Showing 222001 words to 225000 words out of 363280 words

Chapter 75 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1346

ranta ya cika da ambatonsa. Tana ji ya gama yi mata komai na rayuwa.......tanaji ya gama mallakar komai nata...???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?..gangar jiki da kuma zuciya,tana jin ya sayi wani babban gurbi a rayuwarta da rufe babinsa ba abu bane me yuwuwa. A yanzun daya qarasa cika mata burinta.....

Sun gaya mata abubuwa masu yawa da ya yiwa rayuwar su wanda bata taba kawowa mafarkinta hakan zai kasance ba. Wani irin gini da ya yiwa rayuwarsu har ya zarta nata mafarkin a kansu.....ko yanzu ta fadi ta mutu ta godewa Allah......tana da dukkan tabbas da yaqini akan rayuwarsu.

Haka kawai takejin kaman yayi tsaho ace ta jirayi gobe kafin tayi masa godiya.....sai takeji ya cancanci ta abokanceshi a wannan daren. Tafi kowa sanin yadda waje yake masa qunci idan ta matsa......tafi kowa sanin yadda yake qulafucinta da son kasancewarsu tare. Tun saukarsu bai nemeta ba ko a waya,tasan kara kawai yayi mata bawai don hakan yakeso ya kasance ba.

Zazzabinta da komai da takeji ta hadiye,ta shiga bandaki ta sake wanka,ta dawo cikin dabara tana tunanin inda zataga luggage dinta. Ba luggage amma akwai wani bag daban data shigo dashi,kusan duka sabbin kaya ne a ciki,saita samu kanta da neman rigar da tasan zata dace da yanayin. Tsaf ta gyara sumarta cikin hair mist dinta,ta kuma tajeta ta saketa a gadon bayanta. Yadda farar tattausar rigar maras tsaho ta zauna mata a jikinta ita kanta ya burgeta,komai ya fito das das a jikinta da wani irin salo me daukan hankali,saita nema dogon hijabin daya rufe mata jikinta ruf ta aza saman rigar,ta dauki wayarta ta taka a hankali tana fita a dakin.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

113


Waiwaye ta dinga yi don ta tabbatar da kowa bai ganta ba,ta qarasa qofar dakin a nutse tana fatan samunta a bude. Taci sa'a kuwa,don tana murdata ta bude din,sai ta tura ta shige a hankali. Abinda bata sani ba tayi shuka idanun makwarwa,daidai sanda maamah ke fitowa daga dakinta da zummar sauka floor din qasa ta rage zaman kadaici koda cikin reception ne.

Dif wuta ta dauke mata,wata qaqqarfar guduma ta saukar mata. Lalubawa tayi ta nema kujerun da suke ajewa jifa jifa ta cikin hallways din ta zauna ganin duhu yana nemam giftawa idanunta tana maida numfashi,maganar da sukayi da ita ta qarshe ta dawo mata.

"BANA SONSHI....BAZAN KUMA TABA SONSHI BA.....BANMA SHIRYA ZAMA DASHI BA.....AKWAI LOKACIN DA XAN TAFI.....AMMA ZAN TAFI NE KAWAI SANDA NI NA TSARA NA TAFIN,BAWAI SANDA KE KIKA SHIRYA FARUWAR HAKAN BA". kai ta jijjiga tana sake dilmiyewa cikin mamaki. Wato ita yarinyar take rainawa hankali kenan?,ita takewa wasa da hankali?,wai ya akayi kaman ita mariya yarinya 'yar cikinta wadda inda fuad mace ne yaci ace jikarta ce amma take wasan kura da hankalinta haka?. Dukan kujerar tayi ta miqe tana komawa cikin dakin,zata kasa ta tsare taga iya awannin da zata dauka kafin ta fito a dakin.

Matsakaicin haske ne a dakin,da alama ya kashe kowanne qwai banda side lamp din dake gefen Kujerar data hangoshi kwance samanta.

