Showing 249001 words to 252000 words out of 363280 words

Chapter 84 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1445

A muhallin da aka tanada saboda ajiyar motoci abdulgaffar ya tsaida motar sannan ya kasheta. Ta daga idanunta tana jira taji wani a cikinsu ya bude motar da zummar fita amma bataga kowa ya motsa ba. A nutse Alhaji hamza kibiya ya fiddo wayarsa sannan yayi kira,kiran da duka duka bai wuce minti daya ba

"Muns parking lot" Abinda ya fada kenan ya yanke kiran yana dubansu.

"Muje ko.....ga Jordan nan zuwa". Kiran sunan Jordan kadai ya sanya jikinta ya fara rawa,a kasalance ta sanya qafafunta waje tana ambatar sunan Allah bayan musaddiq ya bude mata murfin motar,sai taji jikinta kamar yayi nauyi ta dafa murfin tana fitowa.

Komawa gefenta anni tayi tana saka hannuwanta cikin nata,ta daga kai suka hada ido da anni.

"Karki manta alqawarinmu,kada ki sabashi......be strong please ameenatu......na sani ke din jaruma ce" Kai ta gyadawa anni,bawai don a yau tana jin wannan jarumtar ba,ta dade da sani da kuma fahimtar indai akan fu'ad dinne bata da wani sauran jarumta daya rage,ita din raguwa ce ta qarshen qarshe.

A hankali suka fara takawa suna dosar main entrance na asibitin,wanda basuyi taku goma cikakke ba saiga Jordan din,sukayi kacibus dashi a hallway din yana fitowa daga elevator.

Kallo kawai sabreen take qarewa Jordan,abinda bata taba yi ba,saidai koda bata taba qare masa kallo ba amma ta sani yana da qiba da kuma tsaho gami da murdewar jiki,amma a yanzun abinda idanunta suke iya gane mata shine zubewar da yayi. Ya rame sosai duk da har yanzu wannan kuzarin yana tattare dashi,abinda ya sanya dukka gwiwoyinta yin bala'e'en sanyi tana jin tabbas ko meye ya faru da hammanta ba qaramin abu bane,abun har ya taba jordan har haka?.

"Welcome madam" Ya fadi mata yana tsaye daga gefanta cikin tsananin girmamawa tausasawa da kuma kulawa. Bata iya amsa masa ba,sai idanunta data zare daga kansa gudun kada taje ta rasa ragowar qwarin gwiwar data rage mata.

Musaddiq da abba da jordan su suka fara wucewa saman,kafin su kuma su kuma da saddiq su kira wani elevator din suka shiga suka bi bayansu.

Farouq ne mutum na farko data fara hangowa yana fitowa daga wani balcony na daban bayan doguwar hanyar da kebantattun amenities suke. Faduwar gabanta ya sake tsananta saboda ganin irin zubewar da jordan yayi akan fuskar farouq. Ta kasa dauke idanunta a kanshi,kaman yadda ta lura shima din ita yake kallo. Suna takawa zuwa inda yake shima yana matsowa garesu,har suka riski juna a hanya.

"Adda......haka kika koma?" Farouq ya fadi a raunane yana jin wani irin tausayinta yana ratsashi. Karo na farko da yaji yarda dari bisa dari yau yayi ido da ido da salon soyayyar da yakeji a ransa a baya cewa babu irinta a duniyar zahiri......saidai a duniyar litattafai da kuma fina finai.

Kanta ta dauke tana qoqarin hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya.....tambayarsa kulawa ce ta kawota.....amma da zaiyi mata wani abu da yafi wannan tambayar faranta mata rai. Ya sauketa da labarin halin da hamma fu'ad yake ciki.....ya gaya mata yanayinsa shi zaifi komai mata dadi.

"Kaima bakaga yadda ka koma ba BB?" Ta qarashe tambayar tana kallon fuskarsa kai tsaye muryarta tana rawa,tana fatan ganin wani mode da zai bata haske akan yanayin da fu'ad din yake ciki.

Wani busashen murmushi yayi yana kada kansa,sannan ya maida dubansa gasu anni.

"Sannu da zuwa abba.....anni sannu da zuwa".

"Muje farouq ciki....muje dakin" Anni data kasa haquri ta fada tana yin gaba sabreen kuwa ta sanya qafafunta ta rufa mata baya kai tsaye xuwa dakin da sukaga farouq din ya fito.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*



126


Daga balcony din ma'aikatan lafiyar wajen suka tsaidasu,kowanne aka bashi riga da hula ya sanya,sannan suka musanya takalman qafarsu zuwa wasu ajiyayyun tsaftatattun fararen Crocs da suke wajen.

