Showing 171001 words to 174000 words out of 363280 words

Chapter 58 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1376

da anni ce kawai a dakin,annin ita ta karbi wayar saita miqa mata tana cewa.

"Hammanku ne......basu tafi ba kenan" Ba zata iya musu da annin ba bata kuma fita ba bayan ta bata wayar bare ta aje wayar yadda ta saba masa. Ta latsa ta sanyata a kunnenta,ta motsa labbanta a hankali tana amsa yin sallama.

Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar sautin sallamartata. Yayi jarumtar daidaita yanayinsa don bayaso ta fahimci komai,don yana son komai zai gaya mata ta daukeshi da muhimmanci.

"Ina kika shiga?" Ya mata tambayar a gajarce data rasa amsar da zata bashi. Shuru tayi tana kame kamen abinda zata gaya masa,bata samu ba har ya sake cewa.

"Kinsan tafiya zanyi yau really?" Can qasan zuciyarta tayi qaramin tsuka tana cewa

"To mene ruwana da tafiyarka?,ka wuce mana ta can ma karka dawo Maldives,amma a fili sai ta zabi jan bakinta tayi shuru.

"Alright......yayi kyau....ina wayar dana bawa amna ta baki?,baki dinne bata yi ba?". Ya sake tambaya da wani irin shan qamshi da bata taba ji ya mata ba,hakan sai ya mata kwarjini gami da taba zuciyarta.

"Ta bani" Ta amsa masa a hankali kaman wadda batason tayi magana. Amsan ta bashi haushi kadan,don shi daya yasan yadda ya matsu da jin muryarta amma taja wayar ta ajiye.

"Bakiga daman amfani dashi ba kenan?.....well....bazan miki komai ba a yanzun.....amma kika sake har na dawo na samu wayar a yadda na baki ita.....sai nayi punishing naki ta hanyar da bame iya karbanki......and idan ma kin bude kin fara using da ita....if kika ce zakimin abinda kikemin a wayar anni da amna bawai kin tsira bane.....take care of your self......byee" Ya fada yana sauke wayar. Sai a sannan yaji zuciyarsa ta koma daidai,duk da ba irin wannan sallamar yaso suyi ba,amma at least ya samu nutsuwa kadan. Bayaso ya fiya zafafa mata da yawa....don baida tabbaci ko yaqinin zuciyarta ta karbeshi,saidai ko meye yana da yaqinin bazai qyelata haka ba,sai yayi mata dashe da kuma ginin da bazai kankaru ba.

Wayar tabi da kallo kafin ta ajiyeta a gefanta. Sau tari idan yana wani abun sai zuciyarta ta dinga gaya mata plan ne kawai da siyasa irin ta 'yan kasuwa,kamar kawai yanaso yaci gaba da mata wayo yana amfana da jikinta ne. Har yanzu ta gaza gasgata kanta wai mutum kamar muhammad fu'ad da mutunci ko arziqi ba shine silar gamuwarsu ba ace dare daya don kawai ya amshi budurcinta ya koma haka ba. Kulawa qauna soyayya da wani irin mayataccen yanayi da bata taba ji ko gani ba. A duk mazan da sukayi alaqa dasu a baya bata taba ganin wani abu na musamman kebantacce tattare dasu irin wannan ba. Da gaske wannan shine son?,da gaske wannan din ake kira da soyayya ko kuwa yaudara ce zallarta?.

_to masu karatu ku bata amsa_


& *_Makka/Jeddah_*


Tafiyar awa biyar zuwa shida ta kaisu garin jedda,a nan ya tsaya yayi wanka ya saka hirami ya dauki niyyar umararsa. Daga nan kuma lafiyayyen train ya daukesu kai tsaye zuwa makka.....motar da aka tanadar masa ta qarasa dashi masauki cikin hotels mafi tsada dake dab da harami.

