Showing 231001 words to 234000 words out of 363280 words

Chapter 78 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1415

cuceka. Duk juyin da za'ayi ka tabbatar zuciyarka wankakkiya ce......kana bacci amma sai ubangiji ya zama jinka ya zama ganinka,ya zama me jagorantar al'amuranka,ubangiji ka barmu a naka duniya da lahira,karka bari duniya da abinda yake cikinta ya rufe mana ido don girman zatinka,karka bamu damar cutar kowa don isarka=?O?
Abune a rayuwarta data manta rabon data yishi wato kuka,shekaru masu yawa da suka shude mata,amma sai gashi yau tana zubda hawaye sanadin anni amna da sabreen.

"Lallai dole fansa ta biyo baya.....lallai dole ku biya bashi da fansar zubar wadannan hawaye......dole sadaukarwa ta biyo baya.....wala'alla akwai rayuka da zasu salwanta......rayukan da shudewarsu shine silar wanzuwa da samun nutsuwar zuciyata" Ta fadi a fili tana kallon idanunta da suka tasa saboda kukan data share mintuna tana yi.

A gaggauce ta sake goge fuskarta ta,sannan ta koma wajen luggage dinta ta soma ninke kayan ciki tana zuba wadanda suke gefen gado da kuma cikin toilet din dakin. Tanajin ta qagauta gari ya waye,tana jinta.kaman saman qaya,a jikinta da ruhinta takejin bata da wani sauran zama a garin,bata da sauran abinda ya rage mata da zata zauna tayi cikin qasar(subhanallah).


&Sau tari wata soyayyar tana zamewa madubi kuma abar sha'awa ga wanda ke gefe yana kallo. Wani memories din na wasu masoyan kan samu wajen zama na din din din cikin kwanya ya kasa gushewa saboda girman tsumammiyar soyayya zallar kulawa da qauna me gusar da hankali saboda tsananin kusanci da kulawa tsakanin masoya.

Fu'ad da sabreen......soyayyarsu ta zamewa wasu tamkar makaranta.....ko kuma allon da zaka kalla ka karance ilimin dake shimfide a kanshi.

Wucewar maamah Nigeria ya samar da nutsuwa me tarin yawa ga wasu zukata,wadanda sam basusan gaibun dake tattare da tafiyartata ta barsu ba. Wani lullubabben gaibu me cike da duhun sirrikan da ita kadai ta barwa zuciyarta shi.

Samun sararinta da gushewar wanzuwarta a family din ya bada damar baje kolin soyayya masu dauke da nau'ika kala kala. Sabreen da fu'ad,suna rayuwa da nunawa juna soyyaya da kulawa tamkar sun manta da akwai wasu halittun dake gewaye dasu suna tasu rayuwar.

Sau tari idan fu'ad yayi wani abun saidai kowa ya runtse idanunsa,don ba wanda yake gani sai sabreen da cikinsa dake manne a jikinta. Gaba daya kaman ya mance da kowa sai ita sai hidimarta,wani lokacin hankali yafi zuwa jikinta akanshi,don takan tuna da anni a wajen ta rage wani abun.

Duk da abun ya zowa anni a sabo,amma saita zama suruka me yawan bada uzuri da dauke kai. Bata shiga tarayyarsu ko kadan,saita dinga nesa nesa dasu gudun ji masu kunya duka ita dasu.

Wannan soyayyar sai ya hura wuta biyu......tsohon tsumin soyayya ya balle tsakanin musaddiq da amnansa,duk da cewa daga nesa nesa ake komai don anni bata bari abun ya zurfafa da yawa. Su dinma duk yadda sukaso su boye dole ita soyayya bayyana kanta takeyi koda an boyeta. Sannu a hankali sai wata wutar munafukar soyayyar ta soma kunnuwa kuma daban tsakanin saddiq da huda. Duk wani nuqu nuqu da sukeyi hakan bai hana sabreen karantar komai ba,ranar sun dawo daga masallaci take tseguntawa fu'ad hancinta ya lakace mata.

"Kin iya sa ido duniyata.......banda nidin ina da qarfin kurwa banjin zan qwace filin soyayyar da akewa su huda.......Allah ya taimakeni nayi hasashen tsaf zaki iya guduwa ki barni.......nayi miki yankan baya na kawo miki su.....to me ya rage?". A mamakance ta zare idanu dariya tana qwace mata,sai ta boye kanta cikin qirjinsa tana qoqarin musanta maganar.

Saidai kuma a zahirin gaskiya cike take da mamaki,wanne irin mutum ne fu'ad din me tsananin kula har haka?,ta yarda dari bisa dari baya wasa da duk abinda yakeso.

