Showing 51001 words to 54000 words out of 363280 words

Chapter 18 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1347

a kansa,hasalima a nata ganin waje ne da lokaci kawai take jira ta barshi. Abu biyu take gyarawa,bedroom dinta sai kitchen din da ba wani abun arziqi take dafawa ba. Tun ranar da tayi abincin safen nan rabonta da tayi wani cikakken abinci ta sawa cikinta,iyakar yunwa idan ta ciyota ta soya qwai guda biyu... Kota dafa indomie guda daya kota soya potatoes taci shikenan.

A kwanakin tana jin yadda qirjinta yake riqewa amma taqi damuwa da wannan bare takai hankalinta kai,abu daya kawai take jira ya dawo,tayi duk yadda zatayi ta cika aikin maamah ta samu freedom. Ta sani tana da wata fitinanniyar ulcer data kusa sanyata tabi bayan mahaifi da mahaifiyarta bayan rasuwar ummensu. Ulcer data samo asali daga matsiyaciyar yunwar da tayi mugun horasu,takaita matakin da take xubda aman jini. Ta jima rabon data tashi,tunda ta samu sassaucin rayuwa suke iya ci su qoshi,amma a kwanakin nan da take bata alamu taqi maida hankalinta sam sam.

&"Alhamdulillah" Shine abinda ya furta lokacin da ya fito daga toilet wanda ya barshi wata guda cur kenan.

Shirya kansa ya fara yi cikin butter milk color pyjamas yana tunanin kiran me sunan malam da ameh gobe kowa ya dora aikinsa a inda ya tsaya. Sam har ga Allah ya sha'afa da ita,abinda ya sameshi ya shafe abubuwa da yawa a kansa.

Gidan duka ya masa datti a yadda yake tsantseni da tsananin tsafta,ya kammala shirin nasa sai ya kasa saukowa saboda gajiya,ya bude freezer dinsa dake dining area dinsa na sama yana fatan samun wani abun.

Wuta ce 24/7 da kome zaka ajjiye a fridge din zaka sameshi fresh. Damammiyar fura ya ciro wadda ba komai cikinta daga nono din sai furar da aka markadasu suka hade jikinsu sosai. Furar daya samu ta masa daidai,don abace dame relaxing jiki da bada bacci me kyau da daddare saboda sinadaran da gero ke dauke dashi. Ta masa sanyi,baya kuma shan abu me sanyi sosai har haka,wannan ya sanya ya ajiyeta ya koma ya kunna tv don ya rage mintunan da zaiyi jiran furar.

Kadan kadan takejin kamar wani baqon sauti cikin gidan sanda take baro kitchen inda ta soya qwai guda biyu,tana taraddadin ci ma saboda maiqon dake jiki amma kuma batajin tana da wani abinciii bayan shi.

Fargaba taji tana cikata,wani irin matsanancin tsoro ya saukar mata. Sound ne tabbas wanda bata tantance na meye ba. To ko haurowa gidan akayi?,ko wani ne ya shigo ciki ya boye ba tare da sanin securities din ba?. Duka ba kalar tunanin da batayi ba,jikinta na rawa ta qarasa dakinta ta maida qofar ta rufe tana maida numfashi. Jin still da sound din sai tsoron yaqi barinta,ta taka da hanzari tabi duka windows din ta kulle sannan ta dawo tsakiyar dakin ta zauna tana raba ido tare da sauraron koma meye daga inda zai bullo.

Sai data masa daidai sannan ya kashe tv din,ya dauketa ya hada da cup da spoon ya wuce daki.

Sake kasa kunnenta tayi da kyau,a yanzu ba sound din,saita lumshe ido tana qoqarin saita nutsuwar kanta. Bata taba sanin kadaici masifa bane sai yanzu,bata taba sanin haka yake taba ruhi da rayuwar mutum ba sai yanzu. Wasu hawaye suka biyo ta lumsassun idanunta suka gangaro kan fuskarta. Gaba daya ta koma wata raguwa a kwanakin,zuciyarta kwata kwata ba wannan qwarin da tsaurin sai wani irin rauni da ya sake cikata,sai kawai ta kifa kanta saman pillow din ta saki siririn kuka,fried egg din da bata iya ci ba kenan.

&Bacci yayi sosai wanda da qyar ya tashi sallar asuba wadda duk tsanani zai wahala ta kubce masa. Koda ya koma yunwa ce ta tadashi,cikinsa gaba daya kamar an masa yasa. Yadan yamutsa fuska kadan yana tunanin me zaici?. Inda ameh yana nan ya tabbatar yanzun da yake qarfe sha biyu na rana ya gama breakfast yana jiran umarnin hada lunch da za'a kai company ko kuma ya jirayi zuwan dafa dinner.

