Showing 243001 words to 246000 words out of 363280 words

Chapter 82 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1439

Kai matar ta girgiza,ta juya da gaggawa tana nufar qofa,saidai tuni ma'u ta rigata isa qofar ta danneta ta kulle ta zare key din.

Raba dubanta take kan fuskar anni tana zaro ido waje,hankalinta ya soma tashi tana tunanin girman hadarin da zata shiga muddin ta bari taje hannu.

"Kiban hanya na fita ko kuma na illataku!" Ta fada da wata gurbatacciyar hausa da zata baka tabbacin wani yaren ce daban ba cikakkiyar bahaushiya ba.

Daga annin har matar ba wanda ya zaci haka,saukar kakkauran plastic plate din da sukaci abinc dashi dazu ma'u ta sauke mata a tsakiyar kai,sai gata ta zube qasa warwas zubewar data sanya wayar sabreen silalowa daga aljihunta.

A hankali sabreen data sauko daga gadon ta dauki wayar tana juyata,iya daukar wayar kawai ta bata kowacce irin amsa da take buqata koda matar batace komai ba.

Matsawa anni tayi da hanzari tana kiran security emergency line cikin qasa da minti daya sai gasu sun bayyana a dakin.

Kiran security din ya tayar da kusan duk wani security alert na asibitin,kasancewar dakin babban daki ne,yana cikin VIP rooms da asibitin yake dasu.

Cikin qanqanin lokaci qofar dakin ya cika da security da wadanda ihun security alert din ya tashesu. Kusan kowa yasan wacece a dakin a cikinsu,suna da masaniyar mahaifiyar wace a dakin,don haka fitar security alert daga dakin ya zamana kaman tashin hankali a wajen kowa.

Sanda chief of security service na asibitin ya shigo dakin yana neman ba'asin abinda ya faru ya girgiza. Cikin matuqar tsoro da kuma kaduwa ya shiga bawa anni haquri.

"Am sorry maaa.....muna dukkan iyawarmu wajen bawa madam tsaro,bamusan ya haka ta faru ba.....amma ni da kaina banyi minti talatin da shiga office ba bayan ba gama zagaye na tabbatar kowa yana kan aikinsa,hatta shige da fice na asibitin nan tun bayan faruwan abun muka sake saka ido akai....amma zamu duba in sha Allah,zamu kuma binciketa har sai mun tabbatar daga ina take?,meye kuma ya shigo da ita dakin......muna masu bada haquri". Kai kawai anni ke jinjinawa tana duban matar wadda tuni ta jiqe da fitsari,ainihin mummunar suffarta dukka ta fito saboda yadda tayi wurjanjan da kuka da tsananin tashin hankali. Haquri kawai take bayarwa hannuwanta a sama kaman me addu'a. A haka suka jata suka fice da ita,sabreen ta koma gefan gadonta ta zauna kawai rungume da hannayenta kanta yana cakudewa.

Dr mubeena ta qaraso inda allurar da robar suka fadi ta sanya hand gloves ta daukesu,har yanxu ita kanta a tsorace take jikinta kuma rawa yake. Mamaki ne yake qara kasheta na yadda akayi amfani da kamanninta da komai nata aka shigo dakin za'a cutar da iyalin jadda.

"Zanje dashi lab mu gwada muga meye ma taso zuba mata cikin drip din". Dr mubeena ta fada tana duban securities din guda biyu da suka rage a dakin. Juyawa tayi ta kalli anni da sabreen.

"Ku kwantar da hankalinku,babu abinda zai faru in sha Allah,zasu dan xauna kadan daku kafin daga waje kafin security dinku na gida su iso....don anyi alerting nasu abinda yake faruwa".

"Sannu Dr" Kawai anni ta iya fadi Dr mubeena ta juya ta fice da sauri Dr kamal da yake on duty yabi bayanta abun shima yana girgizashi. Case ne da makamancinsa bai taba faruwa cikin asibitin ba,sai gashi yau yana shirin faruwa akan matar mutum mafi girma da kima cikin idanunsu banda Allah ya kiyaye.

