Showing 336001 words to 339000 words out of 363280 words

Chapter 113 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1421

To yau kam ma duk wani shirinta bata samu ganin shigowars gidan bama kwata kwata. Har sha daya na dare idanunta biyu,batasan kuka ta fara yi ba saida taji damshi saman fuskar fawwaz dake shan mama wanda ya tashi a sannan,daga qarshe ma tana tsaka da bawa fauzan mama bacci yayi gaba da ita,wanda a sannan sha biyu saura na dare.

Washegari taga alamun gidan ya kaana,saidai duk saurint na ta sameshi bata iskeshi ba. Wunin ranar gaba daya dauriyarta a ya qare,wuni tayi a daki ma'au nata cigiyarsu,don batason ta fito ma'u taga canji a fuskarta ta zargi wani abu.

Ranar ta rantse ba zatayi bacci ba sai taga shigowarsa,koda zata kwana ne a zaune,don haka koda goma na dare yayi ta tabbatar yaran sunyi bacci,goma da rabi ta sauya kayan bacci.

Lafiyayyun kayan barci ne masu wani irin sulbi da yauqi,wadanda ta siya a HUGUMA CLOSET da sukazo kai tsaye daga Dubai. Suna da wani irin bin jiki da daukan hankali,lingerie ne sosai na isassun mata.

Curling iron ta saka ta zauna ta yiwa gashinta wani irin nannadewa kaman macaroni,sannna ta tattarashi zuwa left side na kafadarta gaba dayanshi. Daga daya side din tadan tareshi da mabanbanta shapes na hair clips. Tattausan lips nata ta wadata da lips gloss daya qara masa kyau da sheqi,ta wadata kowanne part na jikinta da kalar turaren da musamman aka yishi saboda gurin,wannan turarrukan ta sansu da amfaninsu ne a wajen mummy sultana mummyn twins BATOUL DA BENAZEER(Gudun k'addara).

K'awace ta mummy safuura,ranar da suka isa abuja tazo mata a gaggauce da nata twins din din batoul da benazeer,wadanda aketa shirye shiryen bikinsu dukka su biyun,duk da bikin saura watanni shida,amma tsananin gata idan kaga yadda aketa shiri saika dauja gobe ne ko jibi.

Ita kanta ko yaya ta motsa qamshin jikinta burgeta yakeyi,ta tsaya gaban madubi taga yadda ta ajiye wani sassanyan kyau,ta gamsu da kanta da kanta,don haka saita tofe su fauzan da addu'a ta kuma wuce zuwa parlor na biyu.

Ba sabonta bane kallo,amma yau da kanta ta kunna Tv din,ta kuma kamo tashar tumbin giwa ind suke wani hausa series.

Rabi da rabin hankalinta yana kan wayarta,batasan adadin saqonnin data aike masa a kwanaki ukunnan ba,amma ko qwaya daya tal bata samu amsarsa ba. A baya ta shiga tsanani na rayuwa da barazana kala kala,amma bata taba jin tsananin da yakai mata wannan wahala ba. Bata taba jin nutsuwa da lafiyar zuciyarta tana mata barazana ba irin na wanann lokacin. A wannan lokacinne take tabbatar da ma'anar TASHIN HANKALI da kuma rashin sukuni da gasken gaske.

Ba fahimta take cancan ba,saita yanke kiran fannah kawai suyi hira.

A qalla sun kusa awa daya da fannah din,har sai da taji farouq ya iso kusa sosai,tana jinsa yana saka fannah din dariyar da bata shirya ba,dole ta yanke kiran. A gogo ta kalla,taji kewar nata mijin yana saukar mata,banda wannan matsalar data faru a tsakaninsu da tuni zuwa yanzun shima yana tare da ita,ta sauke idanunta tare da ajiyar zuciya zuwa saman Tv din,daidai sannan ya murxa handle din qofar parlor din ya shigo da sallama muryarsa can qasa,yanajin kowacce gaba ta jikinsa a mugun jigace.

Idanunsa da sukayi laushi qwarai su ya fara zube mata,tayi masa wani irin fitinannen kyau,ya sauke dubansa kan gashinta da yasa kwalliya da wani irin salo,salon da hatta yanayin zamanta saman kujera yau din na musamman ne.....

Cikin wani irin hanzari ya dauke kanshi daga dubanta sanda ta daga risunannun idanunta zuwa kanshi. Yadda ya dauke kan baima ko nuna ya ganta ba ya mata wani irin ciwo,duk da haka ta daure tace masa.

"Sannu da zuwa".

