Showing 114001 words to 117000 words out of 363280 words

Chapter 39 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1419

dan duban fuskarta kadan wajen daya lura a jiya ya fashe,baiga komai ba don ta rufe wajen da dan kwali,sai ya dauke dubansa daga kanta zuciyarsa tana masa zafi.

Ba abinda ya hanga saman fuskartata sai guntuwar wiwin daya gani jiya a bakinta,zuciyarsa ta sake matsewa,baya jin zai samu wani nutsuwa a zuciyarsa muddin bai samu cikakken bayani abinda yake faruwa ba ko kuma ya farun.

Hankalinsa ya maida kan annin ya soma gaidata cikin nutsuwa da girmamawa. Yaji dadin yadda farouq bai daga mata hankali ba ya gaya mata abinda ya faru a gidan ba jiya da daddare,yadai gaya mata kawai sabreen dinne bata da lafiya

"Allah ya qara lafiya.....sai ka kula da ita sosai.....inajin idan zai yiwu ma nabar amna a gidan,don a yanayin mace irin haka zaman kadaici qara miki ciwo kawai yakeyi". Dan satan kallon anni yayi,ya fuskanci tunda ta zauna a wajen kawai kallon me ciki take yiwa sabreen din,inda anni tasan cakwakiyar da yake ciki zama zatayi tayita masa kuka.

Kwata kwata a birkice yake kan lamarin,kusan komai nema yake ya dagule masa,yana jin kamar kwanyarsa ta daina aiki yadda ya kamata. Ya lumshe idanunsa yana jin ciwon yadda mahaifiyarsa ta xama silar qulluwar alaqa tsakaninsa da yarinyar da kullum munanan boyayyun halayenta sake bayyana sukeyi.

"Ashsha......da kinyi zamanki ai,ina ke ina hidima damu ke da ba cikakkiyar lafiya gareki ba?" Anni ta fadi sanda Sabreen din ta fito daga kitchen ta ajiye mata tray dake dauke da spicy black tea soyayyen qwai da kuma farfesun kan rago wanda ta yi tun shekaran jiya waccan amma ta kasa ci,kasancewar ita din cin abinci ba damunta yayi ba. Zataci din amma gutsul gutsul kamar na dan qaramin yaro,shi yasa ko yaya ita ko ma'u suka girka abu sai yayi musu yawa.

Sallamar da akayi daga bakin qofa ya maida hankalinsu can.

"Sannunku dai.....gafaranku" Zuwairan ke fadi tana rarraba idanu. Zuciyarta cike fal da fargaban kada shigowarta ya zama silar barinta aiki.....amma kuma tana jin relief na wani fannin idan ta tuna tana da assurance na bazaice komai ba muddin annin tazo gaidawa.

Zubewa ta gaidashi,amsawa daya yayi mata,ganin hakan sai ta tattara hankalinta ta maida kan annin tana zuba gaisuwa.

"Ya mukaji da wannan abu?" Zuwairan ta fada duk da a tsorace take.

"Ke!" Fuad ya fadi da kakkaurar muryarsan nan dake saurin isar da saqo gun wanda aka kira saboda zurfin muryar da wani irin kaifi


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


62



"Eh......na'am" Ta fadi adan zabure

"Kin taba samun matsalan qwaqwalwa?" Ya tambayeta kai tsaye da wani kallo da yaso rikita duk lissafinta. Kai ta fara girgizawa

"Ranka ya dade.....aah"

"Good" Ya jinjina kai

"Bacen a gun" Ya fada a taqaice wanda yana kaiwa qarshe tana miqewa da hanzari gami da cewa

"Tuba nake.....tuba nake". Daga shi anni har amna binta sukayi da kallo,a mamakance anni ta maido dubanta kansa bayan ta fice

"Allah me mutane.....ina ka samo wannan Muhammadu?"

