Showing 174001 words to 177000 words out of 363280 words

Chapter 59 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1448

karma ta gyara....ni d'ana bazai auri mace daya ba ballantana ta samu daman juyashi da zaton nata ne ita kadai,don haka ka shirya........na zabar maka fareeda mazaunin matarka ta biyu......muna komawa da sati biyu kacal zaayi komai a gama.....don banajin tafiyarka da sabreen zatayi nisan zango,akwai canje canjen dabi'u da halaye da nake ji a tattare da ita" Sosai yake kallonta,ba kuma don komai ba sai don maganganunta masu kama da almara. Auren fareeda wannan yasan wani abune da bashi da maraba da tatsuniyar gizo da qoqi,uwa uba ma fareedan dukkaninta ba damuwarsa bace,don tana under control nashi,kowanne motsi nata yana sane dashi.....abinda kawai yaja hankalinsa shine zancan sabreen. Wanne sauyin halaye take ji game da ita?,meye dalilinta dukka na damuwa da al'amuranta?. Wanne laifi mutumin da baka jinsa ko ganinka yayi maka da zata dinga zarginsa da aza masa laifi kacokam haka?.

"Kar kayi kuskuren cewa zakamin gardama akan auren fareeda,nasani sarai shurunka yana nufin abubuwa da dama.....muna dab da muhallin amsa addu'a,zanje gaba ga Allah na roqeshi ya fiddamin haqqin haihuwarka da nayi" Idanunsa ya lumshe maganganunta suna sukarshi. Baisan me yasa ako da yaushe barazanarta iri guda bace a kansu,yadda ta damu da neman haqqin Allah a kansu bata damu da nema musu albarka haka ba?.

"Relax.....cool down.....badai fareeda bane matsalar?" Kai ta jijjiga

"Itace"

"Done" Ya fada da wata ma'anar ta daban. Shi kadai yasan me ya sake shiryawa me kuma zaiyi. Binta da kallo yake kawai sanda taci gaba da cin abincinta,yana hangen tarin sassauci data samu can boye cikin fuskarta da karbar zancan fareeda da yayi. Wani irin quna zuciyarsa keyi musamnan idan ya tuna duk wannan abun da takeyi fa siyanta fareeda kenan tayi. TO TA YAYA TA HADU DA SABREEN?,MENENE SILAR HADASU AURE DA ITA?,MEYE MANUFAR?. Wasu tambayoyi da suke masa susa a qirji,ya tabbatar tunda take muradin hadashi da fareeda bisa wats manufar.....tabbas haduwarsa da sabreen ma akwai manufa,saidai ita sabreen yasan bata da kudin da zata siya maamah.....to meye SILA?. Ba wadda ta fado a ransa a sannan sai hajja,a take kaman an cillota cikin tunaninsa,saboda muhimmancin abun a take ya ciro wayarsa ya tafa qaramin massage ya tura yana cewa.

_ina buqatar kowanne motsi na rayuwarta ya zama abun bi kafin na qaraso,bata buqatar kamu,amma ina buqatar ayi mata daurin talala_ sai daya tabbatar da shigar saqon sannan ya maida wayar aljihunsa.




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


91


Sosai maamah tayi amfani da wannan damar ta dinga karbar kudade daga hannunsa tana tsaraba. Baice komai ba don ba wannan muhallin bane,bai kuma hanata siyan abinda duka take so ba.


& *_makka to Maldives_*

Kwanaki shida sukayi a maimakon kwana biyu ko ukun da ya tsara zasuyi. Kusan ita ta dinga jan kwanakin duka a nufinta na tafi da tsarinta yadda takeso. Abu daya ne kawai yake dan bata mamaki,yadda take kasa samun wayar fareeda kwata kwata,ta gwada dukka layukanta amma ta gaza samunta,mamakinta yana sake daduwa idan ta irga kwanakin taga ko sau daya bataga gilmawar kiran fareedan ba.

Sun sauka Maldives dab da sanda rana ke shirin faduwa,wannan ya sake haska tsibirin ma'abocin ruwa da wani irin yanayi me daukan hankali.

