Showing 321001 words to 324000 words out of 363280 words

Chapter 108 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1418

Anni ya fara miqawa sannan ya dauki na biyun ya maimaita masa abinda yayiwa na farko ya sake miqawa anni,wadda ita kuma ta miqawa huda na farkon. Tana ganin irin zaquwar da huda ke ciki,ta kasa zama ta kasa tsaiwa. Hannu biyu anni ya karbeshi shima,sai ga hawayen da taketa riqewa sun soma diga saman lallausan abun daukan jariran,sai sautin kukan huda itama ya soma tashi.

Murmushi abba ya saki yana tsokanar annin.

"Da alama wannan kukan za'a yimin tawaye kenan,banda haka nine ya cancanci nayi kuka ai,nida aka yiwa kishiyoyi?,har uku rigis a rana daya a lokaci daya?,to ki daure zuciyarki dai karsuce matar tasu raguwa ce" Ta tsakiyar hawayen nata murmushi ya subuce mata,daga ita sai Allahnta su kadai sukasan irin farincikin da yake dawainiya da ita,yaran wani baiwa ce da rahama daga ubangiji zuwa garesu,lallai bawa ya kamata ya zama me yawan imani da qara girmama zatin mahaliccinsa.

Duk wanda ya dauka kaman kada ya sauke a cikinsu,sun karade wajen har basa ganin wani bare a wajen,ganin yara uku ya janyo hankulan mutane,duk wanda zai wuce sai ya tsaya ya kalla ya musu addu'a kuma.

"Wai ina muhammadu ne?" Abba da baiga fu'ad ba tun zuwansa gurin ya tambaya.

"Yana can wajen matarsa......inajin ko yaran bai dauka ba" Anni ta fada tana nannade yaro daya da yake hannunta.

"An kaita dakin hutu ai,inaga ya kamata sukai masa yaran.......kai saddiqu" Ya kira saddiq da suka lafe shida hudarsa suna tattauna yadda nasu yaran zasu kasance kyawawa kamar haka,sun saka yaro daya dake hannunsu a tsakiya sunata murmushi kaman wasu shashashai. Kai anni ta dauke tana sakin murmushi gami da girgiza kai,daga hudan har saddiq din akwai wauta tamkar 'ya'yan fari. Saida zamansu ya miqa ta fahimci lallai halayyarsu ta dace da juna sosai,shi yasa har yau bata taba jin kansu ko cikinsu ba.

"Karbeshi kuje kukaiwa babbansu su"

"To abba" Ya fadi yana sanya hannu ya karbeshi daga hannun huda,ji tayi kaman kada ta bada shi,shima ya karanci haka,sai ya saki murmushi murya qasa qasa yace

"Namu yana hanya in sha Allah". Murmushi ta saka cikin tsananin jin kunyarsa ta kauda kanta,tana ganin kamar su anni zasuji abinda ya gaya mata.

Dashi da BB farouq suka isa dakin,farouq yara biyu ne saman kafadarsa,yayin da saddiq din yake dauke da guda daya.

Wani irin nutsatstsen yanayi dakin ke dashi,ba yawaitar haske kuma ba yawaiyar duhu,wataqila sun barshi a hakanne saboda cikakken bacci da sukeso sabreen din ta samu.

Yana zaune gaban gadon saman wata farar kujerar,hannunsa cikin tsakiyar nata hannun,ya tattara dukakanin hankalinsa a kanta cikin matsananciyar kulawar da ko cikakken motsi baya so tayi.

Da alama magana sukeyi qasa qasa,wanda a tsakaninsu ne,don kana dakin babu lallai ka iya jin komai. Motsin shigowarsu ya sanyashi daga kanshi,ya zube idanunsa akan yaran dake hannunsu yana jin wani irin abu me nauyi na sauka a qirjinsa.

Cakudadden farinciki ne daya gauraya da nutsuwa da godiya da rahamar Allah a kanshi.

"Wannan duniyar taka ba zata taba barin yarana suyi farinjini a gurinka ba da alama......kawai dadin abun......uba da yawa maganin kukan d'a" BB farouq ya fada yana isa gabanshi ya jeresu daga gefen sabreen din duka su ukun.

