Showing 87001 words to 90000 words out of 363280 words

Chapter 30 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1423

kwashesu,ta tseratar dasu,amma dai bata sare ba,tana da sauran hope,don haka kai tsaye ta fara kiran number huda.

Kiran duniya computer ta gaya mata ta kuma jaddada mata wannan layin a kashe yake. Ta laluba wayarta kaf ta rasa number wayar bokanta tana me mancewa da cewa mutumin baya riqe waya,yo mutumin dake rayuwar tsakiyar dajin Allah ina gaya service ma bare waya ta dameshi?,mutumin da yake kewaye da aljanu,suke kai masa saqo kuma ku amso masa ko daga ina ne?,me zaiyi da waya?.

Hajja harira ce ta fado mata,ba bata lokaci ta danna number dinta tahau kira.

*Hajja harira*

Tun fitar laila bata iya tashi daga wajen ba,idan tace ta qulla tunani sama da dubu da kwancesu tsaf a wajen ba zatayi musu ba. Duk wani tunaninta idan yaje ya dawo a waje daya yake cakewa,tun tana neman qaryata abinda take zargi har zuciyarta ta gama yin ittifaqin amsar dai itace

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta furta da wani matsanancin tashin hankali. Tayi imani muddin abinda take zargi ne ya tabbata.....to lallai laila zata qare rayuwarta kaf wajen bautar maamah...... Asiri ne da bashi da makari sai mutuwa.....yaci uban bita zaizai,yafi uban tace saidai kafin tace. Ita mariya zata yiwa haka?,wannan shine sakamakon alkhairin da ita tayi mata?.

Kamar tasan itace a gaban tunaninta saiga kiranta ya shigo. Kamar kada ta daga amma kuma wani tunani daya darsu a ranta ya sanyata gyaran murya ta daidaita muryarta sannan ta daga din.

"Al'amura kamar suna shirin kwabewa hajja.....ina tsoron kada zancan mutumin nan ya fara tabbata......ki taimakeni hajja". Maamah ta fada da tsananin damuwa,damuwar data saka hajja taji wani bangaren na tata damuwar da tashin hankalin suna samun sassauci.....ko banza ba ita kadai ke cikin damuwa ba......ba kuma ita kadai zata ci gaba da zama a cikinta ba,taci alwashin dukka yadda zatayi zata yi don maamah taci gaba da tabbata cikin damuwar ta,waye ya gaya mata yaro yana wasa da kan maciji koda kuwa ya rasa abun wasa?.

Yanayinta ta daidaita don yayi dai dai da yadda maamah zataso taji,tana mamakin zallar rainin hankali irin nata. Bayan mummunar sakayyar da tayi mata,kuma wai ta nemeta da tata matsalar tamkar ma batasan me ya faru ba?.

"Me yake faruwa?"

"Garkuwata ta subucemin......daga yanzu zuwa kowanne lokaci zan iya fuskantar barazana daga wajen abun hari na,kowanne hope nawa kuma ya subuce hajja.....meye abunyi?" Ta qarasa maganar da sigar tambaya cike da damuwa. Iska hajja ta furzar tana dan bubbuga tafin qafarta kadan kadan,a nutse tace da ita.

"Bani lokaci mariya nayi tunani......mintuna kadan nake buqata". Jikinta a sanyaye ta amsa mata suna katse wayar su dukka biyun.

Wayarta take dan bugawa cikin tafin hannunta cikin salo na tunani. Mariya shegen kai ce,tana da nata matsanancin wayon da kai da kake rayuwa da ita kayi kadan ka fahimci komai idan ba ita taso ba.......saidai kuma a wannan yanayin da ake ciki mariya tana tafin hannunta ne. Bata isa tayi wani motsi cikakke ba ba tare da ita ba,itace ginshiqin.....itace kuma madogarar. To shin batasan abinda tayi mata bane?,batasan me ya faru ba?,ko tsananin iya bariki ce kawai?.

"Inaso na samu tabbaci" Ta furta tana daukar wayarta data aje tun daxun ta sake lalubar number maamah din.

Bugu daya tak ta daga,ta sanya wayar a kunnenta tana kiran sunan hajja.

