Showing 198001 words to 201000 words out of 363280 words

Chapter 67 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1442

ba.....ya fita abinsa ne,bashi kuma da niyyar bata wannan lallashi da kulawar da take yunwarsa. Ranta yakai qarshen baci,da gaske dai bai dauketa uwa ba mahaifiya.....kunnuwanta na tuna mata wata hira da taji musaddiq da saddiq nayi,suna gulmar fu'ad din. Ya fita aiki ranar sai gashi ya dawo da Rana,suka dinga dariya suna gulmarsa,wai da zai fita ne yaga ran anni kaman a bace....da yaje office ya kasa sukuni,dawowar da yayi yazo zagayata ne ya tabbatar ta warware,ba kuma wani a cikinsu bane ya bata mata rai ba.

Tuna wannan kawai ya sake hura wutar zuciyarta,sai kuma ta tsinci knocking da fushi yasa ta kasa tambayar waye,ta miqe kawai ta bude qofar a fusace.

Anni ta gani a tsaye tana duban ta,wani irin kallon kallo dake dauke da ma'anoni da yawa a zukatan kowannensu.

"Zuwa nayi duba sabreen.....ta shiga dakinki kuma har yanzu bata dawo ba?,ina kika kaita?". Me neman kuka ne wanda aka jefa da kashin awaki,wanda yake jiran kadan ya fashe,saita fito daga dakin gaba daya tana duban anni tana huci.

"Dama dab nake da zuwa wajenki na tambayeki wanne irin baqin sihiri kika yiwa 'ya'yana?,wacce irin shirka kika ta'ammali da ita ameena?,da yake bani da haqqinki sai gashi kin kawo kanki da kanki kina tambaya akan abinda ni yafi cancanta na tambayeshi". Mamakin maamah din ya kasheta,ta zuba mata idanu sosai tana ganin yadda take haqilo kaman zata fidda maqogoronta.

"Mariya......tambaya daya ce nayi ina kika kai sabreen?,don bata dawo dakinta ba". Wani banzan kallo ta watsawa anni tana dubanta.

" Au.....bacewar karuwa dama abun mamaki ne?,har akwai mamaki don an wayi gari an tarar karuwa ta gudu daga dakinta?"

"Subhanallah" Anni ta fada tana ware idanunta akan maamah mamaki yana ratsata. Surukarta?,matar d'anta take kira karuwa saboda wani son zuciya nata?.

"Ameena.....ina me baki shawarar warware duk wani qulli da kikasan kin yiwa yarana tun daga zamanin quruciya zuwa yanzu.....idan kuma kinqi wallahi wallahi ni mariya bazan qyale ba......na dauki cikin yaran wata tara na haifesu.....naci kashinsu da fitsarinsu amma rana daya azomin da bariki da salon mallaka?,ubanme kike basu wanda ni bazan iya basu ba?,uban me kike musu?". Sosai zagin ya sosa zuciyar anni,sai ta koma ta zauna tana qare mata kallo hannayenta harde a qirjinta.

Duk wasu sarari da filaye na yiwa maamah kara zuwa yanzu sun fara cika,bata kuma da saura wanda zata bude mata taci gaba da zuba jujinta. Kai tsaye kuma hankalinta kwance ta kirata

"Mariya......abinda na basu baki dashi.......kin kuma rasashi har abada......yadda kika kasa rungumarsu kiji qansu a sanda suke da rauni......to kema kin rasa wannan cikakken tausasawar sai wadda zasuyi miki donsu fita haqqinki da haqqin addininsu......shima wannan din xasuyi miki shine saboda sun mori iyayen goyo da sukasan hagunsu da damansu.....daidansu daba daidai ba......banda haka ke dasu dama dukkan abinda suka mallaka sai gani sai hange daga nesa. Inda ce hankalinki a daidai yake......inda ace hankalinki cikin jikinki yake.....ba cikin dimuwa kike ta neman duniya idanu rufe ita da abinda yake cikin ta ba......da baki buqatar bayani kan me yasa kika rasa kike kuma rasa kowacce dama,take kuma kufce miki.......bari na gaya miki wani abu.....ni ameenatu na tsere miki.....ni ameenatu ba zaki taba kamoni a zukatan naki 'ya'yan ba bare nawa 'ya'yan.....sauran dukkanin abinda zaki zata ko ki tuhuma wannan ke kika sani.....kuma keda zuciyarki......zuciyar bawa birninsa,abu daya zance miki shine......kada ki yarda kada kuma ki kuskura wani abu ya samu sabreen,idan kikayi wannan gangancin to tabbas zan saka a binneki a cikin qasar Maldives me tarin farin rairayi" Ta qarashe maganar tana nuna maamah da yatsa,sannan ta miqe tsaye sosai.

