Showing 315001 words to 318000 words out of 363280 words

Chapter 106 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

6547

daina fita ba

"Ko bayan an cuceka ka yafe.....ba zaka ragu da komai ba sai qaruwar daraja a gunka......ki yafe mana indai mun miki laifi muddin kedin ke kika haifemu" Ya qara fada yana hade hannayensa waje daya alamun roqo.

"Indai kun yadda ni din nice na haifeku me yasa ba zaku yimin abinda nakeso ba?,indai kun yarda nice na haifeku me yasa ba zakubi umarnina ba?,me yasa ba zaku kwanta nayi muku mulki irin na isassun iyaye ba?,me yasa ba zaku fahimci asiri akayimin ba?,me yasa ba zaku gane ba hawan jini bane wannan?!" Wadannan sune kalaman da suke ta kokawa a qirjinta suke koma neman hanyar da zasu fidda kansu,saidai kuma ba wannan damar,illa hawayen baqincikin rashin samun damar magana da batayi ba da suka sake wanke mata fuska.

Tsam ya miqe kawai,ya kama hannun amna da jikinta ya sakeyin laushi qwarai bayan aman da tayi,ya miqa mata takalminta ta sakawa qafafunta suka fice a parlor din sabreen da maamah na binsu da kallo,kowa da mabanbancin yanayi cikin zuciyarsa.

Tausayin musaddiq da hammanta kullum take kwana take tashi,bata tunanin duk yadda sukaso maamah ta shiryu idan har ubangijin daya halicceta bai shirya mata hakan ba saidai kowa yayi haquri. A zuwan da take dubata da duba yanayin gidan da masu kula da ita.....ba kalan lokutan da bata kebe ba zaune da ita,daga ita sai maamah din ta karanta mata dukkan kalar wata nasiha me ratsa jiki da zuciya......amma bata taba ganin alamun rusuna ko sanyi daga idanuwanta ba.

&"laila" Hajja harira ta sake kiranta karo na biyu. Daga kai lailan tayi wadda ke zaune qasan carpet din dakin ta kalli mahaifiyar tata.

"Na'am hajja" Ta fadi dukkanin wani lungu da saqo na zuciyarta dama gangar jikinta suna azalzalarta,tana jin kaman wuta ake hurawa sassan jikinta dama zuciyarta.

"Wacece ni?"

"Mamana ce" Ta amsa mata Kai tsaye idanuwanta kafe a kanta.

"Alhamdulillah" Hajja ta fadi tana sakin murmushi. Cikin zuciyarta cike fal da godiya ga bokan da yayi mata aikin farraqu tsakanin maamah da laila,ya gaya mata cewa wannan din qaramin aiki ne da zai iya aiwatarwa,ya mata alqawarin sai yazo duk duniya ba wanda laila taqi jini taji koda sunansa sama da hajiya mariya.

"Zaki koma wajen maamah mariya?" Hajja ta gwada tambayar laila. Shuru ta danyi na wasu sakanni,sai kuma ta girgiza kanta da qarfi.

"Bana so,bazan koma ba,ina wurin hajja na". Ta fadi bawai don tana nufin abinda ta fada din bane da gaske har zuciyarta.

Da dariya ta qyalqyale sosai,farinciki yana cikata,lallai laila dinta ta dawo,ta dawo hayyacinta.

" Na godewa Allah daya dawomin dake hayyacinki laila" Murmushin qarfin hali ta sakarwa hajjan,tanason ta sake bata tabbaci da yaqinin ta warke don ta ware mata takunkumin hana fita da sanya masu gadi su hanata fita ko nan da can. Ba abinda takeso irin taje wajen maamah,ta duqufa tayi ta mata bauta iyakar qarfinta.

"Na warke hajja in sha Allahu,kawai zaman cikin gidan nan ne hajja na gaji.....ko cikin layinnan kya barni na tattaka da qafafuna ko?" Ta fada a shagwabe kaman yadda take mata a baya.

Fuska hajja tadan bata tana dubanta.

"Aah......ba yanzu ba laila,matar nan makira ce,duk da ance tana can tana jinya amma ba Allah a ranta,kina kallon yadda take kidnapping 'ya'yan jama'a fa?" Hajja ta fadi tana nunawa laila girman ta'addancin maamah.