"Minti kadan na baka ka gama kallonsu zanzo na debe kayana" Farouq ya fada da wani irin cin serious harda duba agogon hannunsa. Murmushi kawai faud ya saki,zuciyarsa na karyewa,nauyi da kunyar ubangiji tana kamashi,yana jin kaman baiwa Allah komai ba daya cancanci irin wannan kyautar da baiwar ba.

Har yayi taku biyu farouq din ya dakata,ya waiwayo yana dubansa.

"Ko barka kayimin ba.....kuma duk wanda baimin barka ba yana cikin black book dina" Murmushi ya sake qwacewa fu'ad,ya motsa labbansa a nutse.

"Congratulations BB farouq......ina tayaka murna da samun 'ya'ya da kayi". Wani ni'imtaccen murmushi ya bayyana a fuskar farouq din,sai kawai ya dawo da dan sassarfa,kafin yakai ga qarasowa kuwa fu'ad ya rigashi miqewa suka rungume juna sosai.

"Barka da arziqi dude......ina maka fatan alkhairi,ina tayamu murna mu gaba daya.....Allah yasa mu da musulunci gaba daya muyi alfahari dasu"

"Ameen dude......ameen na gode" Fu'ad ya fada yana jin jinin 'yan uwantaka yana yawo a jikinsa. Zare jikinsa farouq yayi,yaja da baya yayi saluting sabreen da sai a sannan ya lura idanunta biyu.

"Well done addarmu......" Ya fada yana qamewa. Murmushi ta saki idanunta na lumshewa saboda nauyi da sukayi mata,ta girgiza kai murya can qasa ta furta.

"Na gode BB". Gira ya dagawa faud tare da babban dan yatsansa sannan ya juya yana fita.

Da fari idanu suka zubawa yaran su duka shida ita,dakin yayi tsit sai qarar na'urar kadan kadan. Gaba dayansu bacci sukeyi,sunyi wani irin matuqar tafiya da zukatansu da wani qaqqarfar soyayyarsu data fusgi zuciyarsu lokaci guda.

Tare suka kai hannuwansu kan yaran,sai suka kalli juna kuma kowannensu ya sakarwa dan uwansa murmushi. Tsam fu'ad ya miqe tsaye,ya gaji da bugawar da zuciyarsa keyi,ya dauki.yaron farko ya mannashi a qirjinsa sosai yana jin dumin jikin yaron da qamshin sabbin tufafinsa.

"My heart beat" Ya furta a sanyaye har na tsahon second sittin sannan ya daukeshi daga qirjin nasa ya maida dubansa kan fuskarsa.

"Wannan hamza ne.....hamza ne wannan,jarumin sadaukin nan,baffan manzan Allah......kuma ubana abbana daya bani sabon ruhi da sabuwar rayuwa" Yayi maganar daga qasan zuciyarsa yana jin soyayyar yaron.

Idanunsa ya cire ya maida kanta,tana daga kwnace tana kallonsu da wani azababben kallo me cike da qauna. Rayuwarta take gani a tattare dasu,ruhinta dama komai nata.......daga sabreen ita daya ya daga darajarta ya maidata me rassa har uku.

Kadan ya Matso gareta,ya manna mata yaron itama a qirjinta.

"Ki masa addu'a.....hassan shine hamza"

"Allah kasa ya biyo halin asalin me sunan"

"Ameen" Ya amsa yana lumshe ido.

Juyawa yayi tana nufar gadonsu,ya kwantar dashi sosai yana gyara masa lullubarsa sannan ya dawo kan yaro na biyu.

"My world......dukkansu kamarsu daya.....kama suke da juna ta sosai da sosai......kinga har wani digo dake fuskarsu ma iri daya ne" Ya furta yana dubanta. Ajiyar zuciya ta sauke,ta gani itama,ta gani fadi ne akwai batayi ba.

"Wannan babban aminina ne,dan uwana kuma masoyina.....umar alfarouq" A wannan karon ita kanta saida murmushi ya subuce mata

"Wai Allah hamma......zaka kawo rigima fa.....tabbas BB bazai boye soyayyar hussain a zuciyarsa ba".

