Showing 153001 words to 156000 words out of 363280 words

Chapter 52 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1364

salla. Raka'a biyu rak yayi amma sun kasance masu tsaho sosai,kuka sosai yakeyi cikin sujjadarsa cikin godewa Allah da kuma yaba karamci irin nasa. Ya sake imani da karamcin ubangiji me girma da fadi ne,ya masa wani irin ba zata mara misali da bai taba kawota ba.

Duk kusan inda ya juya fadi dakin yake sakeyi masa,wani irin emptiness yakeji cikin dakin qirjinsa dama zuciyarsa.....wata irin kewa da bai taba jin irinta akan kowacce halitta ba sai a kanta,duk shudewar daqiqa daya tana dawo masa ne da yammacin zaice ko darensu na daxu. Ya zuqi numfashi ya fesar yana jin kaman daren yayi masa nisan da gari bazai waye ba ballantana ya sake ganinta. Bayajin baya ga anni akwai wanda zai masa hakan......bazai lamunci wani ya rabasu koda kuwa na qiftawan ido ne.

"Me yasa ban dauketa ba kafin anni takai ga yanke wannan hukuncin?" Ya tambayi kansa yana jin ciwon nisan data masa. Hannunsa yakai kan qirjinsa daidai inda faffadan qirjin nasa ya manne da nata a dazu.

"Beautiful" Ya furta yana shafa labbansa bayan ya tuna kyan gurin ga qayatarwarsa. A cike suke kuma a tsaye da wani irin shape me jan hankali,ba wata alama data nuna hannu ya taba kawa wajen koda na kwanaki qalilan ne. Wani numfashin ya sake fitarwa........ Yaji yana buqatar sanin duk wani me mummunar shaida a kanta.....yanason sake tusa bincikensa.......yaji yana shaawar bin kowanne diddigi na rayuwarta....koda bata gaya masa da kanta ba dole zaiyi wannan aikin. Bayason kunnuwansa da zuciyarsa su dinga tuna masa maganganun daya gaya mata

"Kyakkyawar Kalma sadaka ce" Ya tuna wani sahihin hadisin ma'aiki akan furta kalma me kyau ga dan uwanka musulmi. Baisan me yasa yake kasa controlling anger dinsa a kanta ba,baisan me yasa yake tsananin jin zafin komai daya shafeta ba.....sai a yanzu daya soma tuhumar kansa da fadawa soyayya a sanda baisan ita bace saboda mummunar shaidar da ya yiwa soyayyar. Yaga mata kala kala da suka kawo kansu gareshi.....mata iri iri dake da wata irin qazamtacciyar rayuwa,amma bai taba jin zafin rayuwar da suke ciki ba saboda ya bawa kansa amsa da baya da issue dasu,bugu da qari ma su suka jefa kansu suka zabi wannan rayuwar.

Daga daren zuwa wayewar gari ya zame masa wani zamani daban me zaman kansa......kamar ba tazarar awanni bane kawai a tsakaninsu. Yayi sallar asuba cikin daki ne karon farko da zai iya tuna sanda hakan ya faru,ya kuma ci gaba da zama a wajen yana hailala istigfari,salatin annabi kaman yadda ya saba,sannan ya zarce da karanta wasu shafuka cikin qur'ani. Sanda ya rufe mas hafin qur'anin daga kan tab dinsa da yayi karatun dashi gari ya soma haske. A irin wannan lokacin yakan fita gym ne,amma a yanzu baya da wannan kuzarin da zai iya fita ko ina,fatansa kawai gari ya qarasa haske yaji motsin su annin ya samu chance na ganinta.