"Yauwa " Ya amsa still ba tare daya kalli sashenta yana takawa zuwa hallway din.

Idanunsa ya lumshe,yana jin wani abu yana harbawa zuwa kowanne sashe na jikinsa. Ta masa kyau iyaka,ta fusgi hankalinsa qwarai,saidai har yanzu yana jin tasirin fushinnan da yakeyi da ita. Ta dauka masa yara sun fita daga gidan daya killacesu ba tare da yasan adadin nisan da zatayi ba,ta dauka masa yara ba wasu cikakkun masu tsaronsu......uwa uba ta taba masa martabar igiyar aurensa......tayi nisan da bai kamata ace ta yishi ba tare da muharraminta ba.....ba kuma tare da izininshi ba.

Idan har ya sake mata haka da yawa gaba yana da guarantee din me zaya faru?. Iyali suke tarawa shida ita,fata yake kuma su gina iyalin da kowa zasu zame masa abun alfahari. Babban abun dake mintsinar zuciyarsa shine......tsoronsa daya karanta cikin idanunta tun wancan ranar,to meye yake mata a shimfidarsu da zai sanyata gudunsa har irin haka?.

Ya sani......duk duniya ita zata fadi wayeshi a wannan fannin.......tafi kowa alfahari dashi........wani irin yanayine da take ji dashi cikin rayuwar aurensu,amma dare daya saita nema sauya hali?.

Alqawari ne ya yiwa kansa tun first night nasu......bazai sake kasancewa da ita ba ta wani yanayi na daban har sai da shauqinta da cikakkiyar amincewarta,koda kuwa son kusancinsa da ita zai masa mene ne.......bare a yanzun da yake cikin fushi da ita.......banda wannan kallon daya mata na yanzu da yake shirin wargaza masa lissafin da baiyi niyyar wareshi a nan kusa ba.

Dakinta ya wuce kai tsaye,kaman yadda ya saba shiga ya gansu suna bacci batasan ma shigar tasa ba bare fitowarsa. Ya qarasa gaban gadon,ya riqe yatsun yaran idanunsa a kansu. Wani sanyi yaji zuciyarsa tana yi.......da gaske da ake cewa yara sanyin idaniyar iyayensu ne.

Yana iya jinta sanda ta tura qofar dakin ta shigo yana tsaka da musu addu'a,bai waiwayo ba,bai kuma tsaya da abinda yake ba har ya gama tofesu da addu'ar sannan ya juya a hankali da zummar fita a dakin.

Dab da zai isa bakin qofar tasha gabansa,ta shiga ta tsakanin hannayensa ta tsaya a tsakiyarsa tana lalubar qwayar idanunsa ta saka nata a ciki.

Narkakkun idanun nan nata da suke kasheshi......narkakkaun idanun nan nata da suke zare masa dukka wata laka tasa,su kuma kashe wutar fushi dake ruruwa a zuciyarsa,idanun da har yau wani haske da qyalli suke kasa kaman ranar farko daya fara ganinsu.

"Zan wuce a gajiye nake.....bacci nakeji". Ya fada da wata maqalalliyar murya daga can qasan maqoshinsa,muryar da takeso lallai saita tona asirin dake danqare a zuciyarsa da gangar jikinsa.

Qwalla sosai ta cika fararen idanunta,ta koma masa kaman wata yar shekara goma saboda yadda ta maqale.kafada.

"Zakaje ka kwanta kayi bacci ko?,sabreen ita kuma ta mutu?". Sai kawai ta fashe masa da kuka.

Cije labbansa yayi,yana jin yadda kukanta ke huda masa sassan jiki yanason kassarashi da kassara qarfin qwanjinsa dana zuciyarsa. Ya dake sasai yana fadin.

"Nifa ba kuka na tambaya ba,hanya nakeso a bani......zancan sabreen ta mutu kuma ai bai taso ba.....ki bani hanya please" Ya fada a dake yana basarwa,yana fata ta matsa ta bashi hanyar kafin ya qarasa karyewa daga hawayen dake fita a fuskarta.

_Wato dai da gaske kai ragon namiji ne indai akan sabreen ne?,zamu gani,zaka iya daurewa?=??=??_
167



"Hamma" Ta sake kiransa muryarta a karye da sautin kuka.

"Am really sorry hamma......Allah bazan sake ba" Tun daga tsakiyar kansa har tafin qafarsa yaji kiran sunanshi da tayi,zuciyarsa tayi sanyi amma tana gaya masa ba yanzun ba......da sauran karatun.