"Na sani ameenatu" Ya amsa mata shima yana imagining fuskar farouq,don ba zata yayiwa kowa,shi kansa baisan gender na yaran ba sai bayan an haifesu bare wani yaji sunan da zai sanya musu.

Shima sai daya mannashi sosai a qirjinsa sannan itama ya saka mata su,ya kuma sanyata ta masa addu'a kaman dan uwansa sannan yaje ya hadashi da dan uwansa ya dawo kan na ukun.

"Gamboliya gambo" Ya furta da wani irin nishadi a muryarsa daya sake saka sabreen din ita kanta a nishadi,duniyar duka sai take jinta kamar tasu ce su biyar dinnan suda yaransu.

"Shi wannan......abbana ne......sanadi na.......masoyina almustapha muhammad jadda" Ya qarasa fada yana kissing nasa sannan ya maidashi qirjinsa yayi masa kyakkyawar runguma. Tana iya hangen hawaye qasan idanunsa,wanda ta tabbatar na rauni ne. Wani tsohon miki ko rauni dake danqare qasan zuciyarsa.

Tanaso ta sassauta masa don haka tagi gyaran murya kadan,sai ya ware idanunsa da suka canza launi akan fuskarta.

"Amma hamma.....anya ba za'a samu jam'iyyu ba.....zakaso abba da yawa fa....." Murmushi ya qwace masa,ya dauke almustapha daga qirjinsa yana cewa.

"Wadannan dukkaninsu masoyana ne......idan kika cire daya daya daga cikinsu to tabbas babu fu'ad......tarihin muhammad jadda bai kammala ba,bazai kuma taba zama kammalalle ba". Ta aminta da maganarsa dari bisa dari,ya matso ya aza mata almustapha din saman qirjinta,shima ta bishi da addu'a.

Dawowa yayi saman kanta,yana shafa doguwar sassalkar sumarta a hankali.

"Kiyi bacci my world.....yi bacci duniyata.....kin cancanci ki huta,kiyi bacci me dadin gaske,mijinki yana daga bakin qofa yan gadinki,ko yatsarki kika motsa zan jiki......ki raya a ranki duk duniya ba wata mace me gatanki......ke 'yar gatan mijinki ce......mata tabbas rakiya sukayo miki zuwa duniya". Wani sassanyan ruwan nutsuwa maganarsa ta sakar mata a tsakiyar zuciyarta,ta lumshe ido tana sakin murmushi bar batasan sanda baccin yayi awon gaba da ita ba.

Ai duk yadda sabreen ta wassafa za'a sha drama da farouq sanda yaji an masa takwara abun ya wuce nan. Gaba daya farouq ya koma qaramin nanny........dariya kawai data sha banda Allah yasa tana qoqarin kiyayewa saboda dinkinta ma da batasan adadin yawanta ba. Duka sunqi gida,asibitin ya zame musu a kwanaki hudun da sukayi,kafin likitoci su taru suyi qaramar walima cikin asibitin da yaran da iyayensu dasu anni,sannan aka musu takardar haihuwa,da shaidar zama cikakkun 'yan qasa......daga bisani kuma suna shirin tafiya saiga galla galla motoci na billions of naira guda uku kyauta daga masarautar saudiyya,saqo daga sarki abdul'azeez zuwa ga d'iyoyin muhammas fu'ad da aka haifa a qasarsa.

Labari ne daya zama abun dauka ga kafafen yada labarai na qasar saudiyya,labarin kuma ya lula ya dira kai tsaye akan akwatin talbijin din da aka kunnawa maamah saboda debe kewa da zaman tunani.

Tana daga zaunen jikinta dukka ya dauki kyarma. A sanda sukayi waya da fu'ad din don yaji lafiyarta,ya gaya mata sabreen din ta haihu,amma batasan me ta haifa ba,mace ne ko namiji,in fact ma ita bata dauki abun serious ba,sai yanzu da idanunta ke nuna mata kyawawan yaran tamkar photocopy na muhammad din sanda ta haifeshi akayo aka manna musu.

Maida idanunta ga rubutun dake wcewa tayi.

