Showing 240001 words to 243000 words out of 363280 words

Chapter 81 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1430

K'arfe tara na safe a nan ta yiwa alhj hamza kibiya.....musaddiq da saddiq da sauran guards na fu'ad wadanda suke gida da wadanda suke kan hanya sanda abun ya faru. Iya su uku suka shigo,don ko amna ya hanata zuwa asibitin gudun kada su hadu suyita yiwa mutane kuka.

A sannan anni na gaban gadon sabreen din,tana ta neman yadda zata sanyata taci wani abun komai qanqantarsa.

Karon farko da magana me zurfi ta hada alhaji hamza da sabreen. Shi ya tsaya kan saita saka wani abu a cikinta. Tana kuka hawaye daya bayan daya haka ta dinga karbar tea din daga hannun momma bahijja wadda ta shigo daya baya.

Sai data soma yunqurin dawo dashi sannan ta barta,ta wuce da mug din ta daurayeshi sannan ta dawo dashi ta ajiye.

Shuru ya ratsa dakin na wani lokaci,kowa ka kalli fuskarsa cikin nazari da kuma alhini yake. Alhj hamza ne ya fara magana.

"Toh.....bamu da abinda zamu cewa ubangijinmu sai godiya.....kafin ya jarabcemu da wannan ya mana tarin baiwa da ni'imomin da ba zasu irgu ba....cikar iko da adalcinsa ne ya jarrabi bawa akan dukkan abinda yaga dama a sanda yaso.....to mu ba zamu butulce masa ba,alhamdulillah da duk yadda yayi damu......mun tattauna da masu ruwa da tsaki cikin sha'anin tsaro na qasar nan dama maqwaftanta,kuma suna bamu tabbacin lalubo inda suke ko wani abu daya shafesu cikin qasa da awanni ashirin da hudu in sha Allah......su kansu guard da suke aiki qarqashinsa dukkaninsu basuyi bacci ba,ba wanda ya zauna ko ya kwanta,aiki suke akan batun ba qaqqautawa....kuma ana samun haske sosai,su kansu na yadda da qwarewarsu in sha Allahu komai zaizo cikin sauqi" Ya qarasa maganar yana basu tabbaci a maganarsa dama fuskarsa.

"Ubangiji ya amince....Allah ya bayyana gaskiya a duk inda take" Momma ta fada cikin sanyi jiki da tashin hankali. Sunan sabreen ya kira,ta amsa masa ba tare data iya dubansa ba,don kuwa ita kadai tasan abinda takeji.

Nasiha sosai yayi mata me ratsa jiki da hankali akan imani da qaddara da daukarta.

"Zan dauka abba in sha Allah.....zan dauka" Ta fadi kawai tana sauke idanunta saman tafin hannunta daya wani qara dashewa yayi haske kaman ba cikakken jini a jikinta.

Da daya da daya suka fara juyawa suna fita.

"Saddiq" Ta kirashi abinda ya dawo da hankalin anni kanta don wNi abune da bata taba yi ba. Shima a mamakance ya juyo yana kallonta,sai ta sanya hannu ta yafitoshi.

Dawowa yayi a nutse,y jawo kujerar da momma ta tashi akai ya ajiye daura da ita.

"Gani adda" Ya fada yana mata duban mamaki.

"Akwai labari da nakeso na fitar kashi uku......kashi daya gidan tv radio dana jaridu......kashi biyun da yayi saura tv radio ne kawai zaiyiwu su haskashi" Ta fada tana dubansa.

Magananta taja hankalin anni,ta kuma tuna mata da duk tattaunawarsu da maamah ta jiya. Sakin kayansu da take kwashewa tayi wanda za'a koma dasu gida,ta tako a hankali har inda suke.

Duban saddiq anni tayi fuskarta ba walwala

"Tashi kaje parlor.....idan na gama hada kayan zan kiraka" Fuskarsa da mamaki da kuma wani zumudi nason jin qarashen maganarsa da sabreen ya miqe,saidai babu yadda zaiyi anni ta katsi hanzarinsa.

Inda ya tashi ta koma ta zauna tana duban sabreen.

"Wanne labari zaki fitar sabreen?"

"Yadda akayi uwa ta zama me dillancin yaronta don kawai ta mallakeshi......yadda wata uwa ta zama azzaluma wadda batasan ciwon 'ya'yan cikinta bama bare na wasu....yadda wata uwa ke burin murqushe 'ya'yanta ta gaji abinda suka bari......yadda akayi sabreena ta zama matar muhammad jadda ta hannun mahaifiyarsa" Sabreen ta fadi muryarta nason karyewa amma tana bawa kanta da kanta qwarin gwiwa,tana jin babu wani abu da zai hanata aiwatar da wannan abun,daga nan zuwa dare muddin bataji komai dangane da muhammad dinta ba. Koda sabreen bata fayyacewa anni komai ba.....annin da kanta ta gama fahimta.....wani tsohon zargi da shakkunta kan maamah lokacin aurensa shine yakeso ya tabbata bayan wani lokaci.

