Showing 348001 words to 351000 words out of 363280 words

Chapter 117 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1390

daga bakin mutumin daya fara zuwa mana da labarin wane yayimin kaza,wane ya batamin ko yayimin ba daidai ba.....nan da nan wannan daya fara zuwa da labarin saimu dauka shine me gaskiya,bisa jahilci irin namu na neman jin ba'asi daga bakin wani sashen,wanda muddin zaka kasance mutum irin wannan a rayuwarka,za'a yita sanyaka batawa da mutane masu daraja da kirki.....zaka yita fada da mutanen da basuyi maka komai ba.....za'a sanyaka ka yita yanke alaqa da mutanen da alaqarku keda matuqar amfani a duniyarku da lahirarku.......wannan ba halin musulmi na kirki bane a matsayinka na babba hilal.....ba kuma dabi'ar qwarai bace.....ba dattako sam a cikin ta,dukkaninku daga yau na horeku da zama masu bincike".

"In sha Allah anni" Ya fada yana saukar da kansa qasa. Waiwayawa tayi ga yara biyun dake gefe tana dubansu.

"Faarees da ra'ess ya tabbata kunyi qarya.....ku bawa Aadeel haquri,sakamakon qaryarku kuma wannan satin gaba daya kada naga uniform dinku a wash room,da kanku zaku wankesu duka satin nan.....sannan idan ummenku ta dawo......kune na qarshen zabar tsaraba har sai kowa ya dauka nashi" Ta fada tana nunasu da yatsa.

Haqurin data buqata suka juya suna bawa wanda ake kira da Aadeel din haquri,ta kallesu daya bayan daya still tana cewa.

"Ku kyautatawa junanku......kyakkyawar mu'amala itace mutum......girmankai na shashasha ne maras wayo.....hassada ta maras rabo ce,don tana cinye kyawawan ayyuka kaman yadda wuta takejin yayi.......shi kuwa sharri dan aike ne,daga inda aka aikashi duk daren dadewa nan zai dawo......alkhairi kuma danqo ne baya faduwa qasa banza.......komai dadewa ka shuka alkhairi shi zaka girba,kaman yadda komai dadewa idan ka shuka sharri cuta ko ha'ince sai ka girbeshi.....kyakkyawar dabi'a jari ce da babu kamarta,wadda duk dukiyar gidanku bata isa ta siya maka ita ba......hakanan duk talaucin gidanku idan ka sameta kaiba talaka bane har gaba da abada".

Ire iren kalmomin kaka ta gari kenan a duk wani zama da zai hadata da yaran,bakinta sam sam baya gajiya da furta wadannan kalmomin a kansu,har sun fara haddacesu tun basusan ma'anarsu ba,zuwa yanzu kuma wadanda suka fara girma a cikinsu sun haddacesu tas a kansu.

Basu fita a wajen ba saida kowa ya gaisa da kowa,kowa ya koma yanayinsa na dazun sannan. A sanda suke fita a lokacin sauban ya koma inda ya taso,ya maida headphone dinsa saman kansa yayi playing karatun yana ci gaba da ji hadi da lumshe ido.

Kammaninsa da dabi'unsa kamar babansa,duk wani harka ta hayaniya ko fada babu shi a ciki,kaman ya yiwa kansa rigakafi daga fushi da zuciyar da yasan yana da ita.

Dauke kanta anni tayi daga inda yake murmushi yana subuce mata. Tana ji a jikinta anya sauban din ba shine wannan HASKEN da take gani tsakanin iyalinta ba?,wannan mai riqon addinin ma'abocin cikakken ilimi daya haura na saura?.

"Allah kayi mana zabi da mafita mafi alkhairi" Ta fada a nutse tana jawo hallul masa'il dinta tana dubawa.

Tsaiwa Amaan yayi yana hango abokin tagwaitakarsa wato muhammad ameen dake fitowa daga sassansu. Sanye da fararen kayan da aka yiwa ratsin baqi sak irin kayan dake jikin Amaan din.

Shima gunsa ya nufo kai tsaye yana dubansa.

"Abbee fa ya shigo yanxun......kuma naga ya shirya.....ina kuma kyautata zaton ummee zaije daukowa daga airport......na tabbatar dukkaninsu sun manta da yaune wedding anniversary dinsu,15yrs" Ameen ya qarasa fada da faffadan murmushi daya qara masa kyau,yana kuma d'age dukka girarsa sama.

"Na tuna......akwai wani abu ne?"

"Yes" Ameen ya fada ya fada yana dariya.

"Ya kamata muyi wani abu,yadda naga abbee yana wani shiryawa yanata duba mirror kaman wani dan saurayi,dolen saiya burge duniyarshi". Dariya suka saki lokaci daya,amaan yace.