Fairmont makkah clock Royal tower nan ya zaba,ko maamah dinma yasa an maidata can,hotel ne dake da kusanci sosai da haram,kai tsaye daga dakinka kana iya hango ka'aba. Baida gurin sauka duk zuwan da zaiyi sai nan din,saboda samun kusanci da Allah da samun daman yin addu'o'insa sosai koda cikin dare ya farka. Sau tari yakan jima gaban window din dakinsa yana qarewa dakin Allah kallo,cike da shauqi da tsoron azabarsa da kuma fatan samun rahamarsa,yana jin inama yayi zamansa a nan ya qare rayuwarsa.

Nutsuwarsa da samun salamar ruhinsa daban yake jinsu a ransa duk lokacin daya shigo wajen,yana jin kansa sosai kusa da Allah,don haka koda ya iso wucewa yayi kai tsaye yayi dawafi da sa'ayi yayi sallarsa raka'a biyu ya sauke umararsa. Bai nema ganin maamah ba sai daya sauke faralin umran da bayajin zata isheshi. Zuwa yanzu baisan sau adadin nawa yayita ba.....bayajin kuma zai daina yin nata muddin da numfashi a jikinsa da kuma damar zuwan.

Dakinsa ya koma royal suit ya sallami abdulbasit da abdul gaffar da abdus sabur wanda su ya sanya suzo su zauna tare dashi. Hiraminsa ya cire ya nema wasu kayan ya sanya yana duba lokaci. Akwai gajiya sosai tattare dashi,yana buqatar ya hutawa kwanyarsa sosai don ya samu space din yadda zai iya tunkarar ko meye maamah zata zo masa dashi. Labulen dakinsa ya daga,idanunsa suka sauka akan dakin Allah,wajen tarwai yake da cikakken haske kamar kullum,da tarin bayin Allah masu neman duniya dama lahirar gaba daya. Bayason wani babban abu ya faru tsakaninsa da maamah a irin wannan wajen,dole yana buqatar neman taimakon Allah.

Nannuyar ajiyar zuciya ya sauke sanda fuskarta ta dawo masa tarwai cikin idanunsa. Idanunsa akan ka'aba din,ya sanya hannunsa saman qirjinsa ya dafe yana jin yadda qirjin nasa ya cika da soyayyarta,a hankali ya furta.

"Ya raheem......kada ka bawa mahaifiyata galaba a kaina muddin da sabonka da kuma son zuciya tazo". Sai ya dakata yana jan numfashinsa sosai.


"Ya ubangiji.....kaine mahaliccin zukata.... Kaine ke iya jujjuyasu a duk sanda kakeso,ya rabb,kafin kowa sanin menene abinda ke zuciyata na ainihi a kanta,ban aikata mata komai ba don na zalunceta ko na cuceta ba,ban aikata mata komai saboda qiyayya ko abisa sanina ba....ya rahman....ka sanya mata matsananciyar soyayyata a zuciyarta,ka sanya ta soni irin son da nagartacciyar uwa kewa d'anta......irin son da bashi da misali.....irin soyayyar da na jima ina fata da burin samu daga wajen macen aurena.....ya ubangiji,na gode maka abisa kowacce ni'ima da kayi a gareni.....na yadda cewa mahaifiyata itace jarrabawar rayuwata......na rasa soyayyarta soyayya ta ainihin da aka santa daga zuciyar uwa zuwa 'ya'yanta.....ya Allah yadda kayimin madadi da anni.....na roqeka kayimin madadi da ameenatu sabreen.....ka maidata sanyin idaniyata......Allah ka azurtani da salihan yara ta tsatsonta.....ka sanya albarka cikin kowacce tarayya da zanyi da ita....Allah ka wankemin idanuna da samun qarin 'yan uwa nagartattu bayan su musaddiq,wato yaran da ameenatu zata haifamin" Ya qarasa addu'ar labbansa suna sanyi,zuciyarsa tana jin wani irin sassauci da sauqi,a take kuma sai kewarta ta cikashi. Baisan me ya sanya dukkanin burinsa a yanzu ya fara karkatawa kan samun 'ya'ya ba......abune daya jima a ranshi,amma halin maamah da yadda ta watsar da rayuwarsu ya kashe wannan burin. Yana ganin duk macen da zai dauko ma haka zata kasance akan 'ya'yansa kaman yadda maamah tayi musu ta kuma yiwa abbansu.