Lafiyayyen parlor ne wanda aka tsarashi cikin wani irin yanayi da zai bawa me jinya dama wanda ake jinyar yanayi me kyau,bisa wadatacciyar iska da haske,irin iskar dake fitowa daga tsirran da aka wadata bayan dakunan dasu,wanda kana iya hangen komai tarwai ta gilasan da dakunan ke dashi daga gaba.

Sam parlor din baiyi kama da asibiti ba,an saka sofas set guda,tv plasma freezer da side tables da babba guda daya,curtains da komai na parlor din fari ne qal tamkar hannu baya tabawa saboda tsananin kula da tsafta,hakanan qamshi ne me kwantar da hankali kawai yake fita.

"Akwai likita a ciki a tare dashi,bibbiyu bibbiyu nake ganin ya kamata a shiga......" Farouq ya fada yana rarraba idanunshi tsananin fuskokinsu.

Sulalewa tayi ta zauna saman sofa din,koda farouq yace ta fara shiga batajin zata iya hakan,gwara a cikinsu wasu su fara shiga din,yanayin fuskar kowannensu shine zai bata qwarin gwiwar shiga ko akasin hakan.

Kaman anni zatayi magana sai kuma ta fasa,ita da abban sukayi gaba farouq yana musu jagora suka buda qofar suka shige.

Zaman jiran fitowarsu annin ba wani abu bane me sauqi a wajenta,sai ta jita tamkar tana zaman jiran isowar layin mutuwa kanta,kanta a qasa ta saka hannuwanta dukka biyun ta dafe kanta tana jin yadda zuciyarta ke harbawa kaman zata fado qasa. Wani motsi takeji mararta tanayi,baqon abune da bata taba jinsa ba sai a ranar kamar ana d'allinta da yatsa.

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem" Ta dinga maimaitawa labbanta kadai ke motsawa. Da yatsunta ta dinga irga kowanne wucewae second,tanajin kaman suna wucewa da kowanne dama na rayuwarta,tana jin kamar suna wucewa ne da farincikin rayuwarta gaba daya.

Sai da su abba suka kwashe mintuna kusan goma harda doriya kafin taji fitowarsu. Duk yadda taso daga kai ta kalli reaction na fuskarsu ta gaza yin hakan,ta kasa koda motsawa,tana jin tsoron abinda zata daga ta gani tattare dasu. Saidai takum tafiyarsu su biyun bata tsinci komai a ciki ba,karsashi ko akasin hakan,wanda hakan ya sake sanyata a taraddadi me yawa da kokwanto.

"Ni zan shiga" Ta fada da wani irin fusgar kalma cikin ba zata a sanda saddiq da musaddiq ke takawa zuwa qofar dakin.

Miqewa tayi ta zauna sosai tana dubansu sanda suka dakata daga shigar da juyyayyun idanunta,tana jin kamar kafin su shiga su fito zata iya rasa numfashinta da rayuwarta gaba daya,koma meye gwara ta shiga ta gani ta kuma fuskanceshi da.dukkan iyawarta,da wannan qudurin ta taho,ba kuma zata iya canzashi ba.

Da baya suka dawo,ba wanda ya musanta mata ko yace wani abu,saita miqe a hankali tana jin kamar qafafunta ba zasu dauketa ba ta doshi dakin.

Ta kusa sakkani talatin riqe da handle din ta kasa murzawa,har sai da muryar farouq dake bayanta ta dawo da ita daidai

"Are you okay?" Ya tambayeta yana leqen fuskarta. Kai ta gyada masa.

"Ko na bude miki?" Ya sake tambaya cikin kulawa saita girgixa kanta ta kuma tattara gaba daya qarfin daya rage mata ta murda qofar tana shiga.

Jijiyoyin jikinta ne taji tamkar suna tsinkewa,numfashinta kamar an musanya mata da wani abun daban me tauri bawai lallausan iskar da kowanne me rai yake shaqa ba. Ta dinga ganin idanunta kaman gizo suke mata,ba ainihin abinda zata gani bane take gani......gani take zolayarta kawai idanun nata sukeyi saboda abinda take kwana ta tashi da fatarsa kenan.....abinda take kwana ta tashi tana mafarki da burin ya kasance kenan.

Yana zaune saman gadon da aka tallafo bayansa aka dago kan gadon sosai yadda zaiji dadin zama. Jikinsa sanye da rigar asibitin ruwan sararin samaniya me haske sosai. Lallausan blanket ne lullube da qafafunsa zuwa qugunsa.

