Showing 303001 words to 306000 words out of 363280 words

Chapter 102 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1441

ya dade ya zaki koma kuma?" Zaqaqurin dan jaridar ya fada. Waiwayowa tayi ta zube masa wani kallo.

"Ni ba uwar qaramin mutum bace,bani da lokacin magana daku kai tsaye haka.....idan ka matsa kuma kasan waye d'ana,ba aikinka kawai zaka rasa ba.....har....." Sai kuma ta dakata tana kwabar kanta duba da irin cameras din dake fuskantarta. Kallon kallon suka farayi tsakaninsu,don kowa da abinda ransa ke raya masa da yanke maganar da tayi bata qarasa ba. Ganin ta dauke musu wuta gaba dayansu saita taka tana komawa ciki cikin jan qaqqarfan tsaki.

"Akwai batun aika b'ata gari da kikayi gidansa don yiwa matarsa fyade da sunan baki sonta.......wannan batun gaskiya ne?". Wani irin suka maganar tayi mata a qirjinta,har batasan sanda ta saka hannu ta dafe saitin zuciyarta ba. Haki ta soma yi tana jin kamar qafafunta ba zasu dauke ta ba,dole ta fara kiran sunan laila saboda tasan duk 'yan aikinta yau basunan cikin mancewa da tarin 'yan jaridar da suke neman tabbacin lailan tana tare da ita kaman yadda cikin rashin sani ta basu tabbacin.

Kome takeyi,komai girman bacci ko uzurinta muddin maamah ta kirata saita bar komai. Kaman yanzun da take zaman cin abinci haka ta watsar dashi ta kwaso da gudu. Fitowar tata ta sake maida hankalin mutane kan laila din da dukkanin kamanninta da hajja harira da suka fito.

"Lafiya maamah?,me sukayi miki?,me ya faru?".

"Kamani muje ciki" Ta bata umarni a tsawace,abinda ya sanyata kamata dukka jikinta suna rawa.

"Da gaske kece diyar hajja harira?" Wata cikin su tayi caraf ta jefa mata tambayar sunason tabbatar da maganar juya mata hankali da sukayi.

"Eh 'yarta ce......amma yanzun daidai nake da baiwa wajen maamah......yadda takeso take buqata haka zanyi,koda ya kama na rabu da ita hariran"

"Ke laila kama bakinki mu wuce ciki!" Maamah ta fada da hanzari gudun kada tsananin mallaka ya sanyata nunawa duniya abinda zai sake zame mata abun fada.

"Laaaaa haila ha'illallahu.....muhammadurrasulillahi" D'aya daga cikin mata 'yan jarida dake wajen ta kasa daurewa abinda ya farun ta saki kuka tana tafa hannu.

"Wallahi 'yar hajja harira ce,da gaske ne,da gaske aikin juyar da hankali tayi mata bayan tayi kidnapping nata......da gaske ne,gashinan diya tana neman mancewa da uwarta?" Wannan kalaman sun sauka daidai kunnen maamah,wanda hakan ya sanyata runtse ido,tsananin jin zafin hajja yana sake ratsata tare da alwashin daukan fansa a tare da ita.

"Ki gayawa malam sa'adu ya fidda mutanen nan,idan ba haka ba zai fuskanci fushi na" Umarnin data bawa laila kenan,ta kuma saka kunne tana jiran daina jiyo hayaniyarsu daga nan inda take.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX




151

Tsahon mintuna talatin ta sauke idonta akan takardar da fu'ad ya ajiye mata,ta zubawa littafin idanu tana lissafa adadin yawan shafukan da yake dasu. Ya fadi cewa zata iya cika littafin harma ta qaro wani....tayita rubuta dukkanin abinda takeso.......wannna babbar dama ce a gareta kenan na zama Mulitibillonier?. Murmushi ta saki ta soma yunqurin daga hannunta ta miqashi don dauko littafin,amma abun mamaki sai taji hakan ya gagara. Ta sake yunqurawa a karo na biyu da zummar gwada daukar nan ma shuru ne hannun yaqi sarrafuwa.