Kansa ya aje gefan gadon yana lumshe idanunsa,hannunsa saman kayanta da tun daren daya zaresu ya watsar bai iya kwashesu ba. Yamutsasu yakeyi cikin tafin hannunsa a hankali wani sabon feeling na sake shigarsa. Kowacce safiya sassanya irin wannan yakanyi fama da irin wannan yanayin tun asali can dama......a yanzun sai abun ya zama double,ya jawo vest din da bra din duka ya cusa a hancinsa yana shaqar sassanyan qamshin nan daya dasa masa tarihi cikin rayuwarsa.
(Tsokaci:- Mostly maza suna samun feeling sosai daidai wannan time din,saiki kula da buqatar mijinki,ko yaro gareki namiji koda qarami wanda bai balaga ba daga lokacin zuwa wayewar gari ki lura da kyau,indai tsiraicinsa yana dagawa a irin wannan lokacin to tabbas lafiyayye ne,idan kuma kikaga akasin hakan to sai a fara nema masa magani).

Ba abind qamshin ke sake masa sai qara tada zaune tsaye,kaman ya shide kayan cikin hancinsa haka yakeji,ya tattarasu ya mannesu a qirjinsa yana qoqarin baiwa kansa haquri.

Baisan sanda wani irin bacci yayi awon gaba dashi ba,wanda ya cika da mafarkanta kala kala,ko wanne waje suna tare cikin shauqattancen yanayi me tafiyar da hankali,da wani irin yanayi mai tafiyar da hankali.

Koda ya farka yanayin daya samu kansa a ciki ya sabbaba masa sake wani wankan ibadan,sannan yayi gama garin wanka ya fito daure da towel yana duban a gogo. Baisan wanne aiki yayi haka ba da har yunwa ke zaqalqalar cikinsa,saidai duk da yunwar da yakeji ganinta yana jin yafi masa cin abincin muhimmanci.

A nutse ya shirya cikin wasu pajama masu dogon hannu butter colors da aka yiwa adon gold color din zare da mix din baqi dan kadan daga gaban rigar da tambarin kamfanin Louise Vuitton. Fuskarsa tayi fresh sosai da wani irin sassanyan yanayi a kanta. Yadda ya gyara sumarshi ya sake zama very calm guy,idanun nan dake da wani irin sirri sun rissuna sosai,ya feshe jikinsa da sassanyan turarukansa yana sake maida dubansa ga agogo.

Karfe sha biyu harda wasu mintuna akai agogon qasar Maldives. Yayi mamakin tsahon lokacin da yaci yana baccin,sai ya maida turaren ya zura flip flops masu taushi da suka dace da adon gaban rigar. Idan ka kalleshi zaka dauka wani guri zai fita ne,haka yake,yana da wani irin tsari da koda cikin gida yayi wanka zaka ganshi neat very well dressed.

A nutse ya murza qofan dakin yana fita parlor din,ba kowa a ciki bama motsin kowa,sai ya taka zuwa saitin dakin anni yana duban dakinsu farouq dake alamta masa har yanzu basu dawo ba.

A nutse yayi knocking,yayi tsai yana irga adadin gudun zuciyarsa tare da raya abubuwa da yawa da zasu iya faruwa cikin dakin.

"Shigo mana" Anni dake fitowa daga toilet ta fada.

Koda bataji muryarsa ba ta tabbatar shine yake knocking qofar,abinda ya sanyata gyara zamanta sosai saman wani tattausan carpet dan madadaici da anni ta shimfida mata ta zauna a kai.

Boubou gown ne a jikinta mai taushi ta asalin 'yar qasar Egypt wadda tafe da mayafinta. Milk color ne da adon lime green a jiki daya sake qawata yadin rigar. Gashinta na tattare waje guda ta kuma daureshi da sassauqan dauri da bazai dameta ba. Fuskarta tayi wani irin fayau ta kuma qara haske da glowing,duk da kana ganinta zakasan cewa ba komai saman fatarta tata,ko man arziqi bata shafa ba. Kwana da annin zata iya kiransa wani abu dake cike da baiwa da kulawa,tayi wani bacci da bata taba tunanin zata yishi ba saboda dinkin dake a jikinta. Ta dauka radadin ciwin shi zai fara tagayyarata,ya kuma hana mata baccinta,sai gashi ta samu wani irin bacci hankali kwance cikin kulawar annin da ko yaya ta motsa itama sai ta motsa,idanunta da hankalinta duka yana a kanta.