Fararen idanunsa tarr bisa fuskarta,idanun da suka dan rusuna kamar wanda bacci yake cike a idanun nasa. Kallon kallo ya wanzu a tsakaninsu,zukatan kowannensu yana bugawa da sauri da wani irin doki da zumudin ganin daya bangaren zuciyar tasa.

Wasu irin abubuwa ya dinga sakar mata suna ratsa sassan jikinta......wani irin shauqi mahaukaciyar soyayya da zazzafar qauna ke kurdawa ta kowanne lungu na zuciyarta. Kewarsa me matuqar qarfi ta taso ta lullube zuciyarta ta sakata jin wani rauni na mamayarta,take idanunta suka cika da hawayen da bata da ikon tsaidasu.

Hannunsa daya ya miqa mata yana ware mata su alamun marabtarta yakeyi,cikin wani irin zaquwa da dokin isowarta gareshi,batayi wata wata ba ta soma takawa da sassarfa zuwa inda yake tana jin kaman lokacin isarta inda yake ma ya mata yawa.....inama zaiyiwu ta zama walqiya cikin qiftawar idanu ta samu isa gareshi.

Jikinsa ta fada gaba daya kuka yana qwace mata,tsam ya riqeta cikin jikin nasa yana mata kyakkyawan masauki zuciyarsa na tsananta bugu cike da wani bahagon so,idanunsa suka dinga lumshewa da kansu,dumin jikinta yana ratsa qashinsa bargo harda jinin dake harbawa kowanne sashe na jikinta. Hannunsa daya ya sanya ya riqo fuskarta,idanunta yake son kallo,qwayoyin idanun nan nata da yayi matuqar kewa yakeson gani.

Bata hanashi ba,ta daga oily eyes dinta masu sheqi da suka jiqe da hawaye tana kallonsa. Nutsewa idanunsu sukayi cikin na juna,wani irin feeling ke ratsa kowannensu wanda yafi qarfin baki ya bayyanashi. Wani deep connection ya qullu a tsakaninsu,magana ce tsakanin zuciya da zuciya kawai wadda tafi qarfin baki ya bayyanata. Idan ya motsa labbansa sai yaji sun masa nauyi.....sai yaji kaman sunyi kadan su isar da saqon da zuciyarsa keson fadi

"Sabrrrr" Ya samu ya fusgi kalman da qyar zuciyarsa naci gaba da bugawa. Itama kaman zai bace mata takeji daga qiftawa qwaya daya tak da zata yiwa idanunta,don haka ta motsa labbanta ba tare da amsar NA'AM din da takeson furtawa ta fita a bakinta ba.

"Love is in the eyes.....eyes don't lie.....sabrrrr.....kalli idona.....me kika gani?" Ya motsa labbansa ya fada da wata irin narkakkiyar murya irin wadda soyayya ta yiwa lahani.

Inda yasan yadda qwayoyin idanunsa suke narka mata bargo da bai buqaci ta kallesu har haka ba....saidai kuma kallon nasu wani abune na musamman cikin ruhi da zuciyarta. Ci gaba tayi da kallon idanun nasa.....taga abubuwa masu tarin yawa.....taga abubuwa masu yawan da sai da taji kaman zata zauce,duka ita daya?,duk ita daya muhammad fu'ad kewa wannan zazzafan son?.

Hannu ya kama ya riqe kumatunta yana aza shimfidadden murmushi kan fuskarsa.

"You're a thousand miles away.......but no one else is closer to my heart than you are" Ya qarasa fada yana kama fuskarta sosai gami da hade goshinsu guri daya.

Musayar numfashi suka fara yi a tsakaninsu,kowanne yana shaqar numfashin da dan uwansa ya fesar,hakan na sake qara musu wani qaqqarfan alaqa tsakaninsu data tsananta bugun zuciyarsu duka su biyun.

"Zan iya mutuwa.......Allah zan iya mutuwa idan ka sake matsawa daga gareni irin wannan matsawar da kayi.......zaka iya rasani......ka rasa kuma babies dinmu gaba daya" Ta qarashe maganar tana sakar masa kukan da ya koma zuwa na shagwaba kuma a wannan lokacin.

"Nayi alqawari DUNIYATA.....nayi alqawari bazan qara ba,i promise" Fuskarta ta qwace ta cusata cikin qirjinsa tana shaqar wannan tattausan qamshin nasa da tayi matuqar kewa kamar zata zauce.