"Duk abinda zaka daukoshi ko ka matso dashi don biyan buqatarka......kuma ya gaza yin wannan aikin sai nakega bashi da wani amfani,kau dashi kawai zaifi.....me zai hana ta gusa daga rayuwar fuad tun kafin matsalolin da boka ya baki a dunqule su fara bayyana har sufi qarfin shawowarki?....ga laila nan?,umarni na da naki sune zasu zama abun binta,a azata a bigiren da wannan ke kai,nayi Imani da laila......tabbas ba zata sabawa tsarinmu ba......sirrinmu kuma a lullube".

Nauyi maamah taji maganar tayi mata,sannan sam bataji maganar ta kama hankalinta ba. Har cikin jininta da zuciyarta takejin laila bata mata ba,kwata kwata bata dace da wannan aikin ba,bata dace ma ta zama matarsa ba koda na minti guda ne kuwa. Tasan wacce hajja farin sani,tana tunanin ita ko yaronta z??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????asu kubuta daga ayyukanta ne?,sai ta girgiza kai a fili tana jin abun bai kama hankalinta ba. To amma dole sai tabi ta takatsantsan kafin ta fahimtar da hajja din,tafi kowa sanin hajjan akan laila bata dagawa kowa da komai qafa.

"Aah fa hajja harira,laila ni dake duka 'yarmu ce......ba zamj jefata cikin wannan risk din da wahalar ba......qyale bare dai,wanda idan ya sabawa tsarinmu kowanne mataki zai iya fadawa kansa........kamar yadda itama wannan din MUMMUNAN SAKAMAKO na rantse miki da Allah zai yita bibiyarta......ba zan qyaleta ba,sai na banbance mata tsakanin aya da tsakuwa!" .

Turqashi!.....hajja ta fada qasan ranta,kai tsaye a bayyana ko a kaikaice maamah bata qaunar laila ta kafa tarihin zama matar muhammad me jadda.....wannan shine amsar tambayarta kai tsaye idan aka cire kauce kauce.

"Ke yanzun wanne shiri ne na gaba kike ganin ya kamata muyi?" Ta mata tambayar tana relaxing kanta don samun bakin zaren daga inda zata dasa nata aikin.

"Ki bari tukunna na samu nutsuwa daga wannan,abubuwa su hau kan saiti,zaki ganewa idanuwanki ba tare da nace dake komai ba". Ta fadi mata kaman yadda ta saba. Tana da boye duk wani shiri nata,zai wahala tana kan shiri ka sani,ko a baya wannan ne ya zama SILA da sanadin da LAILA ta shiga DUNIYAR lissafinta,qila data tsaya neman fashin baqi wajen boka kamar yadda hajja taso suji......ba shakka da qila yanzun haka laila bata fada wannan BAQAR MASIFAR ba....dukka hajja ke wannan tunanin cikin ranta tana jin wani bacin rai yana taso mata.

Hajjan ta bude baki zatace wani abu sautin kukan laila ya mamayi kunnuwanta daga cikin wayar. Wani abu ya daketa,tayi shuru tana sauraren tambayar da maamah keyi mata kafin kiran ya yanke.

"Tashin hankali!" Ta fada a sarari tana miqewa tsaye,ji take kamar ta wuce kai tsaye gidan maamah amma wata zuciyar na jan kunnenta

"Sai kinyi kamar baki sani ba......sai kinyi kamar baki fahimci komai ba,saikin maida komai ba komai ba". Wadannan maganganun suka sanyata rusuna ta koma ta zauna wuta naci gaba da balbala a zuciyarta. Daidai sannan nafessa ta shigo da mopper da broomstick tare da sallama a sanyaye cikin girmamawa.

