Showing 126001 words to 129000 words out of 363280 words

Chapter 43 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1368

Duk da tana da yaqinin baya nan,amma duk taku daya sai bugun zuciyarta ya qaru,kaman yadda numfashinta ke fita da nauyi.

Bude smart door dinsa bame wahala bane a wajenta,saboda tuntuni ya sanyata cikin sahun masu shiga kai tsaye.

Ko ina fes kaman yadda ta saba,yana fita da safe take shiga,tasan lokacin fitarsa,zai kuma wahala ya wuce wannan time din be fita ba,zata shiga ta kintsa komai. Duk da baya barin komai sai dan goge goge da qananun datti,bai taba barin underwears dinsa ba koda kuwa singlet nashi bata taba gani ba,abinda ma ya sanya mata qaramar nutsuwa kenan.

Bedroom dinsa ta wuce,tayi kuma amfani da details din da magaji ya bata ta dinga fiddo da komai,sai data hada shi tsaf sannan ta rufe briefcase da luggage din ta ajiyesu a gurbin da ta tabbatar zai wahala ya kasa ganinsa.

Yadda batayi zaton ganinsa ba haka shima baiyi wannan zaton ba. Batasan ya shigo saman ba kwata kwata. Ta zare idanunta daga cikin nasa idanun da yau take ganin kamar sun rusuna sunyi kuma laushi,can qasan ranta tana mamakin yadda ya balbalawa kansa A.c tayi qau a falon,abinda iya saninta dashi ba sabonshi bace. Idan kaga ya kunnata ma to tabbas ranan ana zafi,ko kuma bai samu irin fresh air din da yakeso ba.

Kanta ta dauke sosai ta fara takawa zata wuceshi,yau daya sai taji tana jin shakkar giftashi,koda kuma bata kalleshi ba tana jin kaman idanunsa a kanta suke.

Allah ne kadai ya sauko da ita,don bibbiyu bibbiyu take hada stairs din tana saukowa,tana jin kamar zai biyota yayi jan masifar daya saba,tana kawowa bakin bedroom dinta ta saki numfashi tana danne qirjinta.

Sai data bacewa ganinsa ya dauke kansa daga wajen yana maida hankalinsa kan wayar huda dake hannunsa wadda yakewa kallon wayarta. Tun ranar yake sake zurfafa bincike cikin wayar......amma kullum abinda zai gani a ciki taba masa rai yakeyi. Tarin massages na nuna zallar soyayya da kewa,zuciyarsa ba irin abinda bata raya masa yayi ba amma yana danneta d wani irin qarfi dashi kansa baisan yana da ita ba. Abu daya ke taka masa burki,cases din da zaiyi tafiya ya bari,amma ya tabbatar zuwa sanda zai dawo komai yayi settling......a lokacin zata kwashi kashinta a hannu,zaikaita ainihin kurkukun da itace asalin wadda ya tanadar mata.

Qarar wayarsa ya janye hankalinsa daga wancan tunanin,ya dauka yana dubawa don kusan duka saqon da zai shigo masa me amfani ne.

_ko a kusa ko a nesa duk inda zaka ina tare da kai,toshe kirana bawai yana nufin toshe soyayyarka daga zuciyata bane........ferree dinka ce_ ta saka sign na kiss da love daga qasa

Matse wayar yayi a hannunsa,yanajin bai taba jin tsanar wani abu a duniya ba irin yarinyar......tabbas tace zataci gaba da bibiyarsa nan da sati daya zai nema mahaifinta yayi magana dashi. Y janye diyarsa ya siya mata girman da ita ta gaza siyawa kanta.

&A daren washegari zai shigo mata amna tayi kawai da wata irin luggage da itadai idan tace ta taba ganin akwatin daya mata kyau irin wannan tayi qarya. Komai da matafiyi zai buqata an kammala mata shi an damqa mata a hannu. Wayar amna ta karba tayi kiran titi bayan ta zuba numbers din titin data rubuta ta aje saboda gudun bacewa. Har yanzu tana mamakin yadda wayar huda ta sake bacewa a dakin,saidai zuciyarta tanata qarfafa mata zargin shine ya sake daukewa.......don tun randa wancan incident din ya faru bata sake ganinta ba.