"Akwai kuskure cikin aikata haka sabreen......kinsan wanne kuskure?" Anni ta tambayi sabreen tana son qwato hankalinta da nutsuwarta,domin kuwa ta hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idanun sabreen din masu kaifin gaske suna kai kawo.

"Mariya bata da asara.....domin kuwa tata rayuwar tazo qarshe idan aka dangantata da taku......mariya bata da wata asara me yawa,kece kike da jini a jika.....kace kike tara zuri'a yanzu.....domme zaki yiwa kanki wannan barnar?" Anni ta fada tana kallon idanun sabreen tanason taga iya dadin yadda maganar ta shigeta. Kai sabreen ta mirgina gefe....kamar anni ba zata fahimci nata shimfidadden takun ba.....wannan abun wani taku ne kuma tarko ne me kyau idan anyi amfani dashi ta hanyar daya dace......tarko ne da zata kama kowacce kurwa ta maamah din.

"Kinsan wace mariya ta gaske?,kinsan yadda me babban suna suka rayu?" Haka kawai taji tanason ta sakeji daga bakin anni,ta tabbatar koda shi ya gaya mata.....koda shi ya labarta mata bazai gaya mata yadda anni zata sanar mata ba,don haka ta kadawa anni kai a hankali tana dubanta.

A nutse anni ta warewa sabreen komai.....rayuwar fu'ad tun kafin tafiyar mariya da kuma tafiyartata,yadda ta samesu da irin wahala da tasha kafin ta maidashi kalar mutumin da yake a yau,duk wani qalubale da kuma gwagwarmayar rayuwa tasa.

Hannu kawai sabreen ta saka ta lullube fuskarta da tafin hannuwan nata,sai takejin a wancan ranar a Maldives tamkar bai gaya mata komai nasa bama.....kaman ba wani abu daya gaya mata daya shafi rayuwarsa. Ta yaya zata iya controlling hawayenta a fuskarta?,ta yaya zara iya.hana kanta zubar hawaye?,wacce irin asararriyar uwa suka samu?,wacce irin uwace wannan wadda da ita gwara babu?. Lallai ba shakka zatayi komai.....har fiye da abinda take hasashe a baya ma zatayi.

Amma da irin wannan abun nata har anni ke duban ta qyaleta?,me yasa anni ba zata fahimci cewa ita sabreen dama mutuncinta bararre ne a idanun mutane da yawa?......me yasa anni ba zata Fahimci zata iya saudar da komai wa fu'ad ba?,don don mutuncin nata da iyakarsa idanun fu'ad dasu anni?,duk da yafi qarfin D'A tunda wata yarda ce da sassanyan aminci ta samu a muhallin da yafi kowanne daraja.

"Ban gaya miki don kiyita kuka ba.....ban gaya miki don kiyita damuwa da sanya bacin rai ba.....na gaya miki ne saboda ki sani........ba kowanne mutum kake qarar da energy dinka a kansa ba". Kai sabreen ta jinjina tana sauke hannuwanta.

"Taso nayi tarayya da ita wajen raya zunibinta anni......ta kawoni da qarfi da yaji da'irar da ban shirya shigota ba.....saidai a yanzun ina kallon juyewar al'amarin daga sharri zuwa alkhairi...." A nutse itama ta gayawa anni yadda duka komai ya kasance tsakanin ta da maamah a wancan lokacin. Tayi shuru anni tana jin komai yana kwaranye mata,lallai duk inda xa'a qaunaci juna saboda Allah dole a dinga ji a jiki a duk lokacin da wani abu zai kasance da dayan biyun. Ashe ba'a banza ba ta dinga jin wani baqin abubuwa dangane da auren?,ba'a banza ba ta dinga jin rashin gamsuwa da komai?.

Al'amarin maamah sai taji yana sake girma a zuciyarta. Mamakinta tana jin kaman zai fasa ko ya kashe zuciyarta gaba daya.


*_WANI DARE!_*


Ranar ta kasance musu wani dare da dukkaninsu suka kwana suna juyayi da mutuwar mamaki kan halayyar mariya da komai nata.....daren ya zame musu wani dare da sabreen ta kwanta tana jin zata dan dagawa maamah qafa saboda anni data buqaci wurga lamarinta a kwandon shara abita da ruwan addu'a,saidai kuma wannan daren ya zama daren da yayi silar da sabreen ta soma sakin UPDATE akan maamah......wanda batayi tunanin akwai wani abu da zai dakatar da ita ba ko waye ko meye shi!.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


122


Har qarfe sha daya na dare anni tana zaune gaban sabreen,lokacinne kuma Dr mubeena ta gama daura mata wani ruwan daya zama shine abincinta yanzu saboda ba wani abu da yake iya shiga cikinta ya zauna,koda ya shiga dimma sai ya fito. Rubuce rubuce Dr mubeena ta kammala yi cikin file din sannan ta rufe,ta ajiye a gefe tana sanya idanunta kan sabreen dake kwance da shirin yin baccin da ta tabbatar qaryarsa ya shammaceta......saidai tasan zaizo ne kadai ta hanyar sinadaran da suka zubawa ruwan dake shiga jikinta,wannan ne kadai yake bata daman yin baccin daya kasance ba natural na qashin kanta ba.

