Showing 150001 words to 153000 words out of 363280 words

Chapter 51 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1388

yoghurt ". A yau ta fahimci ainihin dalilinsa,saita dinga furta

" Alhamdulillah" Qasan zuciyarta. Da gaske Allah ya tsare mata yaranta gabansu da bayansu kaman yadda take yawaita addua a dukka salllolinta na nafila ko na farilla. Tayi imanin inda wani ne ya samu cikakkiyar dama irinta fu'ad din,tarin dukiya kyau ilimi da suna da yayi a duniya ba irin haramtattun ayyukan da bazai aikata ba,ta sani akwai dubban mata dake a shirye su bada kansu ga irin wadannan mutanen,koda ba zasu samu komai ba a wajensu daukaka ce ace yau suna tare dasu.

Sai data zaunar da sabreen yadda zataji dadin zaman sannan ta juya a hankali tana fita parlor din.

Minti daya ta dawo tare da baquwar fuskar. Dr fadwa siririya fara tas,duba daya zaka fahimci shekarunta duka duka ba zasu haura arba'in ba zuwa da biyu. Anni tana gaba dauke da tea tray,Dr fadwa na biye da ita.

Qasa sabreen tayi da qwayar idanunta,ba zata iya kallonsu ba dukka su biyun,har Dr fadwa dake matsayin baquwa a idanunta. Ajiye tea tray din anni tayi tana duban Dr fadwa. Kai Dr fadwa ta gyadawa anni,sai annin ta maida dubanta ga sabreen

"Ga likita na.....zata dubaki in sha Allah,ki saki jikinki.....itama 'yar gida ce" Kai ta dagawa anni a hankali,tana jin takun anni da fitarta a dakin,ta kuma ja qofar ta rufe musu.

Dubanta Dr fadwa take tana kuma karantarta. Ko ba'a gaya mata ba ta fahimci ita din bame saurin sakewa da mutane bace,ta miqa hannu a nutse ta kama hannunta ta sanya a nata,abinda ya sanya sabreen daga kanta ta kalleta da risunannun idanunta. Da sassauqan turanci take tambayarta da sakakkiyar murya.

"Kinci abinci?" Kai ta girgiza mata a hankali. Ba zata iya tuna wani abincin kirki da taci ba,tun na dazun kafin su fita,ko acan wajen cin kifi ma bata saki jiki taci komai ba,kasancewar ita ba ma'abociyar cin abinci cikin jama'a bane. Kai tsaye Dr fadwa ta jawo tea tray din zuwa saman cinyarta tana matsawa dab da sabreen

"Ki saki jiki kici abinci......sai na dubaki,kada ki damu da yawa......hakan yana faruwa ga 'ya'ya mata da yawa,musamman da yake yadda kowacce mace halittanta daban,haka kowanne namiji shima nashi halittan daban......fashewar budurcin mace yana iya kawo fitar jini.....amma komai zai zama daidai kinji?" Kai ta daga a hankali,ta kuma miqa hannu tana karbar mug din da anni ta hada mata tea me dumi sosai da kauri.

Ita kanta tasan ba komai a cikinta,ballantana kuma da abun ya faru sai taji kamar anyi mata yasa,kamar an kwashe 'ya'yan hanjinta gaba daya,kamar iska tana turata zuwa gaba.

Kadan kadan take shan tea din,dr fadwa bata matsa wajen kallonta ko yi mata wata tambaya ba ta daban,ta bata time sosai tana duba wayarta har taga ta ajiye. Wayar ta bari ta daga kai tana kallonta,batasha da yawa ba amma saita qyaleta don tasan lallai yanayin bame dadi bane.

Kauda tray din tayi ta matso kusa da ita tana dubanta

"Sunana fadwa kefa?"

"Ameenatu" Ta furta idanunta suna dan lumshewa

"Sabreen sunan inkiya?" Kai ta gyada,saita fidda takarda fara ta rubuta sunan akai.

"Eheennn......ina ne yake miki ciwo yanzu?" Shuru tayi don tamabayar tayi mata nauyi da yawa,uwa uba ma gurare da yawa ciwon suke mata,tun daga lips dinta......qirjinta....hatta da tafukan hannunta da suka sha murxa zafi zafi takeji suna mata.

