Showing 117001 words to 120000 words out of 363280 words

Chapter 40 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1377

kasa ba......bazan kuma kasa ba......abu daya kemin burki.....duk sanda na kalleta sai naji tayi qanqanta da yawa nayi mata kalar azabobin dana tanadar mata......tayi mitsitsiya na sanyata a prison din dana shirya mata......amma duk sanda ta aikata wani abu kota bullo da wani abun........sai naga nine naketa kuskuren kallon tayi qanqanta......a abinda zuciyata ke rayamin wannan karon......duk hukuncin da yazo na dauka a kanta a tunanina na qarshe dashi zanyi amfani......"

"Banda divorcee......"

"Harda shi idan ta kama" Ya fada confidently.

Ido Farooq ya zuba masa kawai,ga mamakin fu'ad sai yaga ya saki wani irin murmushi yana girgiza kai. Shima duban farouq din yake kafin yaji murmushinsa ya bata masa rai. Bayajin a yanayin da yake ciki ya kamata wani abu me kama da murmushi ya fita a fuskan farouq,don haka ya miqe tsam yana dosar bedroom dinsa. Da hanzari farouq ya miqe yana kiransa

"Wait dude.....wait" Don ya tabbatar wannan bedroom din nasa me smart door idan ya shiga ya rufe baka isa ka bude ba muddin bai sakaka cikin wadanda zasu iya budeta ba. Bai saurareshi ba ya shige dakin abinsa,da qarfi ya rufe qofar yabar farouq a nan a tsaye. A yanzun da baya ganinsa sai murmushinsa ya ninka na dazu,bayan minti uku yayi qoqarin daidaita kansa,ya matsa yana daukan telephone na falo din ya kira cikin dakin nasa.

Yayita kira yana jiyota tana ringing,kaman bazai daga ba kafin ya daga daga baya,ya sakata a kunne ba tare da yace komai ba.

"Am really sorry dude.....na hango wani abu ne daban da yake durfafoka da matuqar qarfi fiye da qarfin guguwa......amma it seems like baka ganshi ba baka kuma fahimceshi ba......anyways kayi aiki da hankalinka da intelligent dinnan dana sanka dashi.......am always free,and then it's time to act for koma waye behind all these issues......na tabbatar akwai wani abu boyayye......think wisely......am always by your side.....take a rest,but please kasha magani".

Sanyaya ranshi sosai maganganun farouq sukayi,yayi shuru kawai yana saurarenshi bai iya ce masa komai ba......shi kansa baisan me yasa a bangaren nan kaman qwalqwalwarsa bata iya aiki daidai ba?. Yana jin kamar ya gaji......yana buqatar hutu da gaske na jiki dana kwanya

"Am tired farouq......I'm feeling burnt,i need some time to unwind and focus on my well-being......kayi magana da saddiq.....i want him to schedule my annual leave cikin kwana uku".

"Kowa ma lokaci????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
n hutunsa yazo......International gateway to Maldives" Ya furta yana motsa labbansa gami da jefa hannunsa sama yana kwatanta yadda jirgi yake cillawa sama yayin daya cirata daga qasa.

"Zan kawo nesa zuwa kusa......zan dawo da mafarki zuwa gaskiya......komai zai warware.....zan kuma baka mamakin yadda zan juya maka rayuwarka dare daya" Farouq ya fada yana dariya kaman mummunan abu irin wannan bai faru ba.

Kawai wani nishadi yakeji qasan ransa idan yayi imagination na yadda komai zai kasance,sai yaji kawai ya qagu shi Kansa lokacin yayi,sai ya juya ya tattare key da wayarsa yana maidawa aljihu ya soma sauka yana barin gidan,ko saddiq dinma bazai nema ba.....shi zai shirya komai,sai komai din ya kammala sannan kowa yaji ya gani.

