Showing 219001 words to 222000 words out of 363280 words

Chapter 74 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1447

Kallo take qare masa tun daga sama har qasa,ta kowanne fanni abun babu sauqi ne wai?,wai me yasa sabbin matsaloli suke sake kunno mata kai?.

"Anya ka samu isashen ilimin sanin darajar uwa kuwa?.....a ina ka taba ganin mutum yabar wajibinsa ya dauki mustahabbi?" Kasa cewa komai yayi,bayason ya fadi wani abu da zata tunzura taci gaba da zazzago maganganun da ya tabbatar anni tana ji,don muryarta a bude take magana ko wanda ke nesa zai iya jin sautinta,kasancewar garin gari ne maras hayaniya sam sam,albarkacin wanda yake kwance cikinta.

"To tunda nayi maka a daki bakaji ba......bari nayi maka a gaban kowa da kowa......ni mariya ahmad.......indai nice nayi cikinka watanni tara na haifeka.....na haramta maka zuri'ar hamza kibiya da ameenatu haramci na har abada.....idan ka sake nuna wani abu makamancin haka kuma ban yafe maka ba".

Idanu fu'ad dake qarasowa wajen ya runtse maganar tana hudashi,duk wani motsi nata qara bashi yaqini yake a kanta,tana sake haska mishi kanta da kanta tana fadada zargin da xai iya cewa qiris ya kusa zama tabbaci.

".......kaji na gay......" Ta dora da maganar da takeyi saidai kuma kasa qarasawa tayi sakamakon qwarewa da tayi da yawun bakinta.

Bawai tayi qwarewar Allah da annabi bane.....ba kuma ta qware bane haka siddan,abinda idanunta suka hasko mata shi ya janyo mata qwarewar ya kuma zarce mata da wani matsanancin tari daya sanya idanunta firfitowa waje.

Fu'ad yana takewa sabreen da qannenta baya kaman wani dan aikinsu......mutumin da shi kansa garada ne masu yawa suke gadinsa....... Saukar idanunta akansu huda ya qarasa dauke duk wata wuta ta jikinta na wasu sakanni. Ta ina yaran suka bullo?,daga wacce shiyya ko jaha?,ko duk cikin zallar iya barikinne na yarinyar?. To waima da kudin ubanwa sukazo madeena?,waye ya dauki nauyinsu?. Indai amsar dukanta FU'AD ne to lallai ta zaunar dashi ta karanta masa komai kenan a kanta?. Indai haka ne ai la shakka zataga wani sauyi ko alamu saman fuskarsa,to amma bataga komai ba.....wai ya abun yake?.

Tarin tulin tambayoyin da suka hana tarin lafawa da wuri,har sai da taji maqogoronta ya fara zafi,ta karbi ruwan da musaddiq yake bata ta kurba still idanunta akan yaran. A yadda suka rabu dasu rabuwar qarshe......bata nuna musu duk wani plan nata ba,tayi qoqarim basu gata da kulawa,a yanzun tana zaton zasu iso gurinta cikin fara'a da girmamawa ne kaman yadda yake a baya,saidai yanzun ga tarin mamakinta sun gaidata ne a tare......irin gaisuwar da zaka yiwa baquwar fuskar da baka taba ganinta ba. Bata iya amsa musu ba saboda mamakin da ya ciyota,ta bisu da idanu sanda suke motsawa gaba wajen anni suna gaidata.

"Ma sha Allah......aah 'yammata,lafiya alhmdlh,da alama kun rigamu sauke taku umrar.....nasan halin saddiqu da kyau,bazai bari ku zauna ba dama.......ga photocopy din takwara ameenatu......ma sha Allah,Allah ya yiwa rayuwa albarka" Dukka muryoyin anni suka dinga dukan kunnenta sanda suke haraman barin wajen bayan rarraba motar da kowa zai hau.

Madeena kusan ta zame masa muhalli,don haka yana da gidaje nasa na qashin kansa kyawawa har guda biyu. Ba wani gari a duniya da yake jin nutsuwar da ko jaririn dake cikin mahaifiyarsa baikaishi samunta ba irin madeena,ta biyunta makka,to amma yanzun saboda yana buqatar sabreen din ta huta sosai,sai yasa aka kama musu amenities a intercontinental Darr alhijra,saboda yafi kusa da masjid annabawi.