"Naji na haqura.....matsa na wuce" Ya sake fadi yana kuma tsare gida. Fararen idanunta da suka dan surka kadan saboda kuka ta daga ta kalleshi,shima idanunsa suna kanta,amma koda ta kalleshin sai ya dauke kansa,saboda tsigar jikinsa ya da yaji gaba daya ta tashi.

"Hamma baka haqura ba....."

"Goyaki kikeso nayi?,shi zai tabbatar miki na haqura ko kuwa yaya?". Yadda yayi maganar da wani basarwa sai ya karya mata gwiwa,gaba daya sai taji kaman ya tozartata da yadda yake qoqarin tankwabe rarrashin da take masa.

"Bani hanya please" Ya sake fada yana kuma hade gira.

A hankali ta janye jikinta ta bashi waje,ya taka hankali kwance kaman wani abu be tsikareshi ba ya fice a dakin.

Sulalewa tayi a wajen,sai wani sabon kukan ya tsinke mata. Tsoro taji yana shigarta,tsoron kada ya zamana fu'ad ya fara juyawa daga muhammad din data sani......zuwan mazajen yau da mata ke complain a kansu. Idan haka ta kasance a kanta bata jin zatakai labari.....don ta ta'allaqa dukka burinta da fatanta a kansa,ta karkatar da akalar rayuwarta a kansa,ta saka buri me yawa kuma akan nasa.

Tas taci kukanta ta godewa Allah,sannan ta miqe tana qarfafawa kanta gwiwa. Ta shirya abincin duka cikin wani kwando na daban ta haura masa sama dashi. Ba kowa a parlor din,tafi sanya ran wanka ya shiga,don haka ta jera komai tsaf saman dining ta wuce bedroom dinsa.

Kai tsaye ta murza handle na toilet din ta shige abinta gaba gadi. Cikin Jacuzzi ta hangoshi,ya sakarwa kansa ruwa wanda yake wanka duk kumfar daya sabawa jikinsa. Idanunta ta Maida ga bathtub din data cika masa d ruwa da kuma sassanyan turaren wanka,ba alamar ya taba ruwan ma bare akai maganar yayi wanka dashi,saita hadiye abinda ya taso mata ta nufi jazucci din kai tsaye.

Zuge qofar tayi,ta taka a nutse tana shigewa ciki. Ya ganta sarai amma bai waiwaya ba,yaso ace sanda bai shiga azumin fushi da ita ba ta kawo kanta a irin wannan lokacin,lallai da ya samu ganima.

Yana jinta ta gama tsokane tsokanenta bai nuna yasan tana ciki ba,ya gama ya nannade jikinsa da towel ya fito. Tana tsaye a nan kamar wata hoto har yabar toilet din,ranta taji ya soma baci,to amma ya zatayi?,duk ita ta jawo,ta tabbatar fushinsa lallai ba abu bane me dadi,tunda ya gwada mata ta gani.

Ko data zuba masa abinci ma cewa yayi ya qoshi baya buqata,ta san halinsa koda yana buqatar abincin ma ba lallai yaci,zaice bazaici abinci bane late,don haka ta shiga kitchen ta hada masa fruit salad me kyau da nau'un fruit din da basu da matsala ga lafiya da dare,a cisu kuma a kwanta.

"Ajiye a nan xanci" Ya fada kawai yana duba wasu file. Ajiye masan tayi,ta kuma sauka qasa tayi shirin bacci.

Still cikin wasu red night gown ta shirya,ta saki gashinta kafadunta yanzun bayan ta tajeshi daga curling nashi da tayi a dazu.

Sanda take kawo yaran zuwa gadonsa dake gefan dakin,yana kwance cikin duvet a qudundune amma tun shigowar farko sassanyan qamshinta ya ruskeshi har inda yake din.

Wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke yana runtse idonsa,bai taba kawowa zai iya jure wadannan kwanakin ba.......bai taba zaton yana da haquri a kanta har haka ba sai yanxu.

A nutse ta gama komai,ta sake musu addu'a,ta shiga toilet nashi tayi brush sannan ta hauro gadon tana rage hasken qwayayen dakin.

Ya jita kusa dashi sosai,amma bai taba kawo zatayi abinda tayin ba a yanzun. Wata kyakkyawar runguma tayi masa ta baya,cikakken dukiyar fulaninta da shayarwa tasa y qara cika ya tokare a bayansa.