"Babu ruwana idan ummee ta jika.....let's go,mintunan zuwanshi da dawowarsa basu da yawa" Hannun juna suka riqe suna hirarrakinsu,wanda kana kallo zakasan akwai shaquwa da qaunar juna me tsananin gaske.

Ita kadai yau take zaune saman wheelchair din nata,kusan awa biyu kenan. Mutum daya take sanya ran shigowarsa kaman yadda ya saba......yaro guda dayan da take mamakin yadda yafi kowa qulafucinta a gidan da qoqarin kula da duk wani motsi nata......yaro guda dayan da ita kanta yafi shiga ranta sosai wato sauban.

Jifa jifa tana jin motsin yaran,guje gujensu kasancewar weekend ce.....amma yau ko wasan kaka da jikan data jima tana nuna musu bataso ba wanda ya leqota yayi mata,duk sai ta jita ba dadi.

Sabreen ce ta fado a ranta,ba yadda za'ayi duk wuya.....duk runtsi idan tana nan ta barta ta zauna shuru haka,koda kuwa bata buqatar komai zata umarci biyu ko uku cikin haihuwa yara rai goma da Allah ya bata wani yazo ya zauna kusa da ita.

Wani abu ta hadiye,karon farko da taji tana dokin ta dawo daga tafiyar kwanaki ukun da tayi zuwa qasar saudiyya.

Daidai nan yayi sallama,sanye da dinkin kaftan da aka yishi da wani fari qall din yadi me daraja. Dinkin babbar riga ne da 'yar ciki dinkin da aka zamanantar dashi,ya kuma sake maida fuad din kaman wani qaramin matashi.

Baiyi amfani da hula ba,sai farin rawani daya nada saman farar hular kanshi,sai ya fito kaman wani basaraken malami.

Duk da ya dubata dazun yanzun bai gaza wajen dawowa wajenta ba,ya tsugunna ya gaidata,ta amsa masa da sautin da ba kowa yake iya fahimtar abinda take fadi ba idan ka dauke shi da Sabreen da suke iya fahimtar kusan komai tace.

Nasarar fara fitar sautin nata ma gaba daya ya samo asali ne daga Sabreen,wani umra da sukaje,ta samu daman tara roba wajen indararon ka'aba ta tari ruwan saman dake sauka ta saitin wajen,ta kumayi tofin addu'o'i sosai data samu daga wajen mallam,ta durfafi bata.

Wani abu ne daya tsayewa maamah din a rai,har yau ta kasa mantawa da abun,duk da sai bayan nasarar ta samu takejin daga ina ruwan ya fito,basu gaya mata ba gudun kada taqi sha.

"Yau zata dawo?,daukota zakaje kayi?" Ta tambayeshi sanda ya miqe yana soma takawa da murdadden harshenta.

A mamakance ya juyo yana duban maamah din,wai yau ita ke tambayar dawowar Sabreen?,wani farinciki yana sauka a zuciyarsa ya gyada mata kai.

"Eh,saura mintunan kadan jirgin ya sauka".

"A dawo lafiya" Ta furta tana jin wani dadi yana mamayeta .

"Allah yasa" Ya amsa wata qwalla tana cika masa idanu. Yau maamah ke masa addu'ar da alamu sun nuna kai tsaye suna fita ne daga zuciyar ta?.

Sai daya tsayar da jordan cikin motar ya daidaita kansa,ya kalli fuskarsa yaga ta koma ainihin mode dinta sannan yace suje. Bayason yaje da wani sauyi ko kadan saman fuskarsa,don yasan abune da tana masa kallon farko zata karanci hakan,shi kuma duka yau din yana buqatar kyakkyawan yanayi shida duniyarshi,wadda yayi missing nata tsahon kwanaki biyar kenan.

Cikin hukuncin Allah JADDA MAJESTY JET ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake abuja.

Mintuna kadan kafin jirgen ya sauke matakalarsa a hankali,tsakanin wasu mintunan kuma mutanen dake da iko da jadda majesty din suka fara fitowa.

Da farko wasu matane guda biyu masu baqar fata,giant dasu,sanye da baqaqen abayas da mayafinta wanda sukayi rolling,sannan kuma suka manne idanunsu da baqaqe glasses.

Mata biyun dake bayansu su dinma abayanne a jikinsu,saidai tasu ruwan wine color ne. Daya janye take da wata qaramar luxury luggage,yayin da dayan ke dauke da wata kyakkyawar jaka.

Kyakkyawar halittar dake takowa daga tsakiyarsu ta dushe kowacce diya mace dake tafiya tare da ita.

