kuma da lailan ta karanci haka,saidai batasan me yasa a kwanakin nan takejin sam bata da damuwa akan wannan lissafin na hajja ba......tamkar wannan lissafin an zare mata shi kwata kwata daga zuciyarta.

"Ban sauka ba hajja......kawai dai saina dinga jin kamar idan mukayi hakan bamu kyautawa maamah ba,kamar idan mukabi komai a sannu zaifi....." . Baki kawai hajja harira ta sake tana kallon laila da wani mamaki daya taru a fuskarta,kuma koda ta zubawa lailan idanu saita karanci da gaske take maganar. Tana shirin yin magana aka turo qofar aka shigo.

Madeena ce dauke da serving tray data jero dukka kayan dadin da aka dafawa hajjan a matsayin abincin safe. Tun asuba take tsaye don kawai ta faranta mata,kuma bata da tabbacin zata yaba ko kuma tayi accepting abincin gaba daya.

"Gasu hajja an gama....." Ta fada tana rusunawa ba tare data iya hada ido da ita ba. Wani abu me nauyi da girma ya riga ya sauka a zuciyarta game da zancan laila,don haka bacin ran daya taso mata maimakon ta huceshi akan laila sai ta fara ragewa akan madeena

"Wannan wanne irin iskancin banza ne?,ina ciki muna sirri da yarinya saiki wani bankowa mutane daki?". Murya a karye cike da ladabi tace

"Kiyi haquri,kin manta ke kikace idan na gama na kawo miki a daki zakici"

"Naji da Allah.....koma dashi ki aje saman table......tsnnnnn" Ta qarasa da tsaki.

"Awnnn..... Me dame kika dafa mata ne?" Laila tayi tambayar tana maida dubanta ga madeena wadda je tiri tirin fita da tray din. Ido kawai hajja ta zubawa laila tana mamakin yadda take nuna halin ko in kula da magana me muhimmanci irin wannan. Dawowa madeena tayi ta durqusa ta bude mata dukka bowls da warmers din,sai lailan ta karyar da wuya.

"Wallahi meat pie nake mugun kwadayin ci da safen nan.......don Allah hadamin yaji naman rago cikin sosai" Ta fada kanta tsaye da sigar umarni.

"Tom" Madeena ta amsawa lailan wadda a qalla tayi qanwa ta hudu da ita,ta miqe ta kwanukan tana sauka.

"Idan da a rayuwa tsaiwa ake duba abinda ya kamata......inda a rayuwa jira ake sannan ayi abinda ya dace........tabbas ke kanki da baki juya matan yayunki kamar haka ba" Hajja tayi zancan tana tsare laila da ido tare da qoqarin maida mata girman zancan cikin zuciyarta.

Dan muskutawa laila tayi tadan kashingida,har yanzu a ranta ita batajin damuwar komai,duk da kuwa bayan kowacce daqiqa sai hoton kyakkyawar fuskar nan tasa ta gilma ta gaban idonta,abinda ke sakata sakin ajiyar zuciya lokaci lokaci gami da sakin qaramin murmushi.

"Inaso komai sauya.....inason ki canza akalarki daga yau.......dole gobe ki dawo ki karbi naki kayan aikin......ki kula da zuwaira......banason tasan komai.....bana son kuma ta fuskanci komai" Ta fada tana tsareta da ido. Saidai bata kai ga amsawa ba wayarta dake saman kanta ta dauki tsuwwa. Tana daga kwancen ta daga kanta tana duban me kiran,saidai ganin sunanta kadai ya sanyata wani irin zabura hadi da tashi zaune.

Hakan kuma baiyi mata ba sai data zamo daga saman gadon ta durqusa a qasa sanda take daga kiran hade da sallama. Dukka wadannan abubuwan da tayi su suka ja hankalin hajjan sosai taji tanaso taji da wanne mutum me matuqar girma da daraja haka a rayuwarta take waya?.