"Ki sake sosai kiyimin bayani,shi yasa madam ta fita ta bamu guri......zai iya zama ciwo me zafi nan gaba idan baki bayani ba". Hannu tasa ta nuna mata wajen ba tare data iya kallon idanun fadwa ba.

"Alright......zan duba wajen idan ba damuwa?" Ta fadi da nufin neman izini. Dif tayi abun yana mata wani iri,shikenan ita kuma jikinta ya zama wani budadden guri?

"Kiyi haquri....saboda lafiyarki,bazai dauki lokaci ba" Ta fada da sigar lallashi. Kai ta gyada mata a sanyaye.

"Kin shirya?" Dr fadwa ta fada tana kallonta sanda ta kwanta kamar yadda ta kwatanta mata. Kai ta gyada mata tana rufe idonta saboda kunya.

A hankali ta fara dubata cikin qwarewa da nutsuwa yadda ba zata fama mata ba.

"Oh my god.......subhanallah" Abinda ta fada kenan tana maida mata doguwar rigarta.

"Kin masa gardama ko musu?" Dr fadwa ta fada tana kallon fuskar sabreen din da tuntuni ta canza kala zuwa red. Tambayar sai ta zama kaman ta bata license din sabon kuka,ita me zata ce mata?,batasan ma me tayi ba.....musu ko taurin kan batasan wanne ne tayi a ciki ba,batasan wanne ne ya faru ba.

"Irinsu sir.......ba kasafai za'ayi musu musu a irin wannan lokacin a wanye lafiya qalau ba.....next time kada ki qara musu ko gardama,mijinki yana da duk wani personality da kowacce 'ya mace zatayi alfaharin samunsa a matsayin miji,.....kulawa da tattali yake buqata,ko don gaba kada ki sake matse jikinki da hana masa kanki haka". Sanda take fadin next time din ji take kaman ta ture Dr fadwa,itakam wacce irin sauna ce da zata yarda taci gaba da zama da mutum irinsa?,wanda bisan ciwo ko darajar dan adam ba?,balle ma har hakan taci gaba da faruwa wai a gaba?.

Daidai nan anni ta tura qofar ta shigo,da murmushi take tambayar Dr fadwa

"Kin gama?" Kai ta girgiza tana dan murmushi itama

"Aah fa......madam yaronki aiki ya baro.....bleeding din data dinga yi ta samu tier ne.....so dole sai an mata stitches..." Idanu kadan anni ta fiddo,har jikinta tana jin wani iri. Lallai Allah kadai yasan azabar da tasha tunda har an kai ga batun dinki.

"Gurin yayi ciwo sosai gaskiya.....harda bruises banda tier din,dole a dinki wajen,inda first degree tier ne da sauqi....so amma yanzun ma idan kina ganin a bari......"

"No.....a dinke Dr" Anni tayi saurin dakatar da Dr fadwa din. A yadda taga yanayin fu'ad din da idanunshi ba yadda zata bari a bar sabreen din a bude,tun sanda momma ta gaya mata marainiya ce takejin kamar kula da sabreen din wani haqqi ne daya rataya a wuyanta.

"Kiyi haquri a dinke sabreen kinji?,wannan gurin shine mutuncin duk wata d'iya mace a wajen mijinta.....akwai zafi amma zai wuce kaman bai faru ba,wannan shi ake kira da cikakken mutunci mijinki ya zamana shi ya karbi wannan abun ba wasu shashashai a waje ba.....nayi alfahari da hakan......na kuma yi alfahari dake kaman yadda nasan yake a wajen mijinki" Anni ta fada a tausashe hannunta saman kan sabreen da kunya ta hanata koda motsawa bare ta bude idanunta.

Sake fita anni tayi ta basu waje don sabreen din ta sake sosai. Dr fadwa kuma ta shirya komai,ta kuma yi mata allurar da sai data zubda qwalla kafin a gama,batasan azaban yana gaba ba sai da aka fara dinkin.

