Showing 339001 words to 342000 words out of 363280 words

Chapter 114 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1359

gaba abinsa suna sheqa baccinsu ko a jikinsu?,ita gata nan wahalalliya ta hana kanta da kanta sukuni duka saboda yaran da nasa tunanin,kawai saita saki kuka me sauti,kukan daya tasheshi ya kuma saka yaran motsawa,daya bayan daya suka farkawa tarwai abinsu,sai kuma a sannan suka fara neman abincinsu ta hanyar fara cilla qafafu suna son fara sakin kuka.

"Alhamdulillahil lazi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur" Ya fada sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta inda ta zauna gaban gadon tana musu kuka.

"Me akayi miki?" Ya tambayeta hankali kwance,tambayar data sakata sake masa hararar da batasan tayi ba,sai ya dauke kansa kawai yana sauka daga gadon a hankali ya wuce toilet don daura alwala yayi raka'atanil fajr kada ta subuce masa. Rigima ce fal idanunta yake hanga,shi kuma indai wannan rigimar ce a shirye yake da ita,ya fita jinta ma.

Ko kafin ya gama alwala ya fito dakin duka ya karade da kukansu su ukun,ga mamar tasu zaune a gabansu itama tana hawaye sosai.

Tausayi da dariya abun ya bashi duka lokaci daya,ya dake yana zura jallabiyyar jikinsa da sauri bayan ya tsane ruwan gargasarsa.

"Baki gani kuka suke kika zauna kika sakasu a gaba kina kallonsu?". Kaman jira take yayi maganar ta miqe tana nufar qofar,kuka takeyi sosai,sai ya qarasa yasha gabanta yana duban idanunta.

"Hamma raino kawai na iya dama?".

"Ni me nace miki ne Sabreen?,me kikeso kuma ehmmm?" Yayi maganar da alama shima ranshi ya fara baci. Ta kalleshi sosai ta kuma fahimci kukan yaranshi ke dagula lissafinsa,kenan yafi jin kukansu a ransa sama da nata?,wannan ya sanya ta soma neman hanyan fita kawai.

Hannu daya ya sanya ya jawota baya kafin ya saka hannuwansa duka biyun ya dauketa cak yana lullubeta a qirjinsa yana jin yadda sassanyan qamshinta ke bulale masa hanci,bai kuma direta ko ina ba sai tsakiyar gadon. Haurawa saman gadon yayi ya dauko farouq da nasa kukan yafi na kowa ya aza mata saman cinya,ya kuma tsare ta da idanun nasa. Zuwa yanzu qwayar idanun nan sun kuma na muhammadun sosai,me babban suna kuma shugaban kamfanonin jadda.
168




"Feed him" Ya bata umarni nakai tsaye da husky voice dinsa. Duk wani annurin fuskarsa yana daukewa,kukan yaran yana jinsa kamar d'igar ruwan dalma saman tsokar zuciyarsa.

Umarnin ya zarce har cikin kwanyarta,saita soma nuqu nuqun fidda maman. Gani yake bata masa lokaci takeyi shida yaran gaba daya,don haka ya buda hannayenta kawai ya balle duka button din rigar tata ya zameta daga kafadunta.

Cikakkun dukiyar fulaninta da suke a tsaye,sun cika sosai irin na masu shayarwa ya bayyana,abinda yayi nasarar karya alwalar da yaketa faman tattalawa kenan.

Hannunsa ya miqa cikin dakiya ya dagoma fauzan abincinsa,nan da nan ya kama,sannan ya saki ya koma wajen su fawwaz da kukan nasu ya sassauta.