Mistress ameenatu ahmad mrs muhammad jadda......the lady of the house itace ke takawa d'ai d'ai cikin wani yanayi da zai tabbatar maka da cikar kamala da nutsuwa gami da kammaluwar hankali da nutsuwarta waje guda.

Sanye take cikin wata Turkish gown ta wani lafiyayyen material,rigar ta bude sosai daga qasa,armless ce butter color me adon gray color da wasu manyan flowers masu ban sha'awa,wadda aka yiwa top gray color me dogon hannu da kuma sarqarta a jikin rigar ta yadda basai ta buqaci wata spare sarqa ba.

Tayi rolling kanta da gray color din wani exclusive veil,qafarta na sanye da wani high hill daya kasance mahadin qaramar handbag din hannunta da batafi taci qananun abubuwa ba sai tsananin tsada da jakar ke dashi.

Rungume take da wata baby girl wadda ke sanye da gown armless fara qal data kasance mahadin takalmin qafarta da kuma dan crown din dake saman kan yarinyar wanda ya hana sassalkan dogon gashinta bazuwa zuwa sassan fuskarta.

Wani irin kamanni ne tsakanin ta da yarinyar na sak da sak.......abinda kawai ya banbanta su shine kasancewar yarinyar 'yar kululluba da ita.

Ameenatu muhammad jadda kenan IFFA......shalelen family din jadda....diya mace qwaya daya da suke da ita cikin villa din tasu. Chubby din abbee......chubby din anni......kuma chubby din triplet da twins na jadda villa.

Cikin kyakkyawar nutsuwar nan tata Madame kuma duniyar muhammad jadda wato ameenatu ahmad ke sauka da takalmin ta me tsini wanda zakayi tsammanin ba zata ita tafiya dashi ba,saidai caf caf take takawa da abinta cikin sani kan ado da gayu daya ratsa jini da jikinta gaba daya.

Wani fitinannen qamshi take fiddawa wanda ya huda jikinta,irin qamshin da sai kazo kusa da ita kake iya jinsa a duk wani motsi da zatayi.

Dawowarta kenan daga qasar saudi Arabia,bisa gayyatarta da sukayi don su karramata da lambar yabo da kuma girmamawa ta musamman kasancewar gidan marayunta gida na farko da kaf nahiyar africa dama wasu qasashen qetaren babu koda kwatankwacinsa.

Gida ne daya fara bawa yara feature me kyau......ya fara inganta musu rayuwa da inganta mafarkansu bisa jagorancin me gayya me aiki muhammad fu'ad jadda mamallakin kamfani guda daya da baida kishiya dake sarrafa gold da Diamond a qasash kusan arba'in cikin qasashen da muke dasu a duniya sama da guda dari biyu.

"Karbeta najma.....tayi bacci" Sabreen ta fadi a nutse tana miqawa nanny dinta ita gami da gyara rolling dinta daya dan cukuikuye.

"Sarkin rigima" Nanny din nata ta fada tana rungumeta a kafadarta

"Kunfi kusa,fadanki dana iffa ko waye ya shiga ma kunya zaiji" Sabreen ta fada tana murmushi.

Murmushin daya samu isa ga idanuwan Muhammad fu'ad dake zaune cikin mota,ya kuma kori Jordan ya saita madubinsa yana qarewa duniyarsa kallo abinsa.

Sam bata ganshi ba,bata kuma san yana mata kallon qurillar nan tashi ba,duk da cikin jikinta tana jin kamar wani kusanci yana wanzuwa tsakanin zukatan guda biyu.

"Welcome maa" Shine abinda dukka ma'aikatan da suka rako boss jadda suke fada cikin rusunawa da girmamawa,yayin da ita kuma take amsawa cikin nuna kulawa da tambayarsu aikinsu.

Abun yana bawa fu'ad mamaki sosai.....gaba daya ta zama tamkar wata uwa tsakanin kowanne ruhi dake rayuwa cikin jadda's villa. Ba iya yaran gidan su huda amna dasu saddiq ba......tsakanin kowa da kowa ma,muddin kana kwana kana tashi a jadda's villa.

"Wannan tsadajjen murmushin rabonshi da akeyi ya isa haka please" Ta tsinci lallausan sautin nan nasa cikin kunnuwanta a sanda ya fito daga motar yana bude mata murfin motar yana kuma gyara babbar rigarsa da daya hannun.

"Wow" Ta fada da wani boyayyen sautin da labbanta ne kawai zasu gaya maka abinda ta fada,tana fidda idanunta waje dukka a kansa.

"Muffin......ka koma exactly ranar da ka zama angon ameenatu sabreen.......sak irin shigar".