Baki kawai maamah ke tabewa,a zahirin gaskiya ba zata ce island din baiyi mata ba,saboda guri ne da yafi kama da aljannar duniya,amma baqinciki da bacin rai suna cikata idan ta tuna cewa ahalin alhaji hamza suka zabi wajen. Ranta ya sake baci sosai cikin wani irin baqinciki da fushi sanda taji tsadar da rayuwa cikin tsibirin yake dashi,da kuma yawan adadin kudaden da ake kashewa kowanne kwana daya cikin resorts da sauran guraren dake kewaye da wajen.

"Nikam banga abun burgewa a nan waje ba.....guri duk ruwa,koda yake ba lafinka bane.....kai ka zama dan amshin shata ne kawai sai abinda aka tsara maka,kuma tsabar zallar mugunta ne saboda basusan zafin dukiyar ba,ba tasu bace......dolla million nawa ka kashe musu?" Ta maida tambayarta ga fu'ad dake zaune a gefanta cikin motar da Jordan yazo daukarsu.

Boyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana rufe idonsa gami da budesu,tunda yake bai taba jin kwanaki masu wahalar wadannan ba,wadansu irin kwanaki ne da sam babu armashi a cikinsu. Ya sanya ran samun nutsuwa daga wajen sabreen tun ranar farko data daga wayarsa,saidai kuma bai sake samunta a waya ba har yau da suke dawowa qasar.

"Farouq ne ya dauki nauyin komai" Ya bata amsar da azahiri haka take,gida ne kawai zai iya cewa nashi sai jet din da suka taho a ciki. Idanu ta dauke tana tabe bakinta.

"Haka dama zaka ce,saboda kana qoqarin basu kariya,ina jiye maka ranar nadamar damqa ragamar rayuwarka a hannun mutanen da basusan ciwon haihuwarka ba.....gefe daya ga matar da nake kyautata zaton zuwa yanzu sun hada baki da ita don su sake cimma manufofinsu" Gaba daya maganganunta baya qaunar jinsu,baya iya daukan kowanne mummunan kalami a kan ahalin alhaji hamza kibiya din. Sun masa komai a rayuwa,idan yace komai yana nufin komai din,don wataqila idan bacin su da yanzun baisan rayuwarsa a wanne matsayi take ciki ba.

Duk maganganunta yayi shuru yana jinsu,qananun mitoci ne da basu da tushe ballantana makama. Banda zata fassara abun da wani yanayi na daban tabbas da gida daban zai kamata tayi zamanta ita kadai,saidai hakan yasan ba mafita bace,ba abinda zai sake jawowa sai wani damuwan na daban.

Tun anesa ya hangi musaddiq da saddiq zaune daga gaban gidan. Sanye suke da kaya iri daya black jeans da white din t.shirt. Tsaf zakayi tunanin twins ne saboda yadda komai nasu ya kusan zama iri daya.

Sosai maamah ta qanqance idanu tana dubansu,wani irin abu yana tsarga mata

"Turqashi" Ta furta qasa qasa. Da alama ameenatu tana ci gaba da mamayar komai daya kasance mallakinta. A sanda hankalinta yayi nisa,ta dogara kuma da sabreen hakan sai ya zamana kaman ta bawa ameenatu wata qofa ko dama naci gaba da baza mallakarta tsakanin yaranta. Ba zata iya tuna watanta nawa bataga musaddiq ba,jininta.....tsatsonta,ya gaya mata fu'ad dinne ya aikeshi wani aiki dubai da Qatar,amma yanzun gashi tare da ameenatu,gashi manne da ahalin alhaji hamza kibiya.

Tsaiwar motan yaja hankalinsu su duka,motar ba baquwarsu bace don haka dukkaninsu suka miqe zuwa gaban motar.

"Barka da zuwa maamah" Musaddiq ya fada yana niyyar karbar jakar hannunta. Kasa jurewa tayi ta jefeshi da harara duk data sakar masa jakar.