Duk yadda yaso ya kasance a motarsu sabreen din amma sai ya dage mata qafa,don wataqila akwai maganganu da suka shafesu da zasuyi a tsakaninsu daya kasance sirrinsu ne,don haka ya tura saddiq motar maamah su tafi tare,amna da anni,shi kuma ya karbi key da kansa ya kira musaddiq

"Shiga muje" Ya fada yana shiga mazaunin driver ya tayar da motar suna fita a nutse. Bayajin xai iya barin wadannan sakannin su wuce maganan dake ransa yana cizonsa,shi yasa da zafi zafi ya nemi kebewa da musaddiq din.

Shuru ya ratsa tsakaninsu har zuwa sanda suka dauki hanyar intercontinental,muryar hamman nasa ta masa saukar ba zata.

"Musaddiq"

"Na'am hamma" Ya amsa a sanyaye har yanzu muryar maamah tana bugun tunaninsa.

"Kanason amna?" Tambayar da bai bata tsammani ba ta fita daga bakin hamman nasa. Har wani firgicewa yaji yayi,yaji kaman baiji abinda fu'ad ya fada daidai ba.

"Nn...na'am hamma?"

"Nace kana son amna?" Ya sake tambayarsa idanunsa nakan titi yana sauraren amsarsa.

"Hamma.....amma hamma"

"Ba sunana na tambayeka ko nace ka maimaita ba......kanason amna?,eh ko a'ah?,banason wani sharhi"

"Ina sonta hamma" Ya amsa masa yana yin qasa da kansa a sanyaye. Kai kawai fu'ad ya jijjiga,bai kuma sake cewa dashi komai ba,yayin da yabar musaddiq din da saqe saqe a ransa masu yawa,ya matsu yaji hamman nasa ya sake cewa wani abu amma bai sake fadi ba,kuma tunda har mintuna sukayi nisa yasan ba lallai ya furta komai din,don haka yayi qarfin hali ya motsa.

"Hamma.....maamah ta fadi cewa bataso ta kuma r......." Wani kallo ya waiwaya ya watso masa duk da tuqi yakeyi sannan ya maida dubansa ga titi.

"Kayi magana akan abinda kowa yakeso da wanda bayaso amma banda maamah......bana buqatar komai nata ciki harda ra'ayinta da meye bataso da wanda takeso......abinda na sani kawai shine na sauke haqqinta na ci sha sutura muhalli da lafiyarta......sai biyayya akan abubuwan da basu sabawa mahalicci da kuma addini na ba.....baya ga wadannan komai a kanmu nata ba dole bane". Yadda hammansa yayi magana ya sanyayar masa da jiki,ya sani gaskiya ya fada....kuma koshi yana yaba masa yadda yake qoqarin bata girmanta.

Sun rigasu isa intercontinental din,don sanda fu'ad ke parking a parking lot na gurin ga motocinsu nan ajjiye,ya tsaida motar yace da musaddiq.





*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?



112



"Ka shiga ciki ina zuwa......ka fada mata zan shigo yanzu.....but idan naga tana kuka zan nesantata da kowa har sai ta daina". Har zuciyarsa abun ya qawatar da musaddiq,ya amsa masa a girmame yana bude motar sannan ya fice.

Da kallo fu'ad ya bishi har ya bacewa ganinsa,iska me zafi ya furzar daga bakinsa,ya sake yarda har yanzun shine garkuwar musaddiq,zai kuma ci gaba da zame masa garkuwa har sai ya tabbatar da cikar kamalar farincikinsa.

Hannu ya dora saman center console na motar ya dauki wayarsa,ya gyara zaman kujerarsa sosai yayi relaxing sannan ya soma lalubar number wayar abbansu wato alhj hamza kibiya.

Bisa jagorancin saddiq suka wuce amenity din,sannan ya nunawa kowa dakinsa. Amna dai da anni,nashi dakin shida musaddiq.....dakinsu huda suma su uku,sai dakin boss din nasu da duniyarshi......farouq ne ya zama shi kadai daban. Sabreen murmushi ta saki sanda suke bude dakinsu huda da sukace tazo taga wani abu,tana jin farouq yana balbalin masifa.

