Showing 345001 words to 348000 words out of 363280 words

Chapter 116 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1431

Gaba daya ya canza,quruciyarsa kuma sai dawowa takeyi saboda wadatar daya soma tsumbula ciki.

"Kawu waye ya kawowa madeena?,kamar bakafi wata shida da komawa bafa" Huda da dama can tasu bata jiquwa ta furta.

Harara ya dalla mata yana neman wajen zama gami da kalmashe carbinsa.

"Ni yanzu har ayimin maganar hawa gajimare da sauka......mutumin da yake da suruki irin me jadda gidan gold da diamond?,to bari kiji yarinya,a yanzu haka aminaina guda biyu dukkaninsu hajjin bana dasu Zamuyi gaba daya,albarkacin me jadda.....albarkacin d'iyar da aka haifa tsiya tana bacci kariris". Neman wajen zama huda tayi saboda kada dariya ta kayar da ita,kawun ya gama bata amsa daidai da ita,saiyayi banza da hudan yana maida hankalinsa kan sabreen.

"Sannu d'iyata.....sannu 'yar nan.....ashe ni ahmadu da fateema suka haifawa ke ban sani ba?" Ya qarasa fada yana matse hawayensa da wasu sabbin qwalla da suka fara taruwa lokaci guda.

"Dama na dade inaji a jikina zanyi kudi.....na dade inaji a jikina zanyi arziqi ashe ta sanadinki ne,ubangijin al'arshi yayi miki albarka,dukka gidanku yanzu ya koma qarqashin kulawarki,masoyanki da maqiyanki,harda 'yan uwanki na dakin aure,Allah ya qara miki riqonda zumunci da kuma zuciyar yafiya da afuwa"

"Ameen ameen kawu" Sabreen ta fada tana murmushi. Gaba daya kawun nata ya canza kaman bashi ba,wata kamala duka ta saukar masa,ga alamun jin dadi da hutu duka tattare dashi.

"Amma 'yar nan ya akayi haka?" Ya fada yana gyara muryarsa. Kai ta daga tana dubansa

"Me akayi kawu?".

" Kinyi qoqari dai.....amma ci gaba ya kamata a samu ai,'yan hudu ya kamata kiyi wannan karon,amma sai aka koma baya kikayi biyu,maimakon ki maimaita ukun?,kinsan innarmu sai da tayi 'yan uku da 'yan biyu kusan kashi biyar,duka rasuwa sukeyi,ni kadai da dan uwana ahmadu ne muka zauna,don ko babanki ai tagwaye ne,ni kuwa mu uku ta haifa,amma ni duka na fisu qwarin qashi ni kadai na zauna".

"Kaine dai Allah baiyi niyyar kashewa ba kawu ba wayonka bane" Huda data goya baby naseem da baby carrier ta fada duka cikin salon tsokana.

Daquwa ya watsa mata yana dubanta.

"Kinci ubanki.....banda kinci darajar mijinki da ya bani kyautar gida harda mota satin nan daya wuce yau da sai na karbi goyon na aza a bayana naci qaniyarki sannan na baki danki ki cigaba da tafita"Daga huda din har sabreen sai a sannan sukasan saddiq ma yayi kyautar,ba zatar data kashe rigimar kawu da huda ya koma maganar da sabreen.

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_HUGUMA CLOSET ON TIKTOK_*
https://www.tiktok.com/@huguma.closet?_t=ZM-8y1pf9yfIVZ&_r=1



171


"Allah ya sambada miki albarka,don Allah.........don Allah ki daure wata shekarar warhaka ki sake tunkudo wasu hudun" Ido ta zaro da mamaki

"Da gaske fa kawu kake?".

" To me zaki tsaya jira?,banda rainon cikin bakisan wahalar komai ba?,shi kuma iri kawai yakeso,ai faduwa tazo daidai da zama" Ya fada yana leqa fuskokin yaran.