Saura kadan numfashinsa yayi qaura daga gangar jikinsa,wasu irin kaifafan kibiyoyi ta sakar masa wanda suka ratsa sassan jikinsa d wani irin matuqar sauri suka aike masa da wani nannauyan yanayi daya sakashi takure jikinsa ba tare daya shirya hakan ba.

Matseshi tsam tayi ta baya,tana bashi wata kyakkyawar runguma. Har cikin jininsa sai da yaji yadda dumin jikinta da tudun dukiyar fulaninta ya zauna sosai saman fatar bayansa.

Sosai ya riqe numfashinsa don hana kansa jin abinda yakeji yana masa yawo a jiki,amma yadda zuciyarsa ke bugawa da sauti ya sanya ta kasa aiwatar da hakan,ya kamo numfashin da qyar sannan ya tattaro juriyarsa yana dan zamewa.

"Stay away please" Ya fada da wata irin kasalalliyar murya.

Maganan tashi tazo mata a bazata,tsam tayi da ranta tana dakatawa da komai,tana jjn yadda zuciyarta ke bugawa da sauri,tana kuma jin yadda itama a yau din take jin ta dokanta dashi.

"Hamma" Ta furta a sanyaye. Qarasa janye jikinsa yayi,sannan ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana dubanta

"I'm not in the mode,im feeling off" Ya furta muryarsa tana qara yin can qasan maqoshinsa. Idanunta da suka fara lumsheea ta ware tana kallonsa. Yau ita jadda yake cewa he's off?,off for what?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta ganshi ya dauki babban blanket nasu da pillow ya aza saman sofa ya kwanta abinsa ya lulluba har saman kansa.

Baki ta sake kawai tana kallonsa,abun gaba daya ya bata mamaki,yau ita abben su fauzan din ke yakicewa?,ita din yake dodging?. Wani matsewa zuciyarta dake qirjinta tayi,sannan a hankali wani hawaye me dumi taji kawai ya sauko mata saman fuskarta.

Da hanzari ta sauko daga saman gadon kai tsaye,ko bedroom slippers dinta batayi ta kai ba ta soma fita a dakin da sassarfa.

Komai da takeyi yana jinta,bai kuma motsa ba har sai da yaji fitarta,kunne ya kasa sosai,kusan mintuna biyar sannan ya yaye duvet din ya sauka a hankali yana fita a dakin.

Bata duka bedrooms din hakanan bata parlor din,abinda ya bashi tabbacin sauka tayi gaba daya daga sassan nasa.

Wani qaramin murmushi ya saki,qasan ranshi yana fadin ashe babu dadi. Maida qofar parlor din yayi ya kulle abinsa ya koma bedroom din duk da yadda zuciyarsa ke jin matsananciyar kewarta.

Yaran gaba daya ya sauke daga nasu gadon,ya maidosu kan gadon nashi,y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a bajesu ya shige cikinsu abinsa ya kwanta sosai yana sakin ajiyar zuciya,yana kuma jin kusancin dake tsakaninsa da yaran.

Kwata kwata bacci qaurace mata yayi,batajin zata iya jurar wannan abun. Yayi mata komai zata jure amma banda nesanta kanshi da ita,ita kanta cikin tsananin buqatarsa take,don ya riga ya horata ta wannan fannin ya kuma maidata irinsa. Abu daya ne ya sanyata ta guje masa stitches nata na CS dinta da take ganin kamar zai farke.

A haka bacci barawo ya lallabo ya saceta,cike da fata da sanya ran zai shigo har dakin ya nemeta,ko don saboda yaran ma. Sam baccin baiyi wani tsaho ba ta farka firgigit,ta shiga buda idanunta sosai tana sanya ran ganinsa ko yaran ko alamun ya shigo ya fita,amma bataga komai a ciki ba.

Ranta taji ya bacu,zuciyarta ta quntata,sai ta shiga toilet tayi fitsari ta daura alwala,ta dawo tayi nafila raka'a shida. Tana saman abun sallan tana addu'o'inta wani baccin ya sake waftarta,wanda shine bacci mafi tsaho da tayi,don bata tashi farkawa ba sai da akayi kiran farko.

Yanzunma bataga alamun ya shigo ba,kawai sai wata qwalla ta cika mata idanunta. Dama yake da ciwo kayi abandoning mutum?. Yaran sun tsaye mata a rai,tasan zai wahala ace duka tsahon daren ba wanda ya nemi nono,kawai saita sauka daga kan abun sallar ta soma takawa a hankali ta fice a dakin.

A Hankali ta bude qofar bedroom din,mamaki da haushi ya cikata fam kaman zata fashe. Wato shi ya sanya yaranshi a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login