A zabure ta maida dubanta ga hannun nata cikin wani irin kidima da dimuwa tana kallonsa. Hannunta ne dai......hannunta ne data sani shekara da shekaru......hannunta ne da ba wani abu daya canzashi.........amma meye ya kawo qin daguwarsa?.

A karo na uku ta tattaro dukkanin qarfinta zata dagashi ya sake motsuwa koda wasa,a birkice ta maida hankalinta kan daya hannun tana qoqarin motsashi shima.

Still shima abinda dan uwansa yayi shi yayi mata. Matuqar qololuwar tashin hankali taji ta shigeta,wani irin mahaukacin gumi ya yanke mata.

"Me hakan yake nufi kenan?,wani ne yayi min asiri?,ko wani ne yayi min tsafi?" Ta tambayi kanta da kanta.

"Kai inaaaa.....a irin wannan lokacin?,a lokacin da dama tazomin?" Ta sake tambayar kanta a fili kaman wata tababbiya.

"Bazai yuwu ba" Ta fada tana qoqarin miqewa don ta gani ko qafafunta suna aiki?.

Miqewar datayi aniya jikinta ya gaya mata bashi da wani sauran motsi me qarfi,qafafun suma suka shaida mata basu da wani sauran qarfin da zasu dauki nauyin gangar jikinta ta hanyar warbar da ita ta zube a qasa tana kifawa saman fuskarta.

Wani irin matsanancin ciwon kai yakeji,wani irin yanayi da yakejin kamar jikinsa yana dab da gazawa. Yana dafe da kanshi tsahon mintunan da suka dauka suna tafiya a motar,har zuwa sanda ya buda bakinsa a hankali yayi magana da driver din

"Badawa zaka kaini......ba gida ba" A yanzun ba abinda yafi buqata irin ya kebe,so yake ya kebe shi daya,bayason magana da kowa bayason kuma hayaniya.

Karya kan motar yayi suna komawa daya hannun. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu m,already yasan gidan,gida ne madaidaici daga waje,saidai kuma daga cikin yana da yalwa da wani irin yanayi da aka tsara me tsananin burgewa. Yakan jima baizo gidan ba,yana ma mantawa dashi sau tari,saidai duk sanda yake buqatar ya kebe ko ya huta a nan din yake zama har zuwa sanda ya gamsu da yanayinsa ya koma normal mode dinsa.

Tun a parlor din ya zube,karo na farko da yaji yana buqatar yayi kuka,karo na farko da ya buraci inama ace shi din yana cikin sahun mutanen da hawaye ke fita a fuskarsu da wurwuri?. Hawaye yake da buqatar ya zubar sosai saboda qirjinsa dama zuciyarsa sun gaji da daukan abinda suke dauka din. Koda zai iya hana kanshi fitar dasu to ba a irin wannan lokacin ba,a yanzun kuka yafi buqatar yayi bawai yaci gaba da nuna jarumtarsa ba.

"Astagfirullah ya Allah......astagfirullah" Shine abinda labbansa dake motsawa suke maimaitawa yana jin yadda qirjinsa ke sake suya idanunsa suna sake d'aurewa da wani irin zafi da kuma radadi.

Wani sabon babi ya bude na tariyar rayuwarsu,tun daga sanda ya bude idanunsa ya zama mutum cikakke zuwa yanzu. Bai tsinci komai tattare da maamah ba banda haihuwarsu da tayi......ko a sanda take rayuwa tare dasu,yadda take mu'amala dasu haihuwarsu ta zame mata kaman wani nauyi wahala ko dawainiya.....abbansu kusan shine komai nasu......abbansu shine duk wata wahala da dawainiya tasu,abbansu shine wankansu abincinsu,shirin makarantarsu da komai na dawainiya......yayi a gida ya fita yayi a waje ya kawo musu. Zuwa yanzu baisan sadaqaul jariya na abubuwa daban daban dubu million nawa yayi saboda shi ba......yana fatan ko a ina yake ya bishi cike da samun salama cikin kabarinsa da rayuwarsa ta barzahu.

