Showing 183001 words to 186000 words out of 363280 words

Chapter 62 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1444

Maamah dince mutum ta farko data fara ganinta,kallo daya tak da sabreen tayi mata ta fahimci abinda ke kawo a ranta. Batason irin wannan kallon haka......saidai ta bawa kanta tabbacin indai wannan dabi'ar na tare da matar zai wahala su rabu lafiya. Ba komai zata iya dauka daga gareta ba,abinda ta dauka a baya ma ya wadatar.....yanzun tana jinta 'ya me cikakken 'yanci ne da bata qarqashin juyawar kowa.

Cikin jikinsa yaji alamun wanzuwarta a wajen,ya daga kansa a natse yana duban sassan da take tahowa. Fuskarta tayi masa kyau kaman ba dazu ya ganta ba,tafiyarta me cakude da nutsuwar nan tana tsananin burgeshi,tun a wani lokaci can baya ba tare da yasan da hakan ba.

Kasa dauke idanunsa yayi daga kanta,yana fatan ta dubeshi da fararen qwayar idanun nan nasa. Ta gefe yaji an taboshi,sarai yasan farouq ne don babu me masa haka saishi

"Ina fata ba idanunka ne a kanta ba?" Ya soma tambayar farouq din ba tare daya dauke idonsa a kanta ba ko g waiwayo ya dubeshi ba. Can qasan zuciyarsa dariya ta taso masa ya danne,shi bama ta dalilin tabashin yake ba,abinda ya dameshi kawai kada ya kalle masa mata?. Ya manta saman table din akwai mamansa?,sam kaman baisan da wanzuwarta ba?,ita yake qoqarin ankarar dashi,don tun fitowar sabreen din maamah din ta fahimci mayataccen kallon da fuad din yake binta dashi,abinda ya sake tunzurata,ta dinga kokawa da zuciyarta da kuma fuskarta akan ta shanye amma ta gagara yin hakan.

"Ni bazan kalli haram ba.....don soon halal dina na tafe......amma dai ka gyara idanunka akwai iyaye a wajen" Shaf har kuma ga Allah ya mance da maamah din a wajen,furucin farouq din ya ankarar dashi,sai kawai ya zare idonsa akan sabreen din yana dojewa kallon maamah,don shine hanya daya da zai kaucewa tuhumarta ko bacin nasa ran.

"Ta yaya zamu rayu a wajen nan?" Ya tambayi kansa da kansa yana jin idanun maamah a kansa saidai yaqi yarda ya kalleta ko sau daya,sai ya jawo tab din gabansa yana ci gaba da duba taswirar da suke magana akai kafin fitowarta shi da farouq.

"Matsa kusa da mijinki kiyi serving nashi". Furucin anni kenan daya sauka a kunnensa bayan fitowarta daga daki tayi joining nasu a dining table din.

Sosai maganar ta anni tayi masa dadi,ya murmusa can qasan ransa yana addu'ar a daren yau ta bashi matarsa. Yana jin yakai taki maqura tako ina,muddin kuma akaci gaba da tafiya a haka baisan me zai faru ba.

Satar kallonsa tayi kaman yadda maamah ta saci nasu kallon. Har ta buda baki zatayi magana sai wata zuciyar ta tunasar da ita,wawa shike saurin fasa abinda ke cikinsa,sai taci gaba da juya abincin tana noticing kowa.

Ganin baiko kalli sassan da take ba bayan annin tayi magana sai ya bata qwarin gwiwar miqewa,ta matsar da kujerar dake kusa dashi a hankali ta yiwa kanta wajen tsaiwa.

Cikin takatsantsan take zuba masa komai,don ya tattara komai ya ajiye ne ya zuba mata idanu yana bata order zuba kaza,rage kaza,kaza kadan zaki zuba. Wannan yaso daburtata,don sau biyu yana kai hannu yana riqe serving spoon din da take zuba abincin dashi da zummar kada ta zuba masa mayonnaise da man farfesun naman kan ragon daya dan taso a sama. Ita daya sai kuma maamah suka fahimci yana sane yake hakan,don duk riqewar sai ya hada da hannunta cikin nasa.