"Maamah ce....." Ya fadi a taqaice yana jin wani abu game da matar tare da bin hanyar da ta wuce da kallo kaman tana wajen har a lokacin. Tun bai qarasa ba ta fahimci inda zancan ya dosa,kai kawai ta gyada tana fadin

"Allah ya rufa asiri......mu zamu wuce.....diyata" Anni ta fadi tana murmushi. Qasa sabreen ta sakeyi da kanta tana dan qaramin murmushi. Karon farko idanunsa suka soma kaiwa kanta,karon farko kuma yaga wani abu me.kama da murmushi akan fuskarta......hakanan lokaci na farko da yaga wani alamu na wata aba wai ita KUNYA a tare da ita. Tsaki yaja qasan ranshi,bayajin wannan abun da takeyi har qasan ranta take yinsa,yadda ta wani sunkuyar da kanta,abinda bai taba gani ba a tare da ita sai yau.

"Allah ya qara sauqi kinji.....ki kula da jikinki da kyau" Anni ta fadi tana jin yaqinin kamar abinda dai take hasashen ne yake tare da sabreen. Har cikin zuciyarta takejin yarinyar,tana kuma jin kamar ta taba ganinta a wani wajen kafin yanxu,amma kuma ta gaza tunawa.

"Ameen anni.....na gode" Siririyar muryarta da yau kadai tayi wani irin laushi ta fito tana furta hakan har yanzu kanta a qasa.

Dukkaninsu suka takawa anni xuwa inda lafiyayyar BMW dinta take jiranta da masu tsaro lafiyarta mutum biyu

"Zamu tafi tare da amna din.....amma anjima da dare in sha Allah zata dawo,sai kinfi jin dadin xaman......nasan halin Muhammadu....indai kin ganshi gida zaune to saidai annual leave dinshi yazo ko kuma baida lafiya da gasken gaske". Haka kawai ta samu kanta da kallonshi ta gefen idonta. Duk da ba dogon zama sukayi ba,gajeran zama ne maras dadi da ma'ana,zaman da baida wani alqibla ko kadan,amma ta karanci dabi'u masu yawa tattare dashi. Aiki kaman baisan ciwon kansa ba,kamar kuma yafi kowa sanin muhimmancin lokaci,bata taba ganinsa ba system ko takardu ba.....sannan zaman kadaici baya damunsa sam sam.

Suna a tsaye motar ta soma motsawa tana fita ta tafkeken gate din gidan. Idanunta akan bayan motar,tana jin kaman ta hanasu tafiya ita da amna din,dan wanzuwarsu na qananun mintuna kadai sai taji kaman an rage mata wani nauyi da takeji a zuciyarta. Lallai maraici babbar masifa ce,ciwo ne wanda bashi da magani har xuwa randa naka ajalin xai ruskeka,wanda ya rasa uwa shi daya yasan irin asarar daya tafka da ba zata fadu ba.

Sai da motar ta gama ficewa tas sannan ta tuna a inda take a tsaye,da kuma wajen waye take?. Ba tare data juya ta kalli inda yake a tsayen ba ta juya a hankali tana komawa ciki.

Da kallo ya bita ranshi yana sake masa susa......idanunsa suka sauka kan hips dinta da suka bayyana sosai saboda mayafin dake saman kanta bame girma bane,take zuciyarsa ta wullo masa hoton hijabinta na jiya da yasha cukuikuiya,wani zazzafan abu me tauri ya taso masa da ya sanya ya gaza riqe kansa,sai kawai yabi bayanta yana jin ya zama dole lallai lallai yasan kome.

Tana dab da isa qofar da zata sadata da parlor dinsu na farko ya cimmata. Bata zaceshi ba ta tsinceshi a gabanta. Kallon kallo suka yiwa junansu,wani irin kallo na tsakiyar idanu,tsakanin shi da ita kowa zuciyarsa na dauke da wani irin nauyi da baisan yadda zai rageshi ba.