*_tom......me karatu?,wanne plan kake tunanin farouq yana dashi akan fu'ad?,muje zuwa_*


Yana driving a mota amma tunani fal kanshi. Tunda yake bai taba hangen wani abu daya jigata fu'ad komai tsananinsa ba kaman wannan......anya ba burbushin wannan halittar daya tsirowa zuciyarsa kuwa?, wadda kusan itace jigo na kowanne tsanani da wahala da zuciya kan iya shiga akan wani dan adam?.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

64



Bayason irin fushin da yakeji cikin ruhinsa da jikinsa gaba daya......yana buqatar yayi cooling down ko yaya ne,a lokacin ayar nan da taxo cikin alqur'ani me girma ta fado masa

"Ku saurara.......da ambaton Allah kadai zukata ke samun nutsuwa"

"Sadaqallahul azeem" Ya fadi yana miqewa hadi da fara jin sassauci daga tuna ayar kawai.

Toilet dinsa ya shiga,ya daura alwala me kyau,sannan ya dawo cikin dakin yana kunna chandelier din dake kafe tsakiyar dakin,wadda ke hade da Bluetooth da kuma fanka me bada sassanyan iskar data banbanta data sauran fankoki. Remote ya dauka ya kashe hasken don baya buqatarsa,ya kuma kunna speaker din dake jiki yana daidaitata da wayarss,take muryar fasihin malamin nan limamin ka'aba wato sheik abdurrahman assudais ta karade dakin cikin sauti mafi tsarki na karatun alqur'ani.

Relaxing yayi sosai soman sofa din dake dakin yana jin wani sukuni ya soma ratsahi,kaf a cikin malamai idan akwai wani sauti da yafi so yafi qauna bazai wuce sautin sheik abdurrahman assudais ba,wannan dalilin yaja ra'ayinsa qira'arsa gaba daya ta juye zuwa ta sudais din sak.....da wannan qira'ar yayi sauka,kuma har yau itace a bakinsa.

Idanunsa a lumshe yana ci gaba da bin sautin,bazaice yana jin yunwa ba ko kadan,zamansa a haka duk duniya yafi komai yi masa dadi,a haka ya shafe kusan awanni biyu har zuwa sanda wayarsa tayi haske,kira kuma ya shigo wayar tasa.

Hannu ya sanya ya jawo yana dubawa,ganin me kiran ya sakashi daukan remote din dake gefansa,ya kashe volume din gaba daya sannan ya daga wayar yana sakata a hands free.

"Good afternoon sir......yanzu haka dukka shugabannin gidan jaridan suna hannunmu". Zamanshi sosai ya gyara cikin kujerar yana harde qafafunsa waje daya

"Well-done,good job khaleed,akaiminsu housing estate na darmanawa.......by 4 zan fito in sha Allah"

"Yes sir" Ya fada cikin tsananin nuna ladabi,bai sake jiran komai daga wajensa ba ya kashe wayar yana ajeta gefe. Bai sake batawa kansa rai da tunani ba ya dauki remote din da xummar qara volume din,cikin ransa yana jin bazai sake barin komai ya bata ranshi har haka ba......ko meye ya faru da ita ita ta jawo......amma fa bazai taba lamunta a taba masa igiyar aure ba,ko kuma sunansa ya fito a ciki ba ko na ahalinsa.

Wani kiran ne ya sake shigowa dole ya aje remote din. Asp ne yake kiran,shima bai jinkiri ba ya daga.

"Sir........mun sama musu gurin ajiya na musamman......kuma zamu tuhumesu da kyau har sai sun fadi gaskiyar wanda ya aikosu".

"Na gode......but inaso ku barmin wannan a hannuna......ku ajiyesun irin ajiyar data dace dasu har xuwa sanda zasu furta wanda ya basu hanya da daman shigowar"

"Okay boss...."

"Thank you" Ya sake fadi labbansa suna motsawa.

Wannan bacin ran da yaketa son hadiyewa still dai ya sake taso masa,ya sanya hannunsa ya shafi kansa. Zai iya cewa tun daga guards dinsa zuwa securities dinsa amintattu ne,bashi da ko kwanto da ko shakka akan koda mutum daya daga ciki,duk da dan adam tara yake bai cika goma ba......kuma wasu daga cikin 'yan adam din masu iya canzawa ne a duk sanda sukaso a karan kansu,walau dalili na son zuciya ko makamancin hakan......amma su kam yayi imanin yadda yake mu'amalantarsu daban yake da sauran yadda masu gida ke mu'amala da yaran gidansu. Kyautatawarsa a garesu ta daban ce kaman yadda qaunarsu a gareshi ta daban ce. To amma a yanzun yadda yakejin zuciyarsa komai ma yana iya faruwa......sannan a yadda yasan ya gidansa yake,abune me wahala a iya keta tsaron gidan a shigo haka siddan ba tare da idon sani ko mataimaki sannanne ba.

