Showing 156001 words to 159000 words out of 363280 words

Chapter 53 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1414

jikinsa a kunyace. Yadda anni ta zuba masa idanu yasan tuhumarsa takeyi ba tare data jefa masa kalmar tambaya akan tuhumar tasa ba. Ta janye Idanunta ta mayar kan sabreen

"Lafiya?" Tambayar ta yiwa sabreen nauyi,batasan me zatace mata ba,sai tayi qasa da kanta ta kasa amsa mata.

"Zaka iya tafiya abinka,amma kasan ba'a takurawa mara lafiya right?" Tuni ya Fahimci me anni ke nufi,sai kawai ya gyara hannun rigarsa yana fadin

"Afwan" Ya juya yana fita a hankali bayan ya saci kallon sabreen din data kasa cikakken motsi.

Gabanta anni ta qaraso a hankali,taja stool din daya tashi akai ta zauna tana dubanta.

"Sabreen" Ta kirata a tausashe. Da qyar ta motsa labbanta tana amsawa sa

"Na'am" Tana lanqwasa yatsunta,ta tabbatar idanun anni sunkai kan littafin da fu'ad ya aje a gefanta,wanda duk wanda ya kalla zaice ita ta aje din don yafi kusa da ita.

"Ki lallaba jikinki ki warke yadda ya kamata,kada ki yarda kiyi sakacin da dadin bakinsa zai sanya ki bashi dama ya lalata abinda ke jikinki.....dukkaninsu 'ya'yana ne....kuma nasan halin kowa......shi namiji da kike gani dukkaninsu halinsu daya,abu kadanne ya banbanta wannan da wancan" Anni tayi maganar kanta tsaye.

Tsoro da kunya suka cakudu suka sanya hawaye taruwa idanunta,kunyar kada anni ta dauka wani abun suka aikatawa,ko ta bashi daman yin wani abu da ita. Muryarta yana raurau,ida?unta cike da hawaye ta daga kai tana duban gefan annin.

"Wallahi Allah anni ni ban......"

"Shshssh.....bance kiyi rantsuwa ba sabreen,kome meye ya faru babu haramci a ciki,mijinki ne halal din juna kuke......amma nasan halin maza sarai.....akan wannan wajen komai ma zasu iyayi.....kusan a nan aka sanya hankalinsu,a nan ne kuma ke kike da power din iya sarrafasu yadda kikeso.... Dole ki bashi kulawa ta musamman,don ke nan ne naki mulkin yake......a yanayin da kike ciki dinnan kuma ba wani abu bane don ya miki dadin baki ya karba,tsaf kika bashin amshewa zaiyi.....amma sabuwar wahala kuma takice". Gaba daya kunya ta sakata saka hannunta ta rufe fuskarta tana sakin kuka,ya cuceta ya sakata jin nauyin anni,ya sanya anni tana tunanin wani abu a kanta

"Wallahi Allah anni......ni ba komai da......"

"Kul....ni ban tambaya ba,namiki bayanin da zai amfaneki ne,nace kuma ki kula,bance ki fadamin sirrinku ba,maza oya......goge hawayen" Anni ta fada tana tashi zuwa gaban dressing table,ta kuma jawo wata locker dake jiki ta ciro wasu kwalaye guda biyu ta dawo wajen sabreen din wanda ta sanya gefan mayafinta tana share hawayen daya zubo mata. Ba zata sake yarda ko fuskarta ya gani ba bare yasa anni ta zargeta,idan shi baida kunya ita akwai kunya a jininta.

"Daga gobe wannan sabun dashi zaki dinga amfani wajen tsarki,idan kikayi sati daya akwai saqon da zai iso zan baki ki amfani dasu,zan miki bayani suma idan sun iso".

" Na gode" Ta fada tana jin kunya tana dawainiya da ita,amma sai ta lura ita anni ko a jikinta,tamkar yadda uwa zatayi magana da 'yartane wadda shaquwa da fahimtar juna yayi nisa a tsakaninsu.