Yana kwance sosai ya miqe dukka wannan tsahon nasa,hasken fitilar ya haske fuskarsa sosai. Qur'ani ne a bude kife a qirjinsa,da alama yana tsaka da karantawa bacci ya daukeshi. Baqar sumar nan dake habarsa da qasan hancinsa girarsa da zara zaran eyelashes dinsa sun sake qawata fuskarsa da wani irin annuri. Ita kanta saita samu kanta da qare masa kallo,har zuwa sanda ta isa gabansa cikin sanda.

A hankali ta tsugunna a gabansa tana sake matsawa dab dashi,qamshinsa ya taso ya daki hancinta,abinda ya sakata lumshe idanunta ba tare data shirya ba saboda dadi da nutsuwa da qamshin ya saukar mata.

Cikin takatsantsan ta miqa hannunta tana zare alqur'anin da yake rungume dashi,ta daga tana duba wacce surar yake.

Alama ce saman ayar muhammadur rasulullah bisa dukkan alamu nan yake karantawa,ta motsa bakinta a hankali ta furta.

"Sallalahu alaihi wa sallam" Ta sanya bakinta kan ayar a nutse tayi kissing nata sannan ta rufe qur'anin ta adanashi.

Sake dawowa tayi ta tsugunna saitin fuskarsa tana qare masa kallo. Karon farko data karanci ainihin sassanyan kyau da Allah ya masa baiwa dashi. Ba banza ba yake da wani irin kwarjini da ba kowa ke iya saka idanunsa kan fuskarsa zuwa cikin idanunsa haka kai tsaye ba,labbansa sukayi mata kyau sosai,ta miqa hannu tana taba dogayen eyelashes dinsa sannan ta sauko zuwa labbansa masu kalan red tadan taba. Motsawar da taga yayi sai ta janye hannunta da sauri zuciyarta tana bugawa,dan gyara kwanciyarsa yayi kadan zuwa hannun damansa,abinda ya bashi daman fuskantarta sosai itama ya bata daman ganin fuskarsa sosai.

Hannunta ta sake miqawa ta kama yatsunsa,a hankali ta motsa labbanta.

"Ka dage sai da ka farauci wannan sabuwar zuciyar......ka dage da qarfin zuciya dana damtse sai daka fanshi wannan ruhin da baisan soyayyar kowa ba saita 'yan uwansa......ka nuna sadaukantaka da jarumta har sai daka yaudari zuciyar marainiya ameenatu......wallahi na sallama......sabreen ta sallama maka,ta mallaka maka......ta kuma miqa wuya.........na baka dukkanin soyayyata dari bisa dari......ka cinye yaqin.....kayi nasara......na karbi faduwar ta wannan bangaren muddin wannan shine faduwar......ka mamaye DUNIYATA ka sabuntata da irin DUNIYAR kowanne mutum.....nima kaine DUNIYA TA" ta qarasa fada tana kallon zara zaran yatsunsa masu farare qal din farce kaman baya taba komai dasu.

Motsin da ya dan sakeyi ya sanya gabanta faduwa

"Idan yana jin duk abinda kika fada fa?" Wata zuciyar ta gaya Mata,saita fidda idanunta dukka waje tana miqewa da hanzari a ranta tana cewa.

"Da na gama jin kunya".

"Ina zaki tafi kibar zuciyar da kika gama lugiguitawa?" Muryarsa ta daki kunnenta me dauke da alamun bacci yatsunta na cikin wanda yaci nasarar cafkesu sanda take juyawa zata fice.

Zare idanunta dukka tayi gabanta na harbawa,kada dai ace yana jinta?.

"Zan iya cewa kunnuwana sun manta dajin wata kalma me dadi a rayuwarsu irin na yau......karki tafi ki barni cikin wayen wadannan kalaman" Yayi maganar yana saukowa daga kujerar sannan ya sakar mata hannum yana takowa bayanta.