"Uwarka ta taso daga wani gurin amma ka gaza zuwa airport tarbarta kana nan manne da uwar wasu?". Maganar ta masa ba dadi har hakan ya bayyana saman fuskarsa. Yadan basar yana amsar jakar sannan yace.

"Hamma ne.....bai bada assurance na yau din zaku taso ba".

" Barka da zuwa maamah ina yini?" Saddiq ya fada yana dan matsowa kusa da musaddiq. Waiwayowa tayi,ta aje masa wani kallo tun daga sama zuwa qasa kafin ta amsa masa sheqeqe tana bin bayan fuad zuwa cikin gidan. Koda riga ta gani a jikinsu baqincinta takeyi,gani takeyi kudin fuad ne ya siya musu wannan riga takalmi da kuma daular da suke ciki ma gaba daya. Tana ganin sunyi amfani da nasibin danta ne kawai suna morarsa bayan sun rabata dashi.

Tunda ta idar da sallar la'asar take manne da earpiece a kunnenta tana sauraron karatun littafin umdatul ahkam. Sanye take da Indonesian set skirt ne da hijab dinsu madaidaici sai rigar da iyakarta qugunta. Dark green ne da suka haska fatarta sosai,ta tattare gashinta ta daureshi tsakiyar kanta bayan amna ta gama jagwalgwala matashi da sunan zata mata kitso. Ta kasa kitson saboda santsinsa,don haka ta bisu da hair clips ta tattare mata shi,ita kuma ta daureshi da ribbons don tace ba zata saka mata hair ppin ba. Kayane masu taushi da sakewa a jiki,duk???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a anni ce ta saya mata su kusan kala shida.

A kwana biyar din sauqi ya samu sosai,ita kanta a jikinta takejin ta warke da taimakon wasu irin herbs 'yan Indonesia da anni ta bata.

A kwana biyar din ta wani murje,hankalinta kwance bata ganin wulgawarsa bare fargaba ta dameta. Hatta anni ta karanci yadda hankalinta ya sake kwanciya,ta daiyi murmushi kawai saboda tasan tsakanin miji da mata sai Allah,bare wadannan data fahimci yanzu ne yake fafutukar gina gwamnatinsa.

Batasan me za'ayi ba a gidan,don duka hankalinta yana kan karatunta,itadai ta shiga kitchen tana taya amna da anni girki. Annin ta fara fita ta barsu a ciki,amna ta fidda Warmers din tana shiryawa,ita kuma ta tsaya tana gyaran kitchen din.

Idanunta d'ai d'ai cikin parlor din tana kallon wata sabuwar duniyar. Fuad ya dauke idonsa a kanta yana sallama don sanar da anni da amna dake dining suna magana shigowarsu.

"Wa'alaikumussalam......marhaba da matafiya" Anni ta fada da murmushi saman fuskarta tana saukowa daga dining area din tana nufosu.

Tun bata qaraso ba maamah ta fara qare mata kallo,tayi kyau cikin super embellished me asalin tsadar. Kwanciyar hankali nutsuwarta da riqonta da ibada sun sanya wani irin kwarjini akan fuskarta gami da fidda ainihin quruciyarta,kai bakace itace uwa ga saddiq da farouq ba.

Tako ta ina sai take ganin annin ta fita samun duniya ne,wannan shine sirrin wannan kyan da take gani tattare da ita. Dom ta sutura tana sanya sama da suturar dake jikin annin a yanzu.

"Barkanku da zuwa.....saddiq ku dauki luggage dinta zuwa daki......me babban suna ya akayi baka bada exact time din da zaku sauka ba?" Anni ta fada tana dauke kai daga irin duban da maamah ke mata

"Na sha'afa ne anni.....amma gamu mun iso alhamdulillah" Yayi maganar yana shafa sumar kansa,gaba daya hankalinsa yana wajen amna yana tunanin ganin sabreen tare da ita.

