Showing 138001 words to 141000 words out of 363280 words

Chapter 47 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1383

Saman kansa homburg hat ce data fidda kyakkyawar fuskarsa da wani irin kwarjini da kwantacenn kyau da zai iya gaya maka lallai shi din ruwa biyu ne da ake kira da halfcast. Sosai kayan suka zauna masa a jikinsa,rigan na dan bayyana muscles din da jikinsa ke dashi,wannan kadai zai gaya maka qaqqarfa kuma ginannen jikin da yake dashi.

"Gayennan yana wuta.....anya ba zamu koma ciki mu canza dressing ba......kada maldivians dinnan su dauka age mate dinmu ne fa" Musaddiq ya fada sounding seriously. Dariya sosai amna ta fashe dashi tana dora kanta kafadar saddiq

"An gaya muku ya fu'ad wai sa'anku ne?,ku sallama kawai ku huta......idan kanajin babban kifi to shine.......kunga maza kun raina kanku ko?" Dungureta saddiq yayi yana janye jikinsa

"Zakiyi dariya da kyau ai......abinda ya kamata ki fara tambaya ko ki damu dashi shine dalilin da yasa ya fito.....ku koma ciki ba zaku je ba,ko ya fito ne mu fita tare kinga yau shikenan......ba sauran sakewa" Tsit dukkansu sukayi,saboda sunsan halinsa zai aikata da gaske. Kowa ya dauke wuta a cikinsu suna fargabar hukuncinsa,har zuwa sanda ya qaraso.

Da ido kawai ya yiwa Jordan inkiya ya fito daga mazaunin driver din,ya zagayo kujerar me zaman banza ta kusa da driver ya shiga yana cewa farouq

"Shiga mu tafi". Da kallo farouq ya bishi,har ya shiga ya zauna,ya daga idanunsa masu cike da kwarjini ya kalleshi yana daga waje

"Ko ba zaka tafi bane ka tsaya kana kallona?" Kai kawai farouq ya kada yana tunanin abinda ya sauya ma fu'ad ra'ayi ya aminta da karan kansa zai bisu.

Yau fitar dadinta sai taji baikai na jiya ba tun akan hanya,duk hirarsu suna kiyayewa da hayaniya ko abinda zasu fadi. Hira suke da farouq a gaban mota duk da batajin me suke fada,a haka suka isa guri na farko.

Sunyi yawo sosai cikin kasuwannin da suke da kayan gargajiya na al'adun qasar Maldives.....sunyi siyayya kaman ba gobe,duk da bata taba komai daga card din da amna ta bata ba,hasalima a cikin mota ta barshi cikin handbag dinta da bata fito da ita ba.

Gurare da yawa idan sunje zamansa yake cikin mota,dama shi din bai damu da shiga gurare irin wadannan ba. Koda sunyi tafiya guraren da yakanje gurare ne da suke da alaqa da kasuwancinsa,ko tarihi na kasuwanci ko kuma zai amfani kasuwancinsa,shi yasa yau din suka cika sosai da mamakin ganin yabi bayansu,duk da dukkaninsu kowa ya ta'allaqa hakan da sabreen ce sila.

Guri na qarshe da suka je,suna fitowa ya miqa hannu ya karba key na motar daga hannun jordan

"Zaka iya komawa gida" Yace dashi kai tsaye. Takawa yayi a hankali ya isa gaban motar,hannunsa daya zube a aljihun wandonsa,yasa hannu ya bude motar ya shige seat din driver.

Junansu suka kalla tsakanin saddiq da musaddiq da amna,mamaki ya cika kowa ganin yau hamma da kansa zaiyi driving?,wani abu da suka jima basu ga yayi ba

"Zaku shigo mu tafi ko na wuce abuna?" Ya leqo kansa yana magana dasu da miskilar fuskar nan tasa. Har rige rigen shiga suka dinga yi kowa mamaki kwance qasan zuciyarsa.

