Showing 276001 words to 279000 words out of 363280 words

Chapter 93 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1372

Kyawawan akwatuna ne har guda shida masu daukan hankali,iya akwatun kawai abun kallo ne,ba zaka gane kuma kallo ya koma sama ba sai daya bude abun ciki.

Wasu irin sabbin designs ne na gold masu matuqar daukan hankali. Uku gold ne uku kuma diamond,wanda ta gane haka ne ta qaramar takardar dake maqale a ciki. Uku ya ware a ciki ya tura gabanta,ya bude wani jaka qarama dake gefan system dinsa ya ciro sabbin rafas na dubu d'aya d'aya na dollars a miqe kar dasu ya dora a sama.

"Wannan shine sabon sadakin ameenatu muhammad jadda.....idan tana buqatar sama da haka tayi magana......wannan kuma" Sai ya tura sauran boxes din

"Wannan kuma ladan rainon cikin da za'a yimin....duk da nasan ban isa na biyasu ba.....duk boxes daya a madadin yaro daya yake.....shima idan baiyi ba kiyi naming price dinki". Kaf jinin jikinta taji ya daskare na wucin gadi,uwar dukiyar daya zube mata kawai take.kallo tana jin zuciyarta tana raurawa,sarqoqi shida masu qololuwar darajar da batasan ya zata kimanta kudinsu ba?,ga tsabar kudi daya kusa naira million dari da sittin?. Tsoro ne kawai taji yana shirin kamata,tsoron ta yaya diyar ahmadu kamarta zata mallaki dukiya dare daya irin wannan?.

Tana shirin zamewa tayi kneeling a gabansa ya dagota.

"Kul karkimin godiya....karki qorafi,kinfi qarfin komai da zan baki,don kema kin bani abinda ban isa ni kadai na bawa kaina ba......kin soni da zuciya daya,kin tsallake duk wani gwaji da nayi miki da zummar gano dukiyar kikeso ko bata gabanki,a yanzu ba abinda bazan iya sadaukar miki ba...bare wannan da ba komai bane cikin abinda Allah ya mallakamin ba.....so komai na dauka na baki kin cancanceshi ne,addu'arki da soyayyarki kadai su nafi buqata a halin yanzu a rayuwata,Allah ya yimin komai". Qasa tayi da kanta tana jin hawaye yana sauka a idanunta,sai ya buge da tsokanarta har sai daya rakata daki,ya tabbatar ta kwanta ya lullubeta da duvet ya tofeta da addu'a. Sai daya tabbatar bacci ya soma cin qarfinta sannan ya dawo falon ya zauna yaci gaba da aikinsa.


&Sake juya rubutaccen katin da yake hannunta tayi wanda akayi da zallar ruwan gold tana bin kowanne ado na jiki da kallo. Ko ba'a gaya mata ba ta sani gold ne zube a jikin katin daurin aure takarda maras daraja,ballantana zance yanata yawo anata yamadidin bikin a lungu da saqo na qasar nigeria,tsakanin maiduguri da kano kuwa dumin bikin ake ba'a cewa komai. Umar Farouq hamza kibiya zai auri fannah maisharif babaghana .

Sake buda katin tayi tana duba schedules din,duka a maiduguri ne za'a yi komai,shima abu qwaya biyu ne rakkin sai daurin aure rana ta uku,kamu da za'a hada da zaman ajo,sai bridal shower sai daurin aure,amma ita kanta tasan ace ma ba za'ayi ta'adin dukiya ba qarya ne.

"Ranar juma'a kenan fannah zata shigo ahalin hamza da ameenatu?" Ta furta ta daga kai tana duban wanda ke tsaye a kanta. Kai ya jinjina mata

"Tabbas" Ya bata tabbaci ta cikin baqaqen gilashinsa. Wani shu'umin murmushi ta aje tana ajiye katin.

"Na samu labarin kai tsaye zasu wuce da ita gidanta.....sai washegari da ameenatu zata gudanar musu da walima haka ne?". Kai ya sake gyada mata don bata tabbaci.

Wannan karon qaramar dariya ta saki.