Volume dinsa ya qaro yana fatan sake samun nutsuwa da daidaituwar zuciyar da zata bashi qwarin gwiwar fita zuwa yammacin. Bai tashi ba sai da akayi sallar azahar,ya daura alwala ya fito don halartar jam'in sallah kaman yadda ya saba muddin yana kusa da masallaci.

Dukkanin ma'aikatan kowa rabe rabe ya dinga yi daga ganin fitowarsa. Zukatansu a razane yake abinda ya sanya gidan ya sake daukan shuru gaba daya kamar ba wata halitta a gidan me rai da tayi saura.

Bai dawo cikin gidan ba sai la'asar,don ganinsa yau free haka da rana ya sanya masu buqata suka dinga shigowa masallacin. Bai hanasu ba ya zauna ya dinga sauraren kokensu daya bayan daya. Ba wanda ya bari ya tashi a wajen ba tare da gaggwaban abun alkhairi ba,jordan na tare dashi shi ya tashi sauraronsu,sukayi la'asar ya miqe ya wuce gida qirjinsa cike da nauyi. Sai yake sake ganin yadda ubangiji ke tsara rayuwa yadda yaso.......matsalar wani bata wani ba......a yadda unguwar take baiyi zaton masu qaramin qarfi dake neman taimako na shawagi a cikinta ba. Ya dubi kansa sanda yake wucewa ta babban glass door din da zaka taras a gate din farko na gidan. Ubangiji ya azurtashi da dukiya me yawan gaske......lafiya da wadata......saidai ya samu naqasu ta bangaren uwa da mace ta gari,wanda wadannan abubuwa biyun sune jigo a rayuwar kowanne dan adam. Ga wasu can su kuma nasu burin shine INAMA MUNE ME JADDA?,ba tare da sunsan ainihin waye me jaddan ba?,me yake fuskanta?,wacce rayuwa take going through......(wannan ya zamana izina a garemu gaba daya,kafin kayi burin inama kaine wane?,kayi tunanin mene rayuwarsa ta badini?,kayi tunanin wadanne qayoyi ya tattaka da tsinika kafin yakai ga isowa nan inda yake?,ko yaushe idan kaga wani mutum da rayuwarsa ke burgeka,ma roqa Allah ta hanya daban bata hanyar Allah yasa na zama kaman wane ba.....bayan fuskar wane dinnan kawai kake gani bakasan cikinsa ya yake ba,Allah ka kyautata rayuwarmu,ka bamu tsira duniya da lahira)"

Da tarin tunane tunane yake ratsowa falon daya xama wani irin shuru. Gaba daya kallon gidan yake wani iri,har a gangar jikinsa yakejin ya gaji da xaman cikinsa. Wuf ya hangi gilmawarta daga kitchen kaman zata kifa tana nufar qofarsu. Har yaci gaba da tafiya wani abu ya sauko cikin tunaninsa

"Ke!" Yayi kiranta da wani amon sauti da a take ya tara zazzafar gudawa cikin tumbinta

"Na'am......na'am ranka ya dade" Zuwaira ta fada wadda ke rungume da wani abu da baisan meye ba. Hannuwansa ya zube cikin aljihun wandonsa yana qare mata kallo,zuciyarsa tana raya masa wani abu game da ita. Wani abu me kama da xargi tuhuma da kuma rashin aminci a kanta yaji yana tsarga masa. Irin kallon jadda din ba kowanne mutum ke iya jurarsa ba,sai mutum me babbar kurwa,me babbar kurwar ma wanda ya cika da gaskiya da kuma amana,ba wani ha'inci cikin lamarinsa,wannan ya sanya zuwaira ta dinga jin kamar yana karance duk wani sirri dake tattare a qirjinta zuwa cikinta,tamkar ya sanya microscope yana tantance adadin qulla qulla da harqallar data taba shiryawa tsahon rayuwarta,wannan ya qarawa adadin zuciyarta gudu,ya kuma hanata ci gaba da daidaituwa akan qafafunta,saita sulale ta duqa saman qafafunta

"Allah ya taimaka.....tuba nake,bansan kana cikin gidan ba ai......da ba'a fito ba,wannana bun daya faru ranka ya dade shine ya hanani nutsuwa.......hajiya naketa son dubawa aga yanayin da take ciki....."