Neman sakayya wajen Alla data dinga yi har batasan sau adadin nawa ta fadi ba,saidai duka cikin ranta takeyi,bakinta baya iya furta komai sai ruwan hawaye dake fita Dr fadwa na mata sannu.

Kasa zama yayi a falon,sai kawai ya tura qofar dakinsu saddiq ya shige. Kwance yayi kawai saman gadonsu,ya kasa tuna komai sai hankalinsa dake can dakin inda ya barosu,yaji shigar dr fadwa da anni da fitowar annin duka,baisan me yake faruwa ba don haka ya kasa samun nutsuwa. Gefe guda wani irin sarqaqiya ya shiga.

"KARUWA" Sunanta ma farko kenan daya fara zuwa kunnensa,yaci gaba kuma da zuwa masa daga bakunan mabanbantan mutane. Kenan dukka wadannan bincike da shaidun duka shaidan zur ne?,duka shaidan qarya ne?. Idan har hakan ya kasance kuma ganin da yayi mata a hotel fa?,mashkur dake hannunsu a yanzu haka yana nemanta afujajan da sunan wadda ta kwashe masa komai nasa?,ganinta da yayi fa tare da mika'il?,a cikin kamfaninsa tana fitowa daga toilet dinsa?,binciken daya tabbatar kuma ita ta kwashe kudaden asusun kamfaninsa fa?,wannan kuma mene?. Ta yaya zai fahimta?,ta yaya zai gane?,waye zai warware masa?.

"Ka nutsu fu'ad.......diban kudi yasha banban da bada mutunci.....don tana kwashe kudaden maza.....don kana ganinsu tare hakan ba yana nufin tana basu kanya bane,kowanne matsayinsa daban,cakudasu waje daya kuma shine zai sanya ka kasa banbance inda komai ya dosa" Wani sashe can qarqashin lungun zuciyarsa ya gaya masa.

Sau uku yana leqa parlor din ko zaiga ko yaji motsin anni ko wani abu da zai bashi haske amma baiji ba. Kunyarsa da kawaicinsa duka suka qare,sai kawai ya buda qofar dakin ya fito kai tsaye yana tunkarar dakin.

Itace ta farko da idanunsa suka fada kanta bayan bude qofar da yayi. Ta wani sake fadawa farat daya saboda masifar dinkin. Ko baka santa ba tsakanin a wannin nan idan ka kalli fuskarta zakasan tayi kalar kukan da bata taba irinsa ba.

Idanunsa ya maida kan Dr fadwa,likitan da sai da tazo ya tuna ya taba saninta a Egypt,ta taba dubashi da yayi wani zazzabi,hankalinta kuma da nutsuwarta shine abinda ya sanya ya bata daman bashi magani.

"Welcome sir" Ta fada cikin girmamawa. Kai ya gyada yaja kujera yana zama hankalinshi a kanta. Daga kallon da yayi mata ta fahimci qarin bayani yake nema. Dama kuma dole akwai buqatar masa qarin bayanin don ta fahimci kaman yana cikin mazan nan marasa haquri akan abinda ya shafi janibin auratayya.

"Mun kammala,anyi mata stitches.....but please sir,tana buqatar hutu na koda 3to 4 weeks kafin a sake tabata,saboda a bawa dinkin daman warkewa yadda ya kamata". Ido ya lumshe sannan ya bude yana jinjina kai.

"Mun gode....ta yaya zaa biyaki?".

"Madam ta biya sir.....Allah ya qara lafiya" Kai ya jinjina yana girmama qaunarsu da anni. Tsantsar kulawa da qauna irin wadda akasan uwa kadai take da wannan zuciyar. Komai idan ya kama qoqari takeyi tayi musu shi ba tare data jira yin kowa ko cewar kowa ba.

Tatttare kayanta tayi ta fice taja musu qofar.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

79


A hankali ya dauke dubansa daga kan qofar zuwa inda take zaune. Idanunsa ya zuba mata yana jin akwai wani boyayyen abu ciki rayuwarta,wadanne irin masharrantan mutane ne tattare da ita haka?,wadanda ba zasu iya fadin alkhairi a kanta ba?,wadanda ba zasu iya suturta aibunta ba a sanda akazo bincike a kanta ba?. Idan bai manta ba,ya samu tabbacin cikin wadanda suka bada shaida a kanta harda matar babanta,sanda yake jaddadawa abdul haleem bayason fake bincike,baya son kuma gurbataccen shaidu.