Umdatul ahkam ne saman cinyarta take duba karatun baya da sukayi da rumasa'u. Annin ta lura bata da waya ko wani abu da zai debe mata kewa,a lokacin Umdatul ahkam din yana hannun annin,taga sabreen din tana yawan kallon littafin,don haka ta tambayeta.

"Ko zaki karanta?" Kai ta dagawa annin a kunyace,tun jiya ta gaza cire kunyar nan da annin tace mata ta cireta,ita ba suruka take a wajenta ba,ita din uwa ce amma ta kasa. Hatta da bubu din jikinta yanzu haka ta annin ce

"Ki amfani da wadannan,saikinfi sakewa yadda dinkin za'a samu ya warke da wuri" Anni tace da ita.

Itace abu na farko da idanunsa suka fara sauka akai. Ya janye dubansa daga kan fuskarta zuwa ga littafin hannunta,haka kawai yaji wani sanyi yana ratsa zuciyarsa,ya motsa labbansa yana yin sallama cike da fatan zata daga kanta ta kalleshi koda ba zata amsa ba,amma maimakon hakan sai anni ta amsa mata tana turr hijabinta data cire kafin shigarta bandakin ta zauna gefan gadon tana nuna masa stool din dressing mirror din gami da karantar yadda dukka hankalinsa yake a kanta tamkar zai wuce gabanta kai tsaye. Ta godewa Alla daya bata basirar dauketa daga dakin.... A matsayinta na babba abinda take gani cikin idanunsa muddin ta barshi da ita tasan dinki koda guda nawa za'ayi mata warkewarsa saita Allah.

Zama yayi saman stool din yana qoqarin maida mode dinsa daidai da yadda ya saba yiwa annin,duk da wata irin kunya dake rugowa da gudu tana dabaibayeshi,ya kasa kallon tsakiyar idanunta yadda ya saba.

"Barka da safiya anni.....ina kwana?" Ya furta yana rusunawa duk da a zaune yake.

"Barka kade......an tashi lpy?" Sassalkar sumarsa ha shafa da tafin hannunsa yana satar kallon sabreen ta qasan hannun nasa. Wannan tambayar ta anni sai yakejin kamar gatse yake masa amma ya amsa da

"Lafiya alhamdulillah......yame jikin?" Ya hada kunyars waje daya yana nufin kaita qasa da kuma son janyo hankalin sabreen da ko motsawa batayi ba ballantana ta nuna tasan yana wajen.

"Alhamdulillah" Anni ta amsa masa a taqaice,don ita kanta tuna abun kawai yana sakata cikin wata irin kunya.

Idanu anni ta maida kanta,zuwa yanzu ko ita yarinya ce ta gama fahimtar wanne irin zama sukeyi,saidai tambaya daya data kasa samun amsarta.....ta yaya ta zama zabinsa bayan baya so?.

"Sabreen" Anni ta kirata,kiran daya sanya ta daga kai zuwa ga annin ba tare data kalli sashensa ba. Wani iri yaji.....shi yake da muradin ta fara kalla,shi takeso ta dinga fara kalla kowacce safiya idan yana da ikon hakan.

"Mijinki ya shigo". Lumshe idonsa yayi yana jin dadin kalmar da yadda ani ta fadeta da wani irin taukidi

"Kul.....ba kyau a wajen mace taqi gaida miji......Allah bazaiyi farinciki da hakan ba" Anni ta fada tana jin wani abu yana taba ranta a kansu duka su biyun

"Ya Allah ka taqaita musu jarrabawarsu......kada ka sanya soyayya ta zama wata sabuwar jarrabawa a garesu".

"In sha Allah anni" Ta fada tana dan jin nauyin abinda tayin,bawai a kansa ba.....a'ah akan anni ne. Tsam annin ta miqe tana cewa.

"Bari na duba matar can ko ta dora abincin rana?". Saita nufi qofa a hankali tana ficewa daga dakin harda jan qofar.

Wani dadi ya dinga ratsashi da anni ta basu wannan space din,sai kawai ya harde hannayensa duka biyun saman qirjinsa yana qare mata kallo.