Tausayi sabreen din take bawa Dr mubeena,tako wacce fuska ta kalleta tausayi take bata. Hannu ta miqa ta dauki abun gwajin BP din data gama gwada mata ta riqe a hannunta,tadan sakar mata murmushi wanda sabreen qarfin hali kawai tayi ta maida mata.

"Kiyi bacci sosai Mrs jadda......fi amanillah.....in sha Allah boss yana cikin aminci,Allah baya bari bayinsa na gari su wulaqanta kosu tozarta ko su wofanta" DR mubeena ta fada cikin kwantar mata da hankali. Murmushi ta tattaro da qyar ta samu ta maida mata martani,Dr mubeena ta kalli anni dake zaune gaban gadon kaman ko wanne dare tana riqe da tasbaharta.

"Yau ba checking din dare,BP dinta ya kusa dawowa daidai da yadda nake buqata,kuyi baccinku,idan Allah ya kaimu qarfe shida ko biyar da rabi zan shigo". Ta fada cikin girmamawa itama tana jin alhini har cikin qasusuwanta na rashin labarin komai akan fu'ad din. Murmushi kadan anni tayi tana sauke qafafunta daga saman kujerar,yau momma ta dage lallai a bawa anni 'yar tayin kwana ko huda ko ma'u. Ta karbi ma'u saboda ta matsanta dole gobe su wuce mali huda taje tayi ton print dinta duk da a goben zasu rufe.

"Sannunku da qoqari kuma,Allah yayi muku albarka"

"Ameen,Allah ya qara lafiya saida safe" Tayi musu sallama tana fita daga dakin.

Idanunta a lumshe suke kawai,ita kadai tasan me yake yawo tsakanin qirjinta da zuciyarta,a duk sanda kwanyarta zata harba da lafazin.

"Sun harbeshi.....ba'asan inda suke ba!" Sai taji kaman zata mutu......sai taji kaman ba wata tazara tsakaninta da tashin alqiyamarta. Takanji faruwar komai kamar a mafarki.....daddadan farinciki da wata iriyar tsaftatacciyar kulawa tana shirin rikida zuwa tashin hankali da firgici.....wannan kusancin tashin farko ya juye ya koma kewa da tsananin buqatar makusanci izuwa zuciyarta.

Duk dare kafin alluranta su dauketa zuwa duniyar bacci.....duniyar dasu Dr mubeena suka matsanta mata zuwanta badon son ranta ba.....sai rayuwarsu tsakanin Maldives da madeena tayita dawo mata tamkar a faifan CD,takanji inda ana maida hannun agogo baya tabbas data maida.......tabbas data hanasu dawowa nigeri da tana da masaniyar ibtila'in da zai fada musu kenan.

Tun tana iya jin muryar anni da ma'u sama sama har ta daina ji,ganinta da ruhinta suka koma zuwa ga wanda ya yisu nadan wucin gadi.

Shuru da anni taji ma'u tayi shi ya bata tabbacin bacci yayi awon gaba da ita,saita gyara zamanta saman kujerar tana ci gaba da jan tasbaharta,tunanuka kala daban daban suna hana idanunta tafiya duniyar barawo wato bacci da itadinma duk dare satarta yakeyi,bata kuma fiya dogon zango ba yake sakinta,takan farka da mafarki ki razani duk dare,saidai ko sau daya bata taba farkawa ba ba tare da ambaton hasbunallanu wani'imal wakeel a bakinta ba.

Batasan baccin yayi awan gaba da ita ba,har tasbhar hannunta ta sulale ta fadi da hasbunallanu wani'imal wakeel data kasance ta qarshe a harshenta.

Dukkanin daukacin asibitin harda dakin ya dauki shuru,dare ya fara nutsawa awanni suna gudu......a irin lokacin da bayinsa nagartattu ke neman kusanci dashi saman darduma,ashararan mutane kuma suma ke nasu aikin saboda neman duniya da abinda yake cikinta.

Daya daga cikinsu ta samu nasarar kunnowa dakin,ta murda handle din a hankali cikin sanda. Sanye da suturarta ta dazu,suturar qarshe data shigo dakin dasu babu abinda ya canza,daidai da takalminta da kuma dan qaramin hijabin kanta,saidai a yanzu akwai baqin face mask saman fuskarta koma bayan dazu.