"Shi tuzuru dama abun rainawa ne......shi yasa aka wareni kaman wani barawo......duk wanda yayimin abu saina rama.....Allah ya kaimu lokaci,sati ukun ai kamar yau ne".

Idanu sabreen ta firfitar waje tana kallon matar dake zaune saman abun sallah.....momma bahijja ce cikin kamilalliyar shiga. Idonta ta murxa tana jin mafarki takeyi da gaske

"Qaraso sabreena.....mommmanki ce". Da gudu ta qarasa jikinta ta zube tana sakin wani irin hautsinannen kuka

"Momma duk kun gama birkitani.....kun gama bani mamaki,momma dama zakuzo?".

"Ko niyya babu me ita,duka aikin mijinki ne". Kalmar ta sauka sosai a zuciyarta,ta ruqunqume momma sosai tana hangen kamilar fuskar nan tasa. Wanne irin mutum ne shi me abun mamaki haka?,wanne irin mutum ne shi wanda ya iya nemowa abokin rayuwarsa maqurar farinciki?.

"Zazzabi kike haka sabreena?" Momma ta fada tana dagata a jikinta.

"Shine momma.....zai sauka,don Allah kada ki bari hamman nan yaji,tsaf zai sakani kwanciya asibiti"

"Kinsha magani?" Ta tambayeta cikin kulawa,kai ta gyada mata,duk da tasan ba wani magani da tasha tun a dubai,ta maida kanta ta kwantar saman qafafunta tana cewa.

"Ya akayi komai ya faru momma?,bani labari?" Ta furta tana riqr hannun haneefa da kyau cikin nata.

Doguwar waya ce da sai da suka shafe aqalla awa biyu ba kadan suna tattaunawa da alhaj hamza din,daga qarshe abban yayi shuru kafin ya sake magana.

"Na fahimceka muhammadu.......kuma na gamsu da bayananka da hujjojinka........amma me zai hana ka jira na qaraso nan din ko ku ku dawo gida?". Kai ya girgiza


" Kayi haquri abba.....bawai inason inyita musu dakai bane.... Amma karka manta annabi ya fada mana,ba'a jinkirta aikin alkhairi gaggauta yinsa ake"

"Na sani muhammadu banaso ka kirawa kanka matsala ne gaka kai daya" Murmushi ya sake saki yana yin gefe da kansa.

"Abba...ka manta muhammadu nake?....ka manta wannan me babban sunan?" Qaramin murmushi ya qwacewa Alhaji hamzan

"Ban manta ba kam.....jarumin gold daga qasar yarbawa da inyamurai" Wannan karon shi kansa fu'ad saida murmushinsa ya fadada

"Ka samu alhaj muhyidden,yana alranuna unguwar da gidanka yake......Allah yasa haka shi yafi alkhairi......amma kabi komai a hankali,idan akazo batun iyaye bin komai ake a sannu"

"In sha Allah abba.....na gode" Ya amsa masa yana jin wani farinciki yana ratsashi sukayi sallama.

Zaune kawai abban yayi da waya a hannunsa. Wanne irin yaro ne wannan Allah ya baiwa mariya amma har yanxu batasan baiwar da Allah yayi mata ba?,tabbas ahmadu ya dace da kalar yaron da yake zamewa mutum sadaqatul jariya bayan ranshi.....Allah ya gama masa komai......baisan wanne irin qauna yaron yake gwada musu ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana tashi

"Ubangiji yasa albarka albarkacin wajen......yasa kuma silar zuwan komai qarshe kenan a tsakaninsu".

Kansa tsaye ya wuce nashi dakin,so samu ace tana tare dashi a wannan lokacin.....to amma kuma yasan yanzu dole ne ya mata uzuri ya daga mata qafa,ya kuma bata dama sosai na ganawa da 'yan uwanta,don haka sai kawai ya rage kayan jikinsa ya shiga wanka. Tsaf ya shirya cikin jallabiyya,sai gashi ya juye sak balaraben madina. Wayarsa ya dauka ya kira saddiq bai sameshi ba,don haka ya kira musaddiq. Bugu daya ya dauka cikin girmamawa.