Wani irin kallo ne da yasha banban d kowanne irin kallo,wani irin kallo dake cike da shauqi da matsananciyar soyayyar da yakeji kaman tafi qarfin wannan faffadan qirjin nasa dama tsokar zuciyar dake lullube a ciki. Wani kalan so da yafi qarfin a hada sunan son shauqi dama qauna duka a dunqule waje guda,baima san sunan da zai bata ba. Yana ganin yadda ta maida dubanta kan hadith din tana buda shafin gaba,alamun ta gama da shafin baya kenan. Boyayyen murmushi ya saki wanda ya tabbatar ba zata gani ba,tayi masa wani irin mugun kyau tamkar furen fulawa. Lips dinta ya kalla da kyau,ta sake tsuke dan qaramin bakinnan nata waje daya,da gani kai basai an gaya maka ba akwai fushi kwance cikin zuciyar 'yammatan nasa.

"Zansha tsiwa.....zansha rashin kunya,amma duka ina maraba dasu,akwai kebantacce kuma killataccen gurin da aka tanada saboda su" Ya gayawa kansa da kansa yana jin shauqinsa yana qaruwa a iya kallonta kawai kafin yaji kallon ya daina gamsar dashi,duminta kawai yake da muradin ji,duk da zuciyarsa tana gargadarsa da cewa kuskure ne aikata hakan,musamman a mode din da take ciki,uwa uba kuma cikin dakin anni?. Saidai kuma magnet din dake jansa yafi qarfinsa,bazai iya controlling kansa ba. Tsam ya miqe ya sauka daga saman stool din,ya zube hannayensa a aljihun wandonsa,ya motsa labbansa a nutse.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

_An tambayi nana Aisha R.A,menene dabi'un manzan Allah S A W,sai tace: dabi'unsa alqur'ani ne(ma'ana yadda qur'ani ke koyarwa da fadin kalolin kyawawan dabi'u dukka haka halayen fiyayyen halitta S A W yake)_



81


"Sabrrrrr" Ya kirata da sautin nan dake ratsa kunnuwanta ya aike da wani saqo me sauri zuwa kwanyarta. Ko motsawa batayi ba bare ya kula da taji kiran ko bata ji ba,sai ya sauya shawara shima,ya cire hannunsa daga aljihun wandonsa ya fara takawa inda take zaune.

Sarai taji takowarsa,amma sai takejin bata da wani sauran abinda zataji tsoro tattare dashi. Batasan gaibu ta gayawa kanta ba sai da taji hucin numfashinsa dab da fuskarta,kafin ta daga kai ya sanya hannu ya zare littafin ya sanyashi a gefanta,ya kuma maida gurbinsa da kansa. Yayi kwanciyar rigingine ne,fuskarsa na kallon sama tana kuma kallon fuskarta,ya hade hannayensa a qirji kaman me sallah,ya tsurawa qirjinta ido daya fuskanci zuciyarta ce take bugawa shi yasa ya fara dagawa sama da qasa kadan kadan.

Boyayyen murmushi ya saki.....tana da raunanniyar zuciya me cike da tsoro,saidai,kuma fushinta taurin kanta da kafiyarta kaman suna so su rinjayeta.

A tsorace take ainun da yadda ya kankane mata cinta,bata so kuma tayi masa magana sam sam,tana jin bai cancanci kalaman bakinta ba. Haduwar jikinsa da nata sai ya tuna mata da wanzuwar fareeda data gani yammacin jiya cikin jikinsa,abinda ya hadu da fushinta ya sake zafafan zuciyarta kenan ta tattara lausasan tafukan hannayenta zata ture kansa daga cinyarta. Hannuwansa ya saka ya riqesu yana kallon tsakanin haskensu da taushinsu da tun a idanu ma suka nuna hakan.

"Kin cewa anni zaki dinga gaisheni....kuma tamkar alqawari ne,bayan ta fita kuma kin karya alqawarin da ko minti uku bai cika ba.....na taso da kaina don nazo na gaidaki sai kuma ki koreni?,kinyimin adalci kenan?". Idanunta ta zuba masa a zafafe kalmar adalcin daya fada tana bata haushi. Shikam har yayi maganan adalci idan akazo batu a kansa?.

