Showing 273001 words to 276000 words out of 363280 words

Chapter 92 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1463

rage.

"Me yasa a kowacce rana kake sake karantar zuciyata?,me yasa a kowacce rana kake abubuwan da suke sake haukatani a kanka muffin?". Idonsa ya lumshe yana budesu duka a lokaci guda. Yanason irin wannan yanayin.....yana son irin wannan lokacin da zaiyi zaune kawai a gabanta yana tana tona masa asirin zuciyarta.

"Sabrrrrr" Ya sake kiranta a tausashe.

"Haqqina ne.....kuma cikar kamalar kowanne d'a namiji kenan,ya karanci wace matarsa.....me tafi so?,me tafi buqata?,me zaiyi ya mallaketa?". Mallakar daya fada ta sakata fashewa da dariya tana zaro ido.

" Hamma.....mallakata kakeso kayi?"

"Nama mallakeki duniyata.....na mallakeki....kedin tawa ce ni kadai har abada" Ya fada yana daga yatsunsa guda biyu.

"Gidan marayu.....gidan gajiyayyu.....yaran da iyayensu suka mutu suka barsu kuma babu me tallafa musu irinmu" Takai qarshen maganar muryarta tana karyewa.

"Ki zauna ki tsara dukkanin burinki akan wadannan gidajen". Ya fadi yana miqewa tsaye. Wani irin sanyi taji yana sauka saman zuciyarta

"Ina fata ubangiji ya lullubeka da dukka rahamarsa......ya yaye maka damuwarka.....ya kyautata qarshenka.....na gode da karamcinka karimin mijina.....na gode da wannan halin dattako naka uban 'ya'yana". Murmushi me sanyi ya kubce masa,yanajin alfahari da wannan addu'ar tata.

"Allahumma ameen matata 'yar aljanna.....amma saura abu daya da baki roqamin ba". Idanunta ta juya,abinda ya sake tafiya sosai dashi

" Me kenan muffin?"

"Baki roqi Allah ya qarawa wannan ameenatun so na ba.....so nake ameenatu ta soni fiye da yadda takeson kanta,don kuwa ta samu wanda zai kula mata da kan nata" . Kunya ta sakata sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta kafin tace.

"Inda ana iya bude zuciya ko qirji a nunawa wani.....tabbas da na bude maka tawa zuciyar kaga abinda yake ciki a kanka,wataqila zakafi gasgatani.....don maganar fatar baki tayi kadan" Rasa me zaya ce mata yayi,sai kawai ya tsugunna yana kissinh forehead dinta a tausashi.

Yana dauke labbansa tana daga idanunta da sauri,sai ta soma rarraba idanun nata tana a narke.

"Kai.......ina doughnuts dina?" . Dubanta yayi

"Wanne doughnut?". Ya tambaya yana tunanin ko mafarki tayi a dazun kafin ya tashera. Tambayar tata da yayi sai taji kaman zata saki kuka

"Doughnuts dina mana da ma'u ta bani......a nan fa na ajjiye naci kadan na ajiye sauran". Qaramin murmushi yayi.

"Kin cinye madam....ni na tattara kwalin na zuba a dustbin". Idanu ta waro waje tana dubansa sosai da salon rigima a muryarta.

"Ka sakamin a shara?,wallahi ban cinye abuna ba,akwai saura" Ta fadi tana miqewa zumbur gami da nufar dutsbin din. Da mamaki yake binta da kallo ganin yadda ta bude dustbin din tana ciro kwalayen.

"Kai?,ka cinyemin?" Ta fada cikin sanyin jiki hawaye yana taruwa cikin oily eyes dinta. Dariya ma abun ya bashi,ya daga hannunsa alamun surrender yana dubanta.

"Innalillahi,Allah ba ruwana,sanda nazo ba komai a ciki sai boxes din da leda". Dariyar tasa ta qular da ita,sai kawai ta fashe da kuka tana sakin boxes din.

"Wallahi kaine.....kaine ka cinyemin kuma bazan yarda ba" Mamaki sosai ya kamashi ganin yadda ta zube tana kuka bilhaqqi,hawaye shabe shabe ta dage wai shine ya cinye mata. Da sauri ya isa inda take yana miqa mata hannu.

"Yi haquri ki tashi.....eh na yarda nine na ci". Ya fadi hakan don ya lura qaryata ba shine yaci din bama qular da ita yakeyi.

"Dama kai dinne ko?" Ta fada tana watsa masa harara da jiqaqqun idanunta,sai ta sake fashewa da kuka sosai kaman wadda aka yiwa dukan tsiya harda shashsheqa.