"Ina kwana maamah.....kin tashi lafiya?,kiyi haquri inata zuci zucin na kiraki na gaidaki da safen nan.....amma na kasa tuna waye zan kira". Maganar ta yiwa maamah banbarakwai,to amma bata wani kawo komai a ranta ba,duk da laila bata taba mata magana da ladabi rusunawa da kuma kirki irin haka ba

"Ba komai,kina gida ne zan baki wani aiki?". Rawa jikinta ya hauyi saita miqe tana daukan mayafinta

"Bana gida maamah.....amma bani minti goma sha biyar yanzu zan isa gidan,saiki gayamin abinda kikeso ayi miki ko mene". Mamaki kadan ya sake kamata,to amma a yanzu garkuwa kawai take nema don haka ta amsa mata da

"Okay......idan kika isa ki kirani"

"Ko kibar wayarma kawai on hold karki kashe yanzu yanzu zan isa,zanyi sauri ma saboda agama komai da wuri". Wani mamakin dai still ya kamata,amma sai tace

" Zan sake kiranki"

"To" Ta amsa mata tana sauke wayar. Jakarta ta kaiwa sura,kamar ma ta manta da hajja dake wajen,kowanne sashe na jikinta rawa yakeyi,ta jefa wayar a jaka ta rataya tana yafa mayafinta. Sai a sannan hajja da mamaki ya kasheta ta kira sunanta da qarfi

"Waike da waye kike waya haka lokaci guda hankalinki ya tashi?". Murmushi ta sakarwa hajjan sanda take saka takalminta

"Maamah ce fa?,ta tambayeni ne ina gida?,wani aiki zata sakani kinga ya kamata na koma ai.....bai kamata ma ace na fita ban tambayeta ba,amma zan bata haquri daga baya.....hajja na tafi,idan na gama mata da wuri zan tambayeta,idan ta barni gobe na dawo zan dawo".

Mamaki da ganin almarar abun ya hanata cewa komai,ta sanqame a wajen kawai baki bude tana bin laila da kallo wadda keta sambada sauri kamar zataci da baka.

*_turqashi?,wai meke faruwa?,nace meke faruwa ne jama'a?,shin qaiqayi ne koma kan masheqiya ko kuwa yaya?,wanda lamarin nan ya yiwa dadi ya danna 1=??,wanda baiji dadi ba ya danna 2_*

*_gasu huda a hanyar zuwa gidan addansu,yaya zata kasance kenan?_*

*_yanzu wasan zai fara tafiya daidai=ت?
*_muje zuwa=?L?
45


_Daga nana Aisha R.A tace:manzon Allah S A W yace:Duk matar da tayi aure ba tare da izinin waliyyinta ba,to aurenta batacce ne,idan mijin ya tare da ita taci sadakinta saboda halastar farjinta a gareshi_



Ware idanunta tayi sanda ta isa dining area,sai ta tsaya cak tana sake ware idanunta da kyau tamkar wadda bata gani sosai,kwanyarta na gayawa zuciyarta kawai yaudarar kanta takeyi,basu huda dinta bane.....ba nadra a wajen......auta haneefa tana hannun waccar azzalumar

"Adda.." Muryoyinsu suka zame mata kamar tsani a gareta na tashi daga wani dogon mafarki,kamar wadda aka daki bayanta,sai ta fara nufarsu tanason ta tabasu don ta tabbatar shin su dinne?.

Allah ne kadai ya sauko da ita daga steps din,don qafafunta hardewa kawai sukeyi har zuwa sanda ta isa garesu. Haneefa da tafi kusa da ita ta jawo,ta miqa hannu tana shafar fuskarta,sai kuma taja hannun huda ta riqe d kyau,sannan ta dafa kafadar nadra.

Murmushi suka fara yi mata,da alama sun gane abinda take nufi,kuma dariya sukeso suyi mata,saidai yanzun ba Lokacin dariya bane.

"Ku tsaya a nan ina zuwa" Shine abinda ta fada kenan tana juyawa ciki cikin gudu gudu sauri sauri. Ko ina a jikinta rawa yakeyi,batasan ya akayi suka kubuto ba,tana ji a jikinta addu'ar data tsananta a wannan Lokacin Allah ya karba mata.

Birkice closet dinta tayi wajen neman hijab daya tamkar idanunta basa gani,da qyar idanunta suka nuna mata wani ruwan sararin samaniya,ta sanya hannu ta fuzgoshi ta saka,sannan ta dawo falon.

"Ku taso......ku taso mj tafi" Ta fada da wani irin hanzarin daya sanyasu tsaiwa kawai suka zuba mata idanu,har sai data fusgi hannun nadra da haneefa sannan huda ta biyo bayanta a mamakance.

Tana riqe da hannuwansun take ratsa farfajiyar gidan,girmanta yasa take ganin kamar ba zasu fita daga ciki ba maamah zata riskesu,kamar tayi nisa da yawa. Security da sauran ma'aikata nata zubewa suna gaidata,amma ita ba wannan bane a gabanta,don ko gane gaisuwar nata basa yi.

Kai tsaye kuma a karon farko security suka bude mata gate ta fice. Taci gaba da jan hannunsu da wani irin sauri da kaf rayuwarta bata tana yin tafiya da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login