Ajiyar zuciya me nauyi sabreen ta sauke tana dora hannunta saman cikinta a hankali. Wat qqqarfar soyayyar abinda take dauke dashi ya ratsa mata zuciya irin wadda bata taba ji ba,wato tako ta ina farautar rayuwarsu akeyi?,so ake a salwantar dasu gaba daya?,kowa rayuwarsu ta tsone masa idanu ta kowacce fuska?.

"Nayi alqawarin baku kulawa da dukkanin qarfina da kuma iyawata.....nayi alqawarin kula daku har zuwa sanda zaku taka doron qasa......da ran mahaifinku ko babu.....da kulawarsa ko babu......zamu zame masa madubi kuma ababen alfahari in sha Allah" Tayi maganar ita daya tana sakejin kaman wata sabuwar alaqa na qulluwa tsakaninta da abinda ke cikinta da batasan meyeshi ba.

Batasan hawaye takeyi ba saida muryar anni ta ratsata.

"Ki rage damuwa da gaske sabreen ko don diyoyin cikin ki.....karki cutar dasu....Allah shike riqe da kowanne bawa yake bashi kariya....musamman idan ka sallama masa ka kuma miqa masa al'amarinka". Tayi maganar a tausashe tana goge mata damshin fuskarta.

Ba wanda ya iy komawa bacci,abinda ya sanyata yanke shawarar yin alwala,ta daura alwalar ma'u ta shimfida mata abun sallah. Ta jima tana kaiwa Allah kokenta wanda tayi Imani shine sarki guda daya da baya maida hannun bawansa ba tare da ya amsa addu'arsa ba. Sanda ta idar tana zaune kanta a qasa,tana jin tattaunawar guards din fuad daga parlor din dakin. Kusan kowannensu zuciyarsa a kusa take,muryar abdulgafar ce ta qarshe.

"Daga yau koda wasa ba wanda zai sake gigin zuwa kusa da inda take ma......daga gobe zuwa jibi ko da numfashinmu da jinin jikinmu zai qare sai mun lalubo duk inda oga yake,a cikin qasar nan ko africa ko a wacce nahiya ta duniya ma".

Numfashi ta sauke a hankali,ta jawo wayarta tana lalubo number musaddiq. Dole ta fara taba mata nutsuwa kaman yadda tayi musu,dole ta taba kwanciyar hankalinta ko yaya ne,saboda itama tasan kifi na ganinka me jar koma.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

123


Cikin qasa da awa daya ta gama turawa saddiq komai da komai da take buqata,sannan ta sauka tana lalubo rubutaccen qur'ani dake kan wayarta.

Ko yaya ne tanaso ta karanta ko zata samu sassaucin zugi da radadin da zuciyarta take mata,don ta dade da fahimtar babu wani abu dake bawa jiki da zuciya nutsuwa irin karatun alqur'anin.


&Zuwa sanda gari ya qarasa haske abba ya iso,already su musaddiq dama tun cikin daren suka qaraso,saidai da safen musaddiq yadan fita sannan ya dawo.

Dr mubeena ta shigo da sakamakon gwajin,a sannan sabreen din tana zaune ana gyara mata cannula dinta data goce. Idanunta a runtse tana jin radadin yadda ake luguiguta qarfen allurar cikin Jikinta.

"Guba tayi attempting zuba mata.....wadda take bin jiki a hankali ta lalata kowanne organ na jikin dan adam......alhmdlh da ubangiji bai bata nasara ba......inda hakan ya faru to fa da saidai addu'a kawai....poison ne da bashi da magani a nan qasar ko makari kwata kwata". Kai kawai sabreen ke gyadawa tana sake girmama rashin imani da rashin tausayi irin na wanda ya dauki nauyin abun. Zuciyarta tayi wani mugun karyewa fu'ad jadda yana fado mata. Allah ne kadai yasan a wanne yanayi yake a yanzu?,a wanne irin hali yake?.