Kane kane yayi a bayanta yana rungumota ta baya ta hanyar aza hannuwansa saman ruwan cikin ta. Ya cusa hancinsa ta wuyanta yana zuqo daddadan qamshinta daya soma aike saqo sassan jikinsa da wani irin hanzari
(Karki raina turare,kada ki rabu da turare amatsayinki na matar aure,duk yadda zan gaya miki rawa da muhimmancinsa a wajen matar aure ba zaki gane ba......amma hatta da sha'awa turare yana tayar da ita,musamman irin masu sanyi da laushin qamshin nan,amma ki lura,akwai inda za'ace ki kama kalar qamshi guda da mijinki xai ganeki dashi,tom wani.namijin ba haka yake ba,wani yafison kullum da kalar da zaiji a jikinki,bayason kala dayar nan,saiki fahimci mijinki wanne iri ne).

"Sabrrrrr" Ya kirata a rikice yana jin wannam feeling din da yakeji a kanta yana taso masa.

"Hamma" Ta amsa masa itama idanunta a lumshe tana jin yadda saukar hannunsa a jikinta yake haifar mata da wani irin yanayi me wahalar fassara.

Magana yakeson sakeyi mata amma ya kasa,sai kawai ya fara tattara hijabin zai rabata dashi. Hannunsa ta riqe sannan a hankali taja baya,ta tattare hijabin da kanta ta zameshi daga jikinta ta wurgar dashi gefe daya.

"Ya subhanallah" Ya furta bakinsa yana rawa. Zai iya cewa bai taba ganin sanda tayi masa kyau irin yau ba,tayi ado sosai da gashinta irin yadda yakeso ya gani. Kowacce boyayyar sura ta jikinta ta bayyana yadda yake da muradin ya gani,kafin ya qara kowanne motsi ta qara sanda bashi mamaki ta hanyar balle hannuwan rigarta suka zame ta saka hannunta da kanta ta zare rigar zuwa qasa sannan ta fara takowa har inda yake ta iskeshi.

Wani irin mahaukacin tarba yayi mata cikin tsananin yunwarta,yana jin kamar yau ne rana ta farko daya fara sanyata cikin idanunsa,martanin data soma maida masa ya sanya yaji bashi da wata jarumta sam,yana gudun suci gaba da tsaiwa tsaf zasu iya zubewa,sai ya sauqaqa musu ya dauke abarsa ya qarasa da ita inda sukafi wayo.

Kirif ya rufe musu fuskokinsu da mayalwacin gashinta dake fesar da qamshin hair mist dinta. Gaba daya ya shiga wani rudani da bai taba shiga irinsa ba tsahon kasancewarsu tare. Komai yayi mata saita maida masa martani,duk inda ya nufa kafin ya qarasa tayi masa jagora,sai yaji kaman ya kurma ihu ko xai samu sassaucin dimuwar dame yawo cikin kwanyarsa.

Yanaso ya gaya mata ta sassauta saboda kada ta jashi yayi mata babban aiki,don yana iya jin dumin dake jikinta,amma inaaa ta qarasa dimauta kowanne tunani nasa,ba abinda bakinsa ke iyayi banda furta sunanta a jejjere da bada zazzafan kiss da karbar martani daga gareta.

"Ki soni sabbrrrrr......na rantse da Allah ni kadai nasan me nakeji a kanki......ki soni,zan miki komai....zan zame miki komai.....zan mallaka miki komai". Fuskarsa ta riqe sosai cikin hannuwanta tana dubansa,gaba daya kamanninsa sun sauya ya birkice sosai.

"Muhammad" Ta kirashi

"Fu'ad" Ta maimaita

"Muhammad jadda......ameenatu ta yarda ta soka......ameenatu ta yarda ta mallaka maka kanta da rayuwar ta,ameenatu ta zama taka har gaban abada....dakai da ameenatu yanxu duka abu daya ne.......ka gayawa kowa wannan cikin alfahari taqama isa da samun tabbaci"

Ya riga ya sallama,gaba daya ta gama susuta qwaqwalwarshi......yasan a yau kam duk wanda yayi kusa da yawa da dakinsa zai iya jin motsin da xai saka zargi a ransa,baisan me yake yi ba kaman yadda ya manta wayeshi. A lokaci ji ya dinga yi inama akwai wata duniyar ta daban da zai iya maidasu shi da ita?,duniyar da babu kowa saisu kadai?,wannan albishir daya samu daga bakinta......daga gari me tsarki yafi komai masa dadi da zame masa tarihi cikin rayuwarsa.