Ta dauka zata iya jurewa ci gaba da kallon tsakiyar idanun nasa amma sai taji ta sare nan da nan,ta janyesu bugun zuciyarta na daduwa wanda batasan meye sila ba. Qasa tayi da kanta,so samu ta rabeshi ta wuce saboda fushi take gani cikin idanunsa,ita kuma yanzu qirjinta bazai iya daukan fada masifa ko tashin hankali ba hakanan. Kai kawo kawai adams apple dinsa keyi alamun akwai abinda yaketa qoqarin hadiyewa,jiyan ce kawai ke dawo masa,yana tuna sanda ya dagata towel din jikinta daya xame warwas a qasa,daga ita sai hijabi. Sai daya tabbatar yayi babban aikin rage fushinsa da abinda yakeji sannan ya soma magana,cikin bacin rai amma kuma yanata kokawar kalmasa harshensa,don bayani yake buqatar ji,duk da cewa ta kowacce fuska.....duk kuma inda ya juya.....kowacce hujja idan ya daga,ya tattaro ta nan data can ba abinda take sake nuna masa sai ainihin WACECE ITA.

"Wancan lokacin.......na taba ganinsa cikin hotel a abuja yana cigiyar karuwarshi da suka kama daki,ta kwashe masa kudade masu yawa kwatankwacin yadda ya faru da kamfanin JADDA DIAMOND CHORES RESOURCES,sanda naga fuskan wayar ba kowa bace a ciki sai KE!......Wanene shi?,ya akayi ya shigomin cikin gidana?,cikin dakin da aka gina da tsaftatacciyar dukiya ta halak?".

Wani irin duka tambayar tasa tayi mata,wadda tazo mata hade da labarin da batasan ya faru ba......eh ta taba binsa abuja.....kuma aikin mashkur kusan shine aiki na qarshe da tayi har yau kuma bata sake sha'awar maimaita wani abu makamancinsa ba.......amma yaushe ya fiddo hotonta ya nunata a matsayin karuwa yana cigiyarta?. KARUWA kalma mafi muni da tafi tsana taji ta gilma a kunnuwanta......duk yadda takai tsakaninka da ita muddin xaka kira wannan sunan a gaban fuskarta......to takan iya manta ya kuke da ita?.

"Am asking you......" Ya fada yana jin ya soma hasala ganin shurun da tayi kamar ba da ita yake magana ba.

"Ban sani ba......." Ta bashi amsa muryarta tana so ta fara rawa. Me zata gaya masa wanda zai sanya ya fahimceta?.

"Baki sani ba kaman yaya?,ya shigo har dakin ba tare an fasa kowanne gini na gidan nan ba......ya shigo dakinki ba tare da kinyi yunqurin kiran koda security daya na gidan nan ba......ya shigo dakinki daidai lokacin kwanciyar baccinki?,a sanda kike daure da towel kadai da hijabi?" Ya qarasa maganar yana qarasawa dab da ita,yana kuma kaiwa qarshe a tsawace har sai data lumshe idanunta ta kuma gaza budesu.

Tsawa......tsawa,bata son tsawa,bata qaunarta,tsawar ma daga wajen d'a namiji.....wanda tuni ta karanci sun jima da raina ajawalin mata. Wani abu data jima da shawa kanta alwashi,raini.....wulaqanci.....izgili da toxarci na da namiji,ita ko 'yan uwanta ba wanda zata lamunta ya daukesu.

"Ban sani ba nima" Ta sake maimaita masa don da gasken batasan yadda akayi mashkur ya shigo ba.

"Harda wayar daya baki kenan itama ita ta kawo kanta?!.....nace ita ta kawo kanta?!!!" Ya fadi da qarfi kaman yana shirin fasa mata kunnuwa.

"Stop it!.....wanne kakeso na amsa maka?,wacce tuhuma kakeso na baka amsarta?!" Itama ta maida masa muryarta na rawa,oily eyes dinta suna qara walainiya cikin hasken ranar daya fara dagawa.

"Ni kikewa shouting?" Ya tambayeta da tsananin mamaki,saidai kuma qarar wayarsa ta janye magana ta gaba da yaso fadi. Bai fiya daga waya a cikin irin wannan yanayin da yake cikin tsananin fushi ba......amma yana expecting kira me muhimmanci daga gurin wani dan kasuwa mazaunin qasar ivory Coast,dole ya ciro wayar.

Shi da ita dukansu akan sunan FAREEDA KHALEED MUSTAPHA ya sauka,ita ta fara janye idanunta tana jin wata wani fushinta yana ninkuwa.