Kyakkyawar farfajiyar gidan ya fita yana tasbihi qasan ransa,ranshi fes da wani irin farinciki da yaji yana samun mazauni a zuciyarsa. Tabbas ya sake yarda...kudi ko wadata ko wani jin dadi na rayuwa bata taba cika saida macen aure.....cikar kamalar namiji itace aure ya yarda da wannan. A tsakanin jiya da yau,duk da birkitaccen yanayin da komai yazo masa sai yake jinsa a wani cikakken mutum me cikar kamala da mutuntaka,duk wani nauyi dake kowanne gaba na jikinsa kaman an sanya ruwa an wanke masa. Kwanyarsa a yanzu a cike yake da tunanin yadda zai gina kyakkyawar rayuwar auratayya ne kawai,gidan dake cike da soyayya da kuma qaunar juna.....irin qaunar da zata maida gidansu tamkar dausayin aljanna ta duniya. Bai damu ko kadan da dukka wadannan boren nata ba,yayi imani na wani dan lokaci qanqani ne,kuma zata yishi ta gama......komai zai daidaita. Yayi alqawarin dimautata da zazzaqar soyayyar da zata mance kanta gaba daya,ko tanaso ko bataso,ko ta yarda ko kada ta yarda......zai nuna mata qarfin qwajin zuciya da nasa salon na sace zuciyar d'iya mace,a banza ma yake aikata hakan ba tare da yasan yaushe hakan yake faruwa ba?,ballantansa wannan me license?.

Zamanshi kenan cab ya tsaya a qofar gidan nasu.ba wani me maida hankali bane shi kan abubuwan da basu shafeshi ba,don haka ya maida kansa ga wayarsa yana duba sunan da yayi saving number CP s.nuhu. a yanzun yana jin wani qaimi da wani irin priority a kansa na tunkarar dukka badaqalar daya baro a Nigeria. Indai har ya sameta a cikakkiyar mace budurwa wadda mutuncinta bai samu koda rawa ba balle tasgaro to tabbas dukka mutanen can akwai daga inda suka bullo,akwai kuma mabanbantan dalilai da suka shigo da ita rayuwarta. Me suke buqata?,wanne dalilai ke garesu?.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862


5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremu=?O?
_bukhair da muslim_


82


Tun yana daga cikin motar idanunsa suka sauka akan fuskar fu'ad din. Wani irin murmushi da ya fito tun daga qasar zuciyarsa ya wanzu a fuskarsa. Tabbas aure rahama ne kaman yadda mata suke rahama ga rayuwar wanda ya dace dasu. Daga inda yake yana iya hangen wani annuri na musamman na fita daga miskilar fuskar nan da ba'a lamunce mata murmushi ba a kowanne lokaci sai lokaci lokaci idan shi da kansa kuma yaso hakan,amma a yau yana ganin wani sakewa akan fuskar daya tabbatar koshi me fuskar ba lalllai yasan da ita ba.

"That's my bro muhammad fu'ad jadda" Ya fada qasan ransa yana taya fu'ad murna gami da kama murfin motar ya fito. Ci gaba yayi da kallonsa ba tare dashi ya sani ba,idan har za'a tambayeshi mutum na farko dake bashi mamaki a duniyarsa fuad dinne.......mutum na farko da rayuwarsa tamkar madubi ce a wajensa.....mutum na farko da tausayinsa bai taba raguwa a ransa ba fuad dinne. Yana da sauqi kayi masa mummunar fassara idan bakasan halinsa ba,bakasan wanene shi ba,amma kuma kuna wuce wannan level din dashi zaka fahimci mutane irinsa a duniya qalilanne.

"Ka kama kanka farouq.....banda tsokana da yawa,kafi kowa sanin wayeshi" Ya gayawa kansa da kansa saboda yadda yakejin wata dariya nason fara taso masa tun bai qarasa wajen da fu'ad din yake ba

"Ka wuceshi kawai kaman baka ganshi ba indai kasan ba zaka iya riqe dariyarka ba" Wani sashen na zuciyarsa ya bashi shawara don da gaske dariyar nan bayajin zata riqu. Yafi yarda da shawarar zuciyarsa ta biyu,don haka ya zaro wayarsa yahau kiran fannah ba tare daya shirya ba,a sannan harsu amna sun wuce cikin gidan.