Duk wadannan abubuwan da yake faruwa bai hanasu ibada ba tuquru........zamansu tsakanin makka da madeena yafi yiwa fu'ad dadi sama da kowa,tunda ko banza yace za'a qiri halittar danshi ko 'yarshi a guri me tsarki da tsarkakken ruwan zamzam wanda shine komin sabreen. Komai da zamzam takeyi,shine ruwanta nayin komai,iya falalar ruwan zam zam kawai ya sanya yake qara jin nutsuwa da zamansu a nan.

Tuni ya mata register da komai na zuwa awo da haihuwa,don yace indai yana da rai da lafiya to tabbas a garin madeena yakeso a haifa masa yaransa,ya tsara komai ba tare daya gayawa kowa bama.


*_K'ADDARA KO GANGANCI?_*

_KALLON KALLO_


Sau uku tana rolling sassalkar luxury Egyptian abaya din tana warewa. Kawai sai tayi zaune gaban madubin tana ware hannuwanta gami da binsu da kallo.

Batasan me yasa ba......batasan kuma me yake faruwa ba,shagwabata da yayi da yi mata hidimar komai ne sila ko kuma cikin jikinta ya sanya ta zama raguwa?.

A karo na hudu ta sake gwadawa sai veil din ya sabule salin alin daga hannunta. Ido ta zubawa fuskarta,sai taji hawaye kawai ya kubce mata.

Murmushi ya saki yana qarasa sanya link din hannun kuftan jikinsa,ya soma takowa a hankali zuwa bayanta. Tun daxun da taketa drama ita da dankwalin yana kallonta,yasan qarshen maganar dama ta sanya kuka tunda ta zama rigimammiya ta gaske.

Kafadunta ya kama ya tasheta tsaye,suka hada ido sai yayi qoqarin danne dariyarsa,saidai tuni ta riga ta gani.

Daga hawaye sai ta sakar masa kuka me qaramin sauti.

"Subhanallah......me kuma nayi?" Ya fada yana dora damuwa saman fuskarsa duk da da gasken dariya yakeson yayi.

"Ya isa....am sorry if I offend you" Ya fada yana sakata a qirjinsa. Shaqa daya ta yiwa turarensa nutsuwa ta fara saukar mata,sai ya bata lokaci sai daya tabbatar ta nutsu sannan ya dagata yana duban fuskarta.

"To mene ne?,.....uhmmm.....tell me" Tabe baki tayi,ta miqa hannu taja kumatunsa.

"Ba mayafinne yaqi dauruwa ba,sannan kuma kai kazo kanamin dariya saboda ina ramewa kai kuma kina qiba". Wannan karon kecewa yayi da dariya sosai harda riqe ciki. B wani bane ya jawo masa wannan jagwal din ba sai amna,haka kawai ta sashi gaba vanilla ice cream takeson sha,suka yiwa anni wayo suka fice wadda ta jima da hanata shan kayan zaqi da sanyi. Koda sukaje kasa sha tayi.ma gaba daya sai ya fita a ranta,shi kuma duk da bai dameshi ba amma sai yaji ya masa dadi,yasa aka kawo masa ya soma sha,ashe tana ankare,ke amna kika ce

"Hamma madeena ta karbeka Allah,ka karbe jikin adda ka hada da naka,kanata kumatu" Ta fada tana dariya.

"Lovey dovey.....kin manta ni yayan mijinki ne kenan?" Ya fadi hakanne don shine abu daya yanzu da yake kashe bakin amna,ya kuma fadi hakanne don ya fuskanci sabreen din har ta kumburo fashewa kawai take jira tayi. Ashe abun dashi ta kwana sai yanzu ake fashe masa shi.

Sulalewa yayi ya durqusa gabanta,ya zagaye hannunsa a bayanta yana dora fuskarsa saman mararta.

"Kazo mu bawa mama haquri....mun hanata qiba mun hanata cin kayan dadi....mun tuba....zamu gyara halinmu" Ya qarasa maganar yana hade hannuwansa guri daya.

Da ido ya bita ganin daga kuka ta koma buga murmushi,ya girgiza kai kawai a ransa yana gulma,wato me ciki sai a barta kawai.....abun kuka ko bacin rai baya mata kadan,cikin dabara ya jata ya sauya mata yalwataccen mayafin rolling din ya daura mata da kanshi,don bayason wani sashe na jikinta ko kadan ya fita wani ya gani.