"Tubarkallah wallahi.....haihuwar masu kudi daban data talakawa,su kansu yaran daban naku suke da namu".

" Wallahi idan banbar dakin nan ba sai kawu ya sanya cikina ciwo.....adda bari naje nima nayi sallah a masallaci" Huda ta fadi tana fita ta barsu.

Wannan karon halastacciyar walima jadda ya fara hadawa a birnin madeena. Walimar maza daban mata daban. Jirginsa daya siya bayan wanda yayi kyautarsa na JADDA WINGS 002 kawai ya bayar akayi jigilar 'yan uwa da suke cikin list na zuwa umra a wannan watan aka gabatar da walimar tare dasu,ciki harda maamah,wadda akan idanunta aka gudanar da komai.

Duk wani motsi na yaran nan guda biyar akan idanunta yake,ta saka damuwa sosai a kansu tana ganin kamar zasu bace ko zaa daukesu,saidai tana komawa daidai duk sanda ta tuna amincin da garin yake dashi.

Wannan karon Sabreen itama ta samu mahaifinta,wato AHAMD(Amaan),dan uwanshi kuma yaci sunan muhammad da kanshi wato takwaran babansa (AMEEN).

Tuburewan tsokana Sabreen tayi.

"Hamma wannan son kai ne.....ni me yasa ba'a fara jira an saka me sunana ba?" Ta fada tana turo baki gaba. Dariya ya saki yana murza yatsunta sanda take zaune tana shayar da muhammad ameen din.

"Ki haifomin baby girl ki gani DUNIYATA.....ke kika mana addu'an boys,gashinan ta shafi kowa cikin familyn jadda,duka maza suke haifa mana,muna da kwadayin mace dukkaninmu amma bansan kusancinki da Allah ba da addu'arki ta riga tawa tafiya ba.....at first nafison na samu daughters so samu.....don na basu tarbiyya na aurar dasu,na kuma rabauta da rabon aljannar da manzon Allah ya yiwa duk wanda yayi irin wannan aikin alqawarin samu". Dauke kai tayi tana sake tsuke bakinta cikin shagwabar nan da bata jin ta girma da yinta,kamar yadda shima baya ganin ta girma dayi masa ita.

"Amma dai it's not fair hamma......sai a jirani sai sanda aka samu baby girl din aka saka ameenatu".

"Ameenatu ta zama wajib akan dukka diya mace ta farko data fito daga tsatson jadda......take it easy maa.....ki qara himma next year by now ki ajiyemin girls" Idanu ta zaro ta bishi dasu,sai ya jinjina mata kai cikin bada tabbaci.

"In sha Allah" Ya fada da yaqinin daya sanyata bata sake cewa komai ba.

Sabreen bata yarda ta koma ba saida jini ya dauke mata,ta sauke umra. Addu'a tayi me tarin yawa akan rayuwarta data zuri'arta,addu'a ce me yawan gaske akan zaman lafiyarta dana familynta gaba daya,qannenta 'yan uwanta dama duk wanda yake da jibi dasu. Ta dade gaban dakin Allah tana neman me kyau a duniya me kyau a lahira(Rabbana Aatina fiddunya hasanatan wafil Aakhirati hasanatan wa qina azabannar/addu'a ce wannan me matuqar muhimmanci,ku dage kada kuyi wasa da ita). Ta roqi Allah dawwamammiyar soyayya a zuciyar mijinta,da kariyar Allah daga jinsa ganinsa da zuciyarsa dama al'aurarsa akan kowacce diya mace idan ba ita ba.

Cikin wani irin aminci sakewa da walwala take kula da yaranta dukka guda biyar din. Tana da wadatattun masuyi mata hidima,yayin da ita kuma ta tattara damuwarta dama kulawarta dukka akan mijinta.

Sai data warware sosai sannan yazo mata da komai da komai na kammaluwar ginin gidan marayu maka maka har guda uku a arewacin Nigeria,da kuma gina sabuwar foundation ta kula da marayu da zawarawa da yara marasa galihu.