"Alhamdulillah.....haka akeso ai.....bismillah Mariya mana kunata tsaye?" Anni ta fada tana jifan maamah da murmushi. Idanu maamah ta janye a kanta,tana jin wani abu yana tokare mata wuya. Yau ita akewa tayin zama a gidan d'anta?.

"Da baki gaggawa ba ameenatu,zama kam nina cancanceshi" Ta fada tana son maida maganar cikin yanayi na wasa wasa. Sosai maganar ta samu muhalli a zuciyar anni,ita kuma ta sani bawai da wasa mariya ke maganar ba,saidai koma meye ta shiryama zama da mariya din albarkacin muhammad fu'ad din.

"Zo mana amna" Anni ta fada tana kiran amna dake zaune kawai. Haka kawai takejin batason rabar matar......bata son yanayin kallon da take binta dashi. Qarasowa tayi inda annin take,ta sani sarai anni na iyayi mata fada don haka ta rusuna tana gida maamah data fidda mayafinta ta aje gefe da bawa kowa na wajen tabbacin tazo gurin data isa ne. Kaman yadda ta saba amsa musu gaisuwa haka ta amsawa amna.

"A gabatar mata da ruwa....sun sha hanya ita da hammanki".

"Karki kawomin zallar ruwa,lemo nake buqata da wani abun tabawar bawai dangin ruwa kadai ba" Daga amnan har anni ba wanda ya nuna yaji abinda tace,illa anni ta dubi amna

"Ki duba fridge kiyi warming pizza da samosa ki hado dashi". Kai amna ta gyada a sanyaye tana nufar kitchen din. Har yanzu ta kasa aminta da gamsuwa matar wai itace mahaifiya ga hammansu.

Gefe anni ta samu ta zauna tana gayawa kanta da kanta. Maamah ta cancanci kawaicinta kawai saboda fu'ad din. Sam sabreen bataji shigowar amna ba sai data gama hada kayan zata fita sannan ta riqota tana cire earpiece din kunnenta.

"Ki cewa anni an kammala,sai meye za'a dora mata?". Kai kawai ta gyada mata ta fice,tanason ce mata hamman ya dawo amma kuma yanayin sanyin jikin data tsinci kanta a ciki ya hana mata.

Sake daga kansa yayi cikin matuqar zaquwa yana sanya ran ganin fitowarta a kitchen din tare da amna. Saidai a yanzun ma amnan kawai ya gani ta fito. Iska ya zuqa sosai yana fesarwa

"Me take buqata dashi ne?,hauka take so ya fara gwada mata tuburan?" Ya tambayi kansa yana jin zuciyarsa tana quntata waje daya.

Sheqeqe maamah tabi tray din da amna ta shiryo,ta tabe baki wanda muraran duk wanda ya kalleta zai gani. Baya amna taja tana gayawa anni saqon sabreen,abinda yasa ruwan da maamah ta kurba yayi mata cak a maqogaro.

Juya zancen takeyi tsakanin rai da zuciyarta. Me haka yake nufi?,kyakkyawar alaqa tsakanin sabreen din kena da ameenatu?,yarinyar ke niyyar zame mata qadangaren bakin tulu ko.kuma ameenatun?,waye ainihin matsalarta a cikin su biyun?.

Ta bangaren fu'ad din sai ya dinga ji ransa yana sake baci....dole ya sake tabbatar mata ita mallakinsa ce,dole ya sake tuna mata muhammad fu'ad mijinta ne.....mijin da bazai juri qaurace masa ba.....mijin da bazai juri bada umarni tasa qafa ta take ba saboda raini.

"Kice ruwan zafi kawai zata dafa......ta fito ga baqi sunzo tazo su gaisa". Anni ta fada tana duban amna. Baisan ya miqe tsaye ba,shidai yaji yana gayaw anni

"Bari na samo warm water.....nasha sanyi a haram da yawa" Yayi maganar yana jin wani magnet yana jansa zuwa kitchen din,ba tare da ya tuna waye da waye a wajen ba.