"Hakan nima yayimin.....amma kuma dan jahannama.......bazan iya jiran washegarin ba......inaso ranar juma'ar ta zama rana mafi muni da qunci a wajensu.....inaso ranar ta juye musu daga farinciki zuwa baqinciki......inaso ta zame musu ranar tonon sililin baqincikinsu". Kai ya jinjina yanajin hannunsa yana masa qaiqayi.

"Baki da damuwa......zamu ajiye musu tarihin da zai zame musu abun lissafi da irga har qarshen kafuwar zuri'ar"

"Da kyau" Ta fadi tana cire sarqar gold din dake wuyanta. Sarqa me tsananin kyau tsada da daraja.

"A auna maka ka saida.....ko nawa ta kama kudin naka ne......bayan kudaden da zaku cajesu". Wata irin dariyar jin dadi ta qwace masa bayan ya karbi sarqar,ko a hannunsa kawai nauyinta ya isa ya bashi amsar kudade ne masu nauyi akan sarqar,baiyi wani mamaki ba ya juya ya fice yana jin dadin yadda zai rabauta da riba biyu.

_uhmmmmm,zamu gani,waye zai rabauta?,waye zai fadi?,waye zaiyi farinciki waye kuma zai shiga sasarin baqinciki?_

_Abinda ake gudu fa yana dab da faruwa.....abin boye fa yana dab da fitowa fili_>?y?



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


137


Dakin amna ta tura ta shiga,komai yana kunne bata kashe ba,ita dinma tana saman abun sallah da hijabinta a jiki,alqur'aninta da wayarta duka na yashe a gefe. Komai anni ta tattara mata ta ajiye inda ya kamata,kafin ta qarasa inda take ta tsugunna tana tashinta a hankali.

A firgice ta tashi,saidai kuma ta farka tana fadin hasbunallahu wani'imal wakil(tana da tsananin tasiri,ko iya ita kadai kike riqe,indai abu ya sameki saidai tsananin qaddarar da take rubutacciya da bazata gogu ba).

Kama mata anni tayi suka sauke tare kafin nutsuwarta ta dawo jikinta.

"Tashi kisha wannan" Anni ta fadi tana jin tausayinta haka kawai yana tsarga mata. Maamah guba ce.....wata irin guba me illata jiki da zuciya.....guba me hadarin gaske wadda ya kamata ka tserewa gwargwadon tseren mutuwa........fuad wani irin ruhi ne me cike da tarin alkhairi.....tsananin kirki kyautatawa da kuma sanin ya kamata. Haduwar guba irin wannan da tsakakkakiya rai wani abune dake sanya rai da zuciya cikin kokwanto me tarin yawa.......maamah lu'ulu'u ce a cikin juji.....kuma tamkar ayar nan ce ta alqur'ani muraran da take fadin cewa "Allah yana fitar da rayayye daga matacce suna fitar da matacce daga rayayye . Saidai abu daya data sani......amna ba zata samu irin soyayyar data dace ba....mariya ba zata taba marabtar amna a matsayin suruka kuma mata ga yaronta ba.

Koma meye tayi accepting saboda girman fuad a gurinsu....yafi qarfin kowacce alfarma,hakanan ya cancanci kowacce alfarma a gurinta,ya kuma isa da amna ta kowacce fuska.

Rabi tasha ta sanyata shafe jikinta da rabin sannan ta jawo qofar tabar mata dakin bayan ta tabbatar ta sakeyin addu'o'i.

&Tunda asuba bata koma ba,da kanta tayi qoqari da taimakon ma'u suka shirya abinci,saboda ya gaya mata mali zasuje a ranar,zasu dawo kuma a ranar.

Ta langabe masa tana nacin ya bari suje tare yace

"Aah my world.....bakiga yanayin da kike ciki ba?....tafiyan awa goma zuwa da dawowa fa?....ban yarda a wahal da triplets ba". Hakanan suka lalace wajen sallama da juna,kaman idan ya tafi bazai dawo ba.