Wani irin dare suka raya,daren data sakar masa dukka ragamarta,ta cika masa mafarkinsa ta hanyar bashi kowacce gudunmawa da cikakken hadin kai,saiga muhammad fu'ad din yana mata kuka sosai kaman qaramin yaro. Kukan daya sake susutata itama,banda abune da ubangiji ya sanyashi ya zama sirri tsakanin ma'aurata......tabbas duniya data cika da mamaki idan akaga matashin zaki gwarzo irin muhammad jadda yau a gaban mace yana mata kuka har haka.

Ita kanta a rikice take,ta kuma aikatu sosai a hannunsa duk da controlling din kansa daya dinga qoqarin yi,kafin wani lokaci zazzafan zazzabi ya sake rafketa bayan amai data yi a jere har sau uku.

Abinda ya daga hankalinsa kenan,ya tsaftacesu shi da ita,ya kuma shiryata cikin abayarta me sulbi shima ya sanya jallabiiyyarsa,ya duba asibiti mafi kusa ya kirasu donsu dauketa aje a duba masa ita,don bayajin zai iya jure wannan zazzabin yaci gaba da taba masa ita.

Cikin mintuna qalilan motar al_ansar hospital ta iso suka wuce da ita. Baiko samu tsaiwa gaya musu ba,don kiran sallar farko kawai akayi,sai ya rubuta saqo kawai ya turawa Farooq.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

114



Ko na second daya bai barta ta matsa daga jikinsa ba,tana kwance cikin jikinsa da wani irin yanayi. Cikin kowanne numfashi da zai sauke ko zai fitar jinsa takeyi da wani irin maqalallen yanayi a cikin zuciyarta,duk bayan minti kadan sai ya tambayeta

"Ina ne kuma yake miki ciwo?,menene yake damunki?,me kikeso?" Ido kawai take lumshewa,don ita kadai tasan me takeji cikin qasusuwanta,saidai tana qoqarin nuna masa all is well saboda ta fahimci a gigice yake,amma duk da haka bataga nutsuwa a tattare dashi ba,kaman me gani har hanji,ya fahimci duk wani motsinta.

Yanayin zazzabin ya sanya suka fara bata taimakon gaggawa a daki na musamman,kafin daga bisani su fara gudanar mata da test har kusan kala biyar suka tafi kan zasu dawo da result din.

Sanda tayi farkawa na biyu bayan tayi sallar asuba gari ya waye sosai,kusan goma saura na safe. Shine mutum na farko data fara gani,fuskarsa ta fito fes yana zaune daga gaban gadonta yana jan tasbaharsa,lokaci lokaci yana duba saqonni a wayarsa.

"Sabahal khair muffin" Cikin ba zata muryarta ta sauka a kunnensa. A nutse ya daga kansa ya sauke mata idanunsa. Itama shi take take kallo da fararen idanunta murmushi na fita daga fuskarta.

"Muffin?......thanks ny world" Ya fadi sunan data bashin yana masa wani mugun dadi.

"Sabahannur......khaifa asbahti?" Ya fada da tataccen larabcin da kana ji zakasan yasan qa'idar kowanne harafi a cikinsa yana nutsa tafin hannunsa cikin nata.

"Asbahatu bikhair walhamdulillah" Ta maida masa da murmushin nan nata data tsinceshi saman fuskarta.

Kansa ya langabe gefe guda kaman wani qaramin yaro,fuskarsa a narke yace mata.

"I'm scared that am going to loose you,i know it's stupid,but i just can't stop thinking about it" Murmushi ta saki tana danjin nauyinsa kadan

"Ka wahalar dani ne kawai......you won't lose me,am not going anywhere in sha Allah". Riqe hannunta yayi sosai cikin nasa.