Da taimakon ambaton sunan Allah da yakeyi ya samu nutsuwa ta fara dawo masa. Yayi amfani da wannan damar ya miqe ya shiga toilet ya daura alwala. Dawowa yayi ya kunna ya kunna TV din dake kashe,ya lalubi tashar saudi qur'an ya qaro volume din ya karade parlor din gaba daya.

Cikin kujera ya nutse,idanunsa a lumshe yana sauraren karatun gami da bin ayoyin tare da shaik abdurrahman assudais. Yana karatun yana fahimtar ma'anar ayoyin,abinda ya sake taimakawa wajen bawa zuciyarsa da ruhinsa nutsuwa.

A nan gurin yayi sallar la'asar,magariba ma ta ruskeshi duka ba tare da ya sani ba. Itama magrib din a nan yayita,ya jima saman abun sallah yana addu'o'i har baisan adadin lokutan daya shafe ba,yadai duba ya tarar da lokacin isha'i har ya shiga.

Isha'i dince ya fita a daddafe zuwa masallacin dake cikin layin cikin shiga ta bad da kama,baya son kowa ya tsaidashi don bazai iya dogon magana ba. Ana idarwa ya taso shida jordan sukayo gida,jordan din ya dan dubeshi cikin matuqar jin tausayinsa qauna da kuma kulawa.

"Sir......ko za'a aika a karba maka abinci gurin madam?,if not a maka order daga wani eatery din?". Kai ya girgiza,a halin yanzu bayajin yunwa,still kuma bayaso ma sabreen ta ganshi a yanayin da yake ciki. Tashin hankalin da take fuskanta ita kanta yayi yawa,tunda ta dauki cikin nan bata huta ba,tana stressing kanta da yawa akan duk abinda ya shafeshi......is over,ya kamata ta huta hakanan,ya kamata ta samu peace of mind......yana shawarwarin yin nesa da ita har sai abubuwa sun lafa,shi kansa yana jin zaya dauki hutu har sai komai ya koma daidai.

"Sakamin order lite abu please" Yace da jordan din yana wucewa cikin gidan.

Saman sofa ya zauna,ya dauki wayarsa dake yashe a wajen wadda sam yama mance da ita. Saqonni da miscalls rututu,amma duka na sabreen din yafi yawa. Ya saki dan qaramin murmushi bayan ya gama karanta wani saqonta na qarshe.....finally ya samu wata kyakkyawar zuciya data damu dashi da gasken gaske,finally ya samu wani ruhi dake craving for him.......finally ya samu wannan madadin da yake qishirwar samu.

_"na kiraka na maka saqo har sau babu adadi amma babu guda daya daka amsamin.....tom.....Even if you're ready to live without me,I'm not ready to let go,ko yaushe zan kasance a tare da kai,koda hakan baida tsada ko daraja a wajenka,bana saba alqawari,forever. Yours mom of triplet"_

Har tsakiyar zuciyarsa yaji saukar da saqon yayi masa. Wata soyayya ta musamman tana sake huda zuciyarsa,qaunar 'yan tayi guda uku dake kwance a cikinta suna sake lullubeshi.


_You're the missing piece that makes me whole,without you,life wouldn't be the same,forever with you is where i want to be.....you're my forever adda sabreen......am safe.....karki damu da yawa,ki bani aron wadannan awannin,zamu kasance tare da juna in sha Allah,ma'u zata kasance tare da ke,ayimin afuwa"_ sai kawai ya tura mata,yana buqatar isashen time da zaiyi healing daga nan zuwa safiya,bayaso ya jefata a damuwarsa,wadda batasan sadda ta samo asali ba,yana ganin kamar yin hakan rashin adalci ne kawai.