Brush ya fara shiga yayi sannan ya fito,ya dauki wayarsa guda daya a ciki ya kunnata. Kamar jira akeyi sabbin saqonni suka shiga turereniyar shigowa,baibi takai ba ya lalubi number ameh,bai sameshi ba,yaja dan qaramin tsaki,wala'alla ya lalata wayarsa kaman yadda ya saba,waya bata fiya dadewa a hannunsa ba zakaji ta fadi ko kuma ta lalace,wannan dalilin ya sanya ameh din kansa baida cikakken number boss din nasa,wanda dama kusan duk wanda ya mallaki number wayarsa ya cancanta kuma yana da connection dashi nakai tsaye irinsu ameh din dame sunan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????malam.

Amna ya kira,bugu biyu ta daga.

"Hamma......barka da dawowa"

"Barka kade amna"

"Good morning hamma......ya hanya ya gajiya?"

"Alhamdulillah......ya makaranta?,kun fara shiga lectures?". Kai ta gyada

"Mun fara hamma......ba dadi hamma ba supporter.......BB farouq yace na cika shirme......ya saddiq tsokanana yake koda kuna nan......nayi missing ya musaddiq har yanzu bai dawo ba......please hamma kace ya dawo haka?" Ta qarasa maganar a shagwabe.

"Zai dawo soon" Ya furta badon yana nufin ya barshi ya dawo nan kusa ba. Tun tuni ya aike da musaddiq din wani aiki don ya nisantashi da maamah,bayason zamansa a nan ya tabbatar idan yana nan watarana maamah zataci galaba a kansa. Hakanan baison fitowa kai tsaye ya nunawa musaddiq komai akan maamah

"Allah ya dawo dashi lafiya....."

"Ameeen amneee......ki hadani da anni idan kin fito.....ki gayawa ameh lallai lallai yazo yau"

"In sha Allah hamma" Tana shirin tambayarsa sabreen ya ajiye wayar.....saita bari kawai ta shigo gidan da kanta tayi mata barka da dawowa.

Yadda taji yunwa na kama mata cikinta da gaske ya sanyata miqewa bisa dole. Yau kam sanye take da silk sleeping dress maroon color,riga ce iya cinya da wandonta dogo har qasa,saidai kuma tana da dan budadden wuya kadan. Duk da ramewa data danyi hakan bai hana rigar mata kyau ba,ta kuma zauna cif a jikinta. Jikinta ta jawo ta sauka daga saman gadon,tasa hannu ta tattare gashin kanta waje daya a qeyarta,ta taka a haka zuwa gaban madubi,ta jawo dan madaidaicin jewelry organizer din dake saman madubi ta budeshi,hair clip guda daya babba ta maqaleshi sannan ta samu vintage scarf ta daure kanta,wanda jelarsa dankwalin ta zauka kafadar hagu da damanta. Akwai socks a qafarta,wadda sanyin ac din gidan ya sanya dole take sakata saboda yadda marbles din yake daukan sanyi sosai,kwata kwata batasan ya ake controlling duka Airconditoners din ba bare ta daidaita shi,hakanan kawai take haquri. Sauqinta daya ana cikin yanayi na zafin farkon kasancewar damuna,banda haka ta tabbatar ba qaramar illa zatayi mata ba.

A nutse ta murda qofar,ta fara leqo da kanta tukunna tana tuna motsin da taji jiya,sai data tabbatar shuru wajen yake ba alamun komai sannan ta fara fitowa a darare tana sanda hannunta dauke da plate din soyayyen qwan.

Yau haka nan ya sauko da qafafunsa bai sanya takalmi ba. Fara tas din qafarsa dake da dogayen yatsu yake takawa a nutse yana sauka daga stairs din hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa ta William,yanason sake tabbatar da komai na company din yana tafiya lafiya lau.

Sanda ta buda qofar da zata sadata da parlor din farko ta sanya qafarta lokacin ya kusa da stairs din qarshe,wannan ya bashi damar ganin wulgawar mutum ba tare daya tantance waye ba.

Dan tsam yayi da ransa sai kuma yadan qara hanzarin saukowar don yaga waye ya gilma din,sam zuciyarsa na masa nisa da tuna tana cikin gidan.

Da wani irin sassarfa take qoqarin fita a falon ta sada kanta da falo na biyu na gidan ta boye kanta a kitchen. Murya takeji sosai tana sake kusanto inda take,tsoro ya sake cikata,kenan wani ne ya kwana a gidan akayi mata kwanton bauna?,har sai da akaji fitowarta sannan ya bayyana?. Ta shiga uku,su waye suka shigo?,abu daya ta sani ko zasu yankata su cinye ba wanda yasan sun shigo saboda tazarar dake tsakaninta da security din gidan.