Ya sanyata a gaba da tarin tambayoyinsa amma shi a daidai lokacin karuwarshi ko yarinyarsa.....batasan da wanne suna zata kirata ba ita ke kiransa?.

Ta nashi bangaren banda muhimmancin da wayar ke dashi a wajensa tabbas ba abinda zai hanashi tarwatsata ita kanta wayar a wajen bama fareeda kawai ba.

"Sorry sir" Yaji an fada da sauri,abinda yakai hankalinsu kenan wajen. Me sunan malam ne,da sassarfa yake barin wajen saboda kunyar yadda ya samesu a tsaye dab da juna,baisan kuma zai samesu a hakan ba da bai biyo ta wajen ba.

"Zo nan" Ya kirashi a nutse yana duban hannunsa dake dauke da newspaper daya saba ajiye masa duk safiya daga kamfanin jaridu daban daban.

Sunkuyawa tayi ta zame ta gefansa tana takawa don barin wajen,haka kawai taji bama zata iya zama ta fuskanceshi ba sam. Kwata kwata bata yarda dashi ba Shima.....wacece faridan?,meye alaqarsu da koda yaushe layinsa cikin karbar kiranta yake?. Yana jin wucewarta amma bai waiwaya ba don hankalinsa yana kan me sunan malam.

"Good morning sir" Ya sake gaidashi cikin girmamawa yana rusunawa ba tare daya miqa masa newspaper din ba kaman yadda ya saba,duk da yawancin lokuta ma yana samunsu ne a daura da dining suna jiran fitowarsa,idan ga kammala dubawa kuma zai kwashesu sai kuma fitowar gobe.

"Morning.....how you doing?"

"Fine sir" Still ya kuma amsa masa amma ba alamun zai miqa masa su. Abun yadan bawa fuad mamaki,yana shirin miqa masa hannunsa don ya bashi kira ya kuma shigo masa.

Kai tsaye aka gaya masa farouq ne don haka ya daga ba wani bata lokaci

"Good morning dude" Farouq ya furta kaman yadda ya saba masa,saidai kuma daga can qasan muryarsa kaman yana iya tsinto wani abun

"Morning......mun tashi lafiya?"

"Fine.....ya jikin naka?,ka fita ne ko ka sauko daga stairs?" Duka farouq din ya cure tambayoyin ya masa,abinda yaja hankalin fu'ad kenan.

"Ban fita ba......na sauko qasa na rako anni yanxun xan koma ciki".

"Good.....but do me a favor mana" Ya fada yana fatan idanunsa basuga abinda ya gani ba.

"Ehnnnnn" Fu'ad ya fada yana jin zaquwa na jin abinda zai fito a bakinsa.

"Kayi skipping duba newspapers na yau mana......instead of that ka bani aron time din muyi magana" Yadda farouq yayi maganan kawai ya sanyashi yasha jinin jikinsa,sai kawai ya miqawa me sunan malam hannunsa yana masa nuni da newspapers din da yake rqe dasu yana kafeshi da idanun nan nasa da kwarjini ke cike dasu kullum ba tare da ya sauke wayar a kunnensa ba.

"Kowanne lokaci na yini na zan iya baka farouq,not the only news time" Ya bashi amsa sanda me sunan malam ya miqo masa newspapers din da hannu biyu cikin mutuwar jiki,ya kuma janye daga wajen da sassarfa don bazai iya tsaiwa yana dubansa a sanda yake kallon labarin dake buge a jaridar ba.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

63



"Wannan abun kawai nake buqata please" Farouq ya maimaita sanda ya shiga motarsa dake farfajiyar gidan. So yake yaja maganan da tsaho sannan ya cimmasa kafin ya duba abinda ke faruwan saidai sanda yake bashi amsa na qarshe yana bashi amsar ne sanda idanunsa suka sauka akan tittle na labarin da yaci shafin farko gaba dayansa na jaridun guda biyu.

*_TSINTAR DAMI A KALA_*

_BABBAR JARABAWA......SHIN KUSAN WACECE ASALIN MATAR MATASHIN MILLIONAIRE DINNAN MAMALLAKIN KAMFANINNIKAN DAKE SARRAFA GWALA GWALAI?_

"Farouq.....you have my time,amma kafin sannan......" Maganar ta yanke masa sanda makeken hotonta ya biyo bayan title din ita da mashkur.