Da qyar ta samu ta kammala zuba masa din,sannan ta aje komai a gabansa. Dubawa take tana neman plate din da zata zuba nata abincin,duk da tasan zai wahala ta iya cin abin arziqi,don ya sanyata a gaba da idanunsa da suke sake zama marasa kunya marasa jin nauyin jama'a. Tun asali ta tsani yawan kallo,to amma shi din ta fahimci ya qware sosai wajen wannan dabi'ar,abinda yafi bata mamaki shine......kana iya wuceshi baisan waye kai ba.....kana iya gama sabgoginka a kusa dashi baima tantance me kakeyi ba......amma ita me yasa yake sha'awar sanya mata idanunsa?.

"Zauna muyi squatting.......wannan abincin ina zan kaishi?" Ta tsinci muryarsa katsam yana fadi gami da gyara mata kujerar dake kusa dashi.

Yadda wuta ta dauke mata haka wuta ta daukewa maamah,kaman kuma hadin baki wajen duka sai ya dauki shuru,sake tura kujerar yayi kusa da ita,bata da wani option sai janyota da tayi ta koma a sanyaye ta zauna a kai. Tayi zaton shikenan,zai tsaya iya haka ne,a'ah......sai daya sake janyo tashi kujerar ta zama kusa da ita sosai har gwiwoyinsu suna gogar na juna.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



*_Kina da buqatar fara kasuwanci amma baki da jari?_*

*_ko kina da jama'a amma baki da jarin fara kasuwanci?_*

*_kin cika wayarki da contact na qawaye da abokai amma bakya qaruwa dasu?_*

*_MAZA ZO KIYI JOINING HUGUMA CLOSET_*



*_Amintaccen guri kuma muhalli na siyayyar ingantattun suturu na alfarma,siyayya cikin aminci,farashi na musamman da babu irinsa_*

*lace*

*kowanne nau'in shaddodi*

*yadika na maza da mata*

*mayafai*

*lafaya*

*takalma da jakankuna na kece raini,masu babban farashi da qanana*

*sarqoqi da agoguna*

*under wears*

*abayoyi na manya da yara da jallabiyoyi domin maza*

*_SIYAN DAYA NE NA AMFANIN GIDA KO KUMA REPOSTING ZAKI DINGA YI KINA DORA RIBARKI?_*

*_me kikeyi tuntuni bakiyi joining group dinnan ba?_*

*Sassauqan farashi me ban mamaki*

*_Qawata adonku da samar muku da latest kaya shine muradinmu_*
_______________________________


95



Ya jima yana tsara yadda bata abinci zai zamo qarqashin kulawarsa. Yana ankare da yadda take walagigi da cin abinci,wani abu sam da bai dameta ba,a iya zamanta a gidansa ya lura da haka,kusan duk sati sai ya leqa store din gidan don ya duba koda akwai wani abu daya qare ba kuma zata iya magana ba a qaro mata,duk sanda ta shiga yana samun kitchen din danqare da kayan masarufi alamun dai ba wani amfani akeyi dasu ba.

Tsahon wahala da rayuwar da yayi zamanin quruciya me cike da rashin gata da wahala yasa yasan illar da yunwa ke dashi,wannan ya sanya sam baya wasa da lamarin ciyarwa,koda kuwa ga mutanen da ba'a qarqashinsa suke ba.

Sau da dama idan ya kalleta yakan ji a ransa zatafi haka murjewa da cika muddin ta maida kai ga abinci,bayason ta zama raguwa ko ta kasa jurewa lalurarsa,shi yasa yake ganin shi yafi cancanta da kanshi ya tsaya a kanta ta wannan bangaren.

A hankali taji saukar sassanyan tafin qafarsa saman qafarta. Wani abu taji ya tsarga mata har cikin kwanyarta. Ta daga idanunta a hankali ta zubesu cikin nasa,kusancin dake tsakaninsu yayi tsananin kusa da har ya sanya ta hangi wani abu cikin qwayar idanunsa.