" Har yau har gobe har kullum ma cikin taya kaina murna nakeyi da mallakar mace irinki......ki taimakeni ki sakayamin kanki cikin motar nan kafin mazan dake airport dinnan kaf su qarasa kallemin ke" Kai ta girgiza tana dariya sanda ta fara takowa cikin jan aji.

"Hammana yaushe xai canza ne?baya kallon madubi yaga yadda ya fara zama babban mutum?,babban mutum din daya ajiye yaran da sati me zuwa zasu kammala secondary school dinsu?"

"Fu'ad bazai taba canzawa ba.....kishinsa da soyayyarsa game da Sabreen suna nan kaman yau aka ginasu" Ya amsa mata yana rufe motar,ya zagaya ya shiga nasa side din.


_wacce addua kuka yimin littafinnan yaqi kammaluwa a yau?_>?y?>?y?>?y?>?y?


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



*_NACE BA......._*>??????
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*=??=??

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*=?G? wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*

*follow us diaries*>?p?>?p?=?O?
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1


173




Wani ajiyar zuciyar numfashi ya sauke yana lumshe ido gami da sauke nannauyan ajiyan zuciya.

"Sai yanzu zuciyata zata koma aiki daidai......welcome home your royal highness" Ya fadi cikin salo na girmamawa yana hada hannuwansa guri guda. Murmushi tayi tana girgiza kai,kullum sabuwa ce a wajensa kaman yadda yake sabo a wajenta.

"Giya nake roohi......hayaty kulliha" Ido ya fidda waje yana tashin motar tasa.

"Wannan ranks din nifa bana gane musu sosai yanzu.......jira n???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ake naga nan gurin ya tasa" Ya fada yana taba lafaffen cikinta kaman bata taba daukan ciki ba.

Itama waro idon tayi tana kallonsa. Mamaki yake bata yadda har yanzu 'ya'ya basu isheshi ba,yara goma cas tara dukkaninsu maza mace daya?,me kuma yake da buqata?.

"Muffin......fauzan fawwaz da fawad ba graduation dinsu next week immediately ana gama bikin nadra da haneefa?". Dubanta kadan yayi sannan ya tada motar hankalinsa kwance.

"What's that supposed to mean? And what's the point?......kin daina haihuwa?". Ganin yadda yayi maganan yana nuna da gaske yake fadi,saita karya wuyanta tana narke masa.

"Hamma......yanka sau hudu fa?...."

"Yanka hudun yana nufin kin gama?" Ya sake tambaya yana tsume fuska. Sosai tayi calming down kanta tana saukar da kanta.

"Ni na isa?" Ta fada a sanyaye. Wani abu data lura dashi yana da bala'in son tara yara,Allah ya taimaketa ya dinga bata bibbiyu har sau uku bayan ukun farko da tayi,iffa ce kawai tazo ita daya abinta,shi yasa idan suka tashi tsokanarta suke cemata me baqinjini,ita ba wanda ya rakota,su kuwa saida suka rako juna,duk da cewa a zahiri kusan farinjininta daban yake,kowa yasan wannan,farinjinin diya mace cikin yara maza.

Shurun da tayi ya sanyashi satar kallonta kadan sannan ya kauda kai,bayason damuwa a tare da ita sam sam,don ta gama yi masa komai a rayuwa.

"Bani labari.....How'd the trip go?". Numfashi ta sauke tana son wadata fuskarta da murmushi,saidai kafin tace komai ya sake magana.

"Banga mamana bafa.....a ina kika barta?"

"Tana hannun Nan najma(kaman yadda iffa din take kiranta)" Kai ya gyada

"I missed her so much......da safen nan abinci sam bayamin dadi idan na kalli gurin xamanta naga bata nan". Baki Sabreen ta tura tana bata fuska.

"I don't know me yasa kakeson min kishiya da iffa ne.......zan bayar da ita fa?". Ido ya waro kaman zai saki steering motar yana dubanta.

" What?,yarona ko daya bazan iya badawa ba koda cikin gari ne dani......in fact ma ni koda mutuwa nayi ban yarda a rabamin yara ba bare ina raye".

"Mu ajiye batun mutuwar nan hamma....." Ta fada tana maida aljihun motar data bude ta dauko mint sweet ta saka a bakinta.

"Komai ya tafi daidai hamma......kuma dukka lambobin yabo dana karramawar da suka bayar naka ne....kaine ka cancancesu......ni 'yar tayi ce,Allah yakai kadan kabarin abba.....sun saka kudade masu yawa a asusun gidan,duk da nace bamu da buqatar wannan,amma sunce zasuyi don neman lada,sannan cikin daliban da muke yayewa duk shekara,a dinga ware mutum goma,maza biyar mata biyar yearly zasu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login