Da sassarfa take saukowa daga saman nata kaman zata hada matakala bibbiyu. Duk sanda taga kiransa tasan tabbas lamari ya baci,ba kasafai take sanyashi ayyuka ba.....ba kuma kowanne lokaci bane take bashi aiki na sai aikin daya kasance babba.

Yana tsaye tsakiyar falon,hannunsa goye a bayansa yayin da idanunsa ke lullube da baqin gilashi.

"Me ya faru?,ya ake ciki?". Baqin hannunsa ya saka yana cire glass din nasa,bakinsa da yake baqiqqirin ya motsa.

"Aiki ya baci,kuma komai na iya faruwa saboda ta fado hannu a sanda kowa yake abun zargi ne". Hannuwa bibbiyu ta sanya yana dafe qirjinta dake wani irin buga mata,duka idanunta a warwaje tana jin tashin hankali yana zagayata.

Wannan shine aiki na qarshe da take sanya ran samun nasara a kanshi,aiki na qarshe da take da kyakkyawan fata da hasashen indai ya tafi daidai ta gama da matsala daya cikin matsalolin rayuwarta guda uku,aikin data kwana jiya batayi bacci ba tana jiran jin kyakkyawan sakamako a kansa.

"Waye ka bawa aikin?,ina fatan sunana bazai fito ba?" Ta tambayeshi zufa tana yanko mata tana jin kan an mata wanka da ruwan zafi. Kai ya girgiza yana dubanta.

"Ko sunan wanda na bawa aikin bazai fita ba bare sunanki bare nawa,don da kika bada aikin na bawa wani shima ya bawa wani shima wancan wani ya bawa sannan aka bawa yarinyar......nasan yarinyar amma ban bata aiki kai tsaye ba saboda gudun qwacewar rana irin wannan......amma.abinda yafi bani mamaki,itadin expert ce,bata taba missing target ba tunda ta fara aiwatar da irin wadannan ayyukan sai yau ta silarki" Yayi maganar abun yana tsananin bashi mamaki na yadda ta fadi warwas a qaramin aiki irin wannan.

Ajiyar zuciya ta sauke,ita komai ba damuwarta bane......kama yarinyar ko tsallakewarta,nata damuwar shine samun tabbacin nata kubutar da kuma tsiran.

Kujera ta samu ta zauna tana juya tambayarsa. Me yasa rashin nasarar yarinyar da faduwarta bai tashi afka mata ba sai da aiki yazo kansu?. Tambayar data kasa samun amsarta kenan,saidai kawai ta sakawa ranta akwai wani boyayyen abu na daban da sabreen din ke amfani dashi.

"Labari na gaba" Ya fada yana fiddo jaridar dake hannunsa. Kamfanin jaridar yafi kowanne kamfani fidda adadin jaridu siyar dasu da cinikinsu,saboda yafi kowanne gidan jarida fidda labarai latest masu daukan hankali,labarai na gaske da suke daukan hankali tsakanin kwanaki da makonni.

Hannu ta saka ta karba tana dan mita,saboda a yanzun ba abinda tafi buqata irin ya barta ta zauna tayi nazarin hasarar data sake fada mata. Kudade masu ciwo ta biya don wanzuwar aikin,sai data siyar da bangles dinta na gold sannan ta biyashi kudin aikin.

Wareta tayi tana mita a ranta,saidai bata samu sukunin sauke mitar ba tafkeken hoton farko daya mamaye jaridar ya dauki hankalinta.

Hoto ne da alamu suke nuna daga cikin video aka ciroshi,fuskar hajja sosai ya fita,yayin da ita dake gefen hajjan kwata kwata fuskarta bata fita ba bata kuma nuna ba.

Bata sani ba.......ta gurin bugun jaridar aka samu akasi tayi damage?ko kuma ana sane aka lalata gurin?.