Magana sosai sukayi da titi din dasu huda,ta kira momma bahijja ma ta mata sallama,hankalinta ya kwanta sosai data samu yaqinin cewa kwana uku da tafiyarsu suma zasu isa mali,kunya tadan kamata sanda momma din ke tsokanarta honeymoon zasuje?

"Saura satittika kadan ya rage nima na biyo bayansu zuwa tushen mahaifiyata momma" Ta furta a ranta.

Sosai taji zuciyarta sakayau,hankalinta ya sake kwanciya,amma saita dinga jinta cikin wani kadaici,tana jin kamar ita daya tayi saura a Nigeria,saidai kuma tana jin sassauci idan ta tuna itadinma kwanaki kadan zata iskesu su sake shimfida sabuwar rayuwa me inganci tare.

_hmmmm,nace ko dama zata bada daman hakan?_


*_MALDIVES........_*


*KOMAI NISAN JIFA*=?G?

*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

68

*_Na muku post saboda jiran kwana biyu da kukayi,don Allah banason complain,dole zaa zo inda kuketa zakwadin>????&? @&?=?D?_


_Allah don isar mulkinka,don buwayarka,don girman soyayyar da take tsakaninka da muhammadurrasulillahi,dukkaninmu bayinka ne,amma akwai bayinka dake zaluntarmu suna fitar mana da pages,Allah kafi kowa sanin yadda muke wahala,mun killace haqqinmu bamu tilastawa kowa ba akan yazo inda yake,amma suna biyomu suna zaluntarmu YA ARHAMAR RAHIMEEN KAFI KOWA SANIN BAMU ZALUNCESU BA....YA ALLAH KO WACECE IDAN BATA DAINA BA ALLAH MUN GATA NAN,MUN KAWO QARARTA KOTUNKA ME ADALCI,YA ALLAH....YADDA TAKE TARWATSA MANA KASUWANCI UBANGIJIN SAMMAI DA QASSAI KA TARWATSA NATA KASUWANCIN,ASARAR DA TAKE JA MANA ALLAH KA NINNINKA MATA WANNAN ASARAR AKAN NATA KASUWANCIN DON ISAR MUHAMMADUR RASULILLAHI A FADARKA AMEEN_




*_REPUBLIC OF MALDIVES_*

*MAL?*

*Velana international airport mal?_*


Misalin qarfe hudu agogon Maldives wanda yayi daidai da qarfe takwas na dare agogon Nigeria private jet din mallakin Muhammad fu'ad jadda wanda ke dauke da sunan JADDA WINGS ya sauka a babban filin tashi da saukan jiragen sama na velana international airport dake babban birnin Maldives wato mal?.

Daidai sanda jirgin ya kammala tsaiwa gaba daya sabreen ta sauke numfashi a hankali tana lumshe idanunta gami da budesu kusan lokaci daya.

Wani abune da take ganinsa tamkar cikin mafarkanta,gata cikin qasar da koda sunanta sai lokuta d'aid'aiku ta taba jinta ballantana mafarkinta yakai ga zuwa qasar.

Tun daga kano zuwa lagos da suka sauka na wasu mintuna,kafin daga bisani jirginsu ya taso zuwa Maldives tasan tabbas duniya cike take da yalwa da fadi. Abu guda daya daya dinga bata sha'awa.....wanda ita kanta batasan abun na burgeta ba,sai data samu kanta tana fatan

"Allah yasa nan gaba kadan rayuwarmu ta kasance kaman haka....ni huda nadra haneefa". Bawai kalan arziqin jadda family bane abinda yaja hankalinta da gasken gaske ba....a'ah.....kalar qaunar juna.....bawa juna kulawa da kuma soyayyan juna da take gani a idanunsu irin na zallar 'yan uwantaka.