Tana saurin isa ga kitchen don ta buya yana sassarfar shan gaban macen daya gani. Kusan dukansu sai abun yazo musu lokaci guda,yana dab da cimmata tunaninsa ya dawo kansa. Ashe yabar wata cikin gida......akwai yarinyar dake rayuwa cikin gidan,wannan tunanin ya sanyashi tsaiwa cak,tsaiwar tasa ta bata damar wucewa kitchen din cikin matuqar sauri ta maida qofar ta kulle harda murza key.

Qofar yabi da kallo yana zare wayar daga kunnensa. Mamaki kadan yana kamashi,anya qwaqwalwarta lafiya qalau take kuwa?. A nutse ya xura wayar a aljuhunsa yana dage kafadunsa cikin I don't care manner,sai kuma ya koma saman daya daga cikin kujerun ya zauna yana canza channel,kadan kadan kuma yana kallon falon. Ba wani tarkace bane ko wani abu a ciki,amma tsaftarsa bata masa ba. Ya saba duk inda ya wurga idanunsa ya ganshi fes yana qyalli da daukan idanu,amma a nan din idanunsa suna iya ganin qura a wasu guraren. Qaramin tsaki yaja can qasan ranshi yana fadin bazai dauki qazanta ba. Minti biyar yana jira yaga ta bude qofan amma ba alama,yunwa yakeji sosai,yana buqatar wani abu me nauyi da zai sanyawa cikinsa. Baya wasa sam da cikinsa,mutum ne me son lafiyayyen abinci musamman wanda ya dace da tsarinsa.

Miqewa yayi ya taka a hankali ya isa bakin kitchen din,har a sannan tana maqale bayan qofar tana tunanin yadda za'a yi ta kubuta daga hannun mutumin da batasan yadda akayi ya shigo gidan ba. Knocking din daya fara yi a hankali ya sake gigitata,ta qanqame jikinta guri daya tana runtse idanunta hankali a tashe. Sau biyar yana bugawar ba wani motsinta,ranshi ya sake baci,sai kawai yabar wajen yana takawa a hankali ya nufi wata qofa daban da zata sadashi da kitchen din ta baya.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862
5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_ZAFAFABIYAR_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

30


Jin an dakata da bugun ya sanyata sulalewa a wajen tana dafe qirjinta. Bata ankara ba hawaye ya balle mata,dama ta yaya za'a barta a gida irin wannan ita daya idan ba dama anyi shirin salwantar da rayuwarta bane da gangan. Tunda take a rayuwarta bata taba sanin tsoro na ainihi irin wannan ba.

Qofar data hanga ya sanya taji relief,ta goge fuskarta ta mmiqe a hankali cikin sanda tana nufar qofar ko zata samu wata hanya da zata fice daga cikin gidan zuwa bakin gate.

Tana miqa hannunta tana riqe handle din da zummar bude qofar daidai lokacin shima ya bude qofar da dan zafin nama,abinda ya sanyata ta biyo qofar takuma yi kyakkyawan masauki a jikinsa.

Dif shi da ita wuta ta dauke musu,ita gaba daya tayi mutuwar tsaye je zuciyarta na wani mahaukacin bugu cikin saddaqarwa kan ta shiga hannun koma waye......yayin da shi kuma ba zatar fadowarta jikinsa ya sanya komai ya tsaye masa can na wucin gadi.

Hannunsa ya sanya ya janyeta gefe yana hade rai da wani mugun miskilanci,ya hade girar sama data qasa yana dubanta sanda ta samu ta dafe kitchen cabinet din don ya taimaka wajen tsaiwa

"What's this?" Ya furta a dake yana hade rai. Can qasan ransa yana jin haushi haushi yana saukar masa. Da biyu ta fada jikinsa ko meye?,ko tsabar sabawa da hada jiki da wasu ne?,a yanzun an turketa kusan wata guda ba tare da d'a namiji ba ta kasa daurewa?.

"Ya kamata ki saita kanki,nan din ba irin sauran guraren da kika saba rayuwa bane....ki koyi controlling feelings dinki" Abinda yace da ita kenan yana takawa zuwa gaba hadi da miqa hannunshi yana bude drawers din sama.

Sosai ta tattara dukka dauriyarta da nutsuwarta ta dawo da ita gangar jikinta tana ta kokawar hadiye tsoronta. Wani irin takaici ya kamata bayan data fuskanci shine. Ya akayi tayi gangancin gaza gane shine ya dawo?,bacin rai ya hanata komai,sai kawai ta juya tana takawa zuwa qofar data kulleta da hannunta ta fara bude key din da wani irin zafin nama.