"Daga yau gobe zuwa jibi naga dawowar diyata cikin gidan nan.....ko da fu'ad ne yace zaiyi ganganci da rayuwarta shi dake aurenta saina hukuntashi.....ballantana ke da nake kyautata zaton kwangilarta kika dauko". Anni na kaiwa nan ta juya tana barin wajen,tanata qoqarin controlling fushinta kada maamah din ta ganshi.

"Aikin banza kenan qafafa da mallakin wani.....ke me ya hanaki haifar kamarsa?,kinga sai kiji dadin yin mulkin mallakar da kyau ba tare da kowa yaga wallenki ko ya qalubalanceki ba" Tayi maganar da nufin fusata zuciyar anni.

Da wani lafiyayyen murmushi ta waiwayo tana kallonta.

"Banda abinki tunda kin haifomin ai kin hutasshe dani......don yadda nake hutawa ko asalin wadda ta kotseshi bata rabauta da wannan ba....idan kinajin tsuntsu daga sama gasashe to fu'ad ne a hannun ameenatu" Ta qarashe maganar tana bude mata tafukan hannayenta sannan ta juya taci gaba da tafiya abinta.

Kamar hauka zai kamata haka taji maganganun anni saman kanta. Kasa shuru tayi ta soma zuba ruwan masifa da zagi.

"Ameenatu.....nafi qarfinki....nafi qarfinki wallahi,bakisan wacece mariya ba....kibar ganin zamani ya cimmata......to ki giwa ta fadi tafi qarfin wawa,tafi qarfin kiyashi ya jata.....zan nuna miki asalin wasan indai na haifu cikin uwata da ubana".

Bataji komai cikin abinda take fada ba,don already ta wuce daki ta kuma maida qofar ta kulle.

"Bari yazo shima zai sameni.....bazan sake kwana gida daya da wannan annamimiyar makirar ba.....dole yazo ya zaba,koni ko ita" Ta fada kaman zararriya tana jawo luggage dinta tana watsa kayanta ciki,sai kuma ta tsaya cak.

"Ina yarinyar ta shiga?" Ta tambayi kanta gargadin anni da fuskar daba wasa tana dawo mata,saita saki kayan hannunta ta koma gefen gadon ta zauna.

Wani gumi ne ya tsargo mata tana jin hankalinta ya fara kadawa. Anni tana da power din da bata da ita.....tabbas ne wannan,don idan akace ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ana buqatar ganin fuskar maman muhammad jadda ta anni ce za'a fara nunowa.....daukakar fu'ad ta sanyashi alaqa da manyan mutane da hankali baya zato,da yawansu kuma suna alaqa da anni a matsayin itace mahaifiyarsa......KENAN UMARNI DAYA ZATAYI A KANTA AYI MATA YADDA TAKESO?.

Tambayar data sanya 'ya'yan hanjinta curewa waje daya kenan,saita jawo wayarta da sauri tana nemam number fu'ad.

Kiran duniya wayarsa a kashe,ta kira tun tana irgawa harta bacewa lissafi,sai ta aje wayar kawai gefe tana tunanin meye abunyi?.

_=??=??=??,maganin dan banza karen maguzawa ko inji hausawa.....shin a wannan lokacin hajiya maamah xata shiga hannu ko kuwa?_

_meye hasashenku?_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


102


Tsaye take gaban qawataccen madubin bandakin me tsananin haske da hasken rana daya soma mamaye sararin samaniya ta bullo ta wasu sassan glasses na bandakin ya kutso ciki.

Daure take da bathrobe me tsananin taushi,fara qal data zauna a jikinta bisa taimakon igiyoyin dake maqale a jikinta,saman kanta daure da towel data nade gashinta me tsaho da santsi,wanda ruwan da ya jiqashi ya sanyashi kwanciya ta gaban goshinta dama wasu sassa na wuyanta. Brush ne riqe a hannunta.....amma sai ta kasa matsa toothpaste a jiki,saita buge da kallon fuskarta ta jikin madubi data fito tarwai kaman ka saka hannu ka ciro.