Hoto ne da aka daukeshi gaban wani hotel da sunan kawai ya iya kalla ba tare daya tantance wanne bane.......sanda ya bude mata murfin motar ita kuma tana qoqarin fitowa a motar yana riqe da handbag dinta.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" Ya fada yana jin dukka gabbansa suna daukan dumi kafin daga baya kuma suyi wani irin sanyi kaman ba'a jikinsa suke ba.

_mrs muhammad fu'ad jadda sabreen ahmad_.

Baya jin idanunsa zasu iya ci gaba da kallon abinda ke gabansa,sai kawai ya hade newspapers din waje daya ya curesu a hannunsa yana takawa zuwa cikin gidan ba tare daya tsaya tuna cewa magana suke da farouq ba,kuma yabar farouq din akan line na waya.

Shuuuu din da farouq yakeji ya sanyashi qarfafa zarginsa akwai abinda ya faru,sai kawai ya aje wayar ba tare daya kasheta ba,ya tada motar da wani irin hanzari wanda yanayin gaggawar da security na gidan suka ga yanayi ya sakasu dage masa qofa ya fice tun bai qaraso ba.

Bazaice ga wani abu da ya faru daga sanda yakai kansa samansa ba banda azababben ciwon kai da yake masa kutufo kota ina. Ba abinda bakinsa ke furtawa sai Astgafirullah yana me kyautata zaton akwai wani abu daya aikatawa ubangiji wanda ba daidai ba shi yasa ya jarabceshi da wadannan abubuwan. Dukka komai akan yarinya daya?.......yarinyar da koda ta zame masa zabi a nasa qashin kan hakan ba lallai ya tabbataba banda miqewa da kafewar maamah akan lamarin?.

Da qyar ya iya amsa sallamar farouq sanda ya bude smart door din ya qaraso cikin parlor din idanunsa akan fu'ad. A yadda yaga idanunsa sun jirkita ya tabbatar labarin ya gama ruskarsa.

Da idanu yabi farouq din,har zuwa sanda ya qaraso,ya tsugunna ya debi duqunqunannun jaridun ya bude ya kuma rufesu a take.

"Da gayya aka buga wannan news din......."

"To menene qaryar da sukayi a ciki?.....ban karanta sauran labarinta a qasa da suka saka ba.......amma wanne ne qarya farouq?" Maida dubansa yayi kan fu'ad da yake dubansa kai tsaye. A zahiri jijiyoyin kansa ke tashi sosai har sun nuna ta farar fatarsa,wanda abadini yake nuna ciwon kai yakeyi sosai,irin ciwon kan da ya dinga addaba masa sanda yake fama da matsalar depression dinsa,wanda ya tabbatar ya jima rabonsa dashi.....

Sakin baki yayi yana kallon fu'ad din daya fara magana cikin sanyi saidai akwai zafi me yawa a kalamansa.

"Stop dude.....ina gaya maka.....don't judge book by his cover.........ka daina judging mutane haka"

"Judging nasu nake ma?,bayan ina da full details na evidence akan duk maganan da nakeyi farouq akan yarinyar?" Yayi maganan da sanyin dai,amma lafuzzansa na nuna zallar zafin da yakeji.

"Evidence kadai bazasu tabbatar da hakan ba.......kayi managing personal boundaries tsakaninku kaman na kowanne miji da mata,akwai buqatar wani sensitive......"

"Haba mana!" Fu'ad da yakeji zuciyarsa na matsewa kaman zata fashe ya tsaida farouq yana zama sosai yana jin jiri daga inda yake zaunen.

"Kada bakinka yakai nan wajen.......bakasan wacece ita bane farouq?,bakasan sunan da kowa yake kiranta dashi ba?,baka gani jikin newspapers ba?"

"Na gani.....na kuma sani......kuma ka rigani sanin haka kace zaka daukota ka gyarata......ya akayi ka kasa fu'ad?" Ya jefa masa tambayar yana riqe habarsa. Kansa ya jijjiga sosai yana duban farouq

"Ban


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login