Showing 195001 words to 198000 words out of 363280 words

Chapter 66 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1425

ya zugeshi,sannan ya dauki bath set dinsa ya soma dosan toilet.

Kadan ta bude idanunta taga yana tafiya bandakin,tasan kuma indai ya shiga ita daya zai bari sai ruwan nan dake kada hankalinta. Zumbur ta miqe da gudu gudu ta rufa masa baya,sai ya tsaya ya waiwayo yana kallonta sanda ya sanya qafarsa a qofar toilet din.

Yadda ya zuba mata idanu ya sanyata yin qasa da kanta,tasan yana neman ba'asin biyoshin da tayin,tana wasa da farcenta tace.

"Tsoro nakeji" A shagwabe har batasan sanda sautin tattausar muryarta ya koma haka ba. Wani numfashi ya zuqa me zurfi yana dubanta,yana bala'in son shagwaba fiye da yadda kowa zai fahimta.......saidai ba wanda yasan da wannan dabi'ar tasa saishi kadai,don ya sanya a ransa ba shagwabar da zata burgeshi saita matarsa. Yana cikin jinsin mazan da shagwaba ke tafiya dasu,yasa hannunsa yana shafan qirjinsa dake cike da gargasa muryarsa a maqoshi yace.

"Ba wani abu fa.....kina cikin aminci,na miki alqawari daga yanzu har qarshen numfashinmu.....ba iya nan kawai ba.....a dukka fadin rayuwarki ba wani abu daya isa ya sake cutar dake muddin fu'ad yana raye". Idanu ta ware tana kallon qasan curtain din,ruwan yadan kada alamun wucewar kifi. Tanason kallonsa ta tabbatar masa da tsoronta amma kuma batason kallon muscles dinnan nasa.

"Still tsoron dai?" Ya tambayeta yana dage mata gira,saita daga masa kanta.

"Okay.....yanzu to ya zamuyi?" Ya tambayeta yana zube mata idanunsa. Satar kallonsa tayi kadan sannan ta dauke kanta,itama bata sani ba......batasan ya zasuyi ba,kawai dai abinda ta sani ba zata yarda ta zauna ita kadai ba. Kaman yasan abinda take saqawa yace mata.

"Zaki shigo ciki ki jirani na gama wankan?" Ya mata tayi yana da tabbacin ba zatayi accepting ba. Waro idanu tayi tana kallonsa kai tsaye tana mantawa da batason ganin qirar jikinsa ma.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

100



_Allah S W T yana cewa "lallai sallah tana hana alfasha da munkari_

_Duk wanda salla bata hanashi qarya ba,zina sabawa iyaye,zuwan gidan boka shirka kenan,cutar da maqota da sauransu,to tabbas ya tuntubi sahihancin sallarsa_




"Ki zauna to ki jirani......bazan iya kwanciya banyi wanka ba.....if not ki shigo sai muyi wankan tare" Ya fada yana matsa mata hanya. Ai da sauri sauri taja baya,ya saki murmushi ya matsa kusa da stool ya dauko mata ya ajiye mata qofan toilet din

"Oya.....zauna a nan". A sanyaye ta zauna din kaman me gadinsa,yayin da shi kuma ya wuce ciki. Sai daya shiga ya kunna shower sannan dariyarsa ta subuce....
Bai taba kawowa a ransa muraaka zai kawo masa wannan kusancin da yaketa fata tsakanin shi da ita ba sai yanzu......tabbas inda yasan da hakan da tuni ya jima da daukota wannan duniyar.

Idanu ta yita rarrabawa,tana sanyawa a ranta muddin taji wani abun da baiyi mata ba zata afka bandakin ne,komai ta fanjama fanjam,saidai har ya gama din ba taji komai ba. Daure da towel ya fito a tsukakken qugunsa,ya fito mata sak kaman wani dan wasan dambe na duniya. Kanta ta dauke ta miqe tana basarwa gami da barin wajen zata koma saman sofa.