Ajiye cup din hannunta maamah tayi tana binsa da kallo sanda yake takawa hankali kwance zuwa kitchen din. Tuni amna ta wuce dakinsu don ba zatayi gangancin komawa kitchen din ba tunda can hammansu ya nufa.

Wani mamaki yake kashe maamah tana daga zaunen. Ita din ba yarinya bace haihuwar jiya ko yau,ta sani sarai ita yabi....sabreena yabi bako shakka. Daga yanayin fu'ad din kawai tasan akwai abinda ke jansa zuwa can din,wani dakiya da shariya ta gani tattare dashi wanda bata taba ganin irinsa ba. Yadda yake tafiya zuwa kitchen din hankalinsa kwance kaman ba wani idon kunya a wajen?.

Sanda tayi nisa da binsa da kallo a lokacin anni itama tayi nisa da qare mata kallo da kuma fahimtar rudewarta da kuma canzawar yanayinta lokaci guda.

"Ya rabb......kasa addu'ar dana bata tsahon dare ina yinta ce ka amsa.....ubangiji ka sanya wannan mummunan qullin ka juyar dashi zuwa kyakkyawa". Anni ta sake jaddada addu'arta can qasan zuciyarta wani murmushin nishadi yana subuce mata.

"Tabbas kina dab da ganin yadda ubangiji ke jujjuya al'amura......kina kuma dab da samun ciwon hauka muddin akan Sabreen da fu'ad ne" Anni ta sake fada qasan ranta.

Ba jiya yau ko shekaran jiya ba take karantar duk wani motsi na fu'ad ba.....me babban suna ya canza gaba daya.....ya shiga wata gawurtacciyar koma ta soyayya wadda tayi imani shi kansa baisan girman abinda ya fada a cikinsa ba......karantar irin wannan yanayin kuma sai uwa ko gawutaccen masoyi.

"Zan shige daki na shirya.....naga magarib tana dab da isowa.....ga masaukinki can,a huta lafiya" Muryar anni ta dawo da ita daga rudanin data shiga. Bata sake cewa maamah din komai ba,saidai ta barta da kallon murmushin dake kwance akan fuskarta. Ita ba zata bari fu'ad ya fito ya sameta ba ballanta yaji kunya ko ya raga daga soyayyar da yayi niyyar nunawa matarsa ba.....ta barwa maamah ta fara kallon sample kafin anihin abun ya bayyana a idanunta gaba daya.

Idanunta ciki ciki tabi anni da kallo har ta isa dakinta.

"Ta ina kuma ameenatun ta sake bullomin?" Ta yiwa kanta tambayar zuciyarta cike da kokwanton murmushin data gani saman fuskarta.

_turqashi=??=??,anya maamah nan din gidan zamanki ne kuwa?_

_maji ma gani dai_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


92


A hankali ya tura qofar kitchen din sannan ya maidata ya rufe a nutse bayan ya karanci earpiece ne a kunnenta,sai ya maida bayansa jikin qofar kitchen din,ya goye hannayensa a qirji yana qare mata kallo.

Ta fidda hijabij jikinta ta saqaleshi a hanger na kitchen din don tafi jin dadin yin aikin,bata da damuwa kan musaddiq ko saddiq,dukkaninsu idan zasu shiga wani guri cikin gidan saisun tsaya daga waje sunyi sallama. Sassalkan gashinta da amna ta kame mata su da hair clips masu kaloli da shapes daban daban jelarsa ta baje sosai a bayanta. Baqi sidik ne yanata shining saboda ko da can ita din bame wasa bace da gyaran jikinta ma gaba daya. Idanunsa ya lumshe yana bin sauran sassan jikinta da kallo,qugunta ya bude sosai ta cikin skirt din dake jikinta,shape dinta ya fita sosai da duk wani sura na kyau da Allah ya bata.

"Ya salam" Ya furta qasan ransa saboda wani irin magnet dake fusgarsa zuwa gareta. Wani sashe na zuciyarsa ya raya masa inda wani tsakanin musaddiq da saddiq ne ya shigo a haka zai ganta?.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login