Daren jiya ke faman mata yawo cikin kwanya......tanata tuna shudewar kowacce daqiqa a tsakaninta dashi. Iya yawan abun kunyar data tafka bazai barta hada idanu dashi ba,ba zata iya ba sam koda daidai da minti daya.

Duk yadda take tunanin abun zaizo kaman na farko sai komai yazo mata da ba zata,saida komai ya kammala sannan ta tsinciki kanta tsakanin hannuwansa,bata da wani zabi illa fashe masa da kukan kunya. Ya sani sarai......yasan abinda takema kukan,amma sai yayi kaman bai fahimta,ya lalace sosai wajen rarrashinta......daga qarshe ya juye mata tashi kalar shagwabar data sake tsumata,ta sanyata tayi luf ba shiri tana jin kunya da nauyinsa suna kamata.

Zare brush din daga hannunta da taji anyi ya sanyata firgita

"Good morning sleepy head" Ya fada yana tsaye daga gefanta ya kashe mata idanu yana qoqarin saka mata toothpaste din.

"Morning" Ta fada tana sadda kanta qasa tana jin wani irin nauyinsa da bata taba ji ba. Tunda taji ya tashi ita taqi koda motsawa,har yayi wanka ya fito yayi sallah yadan fita a dakin,fitar nasa tayi amfani dashi tayi wuf ta shiga wankan da xummar ta shirya kafin ya fito tayi sallah ta sake boyewa cikin duvet.

"Feel free......brush kawai zanyi na fita" Ya fada yana matsowa bayanta. Dab da ita ya tsaya,har jikinsa yana gugar nata,fuskarsa ta fito bayan tata ta cikin madubin,ya zube idanunsa fes da suka qara wani irin haske saman tata fuskar ta cikin madubin. Wani irin murmushi ne kwance a fuskarsa.....wata irin shimfidaddiyar walwala da makamanciyarta bata taba wanzuwa saman fuskar tasa ba da annuri suke fita daga fuskar tasa. Qwayar idanunta yaketa laluba yana son ya kalla amma ta hana mishi kallo,ta zura brush din kawai a bakinta tana wankewa tana kuma jin yadda yake sake shigewa jikinta da sunan brush zaiyi.

Ta gefe da gefen cikinta ya zura hannuwansa ya zari brush dun,ya saka toothpaste duk a hakan yana sake shige mata,ya tura brush din bakinsa ya soma wankewa shima a hankali yana sake maida idonsa ga fuskarta data futo sosai ta madubin. Wani kallo yake mata ko qiftawa baya yi,yana fatan tayi kuskure ko sau daya ta daga kai ta kalleshi,yana son karantarta ta cikin idanunta sosai,ya sake matsawa sosai jikinta yana sansana kanta dake fidda wani irin sassanyan qamshi.

Ta gama nata brush din amma tanata juyashi a hannunta,ta rasa yadda zata gaya masa.....ta kasa daga kai ta kalleshi ma bare ta samu qwarin gwiwar gaya masa. Ya karanci hakan,murmushi ya qwace masa.

"Wannan kunyar daga ina?" Ya tambayi kansa da kansa daga can qasan zuciyarsa.

Yana sane yaci gaba da cinye musu lokaci,yanason tayi magana amma kuma ta gaza,har zuwa sanda taji ta soma tuqewa,saita ajiye brush din,ta kuma juyo da hanzari tana fadin.

"Ni na gama" Qurjinsa ta fada kai tsaye,don babu wani space da zai bata daman wucewa. Kan qirjinsa idanunta suka fada,ni'imtaccen gargasar qirjin tayi maraba,ta daga idonta a hankali tana kallon tazarar nisan tsahon dake tsakaninsu. Ya fita tsaho sosai,duk da cewa ita din ba gajeriya bace,idanunta suka sauka kan Adam's apple dinsa daya fito sosai ta maqogoronsa kaman zai fado.

Wani abu guda daya tal da yake burgeta ga halittan namiji kenan......batasan meyasa yake burgeta ba,amma dai tasan yana bata mamaki,ta jima kuma tanason taji abun ya yake,tauri ne dashi?,yana musu zafi ko kuwa?,ba tare da tunanin komai ba ta miqa yatsanta a hankali zuwa wajen ta tabashi.