"Ubanme kika shigo kiyimin?". Kai ta sunkunyar

"Kiyi haquri,haidar ne ya tashi da zazzabin haqori yau shi yasa ban shigo sharar da wuri ba". Duk da jikanta ne bata tsaya ta nuna kulawa ko alhinin komai ba,hasalima bata fahimci gaya mata take baida lafiya ba yaron,sai ta daka mata tsawa tana fadin

" Sharar da bakiyita dazu ba sai yanzu ko?,baqar munafuka,fita ki bani waje". Tashi sosai hankalim nafeesa yayi,take idanunta suka tara ruwan hawaye,tana tsoron me zata gayawa d'anta a kanta idan ya dawo,tanason aurenta batason ta kashe mata shi,wannan ya sanya ta sulale tana tsugunnawa ta soma mata magiya tana bata haquri

"Ki tashi bani waje kafin na rufeki da duka,sharar ce nace banaso ko ana dole?" A nan ta fahimci bawai iya rashin sharar bane kawai da ba'ayi ba ya sanyata haka,akwai wani abu na daban da ya bata mata rai,wannan ya bata sassauci sai ta miqe tana sake bata haquri ta bude qofar ta fita gami da rufe mata. A qasan ranta tana tafe tana addu'ar

"Ubangiji ka qara mata damuwa fiye da damuwoyin data sanyawa zukatanmu.......ya rabbi ka shagaltar da ita da damuwarta ta yadda zata zame mana mu kuma hutun da bamu taba samunsa cikin gidajen mazajenmu ba".

49


_Daga abi sa'eed RA yace:manzan Allah S A W yace; "idan dayanku yazo masallaci,ya duba takalminsa,idan akwai qazanta ya shareta ya kawar da ita daga jiki,yayi sallah da takalminsa_

*_halal ne sallah da takalmi a qafa,na haramci a ciki muddin ba najasa ko dauda a jiki_*



49


Ta furta har tsakiyar ranta tana jin ciwon bautar da suke ciki,wadda basusan ranar fitarsu a ciki din ba,sunfi kyautata zaton wataqila sai ranar da surukar tasu ta kwanta dama.

Ajiye wayar maamah tayi a gefanta tana duban laila da hawaye ya yiwa fuskarta shabe shabe

"Lafiya laila?,me yake faruwa?" Ta maimaita tambayar tana riqe hannunta

"Hamma fu'ad ne maamah......ya koreni". Fuska ta ya mutse tana duban lailan,tashin hankalin da take ciki a yanzun bata jin yakai korar laila daga gidan fu'ad,duk kuwa da cewa hakan da yayi taji ya tabata ya kuma qara bacin ran da takeji a ranta. Ya nuna bata isa ba kenan kamar yadda ta saba.....amma yanzun ba shine abinda ya kamata ta damu dashi ba.....tanason tasan ina yaran?.......ina suka shige?,meye manufar yarinyar?,meye takunta na gaba?.

"Kina da buqatar ki koma gidan?" Maamah tayi mata tambayar kai tsaye,don son tabbatar da maganar da sukayi da hajja a yanzun. Shuru lailan tayi,tana jin tamkar kowanne tsari na zuciyarta da kuma tunani na qwaqwalwarta ya birkice,tsare tsarenta......burikanta dama duk wani abu dake gabanta sai takejin yana sauya muhalli. Tanason fu'ad sosai......tana kuma jin soyayyarsa.......amma sai takejin zama da maamah yafi mata zama da fu'ad dadi......hakanan ko me maamah ta furta shine umarninta,to tabbas zata iya aikatashi komai tsanani da tsaurinsa.

"Inason hamma fu'ad sosai,inaso na aureshi.......kuma hajja tayimin alqawarin sai na aureshi....." Maganar sai ta zowa maamah banbarakwai,tayi mata saukar ba zata,ta xubawa laila idanu tana mamakin furucinta tare da tantamar lafiyar qwaqwalwar laila din.

"Tayi miki alqawari?,yaushe kenan laila?" Maamah data tattara dukka hankalinta akan lailan ta fada cikin tsananin mutuwa da kuma sanyin jiki.

"Tun sanda ake shirin auren hamma fu'ad.....ta kaini gidan na zauna don na karanceshi tsaf,sannan ta bani ayyukan da zan bashi yaci saboda jawo da hankalinsa kaina da kuma siyan soyayyata......wanda daga qarshe takeson ya dawo hannunta gaba daya".

" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Maamah ta fada tana jin saman kujerar yayi mata tudu da yawa,ba zata iya zama a kai ba duk da laushinta,sai ta sulale ta zauna sosai a qasa. Ta sake zubawa laila idanu sosai maganar na ratsata,amma kuma tana cike da tantama da tunanin cikakkiyar lafiyar kwanyar laila.