Sakin labulen yayi a hankali,yana ji a jikinsa tamkar dukkanin addu'o'insa sun amsu,sai ya koma ya zauna bakin gadonsa yana daukan wayarsa.

Maamah din yaso kira don ya shaida mata ya iso,amma cikin rashin sa'a sai ya kasa samunta. Hakan ya masa dadi,don ko ba komai zai samu ya matse gajiyar daya debo,don haka ya aje mata tex kawai,sai ya tsinci kansa da neman layin wayar sabreen din.

Bai taba zaton zai samu wayar a bude ba,bai dauka zataji warning dinsa ba,amma ga mamakinsa dab da zata tsinke aka daga. Lumshe idanunsa yayi yana jin qarin wani sassaucin da rangwamen yana sauka a zuciyarsa,ya koma da baya ya kwanta akan gadon bayansa bayan ya sanya pillow qasan kansa.

Shuru kawai tayi tana sauraren iskar dake fita ta wayar.

"Baki iya sallama ba?.....me yasa kullum kike maida kanki yarinya sosai?" Ya tambayeta a tausashe yana jin ba dadi baqin halayenta. Ta maida kanta wata sokuwa a gabansa,ba dogon magana sam.....musu ko tsiwarma sai taga dama takeyi masa su.

"Assalamu alaikum" Ta samu kanta da masa sallamar. Qasan ranta a tsorace take da maganansa kadan kadan. Tanaso su rabu ba tare daya sake taba jikinta ko ya kasance da ita ba......amma ta duba ta dubo ba wani hanya daya rage illa ta bishi ta yadda ya bullo mata,ba tare daya ankara ba zai wayi gari babu ita.

Wani sauti na daban yakeji yana shiga kunnensa tamkar yau ya fara jin amsuwar sallama.

"Amincin Allah kema ya tabbata a gareki DUNIYATA.......gani kusa da dakin Allah.....me kike buqatar na roqa miki?". Ya fada da wani kwantacce kuma sassanyan sauti da shauqi da kewa suka cikashi.

Har cikin jikinta taji maganarsa ta mata dadi,tana da tarin buqatun da zata roqa a wajen Allah idan har qaddarar zuwa wajen ta tabbata a kanta. A yanzu dukka ta qosa subar Maldives,tana jin nauyin tambayar amna wanne guri zasu je next.....amma a nata zabin a ture dukka kowacce qasa a barta a tsakanin saudiyya zuwa madeena. Tana tsaka da wannan lissafinne taji muryarsa yana cewa.

"Na roqo ubangiji yasa ki soni....irin matsanancin son da ba zaki iya rayuwa ba tare dani ba.......na roqi Allah ya sanya ki zama madawwamiyar ni'ima a gareni......na roqeshi kada ya baki ikon barina koda kina da nufin aikata hakan.......ya mallakamin rayuwarki gaba daya daga farkonta har qarshenta.......sannan na roqeshi ya bani 'ya'ya masu yawa ta jikinki.....duk shekara so samu ki haifemin tagwaye ko uku uku......"

"Please mana" Batasan sanda ta tsaidashi da fadin wadannan kalmomin ba. Tunda ya fara jero mata abinda ya roqa din zuciyarta ke wani irin bugu,ta sani gurin da yake wajene da babu wasa a cikinsa.....wajene da komai ka roqa amsashshe ne a wajen Allah......tana tsoron kada addu'arsa ta cita.....kada ta kamata,idan hakan ya kasance ina zata saka burin rayuwa tare da 'yan uwanta bisa kyakkyawar rayuwa?.

Dan qaramin murmushi ya subuce masa yana jiyo alamun tsoro cikin sautinta.

"Tsoron me kike haka?,akwai cutarwa cikin addu'ata?" Ya tambayeta yana ji a ransa inama hirar zatayi tsaho tsakaninsu.

Kai ta girgiza kaman yana gabanta,da gaske tsoro yana sake cikata.