Bai nuna yaga hawayen da take zubarwa ba sam,yaci gaba da bata yaran suna sha,har sai kowannensu ya qoshi sannan ya janyeshi. Suna sha yana karbarsu daya bayan daya yana sauka dasu. Batasan inda yake kaisu ba,amma haka yake dawowa hannunsa babu su.v

Almustapha ne qarshe,don kusan ya fisu haquri,sai daya tabbatar shima ya kama sannan ya tashi yayi raka'atanil fajr din. Sanda ya idar ya gama sha shima,ya miqa mata hannuwansa yana kallon fuskarta da tayi ja saboda kukan da tayi. Miqa masa shi tayi shima,sai ya karbeshi ya kuma ajiyeshi a gefe. Hannunsa yasa yana maida mata rigarta yadda take duk da qoqarin maidawa da takeyi da kanta.

"Ka barmin abata zan mayar" Ta fadi cikin rawar murya. Wani kallo ya jefeta dashi.

"Ina ruwanki?,wannan din ba jikinki bane.....jikin muhammad jadda ne.....naki jikin gashinan" Ya fadi yana nuna kansa da kansa da yatsa.

Wani abu me sanyi taji ya sauka a zuciyarta,har sai data lumshe idonta kadan,ya kammala maida mata ita tsaf,ya saka hannu ya dauki almustapha fawad yana tafiya qofa.

"Kiyi alwala kiyi sallah.....zanje sallah na dawo" Ya qarasa maganar yana qarasa fita. Tsaiwa yayi yayi locking qofar da new password ta yadda ba zata iya fita ba,sannan ya gangara ya miqawa salwa fawad yace a gyarashi shima kaman sauran 'yan uwansa sannan ya wuce masallacin.

A sanyaye tayi alwalar tayi sallar,tayi addu'o'inta kaman yadda ta saba. Idanunta sun mata nauyi sosai,kuma da alama rashin bacci ne isashe na kwanakin,don haka sai kawai ta koma toilet ta hada ruwa me dumi sosai tayi wanka,ta kuma nade kanta da jikinta da towels dinsa wadanda qamshin jikinsa ya kamasu sosai. Idanu kawai take lumshewa,wanxuwar towel din me manne da qamshinsa sai ya xame mata kamar shine nannade a jikinta. Wani irin azababben shauqinsa takeji ta kowacce fuska,tana jin kaman takai kanta gareshi ta roqeshi.

"Wanne irin abune wannan?" Ta tambayi kanta da kanta sanda tayi zaune saman stool a gaban madubi. Hirarta da fannah ta dawo mata fes a kanta.

"Wata macen sai ta fara haihuwa take zama cikakkiyar mace me cikakkiyar buqatar namiji..sai a sannan komai nata yake qosawa yake kuma bunqasa" Dauke hawayenta tayi da yatsanta,tana raya cewa wataqila ita din tana cikin irin wadannan matanne.

"Kamar ke kadai keda idanun kuka?,bakisan ni ya kamata na zauna nayita sheqa kuka ba?" Taji maganar sa daga gefanta wanda harga Allah batasan da shigowarsa ba.

"Taso kizo nan" Ya bata umarni kansa tsaye yana nuna mata daura dashi.

Da kallo yake binta sanda take takowa inda yake. Duk da yake shi ba ma'abocin kallon mata bane amma yayi imanin samun takun isa a wajen diya mace irin na sabreen dinsa zaiyi wahala,kaman yadda qirar jikinta tasha banban data dubban mata,don ko a yanzun da take tafiyar saika rantse ba wani yaro daya zauna a cikin ta tsahon wata tara,sai cika da komai nata ya sakeyi. Duk da yanayin halitta ma ya lura macace me gyara sosai(idan kina da kyau ki qara da wanka,karki yadda ki zauna a wargaje waike jego kike ko kin tara yara sun miki yawa,xaki banu zaki lalace fes wallahi).

"Sabrrrr.......don ni bani da gata?,don ni bani da wanda zan gayawa damuwata......don ni namiji ne bani da idon kuka?" Yafada da wata raunanniyar muryar data tilasta mata daga idanu ta dubeshi. Wani irin tausayinsa daya tsarga mata ya sanya hawaye taruwa a idanunta. Miqewa yayi,da alama baiso maganar ma tayi tsayi can.

"Alqawari nayi,tun a wancan daren bazan taba koda yatsarki ba muddin zamanmu sai kina cikin yanayin".