"Kiyi wanka ki sake kaya kizo muje muci abinci" Ita da yayi zancan abinci ma saita rasa cikin wannan rayuwar ruwan ina za'a samu wani abincin kirki.

Bata musa masa ba don itama ya zame mata al'ada yin wankan kafin ta kwanta,saita dinga dube duben wanne sponge xatayi amfani dashi?,in fact ma tafiya ce ta dole dole ko kayan da zata sauya bata taho dasu ba.

Miqa mata bath set dinsa yayi yana kafeta da ido,salin alin ta karba don wannan kallon nasa bata qaunarsa,wani iri yake sata tana ji gaba daya.

A tsorace ta kammala wankan,duk minti guda sai taji kaman kifayen zasu shigo su sameta,data gama ma hakanan ta maida kayan data cire ta fito dasu.

Sanda take shigowa ya kammala shirinsa tsaf,cikin polo shirt fara qal me ratsin black,sai black trouser shima daya zauna a jikinsa sosai yana nuna zallar hasken fatarsa. Duk yadda taso ta qaryata kanta sanda zuciyarta ke fadin yayi kyau amma ta kasa haka,wani irin kyau kayan sukayi masa kaman saboda shi aka qerasu.

Kallo daya ya mata ya dauke kansa,ya dauki wayarsa yana cewa.

"Ga kaya nan ki canza.....ki sameni a sitting room" Yana fadin haka yayi gaba. Taku biyu tayi da zummar biyoshi ya dakata yana waiwayowa. Wata siririyar dariya ta qwace masa.

"Dama matsoraciya ce ke har haka?,bazan tafi na barki ba.....zan baki space ne ki shirya,in kuma kinaso zan zauna na tayaki shiryawar.....nima zanzo hakan" Fuska ta bata tana dakatawa daga binsa din. Kai ta girgiza yana sauke murmushi ya juya yana barin dakin.

Jikinta ta qanqame waje daya kafin daga bisani ta nufi luggage din daya nuna mata,ta kwantar da ita ta zugeta tana duba kayan ciki.

"Turqashi" Ta fada bayan ta ajiye rigar qarshe data daga a kayan. Kusan an sake maimaita abinda amna ta mata,kaf kayan bataga wata riga da zata suturce mata jiki ba,wasu irin kaya ne masu kama da qannen dasu gwara babu su,sai kawai ta zauna a qasa tana saka kayan a gaba gami da buga tagumi da hannu daya.

Lokaci yake dubawa,sai yaga ya wuce qa'idar lokacin wanka da shiryawarta,wanda tuni ya fara riqewa a kansa,aje wayarsa yayi ya miqe yana komawa dakin.

Kanta ta dago suka hada ido,sai ya maida dubansa ga akwatin,tayashi tayi itama,ta kalli akwatin ta kuma kalleshi,idanunta kadai sun gaya masa abinda take nufi,ya saki qofan ya qaraso ciki.

A gaban akwatin ya tsugunna ya fara daga kayan shima,tun baiyi nisa ba ya cire wata gown yana ajeta gefe. Da ido tabi rigar,saboda ta dagata taga yadda take,kusan gaba daya bayan rigar a kwakwashe yake sai zararruka da ake zargawa ta bayan rigar a daure. Ta gaban kuma ajiyayyen breast cup ne da koda me zubabbun qirji ta tabbatar sai sun tashesu tsaye ballantana irin nata.

Da idanu yayi mata nuni kan ta dauka ta sanya,tsoro ya bayyana qarara a fuskarta,tadan ware idanu kadan tana jifansa da alamar tambaya. Idanu ya lumshe mata gami da kada kai,ya tsugunna ya dauki rigar sannan ya soma takawa a nutse yana rage tazarar dake a tsakaninsu. Dab da zai isa ta fahimceshi,saita yunqura da zummar janyewa amma ya fita zafin nama don tuni yayi ram da hannunta cikin nasa.

"Kowanne musu da taurin kai akwai cost dinsa a wajen nan" Ya rada mata a kunne sanda yake rungumeta cikin jikinsa yana lalubar zip din rigar tata.