Cikin kowanne jini dake harbawa a jikinsa yaji saukar yatsan nata,ya hadiye wani abu daya sanya Adam's apple din motsi yayi qasa ya sake dawowa saman. Kasa jurewa abinda yakeji din yayi,sai ya fincikota sosai zuwa jikinsa ya matseta a qirjinsa da kyau yana dora fuskarsa saman wuyanta.

"Wannan tsokana ne ai......yanzun kuma inda zan ritsaki kona nema fansa saiki isheni da kukan banza......har a kiramin anni ma da momma ko?". Kunya ce ta kamata me tsanani,akan jiya yake tsokanarta ta sani......sannan ita kanta batasan ma'anar abinda tayin ba yanzun,taji tana sha'awar tabawa ne kawai.

"Nifa wannan gaisuwar baiyimin ba......ina buqatar zuzzurfan alaqa tsakanin da iyalina......inason ki zama qawata.....aminiyata......mamana.....yayata.....qanwata....oh" Sai kuma ya tsaya yana dagota daga jikinsa gami da dan dukan goshinsa.

"Ashe fa ance sai anyi shawarar za'a soni ko aah ko?" Ya fada yana ware mata idanunsa. Kauda kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani murmushi yana son kubce mata amma tana hana hakan,bata ankara ba taji ya dagata cak ya azata gefan sink din bandakin,hakan ya bawa santala santalan cinyoyinta daman bayyana don bathrobe din ta dage kadan.

"Kinsan me?" Ya fada yana tsayawa tsakanin cinyoyinta,hucin numfashinsa dana daddadan turarensa yana sauka a fuskarta.

"Karki wahalar da kanki DUNIYATA kice saikin koyawa kanki sona......" Daga kai tayi ta kalleshi abinda yakeson gani kenan dama tun dazu,saidai ita din tayi hakanne saboda mamakin maganarsa. Girarsa ya dage mata dukka biyun yana jin dadin ganin qwayar idanunta. Oily eyes daya jima yana kokwanto shin akwaisu?,sai gasu a jikin abinda yake mallakinsa gaba daya.

"Yes.....iya soyayyar da nake miki ma ta ishemu mu rayu ni dake.....bake kadai bama.....har babies din da zamu haifa nan gaba" Ya fada yana dora hannunsa saman plate tummy dinta,abinda ya sanyata jan wani irin numfashi saboda tafin hannunsa guda daya daya dora saman budaddun cinyoyinta.

"DUNIYATA....Kinsan yara nawa nakeso ki haifamin?" Kasa amsa masa tayi,tafi buqatar ya matsa baya kadan kada ya dagula mata lissafi,abinda ta fahimta kaman yana son sake mata wayo ne kawai yake saka kusanta kanshi da ita.

"Karka zaqe da yawa.....har yanzu ban gama yanke hukunci ba" Ta fada cikin tsanani dakiya. Dariya yakeso yayi sosai amma ya dake,ya fahimci qarfin hali irin nata da zallar qi fadi dake dawainiya da ita.

"Don't worry.....kedai ki tayani ji ma kawai ya wadatar dani" Yana kaiwa nan ya sunkuceta gaba daya tamkar ya dauki 'yar jaririya yana takowa zuwa bedroom din.

"Ka saukeni" Ta fada a narke,saboda ta lura gaba daya ya raina dagata,ya maidata kamar wata 'yar bebin roba.

"Ta yaya zakiyi nauyi kina wasa da abinci?,indai kinason mu shirya saikin koyi cin abinci irin na muhammad fu'ad" Yakai qarshen maganar yana direta saman sofa bed,sannan ya fara takawa a hankali zuwa saman dressing table yana kwaso kayan shafanshi data tabbatar yafi qarfin talaka irinta.

Gabanta ya zubesu gaba daya sannan shima yabisu ya zauna a gabanta yana tankwashe qafa tamkar bawa da uban gidansa. Ya soma bude cream cream din da wasu irin abubuwa da batace ga sunansu ba ya fara tatsawa a hannunsa sannan ya kamo hannunta yana juye mata su a ciki.

"Zaki iya haifamin yara dozen biyu?" Yayi maganar murya a sanyaye da wani zuzzurfan sauti yana riqe da hannunta da yake maida cream din daga hannunsa zuwa nata.