Baisan adadin sau nawa murmushi ya kubcewa fuskarsa ba. Duk da waya ce a hannunsa amma ba abinda yake gilmawa idanunsa sai ita din. A wannin da suka shude masa sunyi masa wani irin tasiri da har ya mutu ba zasu taba goge masa ba. Wasu irin mintuna na musamman da suka fara cikin fushi suka kuma qare da wani abu me matuqar ban mamaki da bai taba kawoshi ba a ransa.

Bai lura da saqon ba don haka cikin sauqi hannunsa ya danna saqon ba tare da ya shirya ba

*_Kada ka taba tunanin zaka subucemin.....kada ka taba tunanin zaka kubcemin........a shirye nake nayi komai don na mallakeka.....ciki kuwa harda taba alaqar dake tsakaninka da KARUWAR da kake kira matar aure a gareka,fareeda khaleed mustapha_

Wani irin kallo yakewa saqon yana sake karantashi daga farkonsa zuwa qarshensa,

"Karuwa?" Ya maimaita sunan da wani irin yanayi da yakejin kaman ana yankar naman zuciyarsa.

"Fareeda?" Ya sake maimaita nata sunan yana jin wani irin fushi yana taso masa. Fareeda da ire irenta baya jin zai dagawa waninsu qafa da kalmar KARUWA ta fita a bakinsa muddin suna nufin kalmar ne akan SABREEN. Zaiyi shari'a da kowa a kanta......zai kuma tsaya mata akan duk wanda ya jefeta da wannan kalmar. Har ya fara laluben number fareeda din kai tsaye Muryarshi kawai yaji ya daga kai yana kallonsa. Farouq ne,shi kuwa da gasken gaske wai bai ganshi ba,ya daga hanci sama yana amsa wayar kanshi a sama yana duban qofar gidan.

Ganinsa kawai sai yaji fushinsa ya soma sassauta,dan uwa kuma abokin kuka tun daha quruciyarsa har kwanan gobe bai fasa ba. Tsaf ya gama karantar farouq din,sanin da yayi masa sani ne ba na yau ko na jiya ba,ya gama karantar abinda ya shirya,don haka har ya gotashi ya sanya hannu ya fincikoshi baya gami da zaunar dashi a gefansa.

"Zauna kayi dariyarka yadda kakeso" Ya fada yana shan mur gami da dage girarsa dukka biyun sama tare da qoqarin danne abinda ya taso masa game da saqon fareeda. Maganar fu'ad din sai ta zama kaman tsokana ga farouq din,take kuwa kowacce dariya dake cinsa ta fashe,ya soma qyaqyatata,harda sauka daga kan concrete chair din ya zame yayi Zaman dirshan cikin grass carpet din yana dariyarsa abunsa.

"Kayi me isarka,don wallahi muka shiga ciki kayimin a gaban yaran nan saina faffasa maka baki" Ya sake fada yana hade ranshi

"Aah...me yayi zafi?,bani na kar zomon bafa,wallahi ko ratayar ma ba'a bani ba" Ya fadi yana qoqarin danne dariyarsa. Wani kallo ya watsawa farouq din yanata qoqarin maintaining girmansa.

"Farouq?"

"Allah ya taimakeka" Farouq ya fada yana daga masa hannu da shigen gaisuwar sarakai

"Kada ka batamin mode dina" Ya fada yana ware masa idanunsa duka a kansa.

"Ango ai baka laifi koka kashe dan masu gida......girmanka ne,Allah ya taimakeka tuba nake....." Naushi ya kawo masa Allah ya rufa masa asiri ya kauce ya samu iska,farouq din ya sake komawa da baya yana sassauta dariyar tasa,don magana yakeso suyi me muhimmanci.


& *FAREEDA*

Da qyar ta tattara kanta tana laluben hanyar fita daga dakin. Tunda take a rayuwarta bata taba jin ta muzanta irin na wannan ranar ba,don ko data koma daki kasa hada idanu tayi da lubna qawarta.