"I pray to god that you will stay permanently in my life".

"I pray too my world" Ya fada yana kissing tsakiyar kanta. Qanqameshi tayi da kyau don sake bawa kanta tabbacin reality ne bawai mafarki ba. Kalmar "wash Allah na" Daya fada ita ta sakata saurin sakinsa tana kallon fuskarta.

Idanunan dai nashi ya zuba mata murmushi na fita a fuskarsa,sai ta tabe baki kaman zata saki kuka. Da sauri ya mata nuni da hannunsa,ta waiwaya a hankali zuwa sashen da yake nuna mata din.

Miqewa tayi ta zauna da sauri saidai ya hanata hakan,ya jawota jikinsa ya maidata sosai yadda zaici gaba da jin qamshinta da duminta.

"A nan suka harbeka?" Ta tambayeshi a sanyaye da wani irin emotion na bacin rai saman fuskarta. Girarsa kawai ya dage mata yana dubanta har yanzu fuskarsa da murmushi duk da yadda yadan fada kadan.

"Allah ya isar mana....Allah ya saka mana"

"Very soon duniyata......mu ajiye wannan maganar yanzun......i need you duniyata.....kaman dazu naji kince babies instead of baby right?" Ya tambaya yana tsareta da idanunsa. Tsam tayi tana dubansa,sai kuma ta saka tafukan hannayenta duka biyun ta lullube fuskarta dasu.

"Yes......twins n....." Bata qarasa fada ba taji yana lalube rigarta,saidai jikin ba qwari kwata kwata da alama don haka ya ajiye hannun nasa yana maida numfashi. Koda ta kalleshi kwantaccen hawaye ta gani saman idanunsa,batasan me yasa akan duk abinda ya shafeta ba shi rago ne na gasken gaske.

"Please sabrrrr......ki dagamin rigar na gani,haka Allah ke sona?" Yadda yayi maganar da gaske abun ya taba ranshi,ba zata iya hanashi ba,don haka ba musu ta miqe ta yaye abayan jikinta,tayi qasa da under wear dinta take farar fatar cikinta ta fito. Jawo qugunta yayi sosai,a hankali ya aza labbansa saman mararta.

Har tsakiyar kwanyarta taji wani yaarrrrr,wani abu ya tsarga mata ya saukar mata da wani irin yanayi a sassan jikinta. Lips dinsa nakan marartata ya daga idanunsa ya kalli yanayin fuskarta,kunya ta sakata runtse idanunta sai ya aje mata tattausan kiss sannan ya janye bakinsa ba tare daya saki rigar ba. Batasan me ya karanta ba,amma ya kusa mintina biyu bakinsa yana motsi kafin ya matsa kusa ya tofa mata abinda ya karanta din,ya sake kai hannunsa ya aza akai ya sake karanta wasu addu'o'in sannan ya sake mata rigar.

Still hankalinta yana kan hannunsa,tayi taku biyu zuwa wajen ya sake jawota jikinsa

"I really missed you......kiban koda 10minutes naji duminki......ban taba zaton zan sake rayuwa ba......dazu na tashi daga suman da nayi duniyata" Yayi maganar yana aza kansa saman kafadarta,yana jin ya samu wani peace daya dauke masa duk wani abu da yakeji a jikinsa da zuciyarsa.

Idanunta sukayi rau rau da hawaye

"Ko waye wannan bazan taba yafe masa ba.....ko wayeshi" Ta fada muryarta tana rawa. Ya buda baki zaiyi magana muryar farouq ta ratso dakin,yadan bude qofar kadan amma fuskarsa da idanunsa sun basu baya.

"Su musaddiq kuwa zasu samu yin dubiyar nan?,ko kuma su koma kawai sa dawo?". Sassanyan numfashi ya aje kafin ya motsa labbansa.

"Bansan me yasa baka da imani ba farouq....aidai ka tausayamin ko?.....na yafe dubiyar,kaima ka bisu kuje ku huta......thanks so much dude". Baki kawai farouq ya sake,ya dauka fu'ad din zai tuna dasu anni a wajen ya sakaya zancansa?.

" Dama shi dan adam butulu ne ai,na maka welcome to the world ai ko?,alright.....but kasan hannunka yadda yake......yana buqatan a kula dashi.....still itama me jinyar taka ba'a dade da sallamarta daga asibiti ba.....banajin she can take good care of you".

"I can BB.....i can wallahi" Sabreen ta samu kanta da fadin haka ba tare da wani kunya ko d'arr ba.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......G??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????YARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login