A tsakaninsu zata iya cewa ta zama 'yar kallo kome daukan rahoto,duk kuwa da cewa sunata qoqarin jefota cikin hirarrakinsu da kowacce magana data shafesu. Sau tari saidai ta murmusa kawai,tana karance da halayen kusan kowa a cikinsu.

Farouq nada tsananin kirki......yana da nuna kulawa da soyayya da 'yan uwansa,yana da wasa da dariya da 'yan uwansa.....amma mugun muskili ne kuma hutsu idan baiga dama ba.

Saddiq yana da zuciya,yana da saurin fushi amma kuma yana da saurin saukowa,yana da kula da damuwa qwarai da gaske da al'amarin 'yan uwansa.

Musaddiq dataji sunata waya dashi kafin tashin jirginsu,wanda a yanzu haka shi yayi landing ma a Maldives din,bazatace ga hali ko dabi'arsa ba,illa abu guda daya data lura. Shima me yawan nuna kulawa ga 'yan uwansa ne da damuwa dasu.

Sai oga boss muhammad fu'ad jadda.........shi kadai halinsa yasha banban ta kowacce fuska da 'yan uwansa......ta fuska daya sukayi musharakar halaye,wato ta fannin qauna ga 'yan uwansa......wata irin qauna da a fuska ba zaka ganta ba,hakanan a fili ba zakaga wani alamun damuwa ko kulawa da lamarin kowa bama tattare dashi,saidai kuma yana ankare da motsin kowa da kai kawonsu. Wani irin bahagon miskili da koda magana zaiyi saika rantse ya lissafe take,bayason lafuzansa kuma su qare,kaman tattalinsu yake,baya magana ya maimaita maka,kaman yadda bai fiya nuna damuwa ko zafafawa akan al'amura ba. Zaka dauka bai damu da komai ba,baya kuma kula da komai,saidai kaifin lurarsa akan komai tasha banban data kowa. Yana da wani irin fahimtar komai da kowanne motsi dake kewaye dashi,yana da kaifin lissafi,dogon tsinkaye da nazari kafin yayi magana. Ba'a kan komai kakeji yayi magana ba,ba kowanne abu bane zai kalla yace wani abu ba koda yana sane da wannan abun.

Dukkaninsu sunyi tarayya akan abu guda wato son anni......kowa a cikinsu wani unique love yake nunawa annin da qauna me tsananin yawa......takan shiga lissafi me zurfi idan maamah ta fado ranta,amma kuma idan ta tara da 'yan maganganun da amna ta fara yi mata,sai taga lallai komai yana da nasaba da wannan.

Ko yanzun ma da jirgin ya tsaya,saddiq nata fiddo musu luggage dinsu daga overhead compartment jordan na sauka dasu,shi kam sai a sannan ya rufe system dinsa da batasan abinda yakeyi ba a ciki tunda jirgi ya daga.

Tun zamansu daga lagos har kawo yanzu tana gabanshi. Tana jin farouq daya gaji da yadda ya bata hankalinsa yace

"Yallabai hutu fa zamu tafi,tun yanzu ka fara bata tsarin hutun?,ya kamata komai a ajjiyeshi a side ko?". Kai ya girgiza,kaman bazaiyi magana ba,sai daga baya ya daga idanunsa ya zubewa farouq dinsu

"Ba zaka gane ba.......koda na tafi hutu bazai yiwu har ta internet na tafi offline ba" Baki farouq ya tabe yana jinjina kansa,can qasan zuciyarsa shi yasan me yake tsarawa.

Jordan ne ya qarasa ya tattare masa dukka tarkacensa,yayin da shi kuma ya miqe yana zube hannuwansa cikin aljihun 3pices suit din jikinsa yana takawa gaban anni.

Duqawa gabanta yayi kadan yana gyara mata zaman takalmanta da take qoqarin sakawa.

"Ina fatan zaman jirgi bai saka ciwon qafarki ya tashi ba?" Murmushi ta saki,tana fatan yadda yake da tsananin kulawa a kanta taga yana yin sama da haka akan matarsa.