"Yara maza!!....Yan ukun shahararren attajirin dan kasuwar sarrafa gold da diamond da qasar saudiyya garin madeena ya zame musu mahaifarsu".

" Tayi nasara a kaina......taci nasara kaman yadda boka ke gayamin,dukiya ta zama tata......Muhammad fu'ad ya zama nata" Abinda take maimaitawa kenan jikinta dukka yana rawa kamar wadda aka sawa shocking. Gumi kuwa tuni ya jiqa gaban cotton gown din dake a jikinta,numfashinta tana jin yana mata nauyi har tana zuqarsa da qyar.

Tashinsu kenan a wajen masu kula da ita zasuyi sallah wasu kuma su hada mata abincin rana,me sallar tana dawowa ta sameta a haka tana qamewa kamar wadda aka hadawa shocking.

Hankali a tashe ta dauki wayar da fa'ad ya nuna musu yadda zasu kira likita,musamman aka hadata kawai saboda yiwa likitan kiran gaggawa.

He's always available likitan,saboda albashi kawai jadda ya yanka masa yake biyansa monthly,ko yayi aikin duba maamah ko baiyi ba,kawai buqatar fu'ad din shine ko yaushe ya zama available duk sanda aka kirashi.

Ba jimawa ya iso,ya kuma bata dukka taimakon da zai bata aka samu ta dawo da qyar,saidai danci gaban da ake sanya ran samu komai ya dagule ya koma baya.

Shi mamaki matar take bashi,ba abinda ta rasa na kulawa daga 'ya'yanta,jin dadin rayuwa iya jin dadi,amma taqi kwantar da hankalinta ta warke.

Guri yasa aka basu daga shi sai ita,da zuciya daya yakeson mata fada wala'alla zataji.

"Hajiya.....kiyiwa Allah ki rufawa kanki asiri kaman yadda Allah ya rufa miki......ko kinaso kikai kanki lahira ne?,kina sha'awar kwanan kabari da maqabarta?,wacce irin damuwa kike da ita haka a zuciyarki data hanaki sukuni?,anya ba ciwon hassada bane silar damuwarki?,to amma idan hassadar ce ma waye zaki yiwa ita?,mutum nawa kikafi a rayuwa amma ke baki gani ba?,to na rantse da Allah muddin baki sassautawa wannan zuciyar taki ba zakita shan wahala ne,ana aiki yana dawowa baya ba wani ci gaba" Ya fada cikin jin haushinta da takaicinta ya miqe yana barin parlor din bayan ya ajiye duka magungunan da zasu bata.
160


Idanunta suna kan likitan har zuwa sanda ya kammala ficewa. Numfashi taja sosai tana saukeshi,wani bacin rai yana qoqarin taso mata amma tana danneshi.

"Ba yanzu ba mariya......ba yanzu ba,ki danneshi don ki samu lafiya......ki danneshi don jikinki ya daidaita,akwai abubuwa da dama da kike buqatar aiwatarwa,lafiyarki kuma ita ce jagora,idan babu ita ba abinda zaki iyayi" Ta yarda da wannan sashen zuciyar dake mata wannan bayanin,ta aminta da abinda yake gaya mata. Maganganun likitan sun tsaye mata a rai,lallai ne baisan wacece ita ba.....baisan wacece mariya ba,wato kawai idan baka da lafiya sai abinda ka gani?,idan ba zaka iya yiwa kanka komai ba......idan ba zaka iya cewa komai ba kawai sai abinda ka gani?. Maganar da take nanatawa kanta kenan tana tuhumar wannan ciwon.....ciwon da yayi mata dirar mikiya a sanda ya kasance takun taqi kadanne tsakaninta da arziqinta,takun taqi kadanne tsakaninta da cikar burinta fa......to kuwa me zai hana su kasa fahimtar asiri akayi mata ba hawan jini bane.

Duk inda ta juya ya waiwaya fuskokin yaran take gani,ba daman ta rufe idanunta sai taga yaran guda uku sak masu kama da fu'ad,ajiyar zuciya ta dinga saukewa tana jin wani razana yana kamata.

Fu'ad ya riga daya samu magada,ko mutuwa yayi a yanzu ba a abinda mutuwarsa zata qara mata illa tsira da kaso daya bisa shida na dukiyarsa.......babban sake da kuskuren shine barin yaran suka iso duniya.....kuma duniyarma ta shaida.