Wani irin tashin hankali da kuma bacin rai ne suka bijirowa lailan,ta tabbatar yau ko gobe Hajja ba zata barta ta fita ba bare ta koma wajen maamah,kenan ba amfanin rayuwarta ba tare da maamah ba?". Ta yiwa kanta wannan tambayar.

A take taji indai za'a yanke alaqarta da maamah bata da wani amfanin rayuwa,don haka ta miqe tsam.

"Bari naje kitchen nasha ruwa"

"Ki tahomin dashi" Ta fada hankalinta kwance don tasan a kitchen din dai ba wata hanyar fita daga sassan ma bare akai ga gidan.

Idanu kawai take warawa sanda ta shiga kitchen din,gaba daya kwanyarta a birkice take,neman abinda zatayi amfani dashi kawai take yi idanunta suka sauka kan gas.

Da sauri ta qarasa wajen,ta saka hannu ta kunna dukka makunnansa guda hudun da yake dasu. Fita ya fara yi sosai,kafin kace meye wannan warinsa ya mamaye kowanne sashe na part din hajjan.

Hancinta sosai hajja ta dinga budewa tanason tabbatarwa warin gas dinne?. Da wani irin sauri ta duro daga saman gadon tayi kitchen da mugun sauri. Duka masu aikinta ba kowa yau ballantana tayi tunanin wani ne a cikinsu,laila kawai tasan ta shiga kitchen din.

Cak ta tsaya daga bakin qofar falon,qafafuwanta suna rawa zuciyarta na wani irin gudu mara fasali. Laila ce tsaye a kitchen din riqe da lighter,idanuwanta fes kan hajja dake tsaye daga can bakin qofar kitchen din.

"Laila.....laila baki da hankali ne!!!" Hajja ta fadi a birkice ganin lailan tana qoqarin motsa yar robar data tare bakin lighter din wadda ita zata bata damar tashi. Wani kalar murmushi ta saki tana duban hajjan

"Kina tunanin zan iya rayuwa ba tare da umarnin maamah ba?,ko kina tunanin zan iya rayuwa a inda babu ita?.....sai watarana hajja" Laila ta fada cikin qwarin gwiwa.

A gigice hajja ta bude baki tana son gaya mata cewa.

"Kada ki kunna laila.....indai mariya c na bar mata ke har abada,ki hada kayanki ki koma gareta" Saidai dukka wadannan kalaman basu samu damar fita daga bakinta ba sai hucin tsananin atsabar zafin wuta da qarar bindigar fashewar tukunyar gas din da suka cakude waje daya aka wullota waje,wanda daga nan bata sake sanin abinda yake faruwa ba.

Qarar fashewar taja hankalin sassan matan 'ya'yanta da masu gadi dake waje,kafin balbalin wutar ya tashi hankalin kowa suka nufo sashen hajja din.

Duk saurinsu turus kowa yayi,saboda wata irin muraddiyar wuta ce me azabar duhu da Zafar tana harshe ke cin kowanne sashe na hajja din. Babban sashe da yafi na kowa cikin gidan girma kyau da tsaruwa,sashen da idan ka kalleshi ka kalli na matan 'ya'yanta saika dauka su din duka sashen ma'aikatan gidanne wato boys quarters,duk kuwa da cewa mudin na mazajensu ne,dasu akayi wahalar nema da kuma samu.

Tashin hankalinsu waye da waye a ciki?,suna tsaka da son tantancewa sukaci karo da hajja yashe a qasa,wadda babban jikanta ne kawai ya iya gane itace,saboda shi dinma ya shiga dazu kai mata wankinta ya gane atamfar jikinta,fuskarta kaf da kafadunta zuwa qirjinta sun koma jazur kaman an shafeta da jar hoda saboda yadda wutar ta kwaye asalin fatarta.

"Na shiga uku......wayyo Allah na..... Wayyo laila......laila kada ki mutu ki barni......laila bansan kanki abunnan zai koma ba,wallahi laila bake nace a bawa kici ba......laila don Allah ki fito laila......naci buri a kanki,na shiga uku" Sune maganganun data dinga fada tana ihu tana kururuwa gami da zabura,azabar zuciya dana gangar jiki duka sun isheta aka wuce da ita asibiti cikin ambulance bayan anyi kiran fire service suzo su tsaida watar kada ta soma lasar sassan gidan.

Abun kamar film kamar almara,ana fita da hajjan sanda wutar ta cinye sassan sarai,surukanta dukka dake tsaye a wajen sai kowacce ta dafe kanta.

"Wayyo Allahna.....wash Allah na.... Wayyo kaina" Shine abinda suka fara fadi a jejjere,kafin kace meye wannan sai gasu duka su ukun a zube warwas a qasa sun sume.

Akwai wani malamin makarantar almajirai dake a wajen,kallo daya yayi musu yace basai an kaisu asibiti ba,babban falon gidan yasa aka ajiyesu,ya karbi ruwa yayi musu tofi sosai ya bawa mazajensu yace a yayyafa musu idan sun farka a bawa kowacce tasha.

Cikin qasa da minti biyar sai gasu a zaune,kowaccensu kuka takeyi wiwiwi

"Wallahi saika sakeni......wallahi bazan sake zaman bauta ba..... Idan ta dawo kuma me ya rage mata?,inajin sujjada zata saka mu koma yi mata" Shine abinda matan kowacce ke gayawa mijinta cikin kuka. Duka falon sai ya rikice,ga gobara a waje ga tashin hankali a cikin gidan,su kansu mazan a rude suke,don sam duka abinda matan ke iqirari akai ba wanda yasan anyi a ciki.

Gyaran murya malamin yayi ya kuma nemi su bashi hankulansu. Bayani ya musu me ratsa jiki game da lamarin,kusan abune da kaf unguwar ake magana akai yadda take bautar da uban kowa cikin gidan,kusan duk me hankali yasan aikin sihiri ne.

"Indai har zaku yarda da shawarata ku yafewa mazanku,ku sake sabon zama dasu don ba cikin hayyacinku dukka kuke ba,wataqila wannan gobarar ta qone duk wani binne binne ne shi yasa komai ya warware kansa.....sai ku bita da addu'a Allah ya bata lafiya ya sake fahimtar da ita ainihin rayuwa.....". Da wannan bayanin nasa ya kashe wannan qurar,hankula kuma suka koma kan wutar dake ci wadda an fara samun daman kasheta.
157


&Tana kwance saman kyakkyawan gadon,sanye da fara qal din abaya har veil din da tayi rolling dashi,kaman yadda siraran abun hannun azurfa da zobensa da set din dan kunnensa suka sake qawata mata shigar tata.

Duk da tsufa da nauyi da cikinta yayi hakan bai hanata ado ba......duk da yadda take komai da qyar amma bata yarda ta bari tayi mummunan kama ba.

Ko a yanzunma akan gadon scanning take,daga daidai kanta kuma muhammad fuad jadda ne. Sanye yake da farar jallabiyya ta maza saqar morocco wadda ya yiwa ado da farin hirami daya zauna sosai a kansa,saika rantse da Allah dan asalin qasar saudiyyan ne. Wani irin ajiyayyen kyau na musamman shigar tayi masa,jikinsa da fatarsa dukka suna nuna zallar hutu da jin dadi gami da cikakken sukunin rayuwa da Allah ya bashi. Saman kujera hake,hannunsa cikin tsakiyar tafin hannunta,ya sarqafe yatsunta cikin nasa.

Daga shi har sabreen din idanuwansu suna kan allon computer din,wanda balarabiyar ke yawo da kan na'urar saman cikin sabreen din da yayi wani irin girma.

Sai data kammala scan din tsaf,sannan ta dora hannunta saman board din computer ta danna tana maidashi 3D scan gami da cewa cikin harshen larabci.

"Sa'ureekum shai'an" Ta fada tana murmushi.

"Na'am" Ya fada yana matse hannun sabreen cikin nasa. Maida mouse din tayi saman cikin sabreen din,ta matse hoton cikin take yara guda uku suka fito sosai.

"Allahu akhbar.......subhanallah" Fuad ya fada muryarsa tana rawa. Damqe hannunsa sosai sabreen tayi itama cikin nata,ta kasa magana kaman yadda fuad shima ya kasa cewa komai face tasbihi ga Allah buwayi gagara misali. Yaran na kwance irin kwanciyar jarirai uku cikin mahaifiyarsu,kamanninsu sosai ya fito,har ya dinga jin kaman ya saka hannu ya daukosu.

Cikin qwarewa take juya na'urar tana zoom in musu yaran daya bayan daya. Qosassu kuma lafiyayyu ko a ido,wanda ko daga yanayin girman cikin sabreen din shi kansa yasan qosassunne,duk da akance abun ba daga girman cikin bane.

Murmushi ya subuce masa wanda ya taho da taruwar hawaye cikin idanunsa ganin daya daga cikin yaran da tayi zoom in din babban yatsansa na cikin bakinsa kaman me shan hannu.

"Astgafirullah......alhamdulillah......subhanallah walhamdulillah wallahu akhbar" Abinda ya dinga fadi kenan,yana jin kaman kada ta daina nuna masa fuskokinsu,saidai kuma dole saboda ayyukan da suke gabanta.

Sauke na'urar tayi itama murmushi yana qwace mata,ita kanta yaran sun burgeta,ta kuma jima bataji jariran da taji tanason ta gansu fuska da fuska ba irin yaran. Bata sani ba,ko hakan yana da alaqa da yadda ma'auratan suke burgeta?.

Zata iya cewa tsahon shekarun aikinta,taga spouse kala kala,amma ba wadanda sukafi burgeta tare da qara mata son yin aure a kurkusa irin sabreen din da fu'ad. Da fari ma ita sam bata yarda daga nigeria suke ba,na farko dukkaninsu sunayensu batayi tunanin akwai masu irin sunan a bahaushiyar qasa ba,na biyu kuma yadda fatarsu keda wani irin haske da kadan tasu ta dara nasun,uwa uba yadda sukejin labarin Nigeria da yadda 'yan qasar suka zubda kansu a qasar saudiyya yadda ake binsu ana kamesu kaman kaji ko awaki,bata dauka akwai mutane masu qayatarwa da burgewa kaman wadannan mutanen ba,sam bata zaci zaa samu mutum irinsu a Nigeria ba.

Hannun sabreen kawai ya juya ya dinga kissing,har sai da dariyar likitar ta dakatar dashi.

Da kansa ya taimakawa sabreen din ta zauna sannan ta miqe tsaye,ya gyara mata rigarta da mayafin saman kanta,sannan ya taimaka mata ta zauna saman kujera tayi relaxing sosai,daidai sanda likitar ta dawo dauke da takardu zuwa gabansu.

"Cikinta yanzu haka yana sati na talatin da uku,kuma yawanci 'yan uku bama bari su haura sati na talatin da hudu saboda nauyinsu......don haka ina tunanin mafi kyau sati me zuwa ayi mata CS a ciresu". Murmushi ya sake kubce masa,wannan nesar tazo kusa kenan,wannan lokacin na haduwa da yaranshi yayi kenan. Already sun yanke ayi mata CS din,saboda haka kawai yake tsoron tayi naquda,gani yake kaman zai rasata,tun randa sukazo anti natal suka samu wata mace ta rasu gurin haihuwar twins dinta. Koda ya shawarci sabreen din bata qi ba,don ita don ta ita bata da wani zabi,kome ya yankewa rayuwarta tasan bazai cutar da ita ba. Likitar kuwa dama kai tsaye ta gaya masa cewa.

"Ba kasafai muma muka fiya so ko barin me haihuwar fari triplet ta haihu da kanta ba,akwai risk,CS is the best idan har ma'aurata sun amince.

"Ba matsala,Allah yasa ayi a sa'a.......a turamin komai da asibiti keda buqata na komai da komai din,zamu shirya zuwa sati dayan in sha Allah".

"To yayi.....zaku zo a day kafin ranar aikin,don bayan asuba koda sassafe zamu shiga da ita".

Shi da kansa yayi driving nasu dama zuwa asibitin,yanzunma shi dinne,don wannan karon kwata kwata daga Jordan dan amanarsa sai abdulgafar,da iya mutanen daya taho kenan.

Wani rayuwar 'yanci yake abinsa cikin garin madeena,kusan kullum saisun fita shida ita,strolling ko a mota,suci abinci su dawo gida bayan sun zazzagaya garin. Ya lura yadda yake qaunar madeena haka ita dinma,yanayin garin da calmness dinsa yana sakata nutsuwa sosai ya lura da wannan,don haka a yawan lokuta ma ba hira suke ba,suna tafiya ne kawai a low speed tare da madaidaiciyar qira'ar daya daga cikin malamanmu na addini,sai kaga duk jikinta yayi weak