Yanaso yaji muryarta shima......yana kewar wannan lallausan sound din nata wanda koda fada takeyi ko masifa laushinsa sai ya bayyana,but definitely idan taji muryarsa saita gane damuwarsa.

Cikin taqaitaccen zaman kusa da kusa da sukayi da juna,yana mamakin yadda take da saurin karantarsa,sauyawarsa ko damuwarsa,walwalarsa ko akasinta.

Abu daya daya sani shine baiwa ce,ba duk namiji Allah kewa baiwar mace me kula da dukka damuwarsa da matsalolinsa ba.

Sauran kiran da saqon nasu farouq ne,duka sai ya share,saidai akwai saqo guda daya daya dauki hankalinsa.

"Maamah is sick,she was admitted to the hospital" Idanunsa yaja ya lumshe,baisan me zaice ba?,me zaiyi?,sai kawai ya kashe wayar gaba days ya cillata gefe.

Ya samu yaci abincin kadan,sai ya maida hankalinsa kan tataccen ruwan blood orange natural da aka hado masa dashi,da kuma wadatar kayan fruit,cherry pear jujube sai gooseberry da suka hado masa dashi. Dasu ya danyi fresh up,yadan jira abincin ya narke kadan sannan ya wuce bedroom Kai tsaye.

Duk wani haske da komai da zai bashi sauti sai daya kasheshi,ya zamana daga zallarshi sai sautin alqur'ani da yake tashi kadan kadan ta wata qawatacciyar fitila dake tsakiyar gadon,wadda ke zuwa da qaramar fanka me bada sanyi kwatankwacin na ac da Bluetooth da zaka iya using nashi,sai ya kashe hasken fitilar dake jikin yabar iya sound din.

Yayi lamo saman gadon kaman dazu yana bibiyar karatun,bai tashi gane kuskurenshi ba sai da bacci ya qauracewa idanunshi fafur.

Juyi ya dinga yi saman gadon shi kadai yana jin yadda kadaicinta yake neman hallakashi,kowanne sashe a jikinsa sabreen din yake buqata,kowanne bangare na jikinsa kewarta yakeyi.

"Ya salam ya al-hadi". Yana sawwara ta yadda zai iya yin nesa da ita dalilin tafiye tafiye na kasuwanci......ta yaya hakan zata yiwu?" Ya tambayi kansa da kansa.

Daga qarshe dai ya tabbatar hakan bame yiwuwa bane,ya tashi zaune yana duba qaramin kyakkyawan agogon dake saman side drawers na gadon.

"Oops" Ya furta yana dafe goshinsa,dare yayi,yayi imanin zai wahala idan bata fara bacci ba yanzun,idan kuma har ya zama silar tadata a baccin bazai yafewa kansa ba,sai ya maida kansa ya cusa tsakiyar pillow din yana qagara asuba tayi.

&Tunda ya dawo sallar asuba ya wuce gym,yana fatan hakan ya dawo masa da kuzarinsa daya rasa a kwanakin nan saboda tashe tashen hankulan da suka durfafoshi. Waya ya dauka kai tsaye ya kira Jordan ya bashi umarni ya koma gida ya dauko masa duniyarsa. Yana so nan din ya zame musu wani kebantaccen guri da ba kowa bane yasan da zamansa,da qwaqwalensu zasu huta na koda kwanaki uku ne kafin su koma cikin jama'a.

Sanda ya kammala shiryawa cikin sassauqar shirt da trouser sai ya wuce parlor. Da kansa ya shiga kitchen ya tafasa madarar shanu fresh one da turmeric dan kadan ginger da cloves ya dawo falon yana sipping kadan kadan yana kamo tashoshin daya saba kalla a lokuta irin wadannan da ake labarai na qasa.