Kai tsaye ta wuce parlor din ta kuma tunkari dakin da sabreen ke kwance,ta saka hannu ta bude qofar dakin tana shiga. Daga bakin qofa ta tsaya,ta qarewa kowa kallo,ta kuma tabbatar dukkansu sunyi nisa a baccinsu. Ajiyar zuciya ta saki hakan yana bata nutsuwa da kuma qwarin gwiwar aiwatar da abinda ya shigo da ita,taci gaba da matsawa zuwa gadon da sabreen ke a kwance.

Daidai inda ruwan dake saqale a hannunta ta isa,ta tsaya ta zuba masa idanu. Bisa qa'ida ruwan yake diga kaman yadda ya dace,aiki biyu zatayi a ciki,ta gaurayashi da sinadarin dake aljihun rigarta,ta kuma qara gudun ruwan dake shiga sassan jikinta,wannan shi zai saurin hautsina tsarin jikinta,ya kuma taimakawa sinadarin wajen yin aiki a jikinta da gaggawa.

To amma ta wani bangaren tafison ta fara tabbatar da inda wayar take......wayar itace babban burinta na farko,wanda iya ita kawai idan ta mallaka kaman yadda akayi mata alqawari ya isheta kudin aikinta koda ba'a qara mata komai ba.

Ta tsakanin annin da sabreen ta wuce tana miqa hannunta locker gefen gadon,durqusawa tayi ta soma binciketa a hankali. Sai data hautsine komai bata ganta ba,wannan ya qara gudun jinin jikinta energy dinta ya qaru fiye da yadda ya kamata ya kasance. Tana bala'in son wayar,don itace cikar burinta. Miqewa tsam tayi ta sake wucewa ta tsakaninsu,hannunta gefe da gefen sabreen din ta soma lalubawa ko a nan ta ajiyeta.

Kaman wadda aka tasa ta dinga jin wani sauyin yanayi tattare da ita tamkar wadda aka canzawa muhalli daga wanda take ciki,jin hannu ta gefan kafadarta ya sanyata murmurewa daga yanayin bacci zuwa rayuwar zahiri. Baqon turaren da takeji a hancinta ya sanyata budewa idanunta qanqanuwar qofa da zata iya ganin wanda waye haka keda kusanci sosai a kusa da ita?.

Dr mubeena kamar take gani,amma kuma qamshin da yanayin nutsuwar sam ba ita bace......saidai a idanu a kallon dake a fusge tabbas Dr mubeena ce.

Tabo wayar da hannunta yayi ya sakata sakin ajiyar zuciya,ta saka hannu ta jawota ta jefata aljihun lab coat din jikinta,sannan ta fiddo hannun da syringe da wani irin ruwa a wata mitsitsiyar roba.

Tas ta soma zuqe ruwan a syringe din,wanda tana dab da kammalawa anni ta motsa bakinta dauke da HASBUNALLAHU WANI'IMAL WAKIL Tana shafa fuskarta da tafin hannunta.

Fitar hasbunallahu din ya daki qirjinta,ya kuma sabbaba mata faduwar allurar dama robar ruwan,abinda ya sake sakawa sabreen matuqar ankara da ita,ta sunkuya da sauri ta dauki syringe din qirjinta yana dokawa.

Idanu anni ta zuba mata a mamakance,duk da ta juya mata baya bata iya ganin fuskarta. Mamakin yadda suka canza tsari ne na Shigowar likita dakin mara lafiya haka kai tsaye?.

Kaman Dr mubeena take gani......amma kuma abun da mamaki,Dr mubeena da ta musu sallama sai bayan sallar asuba?,me ya dawo da ita?,kuma ta shigo dakin ba tare da sanin kowa ba?.

"Dr akwai allurar data rage ne?" Kai ta gyada mata kawai tana qoqarin qarasa zuqe ruwan a syringe din a gaggauce don ta qarasa cika aikinta.

Hakan bata samu ba kuwa,don hannu sabreen takai mata cikin shammata ta daki hannunta,da syringe din da ruwan sukayi gefe suka watse,abinda ya darsa wani abu da gaggawa a zuciyar anni,ta miqe sa wani irin zafin nama ta damqo kafadarta tana juyo da ita.

Kallon kallo suka yiwa junansu,tana shirin kubcewa anni,annin ta saka hannu ta yage face mask din fuskarta ta.

Baquwar fuska ce da bata santa ba.....kaman yadda ya bayyana fuskar bata Dr mubeena bace.

"Wacece ke?!" Tambayar da anni ta mata cikin madaukakim sautin tsawa daya qarasa farkar da ma'u ta miqe ta zauna sosai ta yunqura ta tashi.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login