" Ina ciki wallahi" Ta furta da wani irin sauri bayan ta yiwa kanta kyakkyawar masauki a qirjinsa tana cukuikuyeshi. Dariya ta kusa kubce masa duk da yadda sanyin hawayenta daya sauka budadden qirjinsa da wuyan rigan ya zama V shape ya taba zuciyasa sosai.

"I can't live without you.....You're my everything,without you,I'm lost,i need you now and forever,you're irreplaceable hamma........ka yafemin hamma.....bazan sake ba hamma......na tuba" Ta qarasa fadi tana sakin masa wani kukan kisisina me tsayawa a zuciya.

Hannunsa har rawa yake sanda ya riqeta,ya sake mata wani tsatstsauran riqo yana sanyata tsakiyar qirjinsa yayi mata kyakkyawar runguma. Kasa magana yayi,kasa cewa komai yayi,kaman yadda shirunsa ya isheta amsa ta hanyar bugun da zuciyarsa takeyi.

Ta yarda ta kuma amince tabbas taso ta zalunceshi,jikinta ya sake sanyi da kalar soyayyar da yakeyi mata.

"Dukka wannan bugawar da Xuciyar nan takeyi tana yine saboda ke.....ke kadai sabreen,ban taba koda sha'awar daga kai na kalli wata macen ba bare har naji ta fusgi hankalina na ko ta dace da rayuwata ba bayanke".

"Nayi maka alqawarin xame maka aljannar duniya koda shine xai kawo qarshen bugun zuciya dana numfashina" Lafaxinta na qarshe kenan daya iya tantancewa,ya dauketa cak ya ajiyeta inda yafi wayo sannan ya fara rabata da towel din jikinta.

Wata irin sassanyan safiya ta bashi.....wata irin safiya me tsayawa a Xuciyar masoya.....

"Can i have you for breakfast today?" Ya fada da wata narkakkiyar murya dake wani irin rawa.

Yana dire tambayar ta tabbatar masa da abinda yake buri,abinda yake fata yake kuma tsananin buqata. Shi da ita kowannensu da zafinsa yazo,shi da itan gaba daya ba wanda bai gigita dan uwansa ba da wani irin zazzafan salo daya sake tabbatar masa itace DUNIYARSA shima shine DUNIYARTA. Gaba daya ta canza masa,ta kuma caza masa kwanya,yana jin tamkar yaune ranar farko a rayuwarsa daya fara kasancewa da ita. Ta gigita duk wani tunani nasa......ya sake fahimtar cewa lallai macen datasan kanta haihuwa ko shekaru basa saka kimarta zagwanyewa,a yanzunne ya sake gamsuwa da lallai sabreen dinshi ta zama cikakkiyar mace.

Tana kwance luf saman qirjinsa sanda komai ya kammala,kalar alqawuran da yake zayyano mata ya sanyata sakin wani sassanyan kuka,nan ya sake lalacewa wajen lallashin kayarshi.

Sanda taga lokaci bayan ta kalli agogo batasan sanda ta wantsalo daga gado ba ta nufi bandaki tana fadin

"Su fawad" Miqewa yayi ya bita toilet din da towels dinsu.

"Ina da nufina dana daukarwa su fawad nannies,kwanan nan kuma zan qara guda daya kowacce taji da guda daya,lokaci na lokaci na ne.....banaso nayi sharing nasa da kowa" Yaso ya bata dariya,saboda yadda yayi maganar da gaske.

"Ayi musu afuwa naje na dubasu,don zuwa yanzun ya kamata ace an dubasun" Bai amsa mata ba ya turata cikin bathtub din kawai yana sake maqale mata.

Tsaf ta shirya cikin atamfa riga da zani,shigar data jima bata yita ba. Shi kansa yau din saita masa kyau sosai,ta maqala wasu sabbin design na earrings na gold marasa nauyi a kunnenta da siriryar sarqarsu saman dogon wuyanta,abinda ya sake mata kyau kenan.