Kukan farinciki sosai ta dinga yi,saboda cikar ragowar burinta kenan a rayuwa. Wani irin katafaren gida ne da aka tsarasu bisa tsarin ginin unguwa guda wato estate. Da makarantunsu tun daga primary har zuwa secondry,jami'a kuwa a qasar waje yayi planning ya dinga turasu qasashen musulunci,don yana sanya ran a can zasuyi karatu me kyau,ba tsangwamar mutane ba takurawarsu.

Komai an wadata gidajen dasu,abinci sutura wutar lantarki da kayan more rayuwa cikin kowanne gida da dakuna. Cikakken tsaro da tsari na addinin musulunci wanda aka ginashi bisa jagorancin malam da a yanzun shine babban me bawa jadda shawara akan duk wani abu daya shafi zakka da harkokin addini cikin rayuwarsa.

"Wannan gidan da komai dake cikinsa kuma mallakin su ayshatu ne......na kusa dashi kuma na JIB ne,sai kuma guda dayan na busari" Ido ta waro tana mamaki,ya akayi yasan su jib?.

"Maida idon ranki ya dade don ban gaji da kallonsu ba daga nan har qarshen rayuwata......karki ce komai,tun daga randa na sameki cikakkiyar mace na bibiyesu na kuma jawosu cikin rayuwata,yanzu haka busari shine shugaban drivers na kamfanina,Jib kuma yana jagorantar sashen tsaro na daya kamfanina dake lagos" A ranar idan farinciki yana kisa tabbas ta tabbatar sai buzunta. A yadda abubuwan sukazo tana buqatar ma'aikata ita kanta,tana buqatar su zauna su qarasa tsara komai kafin ranar da zaa qaddamar da qungiyar da kuma qaddamar da gidajen marayun dake kano kaduna da abuja.

Sosai ta tsananta bincike cikin danginta na uba harna uwarma,ta kuma zabi amintattu da zasu dinga gudanar da komai,nata aikin kawai tana daga cikin gida xatayishi cikin system sai waya idan ta kama,sai kuma ziyara da duba gidajen lokaci bayan lokaci da zata dinga zuwa,da kuma wani taron idan ya kama,kamar ganawa da ma'aikatanta da sauransu.

Abinda ya bata mamaki shine,albashin da fuad ya sanya mata na million din kudade. Abun ya qarasa kasheta da mamaki,itace shugaba,yayi dukka aikin ya mallaka mata,ya bata dama ta sakawa kowa albashinsa kuma zata dinga biyansa......sannan ita kanta kuma ya yanka mata albashin miliyoyin kudaden da batasan ma me zatayi dasu ba.

Kuka kam wannan karon barinta yayi tayi abinta,ta shimfida fuskarta saman kyakkyawan qirjinsa tayi kukanta yadda takeso ta kuma zarce da godiya ta baki da kuma godiya ta aikace. A ranar ta saje yarda da kanta,ta haukatashi da wani irin salo......ta sake godewa Bgawo's kitchen and aphrodisiac. Mama macace dattijuwar qwarai data iya gyara a gargajiyance,saboda cikar hankali da shekarunta da takai matakin dattijantaka,bata taba ganin gyara irin nata ba,gyara na dattawan tsofaffi da babu side effects akai sai tsimuwa da jikinki zaiyi da kyau,wanda sun shigo duniyar gyara ne saboda bada gudunmawa ga matasan mata dake tasowa cikin rayuwar aure a yanzu.08127084190/08104553105.

Yana jinta da kima a rayuwarsa fiye da duk wani abu me kima daya mallaka......yana jinta a matsayin abu mafi tsada da daraja a rayuwarsa,don haka komai nata ya zama na daban kuma na musamman.