Yana gama mata ana knocking qofar,yasan waye farouq ne,qiri da muzu ya zama fusataccen qarfi da yaji,yace fu'ad ya jawo masa raini,ya hada tuxurantaka da aure da qannensa,in fact ma qanin bayansa ya rigashi amsa sunan me aure,wannan ta saka dole qasa daya data rage musu akayi cancelled trip din sai bayan wani lokaci,aka aikewa da iyayen fanna date na bikin sati biyu masu zuwa wato sati biyu da komawarsu nigeria kenan.

Hannunta cikin nashi yadda suka saba suka fito a dakin,ta zame hannun nata a dabarance ta qarasa gaban anni ta gaidata,ta gaida momma wadanda zasu sauka duka a nigeria,da yammaci kuma jirgi zai wuce dasu mali saboda washegari huda zatayi ton prints na jarabawar kammala secondary school.

Haka suka wuce airport cikin motocin da a nan qasar yake barinsu sai kuma zuwa na gaba.

Anata zuba soyayyar munafunci tsakanin amna da musaddiq,huda da saddiq daketa babbasarwa kaman ba komai tsakaninsu,angon gobe farouq kuwa anata sallama da fanna ta waya shima ya bude wuta sosai don shirye shirye sun gama kammaluwa,ranar kawai suke jira.

Ita kuwa kanta yana kwance kawai saman kafadarsa. Tun bata saba ba har ya riga ya saba mata,wata kasala take fama da ita,bata iya cikakken zama ba'a jikinsa.

Tunda jirginsu ya tashi take jin gabanta yana faduwa lokaci lokaci,tadan rufe idanunta kadan tana jan sunan Allah,ko shima sabuwar faduwar gaban tana cikin laulayin ta yiwa kanta da kanta tambaya.

Idonta ta rufe tana fatan bacci yayi awon gaba da ita wai ko zata samu sassaucin abinda takeji,tana iya jin sanda ya sanya blanket ya lullubeta,sannan ya sake rufeta da faffadan qirjinsa yana rufeta tsam cikin jikinsa,ajiyar zuciya me sanyi ta subuce masa ya dora habarsa saman kanta a tausashe.

Cikin zuciyarta take roqon Allah......kada ya bata ikon butulcewa wannan bawa ko juya masa baya.......ita kanta wani lokaci irin yadda yayi nisa a soyayyarta tana jin kamar tata zuciyar zata narke a kansa. Tsakanin ita dashi batasan waye yafi wani yin nisa ba,waye yafi wani yin zurfi bs,fatanta kawai shine kada su zama masu butulcewa juna a tsakaninsu.

Tafiyar awanni biyu jirginsu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano dake kano. Sai takejin farinciki yana ratsata duk da ta baro wani guri mai muhimmancin gaske a rayuwar duk wani musulmi.

Abu guda daya da yaci gaba da farautarta shine faduwar gaban dake qara tsanantar mata,duk sai take jinta a rikice har zuwa sanda suka qaraso inda jerin gwanon motocin jadda diamond suke jiran qarasowarsu.

Kusan dukkanin guards dinsa sun zo tararsa cike da girmamawa da kuma kewarsa da sukayi na tsahon lokaci.

Sabule hannunsa yayi daga cikin nata,abinda ya sanyata daga kai ta kalleshi kenan.

Murmushi ya sakar mata me taushi yana dubanta.

"Zaku fara yin gaba saboda ki samu zama dasu huda kuyi sallama......zan qaraso yanzun......nasan a gajiye kike amma ma'u ta tanadar miki komai.....kada kice zaki jirani,kiyi wanka kici abinci kiyi bacci sosai......yau akwai biyan bashi" Ya furta maganan qarshen qasa qasa yadda ba wanda zaiji musu sirrinsu.

Duk da yadda gabanta ke tsananta faduwa,duk da yadda takejin kaman zaini wani wawan nisa da ita......irin nisan da takejin tazararshi tayi yawa amma saida murmushi ya subuce mata. A tausashe yayi kissing goshinta yana dubanta. Raunin da yake ganin cikin idanunta shi kansa baisan na meye ba,ya saka hannu da kansa ya bude mata qofar motar dasu huda ke jiranta,ta shiga,ya tsugunna ya tattare mata abayarta data fito waje ya maida ciki.

"Kada ka dade" Ta samu kanta da fadi masa a karye sanda yake shirin rufe mata qofar

"In sha Allah" Ya bata amsa yana jin dadin kulawa da damuwa dashi din data nuna,ya rufe qofar a tausashe sannan yaja baya ya kira abdulgafar sukayi magana,ya kira abdulbasit shima sannan ya sallamesu suka tashi motocin da zasu kaisu gida,ya rage sauran wadanda zaiyi amfani dasu ne kawai.