"Ke da zaki bude wuta kuyi spending night din gaba daya kya dawo haka da wuri?" Ta tsareta da tambaya sanda ta hautsina kayanta tana laluben inda take ajiye kayan mayenta ko zata samu wani abu da zai dauke mata baqincikin da takeji. Bata samu komai ba,abinda ya sake hautsinata kenan,ta kama gashin kanta ya damqe da qarfi sannan ta sake tana dakawa lubna tsawa

"Get out of my sight.....idiot" Tabe baki lubna tayi tana matsawa gefe. Ta sani indai muhammad jadda ne ta qwallafa rai a kansa yanzun ma ta fara wahala da sonshi,?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
bata taba jin wadda a tarihi ta taba samun koda alamu alamun nasara ba a kansa. Da qyar ta iya hada abinda ya bugar da ita ta zube tana bacci ruhinta cike da cin alwashin cikin mutuncin maamah idan ta farka,tare da shaida mata ta dawo mata da kudadenta da dukka taci muddin ba zata iya mallaka mata d'anta ba. Ta dauka duniya ba wadda take da iko dashi sama da ita....ta kuma dauka mallaka mata shi shine abu mafi sauqi da zata iyayi mata.

*MAAMAH*


Tun saukarta a qasar ba zata ce ga wata cikikakkiyar ibada data iya samu ta aiwatar ba,dukka hankalinta da tunaninta yana a kansu. Me dame yake kashewa ameenatu?,me dame sabreen ki shiryawa a kanshi?,ta bayyana masa sirrinta ne kaman yadda taci alwashi ko.kuwa?. Babban a binda yafi damunta da tsaya mata a rai batun fareeda,gashi har yau din ba taji komai daga gareta ba,bata kirata ba ita kuma bata da number wayarta bare ta fara nemanta. Abu daya ta sani shine.......tabbas.....kofa zatayi yawo tsirarara.....koda malami ko babu.....koda boka ko babu saita nunawa SABREEN DA AMEENATU girman isarta akan danta. Idan har bata sanya fu'ad ya auri fareeda ba ba shakka ita din ba diyas halas bace.

Bayan sallar la'asar kawai saita kasa sukuni,tsakanin jiya da yau kawai saita dinga jin kaman wani abu zai faru ko ya faru,wannan ya sanya ta lalubi number wayarsa ta soma kiransa cikin jin isar mallakinta ne shi ya kamata ya zamanto sai yadda tace ko ta lamunce sannan ayi.

Qarar wayar fu'ad din ta sanya hankalinsa ya koma kan wayar daga kan farouq da ya fahimci iya shege kawai yakeson samun dam yayi masa......baisan yadda zuciyarsa ta tumbatsa da wani irin yanayi akan yarinyar ba?. Komai bai dameshi ba irin yadda zai maidata mallakinsa fiye da yadda ya maidata a yanzun......yanaso ita kanta a jikinta ta sallama cewa ita din mallakarsa ce har abada,sai ya kalli farouq ya daga masa yatsa alamun zai amsa wayar. Kai ya jinjina masa,saidai kafin yakai ga dagawar wayar ta yanke. Qoqarin lalubota yakeyi ya kira sai tex ya fado masa

_"Duk wanda kayi gangancin kamawa ko hukuntawa cikin mutanenmu dake hannunka.......ba shakka labarin matarka zai zama labari na farko da zai zama fitaccen labari kowacce safiya saman jaridun qasar mu da qasashen dake huldar kasuwanci dakai,suke kuma ganin kima da daraja a tare da kai_

Wani irin fusgar hankalinsa saqon yayi,saidai kuma kafin ya sarrafa kwanyarsa ya fahimci komai kiran maamah ya danne saqon,dole ya kauda abinda ke taso masa ya daga kiran yana sawa a kunnensa,bakinsa dauke da addu'ar

"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa'anta taj'alal hazna iza shi'ita sahla". cike da fatan ba wani abu bane na daban zata baro dashi ba bayan abubuwan dake dabaibaye dashi ba.