Wani tsaro yake bata,guards ya samar mata na musamman,wadanda suke tare da ita a duk sanda zata fita ko zata tafi zuwa wani gurin. Ya samar mata 'yan sanda mata biyu jajirtattu da zasu kasance da ita a motor din da take ciki,bayan 'yan aikinta dake kula da lamarin yaranta,sauran motocin kuma duka guards dinta ne. Cikin lokaci qalilan Sabreen din ta zama wata me tsada,komai nata kuma ya kuma sake zama na musamman,ya canza mata mota tata ta hawa da duka sabbin motocin da masu tsaronta zasu dinga using.


*_BAYAN WASU SHEKARU_*

*JADDA'S VILLA*


JADDA'S VILLA shine sunan dake rubuce b'aro b'aro daga tsororuwa babban ginin gidan. Rubutun an yishi ne da ruwan GOLD jikin wani qawataccen allon qarfe da aka yiwa wani irin design me azabar kyau da daukan hankali.

Wani irin shimfideden gida ne,wanda a qalla ya qunshi maka makan mansions a cikinsa guda shida. Kusan komai na gidajen iri daya ne,saidai banbancin girma da wani gidan yafi wani yawan dakuna da kuma qawatuwa da kayan alatu na rayuwa,daidai da yadda mamallakan gidan suke da buqata.

Idan ka kira JADDA VILLA da aljannar duniya sam sam bakayi laifi ba,don inda akwai sunan da yafi haka nuna tsananin tsari da cikar suffa da haibar gida ya cancanci ka bashi.

Gidane daya mamaye jadda street gaba daya daga hannun dama,sai hannun hagun dake dauke da qawatattun gidajen hamshaqai masu fada aji cikin unguwar da sai ka isa wane zaka mallaki gida a cikinta cikin birnin tarayyar abuja.

Ba gidan kawai ba,unguwar kanta sai kabi matakai daya bayan daya kafin ka samu nasarar shigarta,bayan kuma ka shiga din zai zame maka barazana hanyar shiga JADDA VILLA. Birnin da ya shiga bakunan manyan masu kudin da suke ganin wuyansu yayi kauri a duniyar naira.....birnin daya girgiza zukatan al'umma da dama ciki harda manya manyan masu kudi na qasata dama qasashen duniya gaba daya.

Manyan gate gate guda biyu da matsakaici guda daya dukka saika wucesu kafin kakai ga shiga BIRNIN JADDA kaman yadda aka rubuta daga cikin gidan gate din farko.

Daga can cikin daya daga cikin gidajen dake cikin jaddas villa din,cikin tsakiyar wani qawataccen courtyard da aka shimfida hikima wajen gini da tsarinsa. Qawatattun shuke shuke ne masu dauke da mabanbantan furanni masu launikan dake kiran butterflies zuwa garesu,daga qarqashin shukokin wata 'yar qwarya qwaryar qorama ce ta zamani da aka qirqireta saboda wucewar wani ruwa me tsananin hasken da kake iya hangen wasu irin mulmulallun stones masu daraja da tsada dake zuwa a oval shape,amma suna da nau'in kaloli daban daban,kaman yadda madaidaita da qananun kifayen dake yawo a ciki suke da wadannan launikan.

Wasu irin Kujeru ne sirara masu taushi aka qawata courtyard din dashi,wadanda suke farare qal,kaman ba'a tsoron kai kawon yaran da gidajen suka mallaka,yaran da suka tasamma rai ashirin da shida.

Zafin rana ko sanyi duka basa rabar wajen,guri ne na musamman da kowanne gida daka cikin gidajen jadda villa aka tanadar dashi bisa tsari na musamman dake iya daidait weather na wajen. Idan zafi ne weather wajen na fidda iska me kyau da dadi,idan sanyi ne weather din wajen na bada temperature da zata dace da yanayin da mutum yakeso.

Saman daya daga cikin kujerun dattijuwa anni ce,sanye da wata sassauqar riga mara nauyi ruwan madara,wadda take hade da hijabinta asalin saqar qasar Indonesia.