Duk da farouq cikin shirye shirye yake gadan gadan,don kwanakin biki uku ne kacal suka rage amma dashi akayi tafiyar. Yayi karamci ta hanyar dauko kawu rufa'i akayi tafiyan dashi a matsayinsa na wanda yake tamkar mazaunin mahaifinta.

Zumudi da farinciki da almarar yau zai shiga jirgi ya hana kawu rufa'i sakat,saidai yayi qoqari qwarai wannan karon ya kama kansa ya nuna surukuta sosai,amma a qasan ransa banda albarka ba abinda yake sawa sabreen da nemawa iyayenta rahamar Allah.

"Rufa'i a jirgi,Allah me iko,da haka da haka fa wataran sai umara ko aikin hajji?" Yayi maganar yana duban Jordan. Dariya farouq ya saki,don yana daga kujerar baya ya kuma jishi. Shi haka kawai kawun yake bashi dariya,musamman sanda ake cikin rigimar auren sabreen da fu'ad din.

"Ka fara kiran kanka kawu,hajjin bana da kai za'a yita in sha Allahu,na baka kujerar hajji.....surukinka kuma fu'ad ya baka ta umra". Wani farinciki ya sanya kawu miqewa tsaye zumbur yana kallon farouq.

" Allaha akabar......yaro da gaske kake?,kace na fara lallabikallahumma labbaik tun yanzu.....haihuwa me rana,sabreena kinyimin ranar da ko d'iyoyin cikina basuyimin ba.....ubangiji ya kare gabanku da bayanku,yaro Allah ya yiwa dukiya albarka,amma fa wani hanzari ba gudu ba....." Sai yayi qasa qasa sosai da muryarsa yana sunkuyowa wajen farouq.

"Kana ganin me jadda zai bani kujerar umara kuwa?". Duk yadda fu'ad dake tahowa gurin yaso danne dariyarsa ya kasa,sai daya murmusa.

"Bayan wannan shekarar ma na sake baka guda daya wata shekarar me zuwa kaida uwar gida". Muryar me jadda ta daki kunnensa. Banda ya tabbatar da dattakonsa,banda kuma ya tabbatar baya magana biyu tabbas bazai yarda ba,to amma ya sani cewa shi din kaifi daya ne,idan yace eh eh ne,hakanan idan yace a'ah to a'ah ne. Sai daya dawo daga suman da yayi na wucin gadi sannan yahau zuba godiya yana shirin zube masa.

"Karka tsugunna kawo,kun cancanci komai.....girmanku ne" Fu'ad ya fada,abinda ya sanya mamaki ya sake kashe kawu rufa'i.

"Ko wanne irin halin kirki diyar nan takewa yaron nan har haka yanzu?,ni na dauka wannan yarinya zatayi sati guda ma kuwa?,nayi tsammanin in ta dade sati dayan taci gaba da tsalle tsallenta,sai gashi ta bada mamaki?" Yaketa tadin shi kadai da zuciyarsa.

Sha biyu na rana agogon mali qarfe daya agogon Nigeria suka sauka a Bamako senou international airport. Kawu rufa'i yanata rabo idanu duk da ya kame kansa amma al'ajabin duniya ya isheshi,kasancewar shi din idan yayi nisa lagos yaje sanda mahaifinsu sabreen yana da rai idan ya aikeshi sari.

Sun isa gidan momma bahijja,babban gida dake nuna wadatar da masu shi daidai gwargwado wanda fuad din ya sake inganta rayuwar tasu silar su huda. Wani irin kyauta taban girma,kulawa ta musamman da dauke dukka wani nauyi da dawainiya nasu.

Wani irin saukan ban girma suka samu,fuad din tamkar rab'a yake,duk inda ya sauka saiya jiqa wajen da damshi d alkhairi,don haka kusan kowa murna yake da zuwan nasa. Bai bari iya su huda da momma bahijja kadai suke cin alkhairinsa ba,aah tun daga maqota har dangi na nesa na sabreen alkhairinsa ya kai musu.

Awa daya kacal aka basu huda.....komai na fuad kai tsaye yake yinsa,take ya nema tattaunawa da momma bahijja da mijin momma din tunda auren zumunci ne,shidinma kaman kawu yake a wajensu akan idan zai yiwu su biya sadaki a basu huda su wuce da ita.