Idanu tadan wara tana dubansa da kyau.

"Please am serious.....ko through IVF ne.....a dinga saka miki biyar biyar.....nayi alqawari ba zaki sha wahala ba.....zan biya ko nawa ne a ciresu cikin aminci.....zan kashe miki ko nawa ne DUNIYATA.....nayi alqawari" Mamaki sake kasheta yayi ganin yadda yake maganan da dukka gaskiyarsa,hakan ya bayyana itama a idanunta,sai ya saki wani murmushi yanayin fuskarsa yana canzawa.

"Kina mamaki ko?" Ya tambayeta yana sakar mata hannu don ta samu daman shafa man daya tatso mata.

"Naso mu da yawa abbanmu ya haifa.....nayi wannan burin saboda gidan masu yara da yawa yana burgeni,saidai kuma mu biyu aka haifa.....inaso na tarawa abbana zuria me yawan gaske.....zuri'ar da zasu dawwama suna masa addu'a da sadaqa jariya.....bani da sha'awa ko burin auren mata biyu.....dake kadai nakeso na rayu DUNIYATA shi yasa nakeso ke din daya ki zama uwar dukka yarana" Ya qarasa fada yana dubanta.

"Baga fareeda ba?" Tayi zancan da wani yanayi da ya sanya murmushi kubce masa,yadan dafa goshinsa yana cewa.

"Maganan fareedan bai wuce ba?..... apologize din da nayi jiya baiyi ba?.....okay am ready to repeat it" Ya fada yana jinjina yadda abun yafi tsaya mata a rai fiye da komai. Kafadunta duka biyun ta daga tana kauda kai

"Ina ruwana nikam.....am temporary......"

"Temporary?" Ya katseta cikin maimaitawa yana dubanta da kyau ba tare da ya barta ta qarasa fada ba,sai ya ajiye boyayyen numfashi

"You're my world.....kece DUNIYATA sabrrrrr....na rantse da Allah.....banda ubangijin daya haliccemu ba wanda ya isa ya qwaceki a hannuna.....ke kanki baki isa ki raba kanki dani ba.......ko mutuwa ina kai qararta wajen Allah.....muddin tana da nufin rabani dake ubangiji ya hukuntamin ita". Sosai maganarsa ta ratsata,taci gaba da shafa wa hannayenta man cikin wani irin kasala ba tare data dago idanunta ta kalleshi ba.

"Ya kamata muje kiyi break" Ya fada yana katse shirun hadi da miqewa. Batasan me ya matsa yayi ba sai daya miqo mata rigar saman cinyarta.

Rigar jiya ce dai da bata saka ba,saita daga ido tana masa kallon Why?. Kafada ya daga yana watsa hannuwansa.

"Zan iya saka miki if ba zaki iya sawa ba" Kai ta girgiza masa da sauri,don ta tuna jiyan,daga saka rigar labari yasha banban.

"To ka fita sai na shirya" Ta fada a shagwabe still

"Inje ina?,bayan ko na fita dinma saina dawo na taimaka miki na daure miki rigar kin manta?" Ya fada hannuwansa na goye a qirjinsa yana qare mata kallo,don hatta cikin bathrobe din ba qaramin kyau tayi masa ba.

"Na rufe idona.....inkin gama sakawa ki gayamin" Ya fada yana juya mata baya gami da maida kallonsa qofa yana ganin gilmawar ruwa ta tsakanin labulayen da basu gama rufuwa ba.

A gurguje ta saka rigar,tanayi tana waiwaye wai kada ya juyo ya ganta bata sani ba. Dariya yakeyi abinsa can qasan ransa,don yana ganinta tarwai ta wani glass dake gabansa ba tare da ta sani ba.

"Zan iya juyowa?" Ya tambaya yana danne dariyarsa.

"Eh" Ta fada tana turo baki gaba,abinda yayi matuqar burgeshi har yaji kaman ya kama lips din ya shanye.

A nutse ya dinga bin igiyoyin yana daure mata,kowacce daya saiya tambaya

"Tayi haka?" Kai take daga masa mafi yawa,ta koma kaman kurman qarfi da yaki,ta tabbatar kaf halittun bayanta ya gama qare musu kallo,tana jin yadda yake sakin ajiyar zuciya time to time. Yadda maroon din rigar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login