"Alhmdlh......last checkup din da mukaje ai sun bada dokoki,kuma na kiyaye alhmdlh......je ka duba matarka" Ta fadi tana miqewa hadi da ambaton bismillah.

A kunnen sabreen anni ta furta hakan,numfashinta yadan tsaya na wucin gadi,ta danyo rolling idanunta tana miqewa. Batason kowanne abu da zai hadata dashi ballantana ya gasa mata magana. Maganan daya gaya mata kafin tasowarsu daga lagos kadai ya isheta basai ya qara mata da wani ba.

Cikin ma'aikatan airport dinne,wani a cikinsu yaketa haba haba dasu ita da amna. Itakam bata kawo komai cikin ranta ba,don bata ma sake masa ba,amna ce kawai ke dan amsa tambayoyinsa,har zuwa sanda zasu wuce sai yace

"You look so familiar madam....." Ya fada yana dubanta da murmushi. A dan mamakance ta waiwaya tana dubansa,kafin kuma tace komai ya sake fadin.

"A abuja......hotel din....."

"Stop mr man!" Dakakkiyar muryar fu'ad ta dakatar da mutumin cikin kaduwar hanji. Sam baiga isowarsa wajen ba,mutumin tun dazu yake masa kwarjini.

Duqar da kansa yayi da sauri cikin rawar jiki yana cewa

"Sorry sir". Bai ko kulashi ba ya kalli amna,da idanu yayi mata sign na ta wuce,sai tayi qasa da kanta tana yin gaba. Ganin amna ta wuce itama saita taka zata bita,bai hanata ba,yabi bayanta shima,saidai ya gasa mata maganar da sai da qwalla ta diga ta samu sassauci

"Shi abun qwarai da mummuna tabo gareshi......mu'amala da tarin mazaje ba shine mutuntaka ba ta d'iya mace.... Mutuncinta namiji daya da zai amsa sunan mijinta,bariki bata da riba kota rana daya ce kuwa......duk wanda zai hada zuri'a da macen bariki saiya shirya......ba qaramin cutarwa bace ga 'ya'yan da zasu haifa idan aka ture nashi matsalan na qashin kansa".

"Macen bariki......mu'amala da tarin mazaje" Wadannan kalmomin su sukafi komai tsaye mata a rai.

Wanne irin mummunan kallo yakeyi mata ne wai har haka?,wanne mummunan fassara yake mata ne?. Tana ji ta soma gajiya,ta fara kaiwa iyaka,daga yanzu zuwa kowanne lokaci zata iya fashe masa.......ba zata iya ci gaba da dauka ko jurar irin wadannan tuhume tuhumen da maganganunsa da basu da tushe ba,tana jin zuciyarta da idanunta na mata wani irin suya,bata samu sassauci ba sai bayan da jirginsu ya doshi Maldives......hirarrakin family din da uwa me goya marayu wato anni ita ta sama mata relief a zuciyarta,saidai tana jin ta wani irin sake tsanarsa,ta kuma sake tsanar hada komai dashi.

Gabanta ya tako,abinda ya sanya amna gocewa da sauri tunda ita ke first seat da zummar yin gaba

"Karki fita......ki jirata" Ya fadi da husky voice dinnan nasa data sake dakewa,tun daga tashinsu daga lagos din bayan wancan abun daya faru zuwa yanzu tana ankare da hamman nata. Sai dacin rai kawai yakeyi wanda shi kansa baisan yana yi ba,jifa jita take satar kallonsa,har a sannan kuma ta tabo sabreen

"Adda........wai dama haka hamma yake da kishi?,daga cewa you look familiar?.....haka hamma yake sonki?" Ta fada tana murmushi kaman abun yana burgeta. Sau daya tak ta kalli fuskarsa sanda yake fama da system dinsa,saita maida idanunta ga window din jirgin tana duban yadda suke dai da daidai da gajimare. Abun yana burgeta,tunda shine karon farko data fara keta hazo......saidai can qasan ranta yana cunkushe da halayensa.