Kaman yadda kusan komai nasa ya banbamta dana kowa haka tuqinsa,driving yakeyi cikin wata irin qwarewa da nutsuwa,gudu baiyi yawa ba......haka babu laqai laqai.

"Ina muka nufa ne sir?" Farouq daya kula ya sauya hanya ya tambayeshi yana kallon fuskarsa dake a dinke tsaf. Shi kwata kwata ma guraren da sukaje kaman basu bashi walwala ba ko kadan.

"Siyar daku zanyi na qara jari" Ya amsa masa a taqaice yana sake maida dubansa sosai ga titin. Dariya sosai farouq ya saki yana relaxing jikin kujerar motar

"Hakan yayi ai......dadin abun bamu kadai ka debo ba ai" Yayi maganar yana turo p_cap dinsa gaba. Sarai ya gane me yake nufi,shi kuwa bazai kulashi ba,saboda neman wajen da zai dan sake samun relief kawai yakeyi.

Sannu a hankali suka shiga Vaadhoo island sunan dake rubuce baro baro a allon sanarwa. Ihu amna keson saki na murna amma sanin wanda ke driving bayason magana me tsauri ko hayaniya ya sanyata danne bakinta ta dole tana duban saddiq dake zaune opposite dinta. Gira ya daga mata alamun tambaya,saita nuna masa map na inda suke ta qaramin screen din dake maqale a gefansu.

"Vaadhoo.......glowing island!......sea of stars" Ta fada da wani irin farinciki daya lullbeta don sai a sannan ta lura da sun qaraso glowing island din.

"Addana.......mijinki is very incredible wollah.......kinyi dace......kin dace....he's very calm,ya iya surprise,komai nashi unique ne" Ta fada farinciki yana kamata,farincikin yau zata ga inda ruwa yake haske......yashi da qasar gurin itama ke haske tamkar an watsa taurari,wannan yana gaya musu qila ya musu booking na kwana a wannan sabuwar duniya,ko kuma zasu kai dare a wajen suka yadda komai yake gudana.

Murmushi kawai tabi amna dashi......babu wani abun burgewa tattare da yayan nata......itace dai bata sani ba. Amma kuma sai itama ta samu kanta da fara sallamawa al'amarin sanda suka isa adhaaran prestige,ma'aikatan wajen kuma suka iso suna maraba dasu,da alama sunsan da zuwansu wajen.

Da idanu kawai take bin gurin,da gasken gaske ta zama 'yar qauye tuburan. Gidaje ko dakuna zatace saman ruwa da wani irin tsari me jan hankali. Bata da sauran abunyi illa bayansu da tabi kaman yadda taga sunbi daya daga cikin ma'aikatan saman wani shimfidadden abu daya zama hanya kuma abu daya da zai hanaka tafiya saman ruwan.

Kai tsaye zata iya kiransa hotel ko gidan saukan baqi. Suka miqawa kowannensu wani dan card da komai da komai,sai amna ta daga kai ta kalleta bayan ta gama dubawa.

"Ga inda zamu zauna can.....zamuci abincin dare a nan.......zami fita sea of stars muyi kallo harmu shiga idan da yiwuwar haka.....komai mukeso zamuje mu karba......amma adda naso kwana zamuyi......inama hamma yace mu kwana?" Amna ta fada tana duban sabreen da hankalinta yake kan ruwan dake gaban door glass din. Shimfidadden ruwa ne iya ganinka wanda yake bada kalan sky blue,abun akwai mamaki yadda mutane keta harkokinsu Kai tsaye suna kai kawo kaman cikin gidajensu suke.

"Muje dakinmu adda" Amna ta fada da doki tana yin gaba,bayan ta fidda wayarta ta fara daukan hotuna da videos.

Bata yiwa kanta da kanta qoro ba,idanu ta bude sosai tana kallo,yanayin iska da tsarin wajen ya banbanta da duk wani guri data taba zuwa.