Tashar farko cikin headline na news din hoton maamah ya gifta da anyo briefing na case dinta daga qasa. Zuciyarsa ta motsa tana bugawa da wani irin yanayi,sai kawai ya matsa remote din yana canza tasha.

Channel din daya kama sun fara news tuni,the next abinda ya faru shima dai hoton maamah ne da title tafka tafka na zargin kidnapping.....wannan channel din sun samu nasarar saka wani d'an yanki na tambayoyin da 'yan press din sukayi mata a Farfajiyar gidanta,wanda kusan duk me hankali idan ya kalla yasan maganganu ne kama kai.

"Subhanallah" Ya fadi yana sauke canza channel.

Already su sun gama,saidai.maimaicin kanun labarai da shima hoton maamah dana hajja harira harma dana fareeda da suka cika screen din. A nan ma baida buqatar yaji komai,yasan tunda haka ta faru duk inda zai kunna ma abinda zasu nuna masa kenan tamkar sunsan yana da alaqa da ita.

Wani zafi zuciyarsa ke mass,wani irin kud'a da quna take masa. Ya dauka ko meye maamah tayi....kuma ko meye akayi mata ba wani sauran abu daya rage da zai tada masa hankali a kanta ko ya qona masa rai,sai gashi bayyanarta a screen na TV dinsa yana neman hana mishi nutsuwa.

Har addu'a yakeyi......har fata yakeyi ta zabi adadin abinda take buqata daga gareshin.....mutanen dake kewaye dashi a yanzun,mutanen da yake rayuwa dasu a yanzun suna da matuqar muhimmamci a tattare dashi,mutane ne da bayajin idan wani abu maras kyau ya samesu ta sanadinsa.....ko ta sanadin arziqinsa lallai ba shakka bazai yafewa kansa ba,bazai iya jurewa ya rasa koda rai guda daya a cikinsu ba. Koda maamah ta karbi abinda takeso ta koma inda ta fito,har kullum,muddin da numfashi a gangar jikinsa bazai fasa mata addu'a ta shiriya ba darajar haihuwarsu da tayi.

Idanunsa basa wajen,amma tsaiwarta a bakin wajen yaji a jikinsa,don haka ya daga risunannun idanuwansa yana dubanta.

Tayi wani irin kyau da shigar mutanen turkey,wasu irin riga da wando da dan hijab dinsu me suturce jiki. Ya sauke idanunsa akan cikinta,sai yaga kaman ya qara tasawa,kaman ya qara girma a kwana daya tak da yayi bai ganta ba. Wani sanyi da rahama yaji yana sauka a zuciyarsa,sai ya miqa mata hannuwansa yana lumshe idanunsa,abinda ya bata tabbacin lallai yana buqatarta kusa dashi.

A nutse ta tako,wanda tun kafin ta iso inda yake qamshin nan nata,qamshin kabbasar nan tata ya soma kasheshi daga inda yake a zaunen(incense by kabo daughter....duniya ne sis,ki gwada ko sau daya,basai nace miki gobe ki koma ba,wannan tasted and trusted ne,bawai just normal tallan da bakasan ya kan abun yake ba(+234 803 211 9803).

Kasa dauke idonsa yayi daga kanta saboda wani salon tafiya da takeyi da yake fusgar hankalinsa,har ya qagu ta qaraso inda yake ya shaqi ni'imtaccen qamshin nan da yakejin inama kowanne second da zai shude a rayuwarsa zai samu daman shaqarsa?.

Kaman tasan da hakan,tana zuwa dab dashi saita cake ta tsaya,ta yamutse fuska,ta turo lips dinnan nata ta kuma juya masa qeya.

Ya masa nisa ya tsaya tambayarta abinda ya faru,don haka kanshi tsaye ya miqe,ya taka ya zagayo gabanta. Tsaiwa yayi yana duban kyakkyawan fuskarta data soma nuna yanayi na masu ciki,yasa hannuwansa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login