Kayan dake jikinta a jikin hoton tabi da kallo,sune dai......sune dai wadannan kayan data sanyasu a ranar da zasuje gidansu sabreen zuwa na farko......gabanta yayi wani mahaukacin faduwa sanda wani abu ya darsu a ranta.

"Na shiga uku?!,me zan gani wannan?" Ta tambayi kanta da kanta hannuwanta suka dauki rawa,da wani irin sauri ta maida dubanta saman manyan rubutun da suke saman newspaper din da aka yisu in bold style yadda zai dauki hankalin harda na nesa.

_CIKIN WADANDA AKE ZARGI KENAN DA SACE SHARARREN ATTAJIRIN KASUWAR GOLD DA DIAMOND KENAN MUHAMMAD JADDA_

Dukka hannunta suka dauki rawa,wata kidima ta saukar mata,ta dubeshi gumi yana sake tsatstsafo mata,yau itace buge cikin calendar da sunan wadda ake tuhuma da satar d'anta?,ba wanda zai aikata wannan sai yarinyar.....don kuwa ita daya take videos din ta tabbatar. Kamar wadda kuka zai qwacewa cikin rawar murya da qwacewa dukkan wani hanzari daga gareta tace.

"Yaushe aka buga wannan labarin?,har ina kuma labarin yakai?". Gyara tsaiwarsa yayi da fuskarsa da bata nuna wanzuwar imani a zuciyarsa ko kadan yace.

"Tun da sassafe....nima a teburin me shayi naga wani yana karantawa,sai naga kaman nasan fuskar,koda na duba sai naga fuskar hajja harira ce.....wannan ta kusa da ita dince dai ba'a gane fuskartata". Wata gauruwa ajiyar zuciya ta sake,tabbas zai wahala a gane fuskartata,amma ga wanda yayi mata farin sani hakan bazai bashi wahala ba sam.

Qarar wayarta ya sanyata zabura tana dubanta,don sam bata tsammanin kiran wayar kowa a irin wannan lokacin. Hannu ta sanya ta dauka tana duba me kiran,hajja harira ce,tayi kaman ba zata daga kiran ba amma sai taji tana buqatar sanin waye.

Karata tayi a kunnenta,tana shirin yin sallama sai sallamar tata ta maqale. Muryar hajja harira ce wadda ta fara da sauke mata zazzafan ashar.

"Ni zaki wulaqanta a duniya?,ni xaki toxarta mariya?,meye ban miki ba a rayuwa?,saboda kin asircemin yarinya na miki shuru?,an gaya miki shuruna yana nufin tsoro ne?,bakisan ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fada ne?,ni xaki buga a jarida akan abinda bani da masaniya?,ke bakisan kuskure bane tarar fada da wanda yasan sirrinka ba?,ganganci ne tarar rigima da wanda yasan waye kai ba?......to kin tara kin samu....mu zuba,dani dake shege ka fasa,hoto na gaba idan kika tashi tsirara zaki sakani......hukuma kuma ina nan ina dakon isowarta gidana,qarqari idan sun kamani su kulleni......idan kuma ya tabbata bani ke da hannu ba dole su sakeni". Daga haka hajja harira ta katse kiran.

Wani tashin hankalin na daban maamah taji yana sauko mata,har numfashinta taji kaman yanason riqewa. Sam ba wani motsi data sakeyi akan hajja harira saboda dalilai.guda biyu. Dalilim farko ita daya ce mutum guda daya data mallaki sirrikanta ciki da bai,birnannun sirrikan da babu wanda ya sansu,babu wanda yasan da zamansu sai ita din tak!. Dalili na biyu laila dake hannunta,tasan wannan kadai ya isa ya zame mata daukan fansa game da cin amanar da hajja taso tayi mata,to amma ko a yanzu ikirari da kurarin da hajja tayi mata bazaiyiwu ta barta ba,don haka ta share gumin fuskarta ta soma tura mata gajeran saqo.