Gaba daya hankalinta a tashe yake,kaman yadda tunaninta yake a jagule waje daya. Iya zunzurutun dollars din data kashe don tsara komai,tun daga zuwanta Maldives da zamanta a wajen ba wani abu bane na damuwa muddin buqata zata biya. Bahaushe yace ranar biyan buqata rai ba'a bakin komai yake ba. Ya zuwa yanzu da take zaune gaban glass door din tunani ne fal zuciyarta,tana jin kamar tayi wauta da take zaune tana lissafin zai wahala fu'ad din ya tsallake wannan island din ba tare daya shigoshi ba.

Tayi zurfi cikin tunanin daya cika mata kwanyarta taji sn daneta daga baya gami da maqaleta da kyau.

"You didn't missed your target......you hit it!" Wanda ke maqale a bayanta ta fada da murya me qarfi.

A zabure ta cire hannuwanta daga wuyanta gami da waiwayowa gareta,tana jin abun kaman mafarki,idanunta dukka a waje take dubanta

"Ki gayan gaskiya.....bazan iya jurewa ba idan kikacemin qarya kike"

"Wallahi wallahi me jadda ya shigo......but shi da familynshi ne duka,but kaman dakuna daban daban ne"

"Thank god.......ki miqawa wannan Chinese boy din wannan abun.......banason kuskure......after 30minutes zan shiga dakin,ya saka cameran daidai yadda zai nuna komai.......ya tabbatar yayi diluting tablet din a ruwa da lemonsa".

"Done!......breaking news zaya fita zuwa ga Nigeria" Ta fada tana barkewa da dariya,yayin da fareeda ta tayata da qaramar dariya mata sauti. Juyawa tayi ta fita,sai ita kuma ta soma zame kayan jikinta da gagggawa tana wucewa wata siririn hanya da zai kaita toilet.

Cikin qasa da minti goma ta fito,ta kuma tsaya a side din dressing ta soma balle wasu turaruka tana shafe lungu da saqo na jikinta,ta ware gashin kanta da kyau ta jiqashi da sassanyan qamshin turare,sannan ta bude wani jaka ta zazzage kayan ciki tana dagasu kafin ta fara shirya kanta a cikinsu.

Wasu gantalallun riga da wando ne,very skinny,ba iya jeans din ba,har rigar data sanya. Ba wani sirri boyayye ko bayyananne da Allah ya wadatata dashi da bai fito ba walau qashi ko tsoka,me tudu ko me kwari.

"Wow......wow" Taji an fada daga bayanta. Kadan ta juya tana kallonta don batasan ta shigo ba. Hannu ta watsa mata tana tambayarta alamun yayi?

"Perfect.......kome kamun kan mutum ya ganki sai ya fada......ga kuma wadancan abubuwan na aikinsu yadda ya dace.......zance zaisha banban nan da nan......fatan nasara" Ta fada tana daga mata babban yatsa. Wani shu'umin murmushi ta saki tana takawa gaban madubin,ta sake juyawa sosai a gabansa tana qarewa kanta kallo. Ita kanta ta yaba da kanta ballantana wata halittar d'a namiji?.

"Yadda bai sassautawa zuciyata ba bazan sassauta masa ba.......sai na tabbatar na zama cikakkiyar matarsa da shaidu na halas sannan zan barshi ya shaqi numfashi me kyau" Ta qarasa maganar tana daukan chewing gum ta jefa a bakinta tana duban qawartata

"Sai na dawo?" Ido ta lumshe sannna ta budesu a kanta.

"Inajin inama ace nice yau zan samu nasarar kasancewa da namiji irin muhammad jadda......koda bai aureni ba babbar nasara ce wannan a wajena......best wishes" Wani kallo fareeda ta watsa mata

"To mayya........wata miyar ai sai a maqota,babban goro sai magogin qarfe kuma" Dariya ta sheqe da ita

"Na sani qawata" Itama saita tayata tana ficewa zuciyarta fes yau din.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

73


Karo na uku ya sake daukan cup din yana kurban tataccen ruwan strawberry din da shine abu na farko daya soma zaba akai masa. Ya maida cup din ya ajiye yana zare belt din suspenders dinsa. Sosai gurin ya masa kyau ya kuma qawatar dashi,banda annin da suka baro a gida ita daya ba shakka ba abinda xai sakashi qin yanke hukuncin kwana a wajen,amma ko iya hakan ma nan da eleven yasan ya samu refreshment din da yakeso ai.