"Tabbas laila ta fara shaye shaye" Shine abinda maamah ke ayyanawa a ranta. Ba yadda za'ayi hankalin laila daidai......lafiyarta kuma qalau ta dauki babban sirri da labarin cikakkiyar cin amana irin wannan ta gaya mata.

"Don Allah kada kiyi fushi dani.....kome kike buqata zan miki maamah" Laila ta fada alamu na bayyana kuka nason qwace mata. Al'amarin ya sake jefa maamah a madaukakin mamaki

"Me kikeso in sake baki labari?" Laila da gabanta keta faduwa cikin matsanancin tsoron kada ta batawa maamah ta fada tana durqusawa a gabanta.

Mamaki ya sake kashe maamah,ta sake saka idanu ko zataga wani abu na tabin hankali ko hauka tattare da laila,saidai ko kadan bataga wannan ba illa tsantsar biyayya da faranta rai da takeso ta yiwa maamah din.

"Ki nutsu mariya.....ki nutsu,makashinka tabarmarka......makashinka yana tare da kai" Wata zuciyar ta ankarar da ita,wannan ya sanya ta aje mamakinta da tunaninta meke faruwa?,ta maida hankalinta ga laila

"Tashi ki zauna sosai muyi magana" Cikin hanzari ta miqe ta koma inda saitin inda maamah ke nuna mata ta zauna.

"Me yasa kika yanke hukuncin gayamin sirrinku ke da mamarki?" Ta tambayeta da matsanancin mamaki.

"Saboda ya zamemin dole na inyi miki biyayya.....inajin cewa ke din kamar uwargijiyata ce.....ni kuma baiwarki,inajin kamar dama can an halicceni ne don na miki biyayya,inajin komai zai iya samu na muddin ban miki biyayya ba......burina na mutu ina miki biyayya.....burina na mutu ina bauta miki". Ta qarashe maganar da zallar gaskiya da kuma yanayin da yake nuna cewa da gaske take furta maganar dake cikin ranta din. Kowacce tsiga ta jikin maamah sai data zuba,wannan shine kwatankwacin abinda take buri,take fata take kuma mafarkin taji ta kuma gani daga wajen fu'ad......ya akayi haka ta kasance akan laila.

"Laila......akwai abinda aka dafawa fu'ad a gidansa baici ba ke kika ci?" Ta jefa mata tambayar da zallar kokwanto a ranta.

Kai tsaye ta gyada mata kai tana dubanta

"Eh.....kwana hudu da suka wuce,naci abincin dare a dining dinsu"

"Shikenan!" Maamah ta furta tana runtse idonta,tayi tsam da ranta bata iya cewa komai ba. Tsahon wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,kafin kuma a hankali taji kowanne tashin hankali yana sulalewa daga zuciyartata. Idanunta ta ware akan lailan

"Meye shirinku a kaina.....meye shirinku akan fu'ad?" Tambayar data yiwa laila kenan tana da yaqinin da tabbacin zata gaya mata komai tiryan tiryan.

Shuru maamah tayi tana biye da laila din har ta gama kwashe mata bayanin komai. Ba bayanin yadda lailan ta zayyane mata komai bane yafi daga mata hankali ba,qulli da tuggun da hajja ta shirya qarqashin nata shirin shine abu mafi tsoratarwa da razanarwa a wajenta.

Don baje sirrinsu tasan zata samu information akan dukkanin abinda ya shafi hajja sama da abinda laila ta gaya mata ma a yanzu.....muddin wannan hadadden tanadin data yiwa fu'ad ne ya isa cikin laila.....to ko kashi lailan zatayi kuma take da buqatar ta shaida mata kafin ta yishi.....lallai ko bayan gida zai kashe laila ba zatayi ba sai da yarjewar maamah.

Take dukkanin wani alhini da fargabar cin abincin da laila tayi ya fice daga zuciyar maamah. Baqincikinta daya asarar data jawo mata,gagarumin shirinta daya baci,wanda ta kashewa maquden kudade masu yawan gaske don ta samu fu'ad a hannunta,yanxu samun laila me zai tsinana mata?,banda kaya da zata zame mata?.