Ya rude sosai don ta maida abun serious matter. Ya sulale ya tsugunna a gabanta yana cewa.

"Am really sorry my world......taso muje ki gayamin a inda aka siyo a sake nemo wani". Sai data galla masa harara sannan tace.

"Kaduna.....kaduna ne wajen maman ummi".

"Kaduna?" Ya maimaita.

"Eh" Ta fada cikin son jiran mutum yayi wani abun ta sake barke masa. Kansa ya daga ya kalli agogo yana duba lokaci. Qarfe goma na dare,wa zaya tasa zuwa kaduna yanzu. Idonsa ya mayar kanta,saiya taras ta zuba masa ido tana kallonsa,dukkan alamu kuma sun nuna rigima ce a kwance idan ya musa.

"Is alright.....bani details na masu abun".


"0803 049 9555,wallahi tunda ummee ta haifeni ban taba cin doughnuts me dadin nata ba" Ta fada bilhaqqi da gaske har zuciyarta tana jin tun kafin ya kawl ma yawunta ya tsinke. Idanu warwaje yake kallonta. Tashin hankali!,ya fadi saboda yadda yaga tsaf ta haddace number,yaushe hakan ta faru oho shima bai sani ba.

"Ina zuwa" Yace mata yana takawa a hankali yana sauka qasan. Shi kam yasam yanzu ba lallai a bawa jadda wings daman tashi ba,kafin ma su nemo umarni,pilot din ya isa su tashi ai asuba yayi,saidai duk da haka bai fasa kiran number din ba.

Ainihin sunan daya fito ameena sai yaji kimar me number ya qaru a idonsa tun ba'a daga kiran ba. Bugu na uku aka dauka da cikakkiyar sallama ya amsa shima.

"Am sorry,na kira late at night......i don't know ko matar aurece.....am sorry idan hakanne"

"Ba komai" Matar me kirki ta fada. Bayanin dalilin kiran yayi sannan ya dora.

"If possible goben zan aiko a taho dake,kizo kiyi mata sai a maidaki.....kiyi naming price dinki,kada ki damu ko nawa ne ki zaba i will pay it". Murmushi tayi.

"Ba matsala.....ko goben da safen ma ana iya samun ko pieces nawa takeso.....akai akai sai a dinga zuwa ana karba mata,Allah ya raba lafiya,kowanne ciki da yadda yake zuwa ma mace,sai haquri". Yaji dadin magananta sosai,don daga yanayinta ya fahimci ba yarinya qarama bace,yayi godiya sannan ya kashe ya kira farouq.

Bugu daya ya samu farouq,da alama bacci ya fara daukansa ma.

"Farouq akwai matsala fa" Maganan da ta saka farouq miqewa ya zauna

"Me ya faru?" Ya tambaya. Ajiyar zuciya ya saki ya masa bayani a nutse.

"I don't know ina zan samu doughnuts?.....kune masu zuwa irin guraren nan".

"Ba damuwa......bari na duba wani guri kusa damu......sun iya sosai zataji dadinsa".

"Thank you dude.....you save me" Ya fada yana dan dafe goshinsa sannan suka yanke kiran.

Lallabata ya dinga yi har aka gaya masa ga saqo daga bakin gate. Sanda yaje har farouq din ya aje saqon ya juya,ya yaba masa sosai irin saurin da yayi don duka duka mintuna talatin ya iso,ya tabbatar wannan gudun nasa ya zuba.

"Ga doughnuts din" Ya fada da murmushi yana aje box din a gabanta. Da zumudi ta jawo ledar ta bude. Tun a yanayin packaging din ta tabbatar akwai matsala,banbamce babance take gani iri iri da wancan,ta danne tana bude doughnuts din.

Kanta ta daga ta kalleshi,ya dage mata gira yana qoqarin lallabata,can qasan ransa yana fatan kada ta ballo rigima kuma.

Kanta ta mayar kai,ta gutsira tana kaiwa bakinta. Taunawa daya biyu ta furzar,muryarta tana rawa ta kalleshi

"Wannan bashi bane.....Allah bashi bane".

" I know sabrrrr.........kiyi haquri kici wannan din,i promise you da safe wancan din zakici as breakfast"

"Really?" Ta tambaya tana tsareshi da idanu.

"In sha Allah" Ya fada yana bata assurance. Hankalinta taji ya kwanta,amma duk da haka ta ture wancan din

"Banasonshi....nata yafi dadi yafi madara" Dariyarsa ya boye,yana mamaki ashe da gaske masu juna biyu suna haka?,idan madara takeso suna da ita kala kala har sai ta ture,amma ya tabbatar yace tasha din ba sha zatayi ba.