Mamaki ya cikashi jin an murda qofar an kuma shigo,ya waiwaya yana tunanin saddiq ne ko musaddiq,saidai kuma fuskar daya gani tasha banban da fuskokinsu gaba daya.

Da kanta ta fito don karbawa amna grilled fish dinta don girmamawa ga yarinyar yadda take kimantata da ganin girmanta,amnan tana da wani irin kirki da sauqin kan da yake bawa sabreen mamaki,don haka tace

"Zauna addanki ne zata amso kifin nan da kiketa kwadayi".

A gurin ta samu musaddiq shima zai karba nasa order din,wani tsari ne dasu akan grilled fish......zaka je wajen da kanka,zasu nuna maka inda kifayen ki ninqayarsu cikin ruwa ba tare da sanin kwanakinsu qayyadaddu bane,zaka nuna irin kifin da kakeso take a ciroshi a gasa maka a baka ka wuce. Kusan tare suka zaba aka kuma musu irin gashin da sukeso,musaddiq din ya miqa mata daya plate din hannunsa

"Addanmu......taimaka ki miqawa hamma wannan please.....kunfi kusa da dakinsa....Allah yasa banyi laifi ba" Murmushi kawai tayi ta karba,tana mamakin yadda suke bata girma haka,bayan duk cikinsu idan ka dauke amna bata girmi kowa ba. Ason ranta tace ya taimaka mata ya qarasa masa dashi,to amma tana jin nauyin kasa masa alfarmar ko don yadda suke daukanta.

A nutse take takawa tana duba dakin da take tunanin kamar ya shiga ciki.

"Na gaya maka.....kana ganin kaman d wasa nake?......zanci gaba da kasancewa a kowanne taku naka......zan kasance cikin kowanne fitar numfashi da daqiqa naka.......makahon so nake maka.......i can't imagining yadda xan iya ci gaba da rayuwa babu kai". Tayi maganar tana karantar qwayar idanunsa. Tanaso ne komai ya kankama a jikinsa kafin takai ga cikar burinta.......tanason kowanne hankali yayi nesa da tunaninsa kafin ta aiwatar da komai.

Wani qaqqarfan yanayi dake taso masa ya sanya ya kasa cewa komai. Kokawa kawai yakeyi da abinda yakeji din,yanason tabbatarwa da ba wannan qaqqarfan abun bane ke qoqarin motsawa?. Yana tsaka da wannan kokawar da duk wani control dake aiki a jikinsa ya tsinci fadowarta jikinsa,ta sanya dukka hannayenta ta masa wata irin bahaguwar runguma kaman zata shige cikinsa tana fadin.

Sake kallon number dakin tayi da kyau,ta sake samun tabbacin shine,saita murza handle din tana murmushin hattararta da yadda ta iya gane dakin,ta tura qofan tana sanya qafafunta ciki.

"I need you......i need you please jadda......kada ka juyawa zuciyar dake sonka baya.....ka bari na sauke maka abinda kakeji.......kaima kana cikin irin yana yina......na gani a qwayar idanunka" Kalaman da ta fara maraba dasu kenan kafin qwayoyin idanunta su sauka a kansu.

Idan idanunta ba qarya sukayi mata ba fareeda khaleed mustapha ce cikin mummunar shiga.......dukka su biyun suna a tsaye,yayin data samu kyakkyawan maxauni a qirjinsa saboda tsahonsa daya shanye nata.

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Ta fusga daga qasan zuciyarta zuwa labbanta,saidai sautin baikai ga fita a sarari ba ta samu ta janye qafafunta ta koma da baya.