"Be serious mana....kisa hannu kici abinci ko na baki da kaina" Ya fada da sound din da babu meji sai ita. Idanun ta kawar don ya gama kashe mata jiki,ta dubi zara zaran yatunsa daya sanya cikin abincin masu farare qal din nails da lunula a qasan farcen daya qarama faratansa kyau.

Batayi ko lomar farko ba amna ta fito cikin skirt itama da riga English wears,sakakku kaman na Sabreen din,hannunta dauke da wayar sabreen da sam ta manta ma da babinta.

"Adda.....na saka miki ita tayi full charge.....nikam ko iya yau ne a bani aronta" Ta fada tana murmushi gami da miqa hannu ta aje mata ita saman table din a gabanta.

Bata gama aje numfashin data shaqa ba idanunta suka sauka akan wayar,

"super nova....diamond edition" Sunan wayar kai tsaye yazo kanta daga kallon farko da tayi mata tana sake kallonta da kyau don tabbatarwa da kanta batayi dimuwa ko kuskure ba.

"Tashin hankali......kambun bala'i" Ta samu kanta tana fadi can qasan ranta a tsananin gigice. Wayar million sabain da kusan bakwai a hannun karuwar 'yar barikin?,ita kuwa tana me?,yarinyar data dauko ta zame mata tsani na samun ire iren wadannan damarmaki sai a wayi gari tana budewa kanta da kanta nata damarmarkin?,wanne irin bacci tayi haka ita mariya?,wanne irin asararren bacci tayi?,yarinyar da a iya duniyanci da qwarewa duka baifi ta lomaceta ba?,me yasa take neman zame mata qadangaren bakin tulu?.

Ba zato ba tsammani naman data zuba a bakinta romonsa ya subuce mata ya wuce mata mashaqar iska,take tari ya sarqeta me matuqar qarfi ta shiga yinsa ba qaqqautawa.

Musaddiq da yafi kusa da ita shi ya bata ruwan data samu tasha tarin ya lafa,sannu kawai suke mata,sai taji gaba daya iskar wajen ta mata kadan ba zata iya zaman wajen ba,don haka tsam ta miqe tana sauka a wajen hannunta saman qirjinta anni na mata sannu cikin kulawa.

"Ku debi abincin ku bita dashi" Anni ta fada. A gareta sai taji kaman chance anni ta bata na matsawa daga wajen,don haka ta motsa da nufin miqewa amma ya maidata ya zaunar da hanyar danne mata qafa. Idanunta ta daga ta kalleshi,sai ya dage mata dukka girarsa biyun yana tsare gida.

Dole taja bakinta tayi shuru gudun tashin tashina gaban anni

"Amna diba kikai mata" Fuad din ya bawa amna umarni kai tsaye,tana kallo amna ta shirya abincin musaddiq ya dauka mata wasu suka gangara zuwa dakin annin.

Koda ta shiga dakinma still numfashinta tana jin kaman baya isarta,sai ta kunna a.c ta dauki remote din ac din tana qure number qarshe,kafin ta qarasa gaban gado tana wurgi da dan kwalinta. Me yasa duk wani kafi da ta sanya aka mata baya aiki a kanta?. Ta tambayi kanta da kanta. Duk mutumin da zata daukeshi aiki cikin tafiyarta.....duk mutumin da zai ratso da kansa tsakiyar harqallarta sai ta tabbatar ta mallaki bakinsa da tunaninsa.....to amma ita me yasa ta kasa samuwa cikin tafin hannunta?.

"KINYI KUSKUREN ZABOTA......AKWAI NADAMA ME YAWA......TAURARINTA BASA TABUWA" Duka maganganun bokan suka dawo mata kamar sannan yake furta mata su.

Juyawa tayi tana neman zama daidai nan musaddiq dake gaba ya shigo amna na biye dashi.

"Anni ce tace a kawo miki daki,idan kin huta sai kici" Cewar musaddiq.