"Ba kishi bane.....izza ce wulaqanci da kuma izgili.....har yanzu banga wani kyakkyawan halayensa guda daya ba......koma dai meye saura kwanaki kadan suka rage na barshi shi da halinsa dama tarin dukiyar dake sanyashi dagawa izgili da girman kan ma" Tayi dukka maganar a ranta,amma a fili murmushi kawai ta yiwa amna. Amnan bata damu ba taci gaba da dauko mata gulmarsa kadan kadan,tunda ta saba da halinta na wannan fannin. Ba komai sabreen din ke bude baki ta bada amsa ba a maganganu da dama.

To a yanzun da yake tsaye a gabanta bata dubeshi,sam bata qaunar hada idanu dashi.

"Ko meye zakiyi a yanzu ki dinga tunawa akwai igiyata a kanki......bazan kuma lamunci kowanne abu da zai zama tozarci ga igiyata ba......zan iya daukan kowanne mataki mara dadi muddin kikayi wani abu daya sabawa shari'a......ki kula,ki kula da kyau". Kasa jurewa tayi,haka siddan daga saukarsu a qasar,kowa ya sauka da walwala itama ta samu ta fara tattalin tata zai watsa mata ita. Fararen idanunta ta daga ta watsa masa wani.kallo tsakiyar idanu. Wani haske suka fitar sosai saboda fushin dake cikinsu,wani salon kallo da baiyi kama da harara ba,shi kuma ba kallon banza ba. Ta motsa siraran lips dinta zata ce wani abu,sau kuma taga hakan baida ma wani fa'ida......bata da sauran lokacin batawa,don haka ta soma qoqarin rab'eshi ta fice.

Sosai taji an damqi hannunta da wani tsatsauran riqo,ta waiwayo da hanzari tana dubansa,ya damqeta ne ba tare da ya ko waiwayo ya kalleta ba,qeyarsa kawai take iya gani,da hannu daya ya jawota ya dawo da ita gabansa,ya sanyata a tsakanin idanunsa yana mata wani irin kallo da taji ya tsaye mata a sassan jikinta,ya kuma soma sauke rashin kunyar da taji tana taso mata

"Duk sanda kika ????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? sake gangancin wuceni ina magana.....na rantse da Allah sai na gwada miki ina da banbancin da lusaran mazan barikinki marasa daraja......dole ki amsa min kowacce magana kaman yadda nakeso.....don banajin muryarki tafi tawa tsada ko daraja.....ko banza adadin mazan da sukaji muryarki baikai adadin matan da sukaji tawa ba......kinjini?!" Ya furta da dan tsauri idanunsa na kallon wani gurin daban sabanin cikin idanunta

"Eh naji" Ta amsa a sanyaye kanta yana kallon qasa. Shigowar farouq ta gani daga bayansu,wanda ta tabbatar shi bai gani ba,sai ya sakar mata hannun yana juyawa gami da takawa a hankali yana ficewa a jirgin.

Hawayen da take riqewa ne suka yiwa kansu da kansu hanya. Ta sanya tissue tana daukesu

"Ya isa......ya isa" Take gayawa kanta da kanta. Tana cin alwashi a ranta ko ya bata takardarta.....ko bai bata ba,sauna sauka a nigeria zaman aurensu ya qare......ko ya sallameta ko bai sallameta ba wannan duka damuwarsa ce,alwashi ta ciwa kanta.....wannan karon babu abinda zai dakatar da ita......ba kuma wanda zai hanata.

A hankali ta fara takawa itama tana nufar qofa da shimfidadden matakalar da aka jinginewa jirgin. A nutse take sauka tana qoqarin daidaita mode dinta gudun saka damuwa a zukatan amna da anni.

Three pieces turkish gown ne a jikinta,wadda take hade da strips skirt da kuma blouse data zauna daidai jikinta,tayi kuma took in da ita kaman yadda tsarin kayan yake,sannan ta kawo doguwar gown din kayan me budadden gaba data sauka har qasa ta kuma bude sosai daga qasan. Qafafunta high hill ne masu madauri da suka dace da kalan rigan. Sosai kayan suka karbeta,baka ganin komai sai fuskarta,zaka rantse


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login