"Wacece a cikinsu?" Ya tambayi kansa da kansa yana takawa gabanta,tausayi da wata irin mahaukaciyar qauna tata tana hudashi. A yanzun yana jin a shirye yake da duk wani mutum da zai taba rayuwarta,a shirye yake ya bada dukkan abinda ya mallaka a kanta.....in fact a yadda ta zame masa mahadin numfashi a yanxun......ba dukiyarsa kadai ba.....hatta da rayuwarsa a shirye yake ya bata ita. Yana jin ya shirya kame duk wani wanda ya bada shaidar banza a kanta,ya shirya tuhumarsu ko su waye....komai yawansu.....komai kuma kusancin dake tsakaninsu da ita.

A jikinta takejin wanzuwarsa a wajen,wannan ya sanya ta sake zabar ci gaba da rufe idanunta,har ya iso gefanta,ya zame kan gwiwoyinsa yana aza qarfinsa akai. Hannusa ya miqa ya kamo tattausan tafin hannunta,ta motsa da sauri ta nufin zamewa amma ya rigata,ya kamo hannun nata da daya hannun ya saka tsakiyar hannayensa yana duban rufaffen idonta. Dukka kalamansa sun gama qwace masa,komai ya auno sai yaji bai hau mizanin bada haquri ba....amma hakanan zaici gaba da gwadawa don ya shirya karbar ko meye daga gareta hannu bibbiyu.

" Can you feel any pain or discomfort?" Ya tambayeta kaman zai maida idanunshi cikin fuskarta. Shuru ne ya zame masa amsa,bata ko motsa ba ballantana ta nuna tasan da ita yake. Sake matsa hannunta yayi kadan a tausashe,ya motsa labbansa yace

"Sabrrrrr" Nan ma shuru ba wani motsi ko amsa. Jawo hannun nata yayi kadan,ya kuma matso dashi ya dora ta????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
fin hannun nata saman qirjinsa saitin zuciyarsa.

Tabbas har cikin jininta taji bugun zuciyarsa.....kaman yadda dumin cikin hannunsa da wanda taji cikin qirjinsa ya tabbatar mata da zazzafan zazzabin da yakeyi,amma ko daya sai taji bataji tausayinsa ba.

"Im filled with regret for what i did,am truly sorry......please kice wani abu man" Ya fadi cikin zaquwar ji daga gareta,amma still ba wani canji. Shurunta sai yaji yana kasheshi har cikin tsokar zuciyarsa,shirunta sai yaji yana masa wani irin ciwo......baya fatan ta zama me hukunci da shuru wanda kusan halinsa kenan,ya kuma san ciwon hakan.

"Sabrrrr......I'll do everything to prevent it on the future nayi alqaw....." Future din daya fada shi ya sanyata janye hannunta sa wani irin sauri,saidai kuma kash zafin namansa ya qure nata,kafin ta samu daman boye hannun ya sake kamoshi yana jin wani nisa da takeson haifarwa tsakaninsu. Cikin yanayi na karaya ya sake aza tafin hannun nata saman kuncinta,ya kuma dora kansa akai kaman wanda ya samu pillow

"My heart was beaten past sabrrrrr........zata iya bugawa wallahi......please sabr say something mana......"

"Ka qyaleniiiiii....." Ta fada cikin daga murya tare da wani irin sautin kuka wanda yayi daidai da shigowar anni. Tsaiwa tayi cak tana dubansa,kaman zata koma sai kuma ta tuna da zancan Dr fadwa,don haka ta qaraso cikin,amma ta dauke kai kaman bataga abinda ya faru ba. Idanunsa ya aza kan annin,sai ya janye jikinsa daga wajen yana komawa inda dr fadwa ta tashi wajen data ajiye documents din da tayi rubutu a ciki.

"Daughter" Ta kira sabreen a hankali wadda ke qoqarin boye hawayenta da mode na fuskarta.