"To me ake jira?,me kuma za'a jira?,ga wakilin ango ga na amarya?" Kawu rufa'i ya fada yana saba babbar rigarsa. Tuntuni farincikin duniya ya isheshi ta yadda zai sake zama surukin JADDA,wani abu daya tabbatar baiwa ce Allah yayi musu wadda shi bai taba kawowa ba,yaransa har biyu cikin ahalin jadda?,tabbas arziqi yana masa sallama a bakin qofa.

Abinda ya dinga daure masa kai yadda zama yayi dadi tsakanin fu'ad din da sabreen har ya sake nemewa qaninsa jininsu?.

Ana dab da kiran sallar azahar a alayin akayi sanarwar akwai daurin aure bayan an idar da sallar azahar. Abun mamaki saiga mutane an taru ba laifi,don cikin masallacinma cika akayi,ana idarwa aka daura auren SADDIQ HAMZA KIBIYA da amaryarsa HUDA AHMAD wanda uban ango kuma uban amarya Alhaji Muhammad jadda ya biya sadakinta akan 364,400CfA wanda yake daidai da naira million daya kudin Nigeria. Ya kuma ajiye set na gold masu nauyin babban gram da kudinsa ya tasamma wasu millions din.

A iya haka kawai an tashi zancan,duk da hudan ba wani saninta sosai akayi cikin unguwar ba,amma abun ya zama wani sabon labari.

Kasa cewa komai huda tayi,yayin da momma ta soma qorafin abun yayi kurkusa da yawa,a dage a basu koda sati biyu sai yazo ya dauketa,kafin nan sun shirya itama kuma ta danyi taronta da dangin mamanta da suke nan.

"Kome ake buqata kwana hudu zuwa biyar zaa yishi in sha Allah,tahowa kuma ayi list na adadin wadanda zasu zo Nigeria rakiyar amarya da ganin dakin amarya,zan ajiye jirgin da zaiyi jigilarsu" Fu'ad ya fada.

To abune na maza,su babu ruwansu,shi kansa mijin momma baiyi accepting maganarta ba,hakanan kawu rufa'i da ya fara sintiri yanaso yaga momma ta kafe ya shiga ya gaya masa shi uban huda ya lamunce,sai gashi salin alin ta saki ta basu huda din.

Abu daya ya ragewa huda tashin hankalinta shine,tarkatosu da jadda yayi su duka,kuma sai taji suna zancan da mijin momma cewa yace lallai shi zaa barwa auta.......nadra kuma zata zauna hannun saddiq. Nan ma momma tace batasan zance ba,ita take buqatar riqe yara tana kallonsu kaman 'yar uwarta. Kawu rufa'i fa akazo wuya,fadi yakeyi

"Ni uban huda da nadra da haneefa na bashi su,duk inda zai kaisu ya kaisu indai ba lahira bace,banda abun bahijja ke ba abun alfaharinki bane?,ace wadannan yaran sun tashi qarqashin kulawar me jadda?,akwai wanda ya samu ko zai samu gata duk ahalinmu da naku kuwa irinsu?" Sauqin abun zance ne isu isu,ba wani bare a wajen bare kawun yayi barin mutunci.

"Ni kaina banda na aurar dasu balaraba yace zai riqesu bashi zanyi da gudun fanfalaqi ma kuwa". Wannan karonma sunci galaba a kanta,hakanan tabar musu yaran suka tarkata suka wuce Nigeria dasu.

Suna sauka ya sanya aka kaiwa anni su,ya tabbatar akwai tsarabe tsarabe na mata idan za'a aurar da yarinya,duk da huda surukuwar anni ce,amma shi a duniya uwa ta gari qwaya daya ya sani wato anni,don haka yakaita wajenta ya tabbatar zata hada da amna duka ta sanya ayi abinda ya dace.