Dukka jikinta bari yakeyi,abinda ya sanya plates din guda biyu duka suka kife ruf a qasa.

"Sorry madam" Wata murya ta tsarga saman kanta,kafin ta dago ma har ya tsuguna yana kwashe duka plates din. Baya taja k????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? awai ta tsaya tana qoqarin maida numfashinta daidai,don bata da wani qarfi na kwashe barnar da tayi sam.

"Relax Sabreen relax mana.....fareeda dince baki sani ba?,ko fareeda dince bakisan yana bibiya ba?,sau nawa kikaga kiranta a wayarshi da luluqin dare?,me kudi ne fa?,yana da kudin da zai iya gayyatar ko wacce mace ta debe masa kewa......that's why aure baya a gabansa......karki yaudari kanki sama da haka ma zaki iya gani...."

"And then waye shi a gurinki da zaki rude har haka?" Wannan gigitacciyar tambayar ta fado mata,abinda ya sanyata gayyato duk wata nutsuwa dake kowacce kafa ta jikinta ta azawa ranta tana duban matashin daya miqe yana dubanta da plates din a hannunsa. Cikin harshen turanci ya fara mata magana

"Sannu ko?,muje su canza miki wani kifin" Duk da ba'a hayyacinta take ba amma koda ta dubeshi da kyau sai taji a jikinta mutumim africa ne,duk kuwa da cewa shi din ba baqi bane.

Duk wani zaren tunaninta ya gama kwancewa,don haka bata da wani zabi illa binsa ta karbowa Sabreen wani kifin,saboda bata da abinda zatace mata idan ta koma dakin haka.

Tana biye dashi yana qoqarin janta da hira da mata tambayoyin da bama iya amsa masa takeyi ba saboda yadda zuciyarta ke tsananin gudu.

Hannunsa daya ya sanya ya yakice fareedan gefe zuciyarsa tana wani irin mahaukacin bugu. Fushi da feelings gaba daya sun hadu suna neman sauya tsarin bugun zuciya dana numfashinsa.

"Wacce irin dabba ce ke?,a hankalinki kike kuwa?" Ya fada da wata irin tsawa data kusa tarwatsa duk wani plan nata......amma data tuna wannan shine plan dinta na qarshe saita miqe da hanzari tana cewa

"Bazan taba iya qyaleka ba,sonka mahadin bugun numfashina ne....ka soni please.....koda na iya yaun....." Bata samu damar qarasawa ba saboda wani bahagon mari daya dauketa dashi yana huci,sai gata qasa warwas ta zube bayan ta tuntsura ta dawo ta zauna.

Huci yake fitarwa sosai yana jin yadda jikinsa ke sake rikicewa

"Daga yau ya zama na farko kuma na qarshe da kika sake shiga hanyata ta kowacce fuska.....if not.....zan batar dake ne a banza......idiot kawai mara amfani!" Yana kaiwa nan ya miqa hannunsa ya dauki key din motarsa da wayar dake ajiye tare dashi guri daya,bai kuma tsaya sauraron kukan data saki tana kiran sunansa ba ya sanya kai ya fice.

Yana ji a jikinsa ba daidai yake ba,hakanan baya jin zai qara koda minti guda cikin island din ba.......kaman yadda bazai iya tsaiwa nemansu farouq ba,haka ya nufi hanyar barin wajen wani irin fushi yana lasar zuciyarsa.

Kaman cikin gizo idanunsa suka sauka a kanta. Tana tsaye suna facing juna ita dashi. Ya miqa mata kifin da aka nadeshi cikin aluminum foil yana sakar mata murmushi. Bata da wani zabi da ya wuce maida masa martani duk da irin abinda takeji qasan ranta.

"Thank you" Ta fadi tana juyawa. Taku uku kacal tayi ta tsinceshi a gabanta babu zato ba tsammani. Wani irin zazzafan kallo take tsinta cikin idanunsa.....wani kakkaifan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login