"Ka fadiwa saddiq ya shirya nan da thirty minutes mu wuce masjid.....banason wannan ragoncin naku"

"In sha Allah hamma......amma maamah tacemin idan ka shigo ka shiga tana son magana da kai". Agogo ya kalla,indai zai bata minti ashirin sauran lokacin zai ishesu tafiya,ya amsa masa da okay yana katse wayar.

Ya sani babu wani lokaci da kiranta ya zama na alkhairi,babu wani lokaci da kiranta ya zama me dadi,shi yasa ya yanke koma meye gwara yaje yanzu ya jishi ya tattara damuwarsa ya tafi masallacin ma'aiki da ita ya juyeta a can. Kafin ya fita ya duba number da abba ya tura masa,yayi kiran alhj muhyidden ya nema inda zasu hadu.

A girmame yace zai sameshi a masaukinsa,hakan ya yuwa fu'ad nauyi,don babba ubane a wajensa,don haka duk wanda ya jibanceshi yana masa kallon uba shima.

"Ka zabar mana guri,zan iskeka in sha Allah ko a ina ne". Nutsuwar fu'ad da hankalinsa ba wani baqon abu bane a wajensa,don haka cikin masallacin yace su hadu bayan sallah isha'i,ya duba lokaci sai ya yanke daga sallar la'asar din yayi zamansa har isha'i acan yayi jiransa,don yana da tarin addu'o'i daman da zaiyi.

"In sha Allah zan zauna ta babus salam". Ya fadawa alhj muhyidden.

A nutse ya dauki casbaharsa,ya sake feshi jikinsa da lallausan turarensa sannan ya saka wasu loafers masu taushi marasa nauyi ya fice a dakin.

Ita daya cikin dakin tunani kaman zai fasa kwanyarta,tana zaune daga gefan gadon,madarar almara'i ce a gabanta tana tsiyaya da kadan da kadan tana sha,don batajin abinci xai wuce ta cikinta. Kwata kwata jinta take kaman akan qaya,lissafin kwanakin da zasuyi a qasar takejin sun mata yawa sun mata kuma nisan da kamar ba zata iya jira ba.

Ganin yaran ya sake gigita tunaninta,tun sanda ta samu ta sabule yaran daga hannunta dama tana tare dasu?,ko wani gurin ta kaisu?,ya akayi suka kasance a nan gurin?.

Tunaninta ya katse sanda akayi knocking qofar dakin,idanunta ta daga ta kalli qofar,tasan ba kowa bane sai fu'ad din,murya a cunkushe tace

"Shigo" Qofar ya murda ya tura ya shigo,don bayan fitar musaddiq tace yabar masa qofar a bude.

Kallo daya yayi mata yasan dai kaman kullum ne,kaman yadda aka saba wani abu da ya shafi buqatar qashin kanta ya sanya ta kirashi,saman dressing mirror ya qaraso,ya dosana kadan ya zauna samansa yana dubanta.

"Gani" Ya fada a nutse yana shirya jin komai da zai fita a bakinta.

"Muhammadu......wai nikam duniya na haifawa kai ne?,wanne irin wauta da hauka kakewa rayuwarka?,sam ba ruwanka da tattala rayuwarka?,ba ruwanka da sanin ya kamata?,ka zama baitul mali ka maida kanka bayin wasu?". Dukka maganganunta tana yinsu ne cikin fada zafi da kuma daga murya. A nutse ya lumshe idanunsa sannan ya budesu.

"Yanzun me akayi?,me ya faru?" Ya tambayeta a nutse yana qare mata kallo. Bayason ranshi ya baci ko kadan,yanayin abubuwan maamah suna neman fara ta'azzara,shi daya yasan me ya adana a zuciyarsa daya shafeta,sirrika masu nauyi da tsanani wanda ita kanta batasan da hakan ba.

Ido itama ta zuba masa,saidai nauyin nasa idanun yafi nata,dole ta janye idanun nata. Tanajin zallar rainin hankali da wayo a al'amarinsa......tanajin wani irin ciwo da yadda ya gagara zuwa hannunta tamkar ba ita ta haifeshi ba.