Itakam anni mamakin me jadda ya cikata,komai nasa haka yake shirinsa katsam?,haka shi.kuma yake daura aure?,indai waliyyai.sun sani ba ruwanshi da batun mata,indai ma'auratan naso ya gama nashi hukuncin kenan saidai kawai aga result,tana qare tunanin ta saki murmushi,ita kanta gidan da ya cika da 'yammata sai taji ya qara mata dadi,amma suna kwashe matansu zasu barta a kewa sai ita kadai?,saita samu kanta da tunanin anya kuwa zata yarda ta bada su nadra?.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



138


Zuwa takwas da rabi na dare ya shigo gida. Tun kafin ya shiga din ya sallami kowa,don ragowar lokacinsa yana jin cewa na duniyarsa ne.

Yau din sai take jinta a cikakkiyar matar aure kaman kowacce d'iya mace. Ta shirya sosai tayi kwalliya da wani farin tattausan lace,fari ne qal babu sirkin komai a jikinsa. Ya kwanta mata sosai a fatarta,ba makeup a fuskarta,daga powder data dace da skin dinta,sai wheat lips da ya sanya pink lips dinta suke wani glowing me daukar hankali.

Sau daya tak ya kalleta yaji tana son raba masa hankali,sai yake ganin kamar canzata akayi daga fitarsa zuwa dawowarsa,kaman yadda yaji qamshin gidan gaba daya ya sauya.

Qugunta ya kamo,ya kasa cewa komai sai daya sada lips dinsa da nata,ya tsotse lips gloss din da kyau kaman bata taba shafa komai akai ba da wani zazzafan French kiss.

Bakinsa ya zare yana sauke numfashi,idanunshi akan fuskarta,yana jin yadda fatarta dama kayam jikinta suke fidda wani daddadan qamshin turaren kabbasa. Idan baiyi kuskure ba har gashinta data harshi baje saman kafadarta qamshin yake fiddawa.

"Those sweet lips sabrrrr....." Ya fada yana zagaye yatsansa akan shape na lips din nata,yana jin wani shauqi yana fusgarsa. Murmushi ta saki tana dan kauda kanta tanason ta karbi wayoyin hannunsa da wata 'yar kyakkyawar briefcase dinsa. Hannunsa ya sanya ya juyo da fuskarta da sauri.

"Nooo......my lips missed yours sabrrrr......" Ya fadi yana sake hade bakinsu guri daya.

Wani yanayi ya fara saukar musu shi da ita,har qafafunta suka fara rawa ta fara jin ba zasu iya ci gaba da daukarta. Shi dinma hakanne,don gaba daya jikinsa ya dauki shock har sai da suka zube saman sofa sannan ya zare bakin nasa.

"Your lips are the ones.....i want to kiss forever" Ya qarasa fada yana tura hancinsa wuyanta qamshinta yana bugar dashi.

"Sabrrrr.....so kike ki haukatani da alama ko?" Ya furta yana Dubanta da juyayyun qwayar idanunsa kaman wanda yasha wani abu. Fiddo idanu waje tayi tana dubansa,hakan sai ya qara mata bala'in kyau saboda yadda sukayi wani haske,eye lashes din kuma suka zame musu tamkar wani ado.

"Muffin.....me kuma nayi?.....idan na kasheka kuma na zauna da wa?" Tayi maganar ne cikin wata irin shagwaba. Hancinta yaja kafin ya lakuce mata kumatu.

"Fisabillahi zan fadi gaskiyata.....wannan qamshin lallai idan kina tare dashi zanfi tape da taya maqale miki......komai kuma zai iya faruwa ako ina sabrrrrr.......daga ina wannan qamshin?" Ya fada yana kashe mata ido. Murmushi ne ya subuce mata sosai,harga Allah da farko ta dauki turaren ne kawai saboda amna tace ta dauka,cikin irin turarukan da akayi musu ita da huda wanda.ta bakinsa tasan huda sun iso,saidai tana sakawa a burners dake lungu da saqo na gidan ta gama giving up.

Lumshe idonta tayi wani farinciki yana saukar mata,ta bude idanun nata ta saukesu akan kwalbar LAB_LAB da tayi amfani dashi,wanda daga saman kwalbar manyan rubutu ne b'aro b'aro dake dauke da sunan INCENSE BY


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login