"That's my wish in sha Allah,you're the most important thing in my life" Sosai maganganunsa suke sake samun mazauni a zuciyarta,maganar amna data taba fada mata ta dawo mata fes akai.

"You're the luckiest woman da kika samu hamma na" A yanzun take sake tabbatar da maganganun amnan,duk da a baya ta qaryata hakan.

"Have your breakfast and then brush your teeth" Idanu tadan bude kadan tana kallonshi kafin ta sauke dubanta kan jerin kayan breakfast din daya jawo gabanta saman dan wani gado.

"Ehnnnn" Ya fada yana dage mata girarsa,ya fahimci akwai abinda takeson fadi.

"Brush din xai zama first ko?" Kai ya girgiza

"No.....Brushing teeth after breakfast helps remove food particles and maintain oral hygiene" Shuru tayi murmushi na qwace mata,ba a banza ba takejin su musaddiq na gulmarsa. Komai nasa yasha banban dana kowa,tsare tsarensa ba irin na mutane bane.

A jikinsa ya ajiyeta,ya dinga qoqarin bata breakfast din amma ta kasa cin komai a ciki. Iya black tea kawai ta dinga kurba,tana sha yana kallon fuskarta yana qarfafa mata gwiwa,a haka tasha rabi da qyar. Saidai tana kammalawa ya dawo duka,ta wankesu tsaf da aman shi da ita.

Hankalinsa tashe ya danna wani guri,qasa da second sha biyar wata nurse ta iso. Zata karbi gyaran wajen ya dakatar da ita da harshen turanci.

"Barmin zan gyara,aman nan da takeyi ne banaso,inaso shima ya tsaya ko ya tafi,ya kamata abinci ya tsaya a cikinta hakanan".

"Likita yana dab da shigowa da dukka result na gwajin da akyi mata,sai a sannan zaa san abinda ya kamata ayi mata,amma yanzun xan sake saka mata ruwa don kada jikinta yayi rauni da yawa".

Yana tsaye a gefe ranshi a jagule ta gama mata komai sannan ta fice,koda ya matso sai ya samu har bacci yayi awon gaba da ita. Ajiyar zuciya ya sauke,yana jin kamar ya dawo da ciwon jikinsa,agogo ya kalla.....yau din juma'a ce,yanason samun sahun gaba gaba a masallacin ma'aiki,duk da zuwa yanzun ma yasan ya makara,baya ga haka akwai wani al'amari me muhimmanci da zai aiwatar a can din,wanda bayajin akwai abinda zai sanyashi jinkirtawa ko dakatawa a wannan ranar ta juma'a. Rana ce mafi dacewa daya aiwatar da al'amarin. Idan yace zai koma gida ya shirya ma ya bata lokaci,don haka ya daga waya kawai ya kira farouq.

"Ka turo saddiq ko musaddiq......ina buqatan Friday attire please".

" Ina kusa da hospital dinma......but bari na koma na duba maka kayan...."

"Thanks dude"

"Don't mention it....ya jikin nata?" Dubansa ya mayar kanta sannan yace

"Alhmdlh....she's sleeping,inaso naje mosque ne na dawo kafin ta farka"

"Zaa kula maka da ita dude....kada ka damu,dukansu na barsu suna shiryawa zasu taho nan"

"Alright" Ya fada a taqaice yana ajiye wayar.

Ba jimawa farouq ya qaraso,dauke da wata leda me kauri. A nan parlor din dakin ya zauna,shi kuma ya wuce ciki inda gadon sabreen din yake.

Cikin qanqanin lokaci ya shirya,Moroccan jallabiyya ce fara tas me asalin tsada me adon gold din zare,sai zagayayyar hular nan irin ta larabawa wadda set ce tare sukazo da hular da loafers din dake ciki iri daya. Wani irin sassanyan kyau ya aje,saika dauka balaraben Morocco dinne,ya matsa inda take kwance tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login