"Tuni na dade da sanin ni din marainiyar wayonka ne........wadannan yaran daka debo meye alaqarka dasu da har ka fara barnatar da dukiyarka a kansu?" Ta tambayeshi a zafafe. Idonsa ya dauke yana qoqarin jawo sabuwar iska zuwa hunhunsa,al'amarin maamah yana daure masa kai maqura......tana yin abubuwa da zummar ba wanda yasan kalarta ta badini a nata hangen?.

"Maamah......nayi tunanin kece me bawa wani labarin alaqar dake tsakanina dasu ko?,a wajenki na fara sanin dacewar kulawa da qannen matarka,na dauka idan nayi hakan nima wani abune me kyau nayi?" Yadda ya amsa matan ya mata wata bulala data ratsata matuqa,shuru ya gifta tsakaninsu na wani lokaci,wani sashe na zuciyarta yana gargadarta

"Ki kula da dukka amsar da zaki bashi.....akwai.magana cikin maganganunsa". Abinda wani sashen yake nanata mata kenan.

" Muhammadu.....ka saurara da kyau ka jini,qannen matarka ko wani abu makamancin haka ba damuwata bane......ba ruwana da alaqarka dasu,bana buqatar wata hidima tsakaninka dasu,wannan maganar da gaske nake gaya maka ita,tunda kai ka zama abinda ka zama,bazan sanya ido mata su sakamin yaro a tsakiya sai yadda sukaga damar yi dashi ba......bazan lamunta ba,tun wuri ka saki dui wata hidima tasu,banaso na sake ji ko na sake gani muddin kana neman albarka daga wajena". Wata qaramar dariya ta taso masa amma.ya kwantar da ita ta hanyar lumshe idanunsa,ya jinjina kanshi da kyau mamaki yana sake cikashi.

"Kana jina?" Ta fada da mugun zafin da takeji a ranta.

"Maamah.....cikin arziqin da Allah yayimin......ina iya daukan dawainiyarsu data danginsuma gaba daya ba tare da komai dana mallaka ya samu matsala ba......dukka mutumin da ka kawoshi nan wajen yayi ibada kana da lada na musamman,duk aikin alkhairin da kayi asalinsa kana da lada daidai da wanda yayi aikin ba tare da an tauye ladan kowa ba.......maamah......tabbas inda albarkar uwa ita ke sawa yaro ya rayu.....ba shakka da tuni mun jima da amsa sunan GAWA,so inaga ba matsala bane ka zama silar sanya farinciki a rayuwar wani......dukiyarmu da kason wasune dole a ciki da ubangiji ya sanyata cikin tamu.....ya zama dole ka raba ka bawa kowa don fita haqqinsu da ubangiji ya dora maka.....ina fatan ba wani magana a ciki daya bata miki" Ya qarasa fada yana miqewa.

Mutuwar zaune tayi kalamansa suna bata mamaki me tsanani,kasa ce masa komai tayi har ya fara takawa zuwa qofa.

"Muna kusa da masjid nabawi,dukka sallolinku zaku iya qarasawa kuyi a ciki.....ni na wuce sai zuwa dare" Ya qarasa fadi yana ficewa cike da fatan kada ta sake cewa komai din bare ya tsaidashi.

A bakin elevator ya samu su musaddiq,sai kawai suka wuce zuwa masallacin. Suna tattaki a qafa yana sauraren hirarrakinsu,yayin da nashi Hankalin yayi nisa zuwa wani guri na daban.


&Sau uku tana juyawa tana qare musu kallo cikin daren,idanunta duka suna tsakanin huda nadra da haneefa da kuma momma bahijja dake kwance saman nata gadon.

Tashi tayi ta zauna sosai,zazzabi takeji yana sake qaruwar mata,ko amai din sai data sakeyi dazu amma bata bari kowa a cikinsu ya gani ba,saboda wannan farincikin da wannan walwalar take so taci gaba da gani saman fuskarsu,batason ganin komai da zai bata wannan yanayin.

Hadewa jikinta tayi waje daya tana jin sanyi,yayin da can qasan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login