Ido ya saka da baki yana kallon kyakkyawan dokin wuyanta,tunda aka fidda design din shi sai yau yaga kyansa saman wuyanta,ya tako a hankali ya sumbaci wuyanta nata,abinda ya dauke mata wuta na sakanni.

"An bani izinin sauka na dubasu?".

"An baki duniyata" Ya fada cikin kulawa da shauqin qauna.

Basa dakinsu koda ta duba,don haka saita yanke duba parlor dinsu.

"Salwa.....Allah yasa ba rigima suke miki b......" Bata samu daman qarasa fadin abinda yake bakinta ba komai ya maqale mata yadda ta zuba mata idanu itama haka ta zuba mata,cikin wani irin kallon me cike da matsanancin mamaki da gigita.

Maamah ce zaune saman wheelchair dinta,an dora mata farouq fawwaz da almustapha fawad saman cinyar tata. Yatsanta cikin nasu yatsan tana tabawa a hankali,duk da bacci sukeyi amma idanunta yana kansu gaba daya.

"Ba wata rigima hajiya......tun dazun suna hannun kakarsu,har sukayi bacci.......fauzan ne ma yaqi zama gashican an goyashi" Salwa ta bawa sabreen amsa.

Maamah ce ta fara cire idanunta akan sabreen din sannan itama sabreen din ta dauke kallonta daga kanta cikin matuqar mamaki jikinta yayi wani mahaukacin sanyi.

"Tun yaushe tazo?" Ta tambayi salwa da harshen larabci data tabbatar maamah bataji murya qasa qasa

"Mintuna kusan arbain kenan,a rubutunta tambayeni ma haka kuke barin yaran a qasa gurinmu kuna sama?" Salwa ta fadi tana murmushi. Ta fada ne saboda yadda taga maamah din tana qarewa yaran kallo,kallon dake nuna zallar qauna da shauqi da kuma kulawa. Tunda tazo idanunta yana kansu,bata kuma saukesu ba ko sau daya.

Kai sabreen ta jinjina,abun yana sake fadada mamakinta.

"A samo mata abinci da abinsha" Ta fadi tana maida hankalinta kan maamah tana takawa cike da qwarin gwiwa.

Ganin maamah a gidan nata ba abu bane me sauqi,ba wani abu bane da zatayi zaton zai kasance haka a nan kurkusa ba.

Gabanta ta qarasa ta kuma tsugunna tana fadin

"Sannu da zuwa maamah......barka rana,ya jikin?,Allah ya qara lafiya". Wani kallo ta dago ta dan watsa mata. Da tana da iko zata tambayeta ne uban me sukeyi a sama kusan sama da awa daya suka bar kula da yara hannun masu aiki?,haka sukeyi kenan cikin gidan?,shi ya ajiye fita office ita ta saki ragamar gida kamar su kadaine suka rage a duniyar?,kaman ba wani abu me rai da yake rayuwa a duniyar saisu?.

Saidai ba wannan damar,sai dai kallon tuhumar data gabatar mata tana jin ya kawo mata dan sassauci a zuciyarta. Sarai taga kalar kallon,to amma ita kanta tasan yasha banban da kallon qiyayya da takeyi mata,wannan din akwai sassauci qwarai a cikinsa,duk da cewa akwai alamu na jin haushi a cikinsa da batasan haushin meye ba?,sai daga baya zuciyarta ke raya mata na barin yaranne a hannunsu salwa?.

Saida salwa ta kawo komai sabreen ta jera mata a gabanta,sannan ta umarceta ta karbi yaran ta bata abincin taci,amma qememe taqi bayar da yaran.

Sanda fu'ad ya sauko ana wannan drama din,don sabreen ta haqura ta koma gefe tana kallon ikon Allah,yadda ta tattara dukka hankalinta akan yaran,kamar bata da wani sauran abu me muhimmanci a duniyarta sama dasu,duk kuwa da cewa ita din daga wannan kallon guda biyu bata sake samun wani kallon ba.