*_Da sauran masu bibiye da rayuwarsa kenan_*

*_Ya zafafa da gaske wajen yin campaign na samun soyayyar ta,xaiyi nasara ko kuma zata zille masa?_*

*_shin fareeda zatayi nasara ta hannun maamah kuwa?,kaman yadda tayi nasarar sanyashi auren sabreen a wancan lokacin?_*

*_munata gangarowa da MAFARIN warwarar kowanne qulli da tonuwar binnannun asirai_*

*_sai ince muje zuwa dai_*


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

_An rawaito daga manzan Allah S A W yace: Daga cikin mutane ukun da baxasu shiga aljanna ba,kuma Allah bazai musu duban rahama sune 1_ _"WANDA YAKE ZINA TUN YANA YARO HAR YA TSUFA YA MUTU BAI TUBA BA_

_2 _TALAKA ME GIRMAN KAI_

_Bukhari da muslim_


83



Cikin cikikakkiyar nutsuwarsa yayi sallama,zuciyarsa bata fasa neman dauki da ambaton sunan Allah ba.

"Wa'alaikumussalam" Ta amsa masa a dake,tanaso ya fahimci cewa lallai shi din me laifi ne a wajenta.....wannan fahimtar tata da zaiyi ya zama sila kuma jagora zuwa ga wanzuwa da amsar babban burinta a yanxu na auren fareeda.

A nutse ya fara gaidata,ta amsa masa a dake kaman dazun. Shuru ya ratsa na wasu sakanni kafin tace.

"Baku hadu da fareeda bane?" Mamaki kadan ya kamashi,mamakin yadda akayi maamah din tasan da zuwan fareeda Maldives.

"Mun hadu" Ya amsa mata kai tsaye,kasancewar mutum ne shi da wahala ko tsanani basa sakashi yayi qarya.

"Amma me ya hanaka zama me masaukinta?......tunda kana da tabbacin ba don kowa tazo ba sai don kai". Mamaki ya sake kamashi,ya lumshe idanunsa yana jin takaicinsa yana sake daduwa. Gaba daya maamah din kowacce rana sake jirkita takeyi tamkar wahainiya,wasu abubuwan nata da takeyi sai ya dinga ganin tamkar ba cikin hayyacinta take ba. Maamah ke magana,uwar data kawoshi duniya,inda wani ne ya masa magana makamanciyar wannan yana da amsoshi masu yawa da zai bata.

"Bansan da zuwanta.....batayi shawara dani ba kafin ta taho.....and a yanzun ina da iyali maamah,bani da wata alaqa da ita ta kusa ko ta nesa,banda dangantaka da ita" Ya amsa mata da kwantacciyar murya duk da tarin quna da bacin ran da yake ji na cin zuciyarsa.

Idanunta ta qanqance cikin jin tashin hankali yana ratsata a hankali a hankali. Meye yake shurin faruwa?,meye yake faruwa da har yau din fuad da bakinsa ke ambaton INA DA IYALI?. Yaushe ne ta samu wannan matsayin a wajensa?,wata kalma da bata taba jin ta fito daga bakinsa ba?.

Tarin masifa da wani irin tsanar sabreen tana ratsata,batasan wanne kalar abu ya kamata ta yiwa yarinyar ba......a yanzun a dukka illar da aka mata a rayuwa bayan ameenatu sabreen din itace ta biyu,koda ta raba sabreen da fu'ad bata jin taci riba idan tabar yarinyar haka siddan taci gaba da rayuwarta,tana jin ya kamata ta ajewa rayuwarta wani babban tabo ko miki da zai sanya koda a gaba zata zamewa wasu izina a kanta. To amma babban qalubale da barazanarta a yanzu shine TA WACCE HANYA ZATA RABASU?. Haka kawai take jin matsanancin faduwar gaba da fargaba idan ta tuna kalaman sabreen akan auren fu'ad,bawai ta fara son fu'ad bane matsalarta,idan hakan zata kasance ma zai zame mata daidai,tsoron shine shi fu'ad din......yana da wata irin zuciya da bata iya soyayya ba kaman yadda bata iya qiyayya ba......yana da wata irin zuciya me riqe abinda takeso


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login