&Tun sanda amna tabar dakin sai taji ta gaza nu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tsuwa sam sam,hankalinta ya kasa kwanciya,itama sai ta samu kanta da rashin nutsuwa da kokwanto.

Toilet ta wuce,ta daura alwala,ta dawo ta shimfida abun sallah. Raka hudu tayi ta zauna ta fara karanta hasbunallahu wani'imal wakil qafa dubu. Ko kadan batajin bacci a idanunta,haka kuma batasan meye ya dauke baccin a idanunta ba.

Bayan ta gama ta sake gyara tasbaharta. Bismillah hirrahamanir rahim 450 ta karanta,sannan tayi salati 450 shima. Bayan ta gama ta karanta (Allazina qala lahumunnasu innan nasa qad jama'u lakum fakshauhum fa zadahum imanan wa qalu hasbunallahu wani'imal wakil zuwa fanqalabu bini'imatimminallahi qafa 45(ko 450 idan zaka iya),ta sake karanta salati 450,sannan ya azizu ya khafi ya qawiyyu ya ladifu 450,duk inda takai guda 100 saita tsaya ta jaddada roqonta ga Allah,neman tsari daga dukkanin wani mummunan abu ko abun qi da zai iya samunta ko ya samu wani cikin ahalinta,ta sake zurfafa addu'ar samun albarka da sanya albarka a dukkanin wadannan aurarraki da akayi dama wadanda suka wuce.(addu'a ce me kyau da tsananin tasiri wajen samun biyan buqata wajen Allah,in kin zama me riqe addu'a da barwa Allah lamuranki kin huta da gasken gaske,shi zai miki komai daidai da yadda ya dace dake,sadaka ce na baku sai a sanyani a addu'a,ubangiji ya bamu dacewa).

Shafa addu'ar tayi tana jin wata nutsuwa tana saukar mata,ta miqe a nutse ta shirya don wucewa gurin abba. Sai data gama shirin sannan ta zauna saman stool,ta debo ruwa a wani babban mug ta soma karanta ayatulkursiyyu qafa ashirin da daya ta fita da mug din a hannunta.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



138


Zuwa takwas da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.

Yau din sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing me daukar hankali.

Sau daya tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya sauya.

Qugunta ya kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss.

Bakinsa ya zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa.

"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa. Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata 'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da sauri.

"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya fadi yana sake hade bakinsu guri daya.

Wani yanayi ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.

"Your lips are the ones.....i want to kiss forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar dashi.

"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu. Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.

"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja kafin ya lakuce mata kumatu.

"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up.

Lumshe idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY KABO DAUGHTER.
(Kunsan ni ma'abociyar son qamshi ce=??,na muku tallan turarukan matar nan TASTED AND TRUSTED ne,duk irin turaren da kike siya ina baki shawara ki gwada nata,yayi yayi yayi,zaki kuma bawa wani labari,muddin kina da dama amma baki siya ba ina me tabbatar miki kin loser=??=??,confirmed=?L?
"Saboda kai ne muffin......saboda kai ne". Idonsa ya lumshe yana sake zuqar qamshin,har cikin zuciyarsa yake sauka,wani nutsuwa qamshin yake bashi,kamar wadda aka tsoma a bahon turare.

"Kiyimin rai please sabrrr" Ya fadi yana sake cusa kanta tsakanin dukiyar fulaninta.

"Name?" Ta tambaya tana murmushi.

"Don Allah kada ki bari wani yaji wannan qamshin idan bani ba". Ya qarasa maganar yana dago kansa gami da sanya idanunsa cikin nata don ta gane har ranshi,da gaske kuma yake maganar.

Tafukan hannayenta dasu kansu qamshin suke ta saka tana dago kansa sosai. Zuwa yanzun tuni ta fara fahimtar yanayinsa....da yayi magana ko baiyi ba....idan yayin daga ina ta fito?.

"Muffin.....kana tunanin zanbar wani hanci ko wani d'a namijin daban bakai ba ya samu wannan nutsatsen qamshin?.....har abada idan kace bakaso ko farfajiyar gidan nan qamshin nan ya fita bazai fita ba......a yanzun hatta da rai ka bani DUNIYATA......Ka bani rai tunda ka kusanto da makusantana kusa dani......dame ne zan saka maka ni ameenatu?" Ta qarashe maganar zuciyarta tana karyewa da wani irin rauni.

Idanunshi cikin nata ya dora hannunsa saman mararta.