Shima nasa kallon aka aje masa,sannan ta kauda kanta bakinta yana motsawa kaman meson yin magana amma kuma ba dama. Mutuwar tsayen da yayi yafi na sabreen,don har sai da maamah din ta sake daga idanu ta kalleshi tana masa nuni da ya zauna ya tsaya mata a kai.

Kaman yadda sabreen tayi mata shima still hakan,saidai shi dinma ba wani muhimmanci ta bashi ba. Ganinta riqe da yaransu kuma gudan jininsu cikin hannuwanta da wata qauna data gaza boyuwa daga cikin qwayar idanunta yafi komai yi musu dadi shida sabreen din. Suna zaune zaman kurame kawai,amma lokaci lokaci suna satar kallon juna shida sabreen din,har zuwa sanda tayi alama da hannu aka bata abun rubutu.

"Ka kiramin driver ya maidani gida,kada ku sake barin yara har tsahon sama da awa a hannun masu aiki ba tare da kuna zagayosu kuna dubasu ba" Iya abinda ta rubuta kenan da rarrababben rubutunta.

Ya dauka idanunsa ne suke masa gizo ko suke nuna masa ba daidai ba,sai kawai ya miqawa sabreen din paper ya qarasa ya karbi yaran ya ajiyesu sannan ya tura wheelchair din da take kai da kansa.

Sanda yake turata da kansa sai taji wani abu yana sauka saman zuciyarta,tana iya qididdige takunsa da kuma yadda yake tura kujeran cike da karsashi,sai takejin kaman ba'a taba tafiya da ita saman wheelchair din irin haka ba.
169



Koda suka isa key ya karba hannun driver din,yace su biyoshi a daya motar. Shi yayi driving nata har gida,ya kuma danganata da bedroom dinta. Tsugunnawa yayi a gabanta a hankali,yana jin wani abu me kama da qaqqarfan farinciki yana dawainiya dashi.

"Zan koma......ba wani abun?" Kai ta girgiza masa alamun ba komai,sai ya miqe a nutse yana furta.

"Sai da safe,Allah ya huta gajiya" Ya fada yana dan rage Ac din dakin. Idanunta ta lumshe,wasu hawaye masu dumi suna silmiyo mata wanda ba nace ga dalili ba,ta miqa hannunta da qyar dake yawan yo mata nauyi tana goge hawayen fuskarta.

Riqe da paper din kuma a inda ya barta ya sameta a zaune tsakanin yaqini da kokwanto. Cak ya dagata yana juyi da ita sannan ya direta yana duban tsakiyar idanunta.

"Na gode sosai duniya.....na gode da tayani siyawa yaran nan soyayyar maamah......koda ni ko ke mun rasa soyayyarta.......soyayyar da zata bawa su fauzan ta ishemu". Da mamaki take kallonsa,sai ya lakace mata hanci.

" Ko an gaya miki bana sane da boyayyar addu'ar da kikewa iyalinki.....ni number one,addu'ar kariya samun nasara da cikakkiyar lafiya,yaranmu shiriya da zama nagartattu.....sai samun qauna daga wajen kakarsu" Kunya ta kamata,ashe dukka kukenta da fatanta cikin sallolinta na dare fakare yakeyi mata?.

&Cikin kwanakin kwanciyar hankali da nutsuwa ta samu ga kowa,ci gaba ta fuskokin rayuwa kala daban daban.

Wata irin soyayya ake murmushewa cikin gidan me jadda me license,irin soyayyar da yaran da suka fito ma daga jikinsu saidai a sanmusu. Tsakanin DUNIYOYIN guda biyu wani irin dangantaka ce me qarfin gaske.....wadda ta gwada musu lallai WA YASAN GOBE? banda Allah?. Wata irin DANGANTAKAR ZUCI me tsakanin qarfi da power,wadda take sake basu yaqinin ABADAN ba wanda zai iya rayuwa ba dan uwansa. Sau da dama idan suka zauna labarin rayuwrsu ta baya suna jinjina


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login