Ta cikin side mirror din motar tasu ta zuba masa idanu,suna sakeyin gaba yana nisa da madubin har ya bacewa ganinta,saita lumshe idonta tana sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Tana jin karadin su huda sanda suke fita daga airport din amma ta gaza saka baki a hirarsu,kawai tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa ne.......har zuwa sanda qarar harbin bindiga har sau biyu ya sauka a kunnenta.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta fada da wata irin zabura tana ware idanunta gami da miqewa ta zauna sosai faduwar gabanta yana ninkuwa.

Salatin da taja shi ya sanya kowa a motar ya dauke wuta,momma dake seat din gaba ta waiwayo da hanzari tana kallon fuskar sabreen din. Huda ce tayi qarfin halin fara tambaya

"Lafiya adda?".

" Qarar harbin bindiga huda......bakuji ba?" Ta tambayesu a rude tana raba idanunta akan fuskarsu.

"Nidai banji ba" Huda ta fada tana girgixa kai

"Naji....harbi ne,amma kamar nesa da nan" Momma ta fadi tana dubansu daga inda take

"Nima naji momma" Nadra itama ta fada tana dubansu. Kan hanya hankalinta yakai,sai taga kaman driver din nasu ya qara gudun motar fiye da yadda suka fara tafiyar,hankalinta taji yana neman dagawa sosai,sai ta kalli su momma din tanajin kaman haki yanason kamata saboda tsananin bugawar da zuciyarta takeyi.


*_Tabdijan.......meke shirin faruwa ne?,me kuke hasashe?,me karatu mu hadu gobe idan me duka ya kaimu_*

*_akwai yaqi kenan_*



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ? 118


118



"Momma ba'a nesa harbin nan yake ba......koda a nesa dinne bawai ness can damu ba......mun baro su hamma a ciki momma.....bamusan me yake faruwa ba.....driver!" Ta ambata da qarfi kaman numfashinta yana son qwace mata.

"Yes madam" Ya fada da dan qarfi shima yadda zata iya jiyoshi.

"Mu koma mu duba boss......qarar harbi nakeji".

" Am sorry maaa.......nima naji,kuma umarni ne na boss din shi ya horemu,duk sanda mukaji abu irin wannan kada mu sake mu koma da baya......kuma ko a tsarin tsaro ma hakan ganganci ne.....kiyi haquri mu qarasa gida.....we are safe in sha Allah". Yana kaiwa qarshen maganarsa qarar wani harbin a jejjere har guda biyu ya sauka a kunnensu. Qarasa gigicewa tayi gaba daya,jikinta da muryarta gaba daya suka dauki rawa.

"Ta cikin airport dinnan ne momma.....idan safe nake hamma fu'ad fa?" Ta jefawa momma tambayar cikin rauni hawaye na gangaro mata.

Girgixa kai momma tayi wadda ke qoqarin boye nata tashin hankalin.

"Bazaiyiwu a koma ba kaman yadda kika ce.....hasalima baki da tabbacin a inda suke abun yake faruwa ko wani shiyyar ne na daban.....koda a inda suke ne ma shima bazaiso ace koma meye ya hada dake ba....." Momma take fadi cikin son lallashinta. Sam hankalinta ba'a jikinta yake ba,bata ma kama maganar momma ba saita jawo jakarta jikinta dukka yana rawa ta fiddo wayarta tana cewa.

"Gabana yanata faduwa ne momma,tabbacin akwai wani abu da ba daidai ba" Tayi maganar tana zaro wayarta da zummar kiran number fu'ad din.

Abun takacin abinda kuma ya sanya a karan farko tayi Allah wadai da halinta shine. Ba number wata number da tayi kama da tasa cikin contact dinta,sai a sannan ta tuna,waccan tafiyar da yayi ya kirata sau daya,batayi saving number nasa bama,kuma koda ta duba call log babu number a wajen.

Kuka ne ya qwace mata ganin yadda suke qara nisa da airport din ba tare da tasan halin da yake ciki ba.....don gaba daya jikinta yana gaya mata akwai gagarumar matsala.

"Ni ku saukeni......xan koma na dubashi,zan tabbatar da lafiyarsa saimu taho tare dashi" Ta fada muryarta na rawa.

"Kiyi haquri madam......aikina bazai cika ba saina kaiki gida lafiya.....aikata hakan zai zama zunubi mafi girma a wajen boss,har gwara na kaiku gida na miki alqawarin dawowa na duba miki lafiyanshi". Abdul rauf ya bata amsa shima yana jin damuwa sosai da fargabar kada wani abu me muni ya faru da ogansu.

Sam bata gane abinda momma ke fadi mata ma,ta rarumo wayar ta soma lalubar number anni ko


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login