Kai ta soma kada masa,don indai zai rabata ne da wannan rigar tamkar ya rabata da komai ne,saboda ba komai din a jikinta,don bata iya maimaicen pant da brazier ba don haka ta zura rigan kawai ba tare data sanyasu ba,da nufin ta nema wasu idan ta fito.

"Ka bari......zan saka Allah" Ta fada a tsorace muryarta tana rawa.

"Is too late" Ya furta can qasan maqoshinsa yana shaqar daddadan qamshinta duk kuwa da cewa wanka tayi. Bai bata damar fadin kalma ta biyu ba ta zuge rigar tsaf da jan zip qwaya daya tak.

"Don't move.......saka miki kawai zanyi muje muci abinci......musu ne banaso.....kinqi ki gane kuma.....leave me mana na gama miki a nutse mu wuce?,idan da rigima kuka kikeso to na iyata kwando kwando" Ya sanya labbansa saman kunnenta ya karanta mata. Idanunta a runtse tsigar jikinta na zubawa,daga yadda yayi maganar tabbas da gaske yake......wata zuciyar ya shawarceta tayi haquri na sakanni ya saka matan kaman yadda yace.....dole ya barta idan ya saka mata din ai. Wani abu ta hadiye a maqogoronta cikin matuqar tsoro tana kulle idanunta,tana jin wani iri na yadda zai sake samun damar kallon surarta da taba jikinta a karo na biyu bayan alqawari da tayiwa kanta makamancin hakan bazai sake faruwa ba......tana jin sanda iska ta hura fatar jikinta,tana jin sanda yadan rabata da jikinsa ya salube rigar ta sulale qasa. Dukka jikinta ya dauki rawa da bari ganinta cikin yanayin da ko mahaifiyarta bata taba ganinta ba.......duk da ba haske bane tarwai a dakin amma ba abinda zai hanaka ganin mutum sosai da sosai,tsoronta ya ninku,ta dinga jin kaman qasa ta tsage ta hadiyeta a ciki.

Da qyar ya kamo numfashinsa dakeson kubce masa saboda sauka da idanunsa sukayi a wajen. Ya miqa hannunsa yana me burin isa gurin,sai kuma ya tsaya cak yana janyesu a hankali,wata qatuwar ajiyar zuciya ta kubce masa kaman yaron da aka yiwa dukan tsiya yaci kuka ya qoshi,da wani irin zafin nama ya juyata fuskarta ta daina facing dinsa,saidai can dinma ba sauqi,hips dinta ke tsokane masa idanu,sai kawai ya rabata da jikinsa waiko hakan zai sanya ya rage ganin abubuwan da yake gani din.

Baisan shima nasa hannuwan rawa sukeyi ba sai bayan ya zura mata rigar ya dagata daga jikinsa yana zazzarga mata igiyoyin dake riqe da bayan rigar. Sosai hannuwansa suka kama rawa,daure igiyoyin suka gagareshi. Ya runtse idanunsa da matuqar qarfi yana fatan daidaituwar mode dinsa,saidai ko daya bude ba abinda ya canza saima numfashinsa daya fara fuzga kaman me ciwon asthma.

Hannuwansa ya dora saman kafadunta gaba daya ya juyo da ita da wani irin hanzari,yadda red din gown din ta sake haskata sai yaso.tafiya da ragowar numfashinsa da yake kokawa dashi. Gaba daya labbansa rawa suke kaman me rawar sanyi ya soma lalubo kalmominsa......