Batajin zata bari yaji koda kalma guda a bakinta,don haka ta gwammace hadiye takaicinta,ta maida kanta gefe bata furta komai ba tana qoqarin zame kansa daga cinyarta. Ganin haka sai ya juya da zafin nama ya koma rub da ciki,still kanshi yana kan cinyarta. A wannan karon ma sai ya qaro da sanya hannayensa ya zagayo bayanta dasu ya mata zobe kanan ya sakata a Tsakanin hannayensa.

"Good morning my sweetest women..........ina fatan kin tashi lafiya?" Ta fada yana sauke wani irin ajiyar zuciya gami da lumshe Idanunsa yana mamakin yadda take saka zuciyarsa bugawa haka.

Duk da baya dubanta haka ta zubewa qeyarsa me kwantacciyar suma idanu,tana jin gaba daya ya zame mata qarfen qafa. Duk wani motsi da zatayi don qwatar kanta sake qanqameta yakeyi sosai,hatta da tafukan hannayenta ya mannesu cikin nasa,ya saki ajiyar zuciya sannan yace

"Ina fatan kowanne ciwo da kika ji ya zame miki silar samun rahamar ubangijinki.......na gode......na gode.....na gode sau babu adadi da killacemin kanki da kikayi......na gode da kika qaryatamin zancan mutane a kanki.....kika kuma bani tabbacin da bandashia baya" Kaman susa bisa ciwonta haka maganganunsa suka zame mata,ta qwace hannun nata da qarfin zuciya irin nata tana ture kansa,amma sai ya sake rungume hips dinta sosai kaman zai maida kansa cikinta.

"Duk yadda zakiyi qoqarin korata daga rayuwarki wannan din mafarki ne......bazan iya ba......bazan iya barinki ba koda na second guda ne,indai zan iya rayuwa babu ruhi ko numfashi......tabbas zan iya rayuwa babu ke.....ke din ruhina ce.....numfashi na ce.....kuma jinin jikina,a cikinsu wanne ne idan babu rayuwa zata tabbata da cikakkiyar ma'anarta?"

"Ya isa......ka dagani" Ta fada adan tsaurare saboda wani irin nishi da sauti da yake sakar mata daya sanya ta fara daina gane komai,wata irin tafiyar tsutsa yakewa tafukan hannayenta da take jinta har cikin qasusuwa da bargonta.

"Ka daga ni ko na maka ihu na kira anni......." Murmushi ya sakar mata hankalinsa kwance ba tare daya motsa ko ya fasa abinda yakeyi ba

"Ki taimakeni ki kiramin ita......wataqila zata tayani gaya miki irin matsayin da me jadda ya baki.....ita din uwace dake fuskantar kowanne yare da 'ya'yanta zasuyi magana dashi". Da gaske yake mata,bataga wani alama ko kadan a tattare dashi na razani ko tsoro ba,saima sake gyara zamansa da yakeyi saman cinyoyinta kamar ya samu wata DUNIYARSA a wajen.

"Zan sake maimaita miki.....zanta baki haquri.....zanta baki damar horani har zuwa sanda zaki huce........amma karkiyi zaton akwai wani kalar bore da zakiyi da zai sanya na haqura dake.....kece rayuwata.....banajin bugun numfashi na yana fita da sunan kowacce mace a duniya sai ke" Ya qarasa fadin maganan yana sake qanqameta.

"Wayyo dinki na" Ta fada da qarfi,abinda ya sanyashi miqewa a gigice a kuma razane yana riqeta da kyau.

Ya bude baki zaice wani abu ta sanya duka hannuwanta ta tunkudeshi sai gashi ya tafi da baya ya fadi. Ba wani abu da taji na zafi ko ya samu dinkin nata,tayi hakanne dama kawai don ya saketa.

Baiyi wani qoqarin tashi ba saima sake bajewa da yayi yana sakar mata murmushi

"Next time ba zaki nasara ba" Daidai nan anni ta turo qofar a gaggauce saboda sautinta kaman da taji. Shigowar anni ya sakashi miqewa da sauri,yana dan kade


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login