Duk da a rude take amma tasan sau biyu ta murza key din,yanzun ma sau biyun ta bude amma kuma data tura sai qofar taqi budewa. Sake murzawa tayi daya biyu har sau uku amma ba alamar qofar zata budu. Wasa wasa haka ta sake gwadawa amma jiya i yau,sai taji gudun zuciyarta na qara daduwa,don burinta kawai shine ta fita a kitchen din.

Tayi iya duka qoqarinta amma ko gezau qofan baiyi ba,wannan ya sanya duk wani karsashi nata ya sulale,ta zame hannunta daga jikin qofar zuciyarta fal da tunanin ta yaya zata juya tabi ta daya qofar bayan yana kai kawo a kitchen din yana harkokinsa?.

Duk wani motsi nata yana ankare dashi,har yadda ta dinga qoqarin bude qofar amma taqi koda motsi. Idanunshi jifa jifa a kanta sanda yake kai kawo tsakanin store din yana duba abinda zai iya sarrafawa da kuma dawowarsa kitchen din ya fara marinating kifi da zummar ya gasa shi,abinda ya manta rabonsa da yayi. Ya kammala cikin sauqi,saboda akwai komai kawai zubawa zaiyi ya saka a oven ya saita masa lokaci,sai ya saka din ya saita time ya koma ya jingina da kitchen cabinet din yana harde hannunsa a qirji yana jiran time ya cika yayin da yake sauraren voice note din da ya tarar daga William.

Da fari baiko kalli sashenta ba koda sau daya kuwa,amma a hankali sanda hankalinsa yayi nisa da sauraren voice din sai kunnuwansa suka sauko masa raguwar sautin yunqurin bude qofar da taketa yi.

A nutse ya daga idanun nan nashi dake da wani irin shape da yanayi me daukan hankali ya saukesu a bayanta daya fidda cikakken shape dinta saboda yadda kayan suka zauna mata cif da cif,daga kafafunta zuwa qugunta yayin da qugun zuwa cinyoyinta suka bude sosai suka bada wani faffadan qugu da yalwatattun cinyoyi.

Vintage scarf din dake kanta ya zame ba tare data sani ba,saidai yana maqale a wuyanta,wannan ya sanya har clip din kanta pink color daya matse gashinta ya rage tsahonsa da yawansa ya bayyana.

Baisan me ya maida idanunsa saman mazaunanta ba da suka bayyana sosai saboda silk material din dake jikinta,uwa uba kuma rigar bata qarasa rufe mata su ba. Abinda ya fara fado masa shine hirar amna da wasu qawayenta daya taba tsinta dake maganar maganin hips da sauran wasu hanyoyin qarawa mace hips.

"Ita dinma ba zata kubuta daga amfani dasu ba......" Ya furta a ransa bayan da zuciyarsa ta tuna masa wacece ita?.

"Allah ne yasan maza nawa ne suka taba kai hannunsu wajen,maza nawa ne suka taba taba wajen sukasan ya fadi da tudunsa yake" Wani mahaukacin tsaki daya cika kitchen din yaja,wani mummunan bacin rai yana saukar masa. Hannayensa ya saki kawai yana komawa zuwa bakin oven din yana jin zaman kitchen din yana gundurarsa. A duk sanda ya tuna iya shekarun haihuwarta a duniya da tayi kwata kwata na shekara ashirin da hudu cikin ta ashirin da biyar......da kuma adadin yawan mazan da akace masa takai qasa ko kuma ta taba mu'amala dasu,duk sai yaga ta masa baqiqirin,sai yaji wani abu ya tsaye masa a rai idan ya kalli koda gilmawarta ne

"Idan tasan me yawan sha'awace me ya hanata ta fadi gaskiyarta a gida ayi mata aure?" Ya sake rayawa a ransa.

Kwata kwata baya cikin jerin mutanen dake da ra'ayin riqau akan yaransu mata na sai sun gama karatu kafin a aurar dasu. Ya dauki izinina daga yadda yanayin halittarshi yake......wanda hakan yana daya daga cikin abinda ya sanya ya maida kwanyar da zata tsarta masa tunani na sha'awa a ransa cikin muguwar hidima da sabgar da idan ba mugun qaddara ba baida time da zata dauki wannan feeling din ta harba zuciyarsa har zuwa sassan jikinsa. Saboda kwata kwata bai shirya aure ba,totally mata basu taba burgeshi ba.....uwa uba bai tsara tsomasu a rayuwarsa nan kusa ba,saboda abinda yake kalla kusan dukkaninsu dukiyarka ko nasararka suke aure.

(Kira


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login