"DUNIYA TA.... please,kiyimin alfarma na sake kasancewa dake karo na biyu......please na roqeki karkice zaki hanani" Firgicin data shiga ya kusa fin nasa,take itama jikinta ya kama rawa,ta zare idanunta duka a kansa tana jin kaman zasu zazzago tsabar tsoro. Ta motsa labbanta zatayi masa magana a tsorace amma ya rigata

"Am so sorry.....naso na barki har sai sanda kika fara sona.....naso na barki har sai sanda kika gamsu da kanki kikayi accepting muhammad fu'ad......but.....kece DUNIYATA bani da wani gurin zuwa sai wajenki din dai" Sake rudata kalamansa sukeyi,batasan yadda zata masa bayani bama,neman gurin tsira kawai takeyi,saita saka hannunta tana neman zame hannuwansa daga kafadarta. Sarai ta fahimci a rude yake kaman yadda take a rude,idanma tace zata tsaya masa bayani bazai fahimta ba. Damqe kafadun nata yayi idanunsa suna sake juyewa hadi da canza launi.

"Please mana.....na miki alqawari wannan karon......I'll be gentle with you.....i will never harm you again" Ya fada yana jin kaman ana qara izashi zuwa gareta.....kaman yana qara loosing tunaninsa gaba daya. Sake buda baki tayi still bata sare ba,duk da tsoron dake sake dabaibayeta da nufin masa bayani ko kadanne,amma sai.ya kama hannuwanta duka ya sanya tsakiyar tafin hannunsa kaman me begging dinta

"Please....please.......na yadda da kowacce kalan tuhuma zakiyimin......na yadda da kowanne zarginki a kaina......kome kikace nayi ina neman gafara akai......kinqi bani dama tun a baya nayi bayanin kaina......I'm pleading with you.......grant me this favor" Ya qarasa maganar yana zubewa a gabanta......

Ji yake ya shirya rasa komai.....ya shirya kuma sadaukar mata da komai,yayi qasa da kansa yana jiran cewarta jikinsa naci gaba da rawa.

Wani abu ya tsarga mata jin digar wani abu me dumi saman tafin qafafunta,wata irin faduwar gaba ta ziyarceta saboda abinda zuciyarta ta raya mata.

"Muhammad fu'ad jadda ne kuka a gabanta?,muhammad fu'ad fa?,wanda gidan jaridu da mujallu kowacce fitowar rana zuwa faduwarta suke rububin buga labari akan kamfaninsa......suke rububin fidda labari akan kalan jarumtarsa tun kan ya balaga har zuwa girmansa......jaddan da qasashen duniya keyi dashi?,jaddan da maganarsa manyan kamfanonin qasashen qetare dake sarrafa diamond sukeji?,yau shine under her feet?.

Daidai inda zaren tunaninta ya tsaya kenan,sai dauko mata sunkutarta da fu'ad din yayi zuwa lafiyayyar shimfidar da muraaka suit suka zubeta musamman saboda masoya masu yawon watan zuma wato honeymoon irinsu fu'ad din.

"Am sorry DUNIYATA.....am sorry my world" Shine abinda ke fita daga bakinsa cikin wani irin gigitaccen yanayi. Tsoro ne fal qirjinta da zuciyarta,tuni ta fara sakin nata kukan tana hango kanta gaban Dr fadwa ana sake dinketa. Tana sake rewinding azabar da tasha wancan ranar.....ta kasa mantawa da yanayin daren da kuma lokaci. Hatta da wucewar kowacce daqiqa a lissafe take a wajenta....abune da ya kasa barin kanta da mafarkanta.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

101


_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_

_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_

_Bukhari da muslim_




"Kar ka cutar dani" Ta fada a galabaice tana jin yanayinta yana canzawa.

"Bazan iya cutar dake ba.......sonki ne yayimin yawa.....ki taimakamin na koyi controlling nasa" Ya fada ba tare daya saurara mata ba.

"In ka cutar dani ko ka zalunceni......"

"Ki daga hannu ki roqi Allah ya hukunta miki ni.....ki roqi Allah yayi miki sakayya......ya jarabceni da wani son da yafi wannan yawa da fadi" Ya fadi yana tallafo kanta gami da sanya jirkitattun qwayar idanunsa cikin nata dake cike fal da hawaye......dukka hannayensa suna rawa kaman wanda aka tsamo daga ruwan sanyi. Idanunsa kawai firgitata suke,ta saka hannu zata riqeshi saidai ko kadan bayason sakejin wata magiya tata,don haka ya rufe bakinta ruf da nasa.