"Kin gama sakamin ameenatu.....kin gama sakamin sabreena.....kin gamamin sakayya duniyata da kika bani iri.....yara uku fa?,lokaci guda?,a qaramin lokaci har haka?,kika cikamin muradin zuciyata?......abu daya ne ya rage kiyimin,karki guje ni tsanani ko dadi.....karki bari tarbiyyar yarana ta zama abun Allah wadai......ki soni irin son da ba wanda zaki bawa katankwacinsa.....that's all" Ya fada yana dage hannuwansa sama.

Hannunta ta saka daga qeyarsa sannan ta hade goshinsu guri daya suna musayar numfashi.

"Ka samu muffin.....ka gama samunsu.....amma zan qara da addu'a ga Abba......mutumin da yayi sanadin haifamin irin wannan mijin.....ubangiji ya jiqa kabarinsa ya kuma lullube kabarin nasa da dukkanin wani nau'i na rahamarsa"

"Allahumma ameen" Ya fadi muryarsa qasan maqoshi yana sake jin ta masa kima sosai.

"Abinci ko wanka?" Ta tambayeshi ba tare data dauke goshinta a nasa ba still kuma tana zaune saman cinyarsa.

"Cin abinci sannan kazo kayi wanka yana raunana jiki my world" Idanu ta fitar tana dubansa bayan ta janye fuskarta.

"Muffin.......da gaske komai naka dabanne,tsarukanka dabanne kaman yadda naji ana gulmarka......kasan duk wani abu da zai kiyaye lafiyarka"

"Wait" Yace yana hade ransa da wasa.

"Wake gulmata?,farouq ko?" Dariya sosai ta kubce mata har tana sake riqeshi don kada ta fadi.

"Komai farouq?,komai farouq?.....BB ya kusa hutawa dai,nasan fannarshi zata siya masa 'yanci". Murmushi shima yayi yana kama hannunta suka miqe,shi kansa baisan ya wannan ranar zata kasance ba.....kowa ma ya shiga uku.

Tsaf ya janyeta suka shiga wanka kaman yadda rules dinshi yake,har ya fara zame mata jiki,ya gaya mata sunna ce kuma bazai gaji da rayata ba,don duk wanda yayi koyi da wani abu cikin abinda manzan Allah yakeyi da zummar koyin yake dashi,to tabbas yana da ladan koyi dashi.

Cikin wasu sauqaqan couples pyjamas suka shirya dukkanin farare da adon black wuya da hannu da qafan wandon da bai qarasa idon sahu ba. Kamar wasu ma'auratan daga wata qasar,suka sauka qasa tare.

Bayan kammala cin abincin basu kwanta ba,dukka maganganu ne da shirye shiryen biki yaketa fama. Itadai tana gefe tana kallon zallar aikin zumunci irin ma fu'ad din,ta sake tabbatarwa bawai a banza Allah yaa sanya wannan dukiyar a hannunsa ba(Tabbas idan har Allah ya baka wadata fiye da sauran abokai ko 'yan uwanka,to ya baka ne don ka taimakesu,wala'alla duka harda arziqinsu ya saka a hannunsu don ka zama.silar ciresu daga matsi ko matsala,Allah yana sonka da yayi maka wannan baiwar,don zaka samu lada sanda kake basu ita ta hanyar data dace,don ka zama kamar wakilin Allah a bayan qasa,idan kuwa ka riqe ka hanasu yana kallonka.....tabbas! Kuma sai yayi hukunci akai, 'yan uwa dukiyarka kenan fa.....inaga wanda zai danne haqqin wani?,ina ga wanda zai cinye dukiya ko gumin wani?,Allah yasa mu dace,ya rabamu da taba abinda ba namu ba ya hayyu ya qayyumu).

Ganin ta langabe masa zata yi bacci ya katse maganan da yakeyi da kowa ya dubeta.

"Gate up ameenatu.....naga list na amna.....ke banga naki ba" Ido ta zaro,cikin muryar soma jin bacci tace

"Muffin.......nawa name?"

"Naki lefan.....naki lefen sabrrrr" Ya fada yana kama hannunta.

"Banda wanda akayimin hamma?" Ta tambaya tana dan dariya saboda ta dauka zolaya ne. Kai ya girgiza.

"A yanzun ke din cikakkiyar zabin MUHAMMAD FU'AD JADDA ce,sabon lefe sabon sadaki daga hannun jadda" Ya fada yana zame hannunsa a nata. Qasa ya saka hannunsa ya fiddo wata kyakkyawar leda ya zube kayan ciki.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login