"Saboda ga mayunwaciya?.....shi zaki a jejinsa har sai an masa tayin abinci?,aisaidai abinda ya farauto yaci ya bawa sauran namun daji su qarasa abinda ya rage din" Ta fada tana makawa amna harara. Amna din bata ko daga kai ta kalleta ba,tadai qarasa ta ajiye tray din kusa da inda musaddiq ya ajiye nasa ta juya tana ficewa,sai shima ya soma bin bayanta ba tare da kowa yace komai ba.

"Kai musaddiqu zo nan" Ta kirashi a fusace ganin yabi sahun amna. Qofar ya saka zai dawo ciki ta watsa masa harara

"Rufen qofata shashasha mara kishin uwarsa,kaima ka soma hawa turbar dan uwanka ko?,an zagi uwarku shine zungui zungui zakabi bayanta?" Ta fada a matuqar hasale,a yau tana jin shi kansa musaddiq din ya zama silar faruwar wasu abubuwan. Yau inda ace ya bata goyon baya da nasarorin da zata samu zuwa yanzu sun haura haka.

Baice komai ba ya rufe qofar ya dawo ya zauna yana dubanta.

"Uban waye ya siyawa waccar karyar 'yan barikin waya me tsada har haka?" Ta fara jifansa da tambayar da tafi damunta. Fuska yadan yamutsa kadan yana maimaita sunan,hankalinsa ma gaza cafko ainihin wa take nufi.

"Kai maida hankalinka.....sabreena nake nufi" Cak tunaninsa ya dakata na wucin gadi cike da mamaki. Dama addan take kira da wannan mummunan sunan?.

"Hamma ne....amma ai ta cancanci abinda yafi waya ma maamah,tunda ita din matarsa ce,kuma yana da halin siya mata,uwa uba ma kuma tana da hankali da nutsuwa,ta cancanci fin haka ma"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....kasan me kake cewa musaddiq?" Maamah ta fada cikin tsananin tashin hankali,idan har abinda kunnuwanta suke jiye mata lallai shima ya shiga tarkonta......sai taji gaba daya hankalinta yana qoqarin kubce mata. Amma da yake bariki iyawa ce,sai tayi qoqarin maida hankalinta gangar jikinta sannan ta zauna a gefansa.

"Amma meye amfaninka a gurinsa musaddiq?,dan uwanka yana irin wannan almubazzaranci da dukiya amma kana ganinsa?,ba zaka saitashi ba?,ba zaka hanashi ba?,ba zaka sanarmin ba don in daidaita al'amuransa ba?,wayar million saba'in wa matarsa uwarsa bata da ta ko million talatin?". Shuru kawai yayi maganganun maamah suna masa banbarakwai. Kai tsaye zai iya cewa ta jahilci rayuwarsu da gasken gaske,kuma kome zai gaya mata ba fahimtarsu zatayi ba,don haka ya zuba mata idanu kawai yana dubanta har takai qarshen maganarta. Da kanta ta sallameshi ta koma tana zama cikin matuqar firgici da bacin rai,zuwa yanzu tana kyautata zaton BOKAnta tabbas ya gaza.....yaqin nan da bakinta zata yishi,da dukka wata power irin ta uwa da Allah ya bata.

Wuni guda gaba daya bata bawa kwanyarta wani sukuni ba ko kadan,gaba daya tunaninta ta tattarashi akan yadda zata yanke wanzuwar sabreen cikin rayuwar d'anta. Zuwa sannan jikinta yana bata ci gaba da wanzuwar sabreen din bazai haifar mata da d'a me ido ba. A dukka shawarwarinta zuciyarta tafi rinjayarta ta bangare guda......ta raba auren ko da tsiya koda tsiya tsiya......da qarfi da yaji koda kowa hakan bai masa ba.....zata gwada qarfin qwanjinta da kuma adadin girma izza da nata ikon na uwa.

Wannan saqar data gama yi ita ta sanya ta fita cin abincin daren ranar da wani irin izza da cikakkiyar qwarin gwiwar samun mafita.