A hankali ya shiga aike mata wasu irin zafafan saqonni.......wasu irin abubuwa da tun tana turewa har suka fara kama mata kwanya.....suka jefa ta a duniyar tunani.....suka dauki duk wani tsoro nata da fargabarta sukayi cilli dasu can bayan gadon.....suka gusar da duk wani hankalinta tunaninta taurin kanta tsiwa dama tsoronta. A hankali saiga me jadda yana komawa fagen,fagen da bai taba zaton zai sake ziyarta ba karo na biyu cikin rayuwarsa.......yayi musu ragama da jagora zuwa wata sabuwar duniyar da shi da ita basusan akwaita daban bace.....tasha banban da duniyarsu ta wancan karon nasu.

&Tun yana dakon jiran fu'ad har ya soma lalubarsa cikin gidan,don dakinsu ya shiga zaman jiransa. Ko ina ya duba bai ganshi ba,bai wani zurafafa tunani ba ya dauki wata motar ya fita ya zauna da baqin nasu,suka kammala meeting din ya sallamesu,ya kuma hada duka documents din a take ya aika masa ta email. Kaman yadda suka tsara daga wajen sai ya wuce dauko anni data tafi wani herbal center a traditional market dinsu. Suna mota take tambayarsa fu'ad din

"Mun fito tare so uzuri ya maidamu,sai nace bari nazo na daukeki" Daga haka suka rufr chapter din suka dauko wata har suka isa gida.

Komai anni ta gama har tayi shirin kanwaciya amma bataga sabreen ba. Tana saman abun sallah tana shafa addu'ar shafai da wutirinta tace da amna.

"Ina ameenatu ta shiga ne?" Kai ta girgiza,itama tun dazu take nazari

"Ban sani ba wallahi anni,maamah dai tayi kiranta,tunda ta fita kuma bata dawo ba". Shuru anni tayi haka kawai taji gabanta yana faduwa.

" Maamah ce ta kirata?,tunda ta fita kuma bata dawo ba?" Ta sake maimaita statement din tana duban idanun amna. Kai ta gyada mata.

"Turqashi" Anni ta fada tana miqewa hankalinta yana tashi,zuciya ta fara fasalta mata abubuwa kala daban daban da zasu iya faruwa.

"Indai wani abune ya faru kaman yadda zuciyata ke gayamin......indai wani abu mariya ta aikata na cutarwa ga ameenatu.......tabbas saita gane bata da wayo......a wannan karon saina nuna mata ainihin kalata" Anni tayi maganar a zuciyarta tana zare hijabin jikinta,ta dauki dankwali ta daura tana duban amna

"Ki zauna ina zuwa" Abinda kawai tace da ita kenan ta murda qofar tana ficewa.


_tofa.....=??=??=??,me anni zatayi?,masu karatu ku tarota,ku gaya mata ba ruwan maamah a nan......dan annin ne yayi kidnapping takwararta da kansa_ @&? @&? @&? @&?=??=??=??


Daidai lokacin da maamah ke dakinta,abun duniya yana sake ta'azzarar mata da wani irin zafi qunci da tashin hankali. Kaf tunaninta ya karkata akan yadda zata raba sabreen da wannan copy din video din da yake hannunta.....rabata dashi din shine tamkar mabudin iya wurgar da ita daga rayuwarsu cikin qasqanci da tozarcin data tanadar mata.

Ta duba agogo ta duba agogo har sau babu adadi......ta duba agogo duk bayan kowanne wucewar daqiqa.....cikin saka ran fuad zai dawo ya lallasheta......fu'ad zai dawo yaji meye damuwarta kaman kowanne d'a yakewa iyayensa,saidai tun tana dubawa tana kuma lissafawa har ta bacewa lissafin.

Kowacce alama da shaida ta nuna mata bazai dawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login