Idan akwai riba guda da zata samu itace......ribar nunawa hajja kuskurenta na ha'intar qauna da aminci da tayi

"Lallai zan mulki laila ko don na nunawa hajja itadin qanqanuwar maciyar amana ce.....zan mulki laila a gaban idanunta.....zan kuma bautar da ita yadda take bautar da d'iyoyin mutane cikin gidanta".

Duk da takaici tashin hankali da baqinciki daya cika mata zuciya amma saita dubi laila da dan murmushi

"Zaki zauna dani?" Da sauri ta daga kanta tana jin kamar an mata rahama ne

"Zan zauna.....zan zauna dake maamah.....hakan yafimin komai dadi a duniya"

"Da kyau" Ta fada a hankali,dan daga murya tayi sannan ta kira daya daga cikin masu aikinta na gidan tace

"A bata daki" Ta bisu da kallo sai data tabbatar sun fice a falon sannan ta maida hankalinta cikin jikinta,

Iska me zafi ta furzar tana lula kanta cikin duniyar tufka da warwara......babu babban target dinta a yanzu haka idan ba sabreen ba. Bata gidan ta fita.....shine abinda ta yita nanatawa tana shafa lips dinta da yatsantsa. Da sauri kaman wadda aka tsikara ta jawo wayarta,ta tafi kai tsaye izuwa ma'ajiyar lambobi ta zarce can qasa.

A jere numbers din nasu suke,saidai kuma tayita kai kawo akan waye zata kira a cikinsu?,waye yafi zafin aiki?. Cak idanunta ya tsaya akan wata number da aka rubuta sunan HANZARI bata tsaya jinkiri ba ta danna kan number ta tura gaba izuwa kira.

Bugu daya tak aka daga,da wata iriyar birktacciyar murya ake fadin

"Allah yabar mana ke uwar dakina maganin kuka na". Wannan kirarin nasa yana fasa mata kai ainun,kuma ko a yanzun shi kadai ya bata tarin qwarin gwiwa

"Nayi missing target hanzari.......ka shirya ko da kowanne lokaci zaka iya jin kirana......idan kiran kuma ya tabbata......babban aiki nake da buqatar ayimin wanda daga shi bani da sauran haufi ko matsala"

"An gama uwar dakina" Ya fada da qatuwar muryarsa,bata jira komai ba ta kashe kiran,ta kuma maida akalar kiran nata zuwa ga number huda.

Abu daya dai ake sake gaya mata,layin a kashe yake,saita saita lokutan da zataci gaba da kira daga nan har zuwa awa ashirin da hudu,ta aje wayar ta kuma shiga tunanin meye abunyi na gaba?.


*MASHKUR*


A hankali ya sake gilmawa da motar ta gaban gidan,ba kuma wai don yana da wani abunyi ba ko kuma lalura ke sanyashi wannan zirga zirgar da yakeyi ba......aah,yana yine saboda nazartar gidan da kuma dukka wani kai kawo na jama'ar gidan dama ma'aikatan dake aiki cikin gidan daga dare har rana. Wadanda suke shifting da kuma wadanda zamansu kenan.

Yayi gaba,amma sai yaci gaba da kallon gidan ta rearview mirror yana kada kansa a hankali. Babba duk inda yake babba ne,gidan na daya daga cikin dream house dinsa daya jima yana tunanin idan har ya samu yadda yakeso a shekaru goma masu zuwa zaya mallaki irinsa. Hannunsa ya sanya ya daki steering din motar yana jin wani zafi cikin ransa. Yarinyar tasha dashi da yawa a rayuwa,banda wani abu daya rinjayi zuciyarsa tabbas plan A dinsa a yanzu shine zai zama plan B,plan B kuma shine a plan A,to amma duka wannan bazaiyi aiki ba......yana ganin gwara ya fara diban ganimar tukunna,idan yaso ko meye zai faru daga baya me sauqi ne.

"Ina fata ka gama kallon komai?" Yayi magana da mutumin dake zaune a back seat wanda zai wahala ka iya fahimtar da mutum a gurin.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login