Ta samesu duka saman dining din,ta bisu da kallo daya bayan daya tana jin ciwon yadda annin ta samu daman hade kansu duka,yaran da suke nata da wadanda suke ba nata ba. Ta saki qaramin shu'umin murmushi qasan ranta tana bawa kanta tabbacin komai dab yake da qarewa.....muddin ta samu nasarar yage KASKA wato sabreen daga jikinta,sauran zata qarasashi ne da dukka qarfinta.

Kujera taja ta zauna tana shaqar iska d'ai d'ai,ta sake ware idanunta tana nan sashen da fu'ad yake saidai bata ganshi ba,ta buda baki zatayi tambaya ya shigo parlor din da nutsatsen takunsa.

Sanye yake da suspender da Fedora hat datayi matuqar masa kyau,tamkar wani baturen England,kunnensa maqale da earpiece amma dukka hankalinsa yana kan sabreen dake zaune gefe idanunta akan amna da wunin yau duka take more wayar sabreen din. Wani abu ya sosa masa zuciya,baisan wanne irin taurin kai gareta ba......koda wasa bai taba tunanin zata sanya qafa ta shure maganarsa ba,saidai nan kusa yayi imanin zai ladabatar da ita don duka cikin halinta shine hali guda daya da bazai iya jurarsa ba.

Kaman dai dazun anni ta sanyata tayi serving nashi,ta miqe a hankali daga gefansa tana qoqarin zuba mishi soyayyar shinkafar. Hannu ya sanya ya jawo cucumber a gefansa ya tura gabanta yana fadin

"Slice it" Ya fada da wani irin shanqamshi daya dan bata mamaki. Hannu ta saka ta jawota,ta dora saman plate ta soma yankawa. Sosai zuciyarta tayi zurfi a tunani,abinda ya janye hankalinta kenan har wuqar da take yanka cocumber din ta taba hannunta.

"Wayyo Allah na" Ta fada tana yarfar da hannu tana jin zafi da radadin wuqar yana shigarta.

"Yankewa kikayi adda?" Amna ta fada da sauri tana matsowa,abinda yaja hankalinsa kenan zuwa gareta daga kan wayar da yake latsawa.

"Ya salam" Ya fadi yana jin tsigar jikinsa na tashi da jinin dake biyo hannunta,har baisan sanda wayar hannunsa ta sulale ba maamah tabi wayar da kallo.

Tuni ya miqe ya kama yatsan da jinin ke fita yana kallo,har cikin jikinsa yakejin kamar shi ya yanke din.

"Me yasa bakiyi a hankali ba?" Ya fada yana zube mata fararen idanunsa. Kanta ta kawar gefe tana jin kallon nasa ya aza mata nauyi da yawa,uwa uba ga maamah a wajen da batason komai ya sake hadasu.

"Musaddiq......duba dakin anni ka samo mana abun wanke ciwo" Ya fadi yana janyeta daga tsakanin dining din zuwa kujerun falon ya samu waje ya zaunar da ita yanayin tsaye a kanta.

Da qyar maamah ta iya lalubar numfashinta,ya zama dole a yau ta datse wannan igiyar......ya zama dole ta bata ta kuma tarwatsa koma meye yarinyar ta qulla.....kowanne irin shu'umin malami ta samu ita mariya saita nuna musu qarya suke duka ita dashi din.

"Idan ya gama qaramar haukar......ka gaya masa ni uwarsa mariya ina kiransa zuwa dakina" Ta bawa musaddiq saqon don tana jin kota gefansu ba zata iya rabawa ba bare ta tsaya tayi magana da dayansu shi ko sabreen din. Kai tsaye hanyar dakinta ta nufa tana harhada hanya.....a yau koda sakin sabreen shine abu na qarshe da zata aiwatar a rayuwarta saita tabbatar ya afku kafin ranta ya fice daga gangar jikinta.


*_dan dan dan dan dan dan.........masu karatu.....uhmmmmm......bakina da goro.....zamu gani kuma......shin xai tabbata ko kuwa?,sai nace ku tara dani ranar litinin in sha Allah,na gode_



*_DUNIYATA LITTAFIN


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login