_"kiyi komai harira,bazan hanaki ba,amma kada ki manta a hannu kike,laila tana gaidaki da kyau da kyau,tace kuma na gaya miki ki kula,ki kuma kula da kanki"_

Kamar jira shigar saqon yakeyi wani kiran ya sake shigo mata. Baquwar number ce da haka kawai ta sanya gabanta faduwa,ta dinga bin number da kallo tana raba daya biyu. Special number ce,simple da bata cika tarkacen lambobi da yawa ba,ta jima tana kallonta kafin daga bisani dab da xata tsinke ta daga.

Karo na farko da muryarta kawai ta saukar mata da wani mummunan faduwar gaba da bata taba jin irinsa ba.

"Ina fatan saqona ya riskeki zuwa yanzu?,idan ma bai iskeki ba to na tabbatar yana dab da iskeki......somin tabi ne kenan wannan din.....iname sake aike miki da gargadi.....ki nemo min mijina kuma uban 'ya'yana a duk inda kika kaishi.....ba sassauci ba daga qafa.....idan nar yakai awa saba'in da hudu.......abinda zai faru na gaba yafi qarfin wannan......yanzun ba irin wancan lokacin bane.....lokacin da zaki zubdasu ki watsar dasu a duk inda kikaga dama,yanzun rayuwarsu gewaye take da masoyansu......rayuwarsu gewaye take da rayukan dake buqatar su,suke da muhimmanci a wajensu.....suke muradi da mararin ci gaba da wanzuwa tare dasu,da dadi ko ba dadi.....da dukiya ko babu,da lafiya ko babu,saboda su din akeso.......zallar su din ba abinda ke tattare dasu na ni'ima ba".

Har sai da maamah taji numfashinta ya sarqe guri daya da zafafan maganganun data soka mata,to amma zuwa yanzun ko taqi ko taso tana ji a jikinta itace a hannu,duk da tana ji nadan lokaci ne hakan zata kasance,sai maganan harira da suka gama yanzu ta dawo mata.

_"Kuskure ne tarar fada da wanda yasan sirrinka.....yasan waye kai ciki da bai"_ tabbas a dazun kawai.harira ta bata wani darasi daua kamata ace kanta ya kawo mata,amma ko banza a yanzun ma ta zamu wani ajiyayyen darasi da zai zame mata makamin yaqi tsakanin ita hariran da sabreen.

"Sabreena......ki saurareni kiji.....kuskure kikeso ki aikata wanda zaki dana sani daga baya.....ta yaya zan zama silar batan yaro na kamar a film ko a rubutaccen wasan kwaikwayo?" Wani numfashi sabreen ta sauke sannan tace.

"Komai da kika taba aikatawa a kansu a baya din ai hankali bazai dauka ba......hakanan idan ka saurari labaran ba abinda zai hana kace cikin litattsfan labarai ne ba cikin rayuwarmu ta zahiri ba....."

"Ba maganar baya akr ba......maganar yanzu akeyi sabreen" Maamah ta fada karon farko tana sassauta muryarta gudun ballewar sabreen din.

"Da da da yanzun duka daya ne......ba wani abu da zai canzaki......ko a yanzun akwai wani abu da kikeson cimmawa shi ya sanyaki tsaiwa kina bayanin nan,bawai don kinga ya dace kiyi ba,ba kjma wai don kin damu da batan dama faruwar komai ba......kawai abjnda nake buqata daga gareki shine......ki sakarmin mijina.....ki fice a rayuwata.....kije kiyi taki rayuwar duk yadda kk so kika kuma tsara"

"Bani da masaniyar komai sabreen,karki manta mana.....nifa uwa ce"

"Ni kuma me shirin zama uwar,uwarma kuwa ta gaske ba MUNA UWA BA,uwar data shirya tsaf don bawa rayuwar yaranta kariya.....wadanda zasu zo dama wadanda basu taho ba.....kariya daga dukkan wani kalar farmaki daga miyagu da mafarautan mutane,irin kariyar da sunanta zai tumbatsa da tambarin SADAUKARWA.....sadaukarwa mafi girma kuwa cikin rayuwar 'ya'ya akan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login