"Ke" Ya sake kiranta yana dage dukka girarsa sama guda biyun.

"Na'am yallabai na'am......."

"Ki tarkata komai naki kibar gidannan cikin qasa da minti goma....."

"To an gama ranka ya dade,aisai a komawa hajiya maamah baya goya marayu" Ta furta tana jin wani sassauci da rangwame a ruhinta. A abinda takeji yanzun sallamarta shine babban gatan da yayi mata,duk sanda taji muryarsa sai kowacce kafa ta jikinta ta jiqe da gumi. Sai a yanxu take ganin cewa da gaske xaman gidan jadda yafi qarfinta,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa. A baya tana tunanin duk randa yace taje ya sallameta zataji tashin hankali maras iyaka......amma a yau sai takejin kamar 'yanci ne daga bata zuwa zamowa halastaccen d'a.

"Kinsan me?" Ya fada yana sake dubanta,saita dakata tana saurarensa.

"Bazan dubi tsufanki ko digon furfura koda qwaya daya dake tsakiyar kanki ba......muddin naxo na sameki kin koma gifan gidan maamah........ki tabbatar daga ranar kin tashi daga aiki......kiyi nesa da ita da komai da kowa daya danganceta.....and hakan bawai xai sakaki kin tsira ba,duk mutumin da yake gidan nan daga kwana uku baya zuwa jiya da abin ya faru baxai tsira ba a waje na......wanda kawai zai tsira shine MAI GASKIYA ". Duburbucewa tayi har akwatin kayan asirin maamah na shirin tarwatsewa daga hannunta. Gab gab gab haka hannuwanta da qafafunta suka dinga haduwa waje daya,wannan wanne irin kalar tashin hankali ne?,wanne irin yaro ne wannan maras imani.... Lallai dole mallakarsa ta yiwa mariya wahala,zuwaira ta furta hakan a ranta sanda take ta qoqarin kai kanta ga sassansu don ta samu ta sulale kaman yadda ya shawarceta. Ayadda ta sanshi tana ganin ko cinye namanka yace zaiyi zai iya......musamman shi daya mallaki masu gidan ranar da babu me tuhumarsa ko bin ba'asin abinda yayin.

Gaba daya wunin yau duka hankalinta yana kan wayoyinta,bama ita ba.....hatta da fareeda kowanne motsi nata yake kan social media's tana hasashen watsuwar abun a kowacce kafan sada zumunta. Sanda taga ankai azahar shuru sai duk wata nutsuwa ta soma barin gangar jikinta,hankalinta ya gaza kwanciya kwata kwata,ta kuma shirya kai tsaye ta kira driver ya dauketa zuwa gidan maamah.

A sannan ita dinma duban wayar take tayi.......tanaso ta samu wani haske ko yaya yake.......tunda ta zauna take saqa yadda komai zai kasance.......take qiyasta irin tozarcin da zata yiwa sabreen. Lallai sai ta sanyata ta fahimci wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa.......ita kanta batasan adadin yawan tozarci da qasqancin da zata sanyata ta fuskanta ba.

Mamakinta ya tsananta ainun da rashin samun kai,sai taji ta kasa jira,kai tsaye ta daga waya don kiran fareeda,amma sai fareedan ta hutashe da ita saboda turo qofan setting room din da tayi ta shigo tana taunar chewing gum kaman yadda ya zame mata al'ada,duk kuwa da cewa yau din bata cikin wannan mode din,amma cin chewing gum din ya zame mata dabi'a.