"Wannan son kai ne.....zallar son kaine a cikin addu'arka,ka roqi Allah wani abun daban ba wannan ba" Tayi.maganar da dan hasala a muryarta tana ganin kaman da gayya yayi hakan. Boyayyen murmushi da bai bari taji sautinsa ba ya subuce masa.

"Me ruwanki da abinda zan roqa Allah yayimin?"

"Ina da ruwa dashi.....saboda a kaina ka roqi ubangiji...."

"Ke kuma kina tsoron hakan ya tabbata?.....to idan akan wata daban na roqa fa?" Shuru ya ratsa kunnensu na wasu sakanni kafin yaji tace

"Wannan kuma ruwanka bana sabreen ba" Ta samu kanta da fada,sannan ta gimtse wayar tana kasheta gaba daya.

Yaji saukar layin nata,sai ya zame wayar daga kunnensa murmushi yaqi barin fuskarsa. Me yasa tun asali baiyi dabarar bata waya ba kaman haka ya kuma kafa mata sharuda ba,haka hira da masoyi take da dadi dama?. To amma wani hanzari ba gudu ba.....me yasa tayi shuru sanda yayi mata tambaya ta qarshe kafin tace ruwansa?.

Maido fuskar wayar yayi saitinsa,ya rubuta mata gajeran saqo ya tura mata,ya koma ya kwanta rigingine wayar ba rungume a qirjinsa. Wani murmushi ke fita saman fuskarsa kadan kadan,zuciyarsa cike da fatan saisaita kansa akan yarinyar.....don da haka ne kawai zai saitata a hanyar da yakeso ta tabbata a kai.

Shidai baisan ya akayi bacci yayi awon gaba dashi ba,saidai ya cika mafarkansa duka,cikin kowanne gani da zai mata cikin qauna soyayya da kuma kulawa. Harda wanda ya gansu kewaye da yara qananu masu kama dashi sosai. Wannan mafarkin shi ya haska asubarsa,ya shiga bandaki ya daura alwala cike da wani kwantaccen farinciki qasan ransa.

Cikin jallabiyya 'yar Indonesia fara qal ya shirya ta maza,ya shafe jikinsa da lallausan turarensa ya saka hular tashi ka fiya naci saman kansa fara qal itama,ya dauki tasbaharsa counter data kasance farar itama.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


90


Wayarsa ya zura a aljihunsa bayan ya duba number dakin maamah. Kai tsaye can ya nufa yana tafiya da cikakkiyar nutsuwa a tare dashi,bakinsa dauke da ambaton Allah. Yanaso ya samu sahun gaba gaba,wannan ya sanya yake tashi da wuri koda yaushe,ya kuma isa masallacin da wuri.

Kallon kallo suka yiwa juna shi da maamah din,alamu sun nuna tashinta kenan a bacci. Bata ce masa komai ba ta saki qofar ta juya zuwa ciki ya bita a baya. Guri ya samu ya zauna yana duban dakin dake cike da kaya wanda ya tabbatar tsaraba ce. Yaushe ma taxo?,yaushe ta samu daman yin ibada sosai har ta fada yin wata tsaraba?. Duk abinda zata siya din ba abinda bata dashi a gida,amma fadan hakan kaman laifi ne a wajensa.

Bandaki ta shiga ta daura alwala sannan ta fito,tana sauya hijabin jikinta ya soma gaidata kaman yadda ya saba cikin bata haqqinta na uwa daidai misali na girmamawa.

"Ka shigo tun jiya.....sai yanzu aka baka daman zuwa inda nake?". Idonsa ya kawar,shi yasan ko.meye zai faru tsakaninsa da maamah din bame sauqi bane,saidai ko meye ya gayawa Allah yana kuma da yaqinin komai zaizo masa cikin sauqi.

"Nayi qoqarin kiranki ban sameki ba,na aje miki saqo na dauka zaki amsa,banyi zaton a irin lokacin zan sameki a daki ba shi yasa na koma na huta,sai bacci ya daukeni" Ya fada a taqaice. Qwafa kawai taja tana qare masa kallo a fakaice. Ita kadai tasan me takeji a ranta,ita kadai kuma tasan me ta shirya zata aiwatar.....tana ji a ranta idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba lallai ta cika lusara asararra,wala'alla fareeda din itace wannan hasken nasarar guda daya da boka ya mata albishir dashi.