Ko sanda ta samu bacci yayi awon gaba da ita su ta dinga mafarki,a mafarkinma su shida suka koma,wani akan qafarta wani a bayanta,wani a zaune saman kanta,wani a gefenta haka dai,na saman kan nata ne ya sheqo mata kashi daya rufe fuskarta da jikinta gaba daya,abinda ya sakata farkawa kenan.

Jikinta rawa yakeyi sosai,ta jiqe da gumi cikin tashin hankali,takai idanunta inda su sahura ke bacci,tanason tashinsu amma bata da wannan ikon.

"Meye fassarar kashi a jiki?,anya ba ajalina aka haifo yaran nan suyi ba?" Ta tambayi kanta da kanta can qasan zuciyarta. Juya mafarkin taci gaba dayi da ma'anoni daban daban,hankalinta kuma yana sake tashi,har sanda Allah ya tashi sahurar ta dubata ta bata ruwa ta sake gyara mata kwanciya. Tanata kallon sahurar,tanaso ta tambayeta fassarar mafarkin kashi,amma ba bakin magana,haka ta maida idanunta ta kulle tana jin zuciyarta tana mata quna,tana Allah wadarai da rashin damar yin magana da bata dashi.

"Mafarkin kashi fa arziqi ne....alheri ne" Wata zuciyar ta gaya mata tana tunasar da ita shekarun baya can sanda fu'ad yana yaro. Tasha yin wannna mafarkin a kanshi,duk sanda ta farka kuwa an yita tafka tsiya kenan ita da abbansu.

"Ni wannan yaron bansan meye tattare dashi ba......kai baka da aiki saidai ayita mafarkin ka shafe jikinka da kashi koka shafeni?,inda Alla yake taimakona wankewa nake zuwa ni nayi a mafarkin ina dalili?,kai kuwa kaida Musaddiq duk yadda zan jaku ku wanke qi kukeyi.....kashi ai masifa ne qazanta ne". Tofa a ranar haka zata yita maganganu,hantara da kyara kuwa ranar fu'ad ya gamu dashi kenan har sai ya fita a gidan ya wuni a layi sannan hankalinta yake kwanciya. Ba fadan da abban baiyi mata ba amma bata ji ba,dole ya kawo idanu ya zuba mata,shi kuma bai taba gaya mata cewa ana tunanin arziqi bane.

Abun ya tsaye mata akan jariran,tanason gasgatawa amma kuma tana qaryata hasashen nata.


&Sati biyu sukayi a madeena kaman yadda fu'ad ya tsara. Cikin sati biyun yake sanya ran sabreen taji qarfin jikinta,hakanan yaran sun sake qwari.

Hakanne kuwa ya kasance,zuwa lokacin sabreen din ta warke sosai saboda irin kulawar data samu daga kowanne bangare,duk da cewa anni tun suna da sati guda ta koma Nigeria. Tana da buri sosai na hadawa yaran gagarumar walima,saidai taje ta tarar amna ta gama shirya komai da taimakawar musaddiq. Wani irin gagarumin suna da akayi sati guda ana shelarsa,sunan da duniya ta jima bataga irinsa ba.

Cikin sati gudar nan fadin irin dukiyar da fu'ad ya sadaukar ma bata baki ne,irin yawan kyauta da yayi abun ba'a cewa komai,mutane da dama ya fidda da prison,mutane masu yawan gaske ya biyawa bashi,mutane masu yawa ya siyawa gidajen zama,mutane masu yawa ya dauki nauyin aurar da 'ya'yansu,a cikin dangi kuma ya sake ninka adadin mutanen da ake bawa kujerar hajji da adadin ninki uku. Mutane da yawan gaske ya dauka nauyin maganinsu da samar musu lafiya,hakanan ya qara yawan adadin marayun da nauyinsu ke wuyansa. A sannan sai ya ke qara jin yana da kyau idan sabreen ta koma hankalinta su zauna,foundation yake da sha'awar ya bude mata saboda taimakon iyayen marayun da marayun kansu.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login