"Ke nake shirin kira yanzun.......banga tasirin aikinki ko wani motsi na daban ba" Maamah din ta furta kanta tsaye tana duban idanun fareeda. Idanu tadan xubawa maamah din,mamakin dabi'arta tana dan kamata. Kanta tsaye take magana akan duk wani abu daya shafi buqatarta,ba ruwanta da wata matsalarka ko fuskantar yanayin da kake ciki.

Kanta ta dauke tana qarasowa ciki,sannan ta yiwa kanta mazauni saman hannun sofa din tana harde hannuwanta a qirjinta

"Wannan shine aiki mafi kashe kudi da nayi......sannan shine aiki mafi jinkirin samun nasara" Tayi maganar tana duban maamah din.

"Masu aiki sun kammala.......naki aikin da nawa duka ba wanda ya kawo result me kyau........abu daya ya rage shine,ki kira d'anki ki tuntubi sakamako daga gareshi". Gyara zamanta maamah tayi tana duban fareeda,ta soma fahimtar wasu halayenta da inda dabi'unta suka sanya gaba,bata gayawa fareeda tayi failing a nata agenda din ba.....ya akayi amma ta sani?.

"Na yarda har abada yaro yaro ne.......kina tunanin samun galaba akan duk wani lamari daya shafi fu'ad abune me sauqi?,inda kuwa hakanne da bakizo gabana ba......da babu ke cikin babin qaddararmu sam sam" Maamah ta fadi tana duban fareeda.

"Duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau bishiyar rimi bazai hango ba..........a naki lisssafin kiran fu'ad kai tsaye na jefeshi da salon tambayoyinki abune me sauqi da zai sanya mu wanye lafiya?" Ta qarasa maganar tana duban fareeda data zubawa maamah nata idanun.

"Kina iya kiransa ta wata siga daban ki kuma zaqulo bayanan da kikeso......amma zai zama babban kuskuren rayuwarki ki biyo masa ta waccan hanyar taki....."

"Amma bisa alqawari da yarjejeniya.......xaki zama tsanina na mallakar fu'ad haka ne?"

"Har yanxu ina kan wannan bakan.......amma fidda sabreen daga gidansa aikinki ne......zai iya zama nawa aikin,amma kuma salon aikin nan da yake zamowa ba waji bi". Sun jima suna kallon kallo tsakaninsu,kowanne da kalar saqar dake cikin zuciyarsa game da dan uwansa,kafin fareeda ta fiddo wayar da musamman saboda kiran fuad din ta tanadeta. Da kowacce waya da kuma kowanne layi ta kirashi ba zata sameshi ba saida wannan wayar kadai.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

65


_Manzon Allah S A W bai taba aibata abinci ba,idan ya burgeshi sai yaci,idan kuma baiyi masa ba sai ya qyaleshi(ba tare daya aibatashi ba)_



Tsaf ya shirya cikin trouser dark blue na yadin vicuna,yayin da sanya black shirt data fidda ainihin kan sassalkar fatar nan tasa me tsananin haske,wadda ta cakuda da hutu da jin dadin dake bayyana kansa cikin kowanne hali yake. Kyakkyawar qasumbar fuskarsa da bata da cika irin ta cukus ta sake qawata fuskarsa da sanya masa kwarjini,tana da santsi kwatankwacin sumar dake lullube saman kansa. Baqa ce sidik kaman gashin girarsa dana idanunsa,hakanan kaman sauran gargasar dake lullube da sassan jikinsa. Agogo fata ya daura a tsintsiyar hannunsa me tsananin tsada daya dace da shigarsa dama tsadar kayan jikinsa,yabi ko ina na jikinsa ya feshe da lallausan turaren nan nasa me taushin qamshi.

Tsananin dauriya kawai ta sanyawa ruhinta,tun bayan dawowar amna da batakai magarib ba kaman yadda anni tace taketa qoqarin shimfida walwala akan fuskarta,duk da cewa abun ba haka yake ba daga qasan zuciyartata. Amna din ta dabance,tana da barkwanci da sakin jiki ga duk wanda ta yarda dashi,wannan ya sanya cikin qasa da awa guda taji nauyin dake qirjinta yana raguwa,lokaci lokaci labarun amnan suna sake dauke hankalinta daga yanayin da take ji.

Ita ta tilastata da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login