Har ya gama shiryawa suka fice tare bata sake cewa komai ba,dama ba wani sabo ko shaquwa tsakaninsu ballanta hira me kama da irin wannan ta biyo baya.

Zata iya cewa bata taba samun sallar asuba irin haka ba kaman yau,basu bar masallacin ba sai da gari yayi haske,suka hadu gaban hotel din nasu ya dauketa yin breakfast duk da akwai bada breakfast a tsarin hotel din nasu.

Ba wani abu ya karba ba illa coffee,itakam abubuwa da yawa yasa aka ajiye mata,yana sipping coffee din nasa amma hankalinta yana kanshi. Inama ace wannan kulawar ita daya a duniya yake bawa irinta?,inama yadda suka zauna a haka haka yake zama da ita koda yaushe yana kula da duk wani motsinta......yana jira yaji umarninta ko haninta?.

"Muhammadu" Ta krashi bayan ta gama tauna yadda zata fuskanceshi. Burinta a yanzu bai Gaza ganin fitar sabreen cak daga rayuwarsa ba. Da idanu kawai ya amsa mata ta hanyar kallonta.

"Wacce irin mace kake aura mara hankali da tunani kuma mara kirki Muhammadu?". Gaba daya sai maganar tazo masa a bazata,ya kasa kuma fahimtar abinda maamah keson cewa.

"Banda yarinyar nan bata da kirki bata da mutunci batasan girman uwar mijinta ba.....bata taba kirana ta gaidani ba?,bata taba tambayar lafiyata ba.....bata ma taba nemana ba wai sunan tana auren d'ana?,ni kuwa wallahi ba'a haifi diyar da tana auren dana kuma zata min riqon sakainar kashi ba" Ta fada cikin fada sosai tana dan dukan table din da suke kai kadan.

Zame hannunsa yayi daga jikin mug din yana zubawa maamah din idanu. Zaren tunanukansa suna qulluwa waje guda cike da wani irin mamaki. A nan dimma akwai wani qullin?, ya tambayi kansa da kansa. A abinda yake kallo akwai cikakkiyar fahimtar juna tsakanin maamah da sabreen wanda shi ya zama silar daukota zuwa rayuwarsa,a yanzun me ya bata wannan alaqar da jikinsa ya jima yana gaya masa gurbatacciya ce?,to kodai zai samu wani hint din a nan ne?.

Tabbas inda a watannin baya da suka shude maamah ta fadi haka akan sabreen bazai dameshi ba.....in fact ma zai dauka ta fara gane wacece menene kuma halinta,amma kuma a yanzun sai yaji kalaman kaman sunyi tsauri da yawa. Ya shirya tare mata fada ko batanci kowanne iri ne kuma koda waye,don haka ya gyara zamansa yana fadin.

"Maamah.....inajin kinfi kowa sanin wacce iri ce sabreen.....tunda daga hannunki ta fito,kuma na tabbatar ba zakimin zaben tumun dare ba.....amma maganan waya bata da waya,duka wayoyinta suma hannuna". Har tsakiyar kanta taji wani abu ya tsarga mata,wato ita yarinyar zata gwadawa bariki ta bashi wayoyinta?,a tunaninta yin hakan shine zai sanya ta tsallake tarkunanta?. Ta jima tana zaton salwantar da wayoyin tayi,wannan yayi saving nata bata taba gwada Kiran layukan ba,inda ta kira din kenan yana iya zargar komai ko ya binciko komai?.

"Sannan kiyi haquri zan mata fada zata gyara" Ya sake fada yana kallon reaction na maamah din. Yadda ta daga kai da sauri tana dubansa ya sake bashi wani qarin percentage na zarginsa a kanta. Yaushe alaqa tayi nisa tsakaninsu da yake kareta?,yaushe ma duka duka ta kirashi ta masa jan kunnen ya kula da ita?,bariki ce ko nata kalar tsubbun ta shayar dashi kaman yadda jikinta keta bata zata aikata haka?.

"Ai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login