Daga gabanta kuwa yara ne matasa maza da mata kusan guda biyar,masu kamanceceniya da juna,wasu kamanninsu sun fita sosai......wasu kuma kamanni ne na baya baya. Daga gefan daman annin wasu yara ne guda biyu da duka duka shekarunsu ba zasu haura takwas da tara ba,dukkansu share hawaye sukeyi fararen fuskokinsu sunyi jajur.

"Kowa ya gama bayaninsa?"ta fada tana duban fuskokin su daya bayan daya. Da fari gurin shiru ya dauka kafin daga bi sani,ta sake bin fuskokinsu da kallo tana sake maimaita tambayarta. Kai suka gyada daya bayan daya.

"Da kyau" Ta fada cikin cikakkiyar nutsuwarta dinnan tana ajiye littafin hallul masa'eel dake hannunta a gefe.

"Ameen" Ta kira sunansa kai tsaye. Yaro da yaci sunan muhammadun ta hanyar fadin gaskiya akan komai da aka tambayeshi,koda hakan zai ja masa duka......yaron da kusan halayensu suke kamanni iri daya dana MUHAMMAD SAUBAN(Ku ajiye wannan sunan a next novel nawa idan rai yakai mana=??=??). Sauban din da shike binsu muhammad ameen da ahmad amaan.......amma halayensa sak irin na mahaifinsa......halayensa sak irin na ameen......shekarunsa duka duka basu wuce goma sha biyu ba......amma wani irin girma da dattako gareshi.

"Me ya faru ameen?" Anni ya qarasa tambayarta. Bayani yayi mata na iya abinda ya sani,ya qara da cewa.

"Amma a gaban sauban akayi.....ki tambayeshi". A nutse ta waiwaya ga sauban din,wanda yake zaune shi daya saman kujerar da babu kowa kusa dashi. Ita kanta kujerar tayi dan nesa kadan dasu,kunnuwansa manne da headphones wanda ko daga nan kana iya jin sautin qira'ar qur'ani na fitaccen shaik dinnan wato maheer almu'aiqaly.

Duk wanda yasan sauban ya sanshi da yawan sauraren karatun shaik maheer duk sanda yake kebe shi kadai,wannan ne anni take kyautata zaton sanyashi ya zama na daban cikin 'yan uwansa......hasken alqur'ani kuma take tunanin ya qara sanyashi me tsananin nutsuwa,duk da tarin zuciya da yaron yake dashi.

"Sauban" Ta kirashi tana yafitoshi da hannu. Kallo daya ya yiwa annin ya saka hannunsa ya cire headphones dinsa sannan ya taso ya qaraso wajen




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
__________________________

*_NACE BA......._*>??????
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*=??=??

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*=?G? wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



172


"Me ya hada arham da ahsan?". A nutse ya zube kyawawan idanunsa masu girma kaman na mamanshi akan dukkaninsu,sai ya matsa a hankali ya zauna gefen anni.

Baiji tsoron idanun kowa ba ya zauna ya yiwa anni bayani filla filla har yakai qarshe.

" Haka akayi?" Ta sake tambaya,dukka wajen ba wanda ya musa banda hilal da yayi shuru. Maida dubanta tayi ga hilal.

"Allah yana cewa cikin qur'aninsa,yaku wadanda kuka bada imani da Allah.....idan fasiqi(mutum)yazo muku da labari,to kuyi bincike,gudun kada ku afkawa wasu mutane bisa jahilci(rashin sani dalilin rashin bincikenku).saiku wayi gari kuna masu nadama.......a duk sanda wani mutum yazo maka da labarin anyimin kaza,ko wane yayi maka kaza,ko kaza ya faru,dole ne akan musulmi ya nemi hujja ko dalili na abunnan ya faru,dole ne......muna da wata dabi'a ta saurin yanke hukunci,da daukan zance


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login