"Naam" Ta amsa tana murmushi

"Akwai ciwo ko ya ragu?,idan akwai tace tayi prescribing wasu magunguna,ta tura ta pharmacy dinsu zaa karbo ko a kawo miki".

" Akwai ragowa" Ta fadi tana jin yadda gurin ya daddaure mata

"Zai daina in sha Allah" Maida kallonta tayi kansa.

"Ka hada mata kayanta da duk zata buqata......zatayi matsa zuwa dakina,zan kula da ita zuwa sanda ciwon zai warke" Anni ta fada adan dake. Da mamaki ya kalli annin yana jin rashin dadi yana saukar masa,abun sam bai masa ba,yana ganin kamar shi yafi cancanta a bari yayi jinyarta,yayin da sabreen taji kamar an mata rahama,wani sanyi ya fara sauka saman zuciyarta.....zata matsa daga kusa dashi......zata bada rata me yawan gaske kuwa tsakaninsu,tana jin sai taso ma zata bari idanunsa ya hadu da nata,tabbas da wannan damar zatayi amfani tayi nesa dashi,nisan da zai fara tun daga yanzu har kuma abada

_uhmmm.....sabreen,anya me jadda zai bari kuwa?,to dai zami gani_


Kaman yadda ani ta buqata haka ya hada mata kayan,yana kallo anni ta kamata a hankali har suka fice a dakin. Ba jimawa ta dawo ta dauki luggage din nata ta sake fita,sai ya koma ya fada saman Kujera kaman wanda baida laka a jikinsa. Dakin yake bi da kallo,sai yake ganin dakin ya masa wani mugun fili kaman an dauke wani abu da yaci gurbi me yawa a dakin.

Hannunsa ya kutsa cikin sumar kansa yana fidda numfashin daya qara zama me zafi saboda zazzabin jikinsa. Wannan zaman bazai masa ba,yana jin kaman bazai iya kwana a dakin shi daya ba,kaman ya masa girma,abinda bai taba ji ba kenan tunda yake kwana a daki shi daya ba sai yau.

Wayarsa ta dake gefe ce ta dauki ringing,kaman bazai daga ba amma ya daure ya miqa hannu,anni ce,a sanyaye ya daga yana fatan ba wani abun bane da zai sake sanya nisa tsakaninsa da sabreen din ba

"Ka nema magani kasha kaima jikinka akwai zazzabi". Da qyar ya motsa labbansa yana fadin

"To" Ta katse wayar ya sauke shima yana jinjinawa da kulawa tare da damuwa da lamarinsu irin na anni.

Hannu ya dafa zai miqe ya aza hannunsa kan takardar da Dr fadwa ta rubuta,ya dauketa zummar sauya mata waje,idanunsa suka sauka kan sunanta.

"Ameenatu Ahmad" Ya furta sunan a fili

"Is her real name ameenatu?" Ya tambayi kansa a mamakance. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi,wani abune da bai taba sani ba sai yau

"Ya rahman" Ya furta a karye. Duk wata me suna ameena darajarta daban yake a ranta,kima da mutuncinta ya zarta na sauran mata a wajensa duka dalilin anni. Koda list aka kawo masa idanunsa ya sauka kan sunan ameena yana fara tsinceta daban kafin kowa.

"Ameenatu" Ya maimaita sunan can qasan maqoshinsa yana jin wani abu me matuqar qarfi yana kwaranya tare da jinin jikinsa zuwa zuciyarsa da kowanne sashe na jikinsa. Qarfin abun yana jin kamar yafi qarfinsa da gasken gaske bare ya tareshi.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


80


A daddafe ya nemi magani yasha,har cikin ransa yake ji tabbas Allah yana sonshi,ubangiji na qaunarsa......bai debe komai da kowa daga hannunsa ba......Allah ya dubeshi,ya killace masa ita da wani irin tsaro da bai taba tunanin wanzuwarsa a tattare da ita ba. Duk da ciwon kansa sai ya samu kansa da tashi ya wuce toilet,qarfe daya saura na dare,ya daura alwala ya dawo ya shimfida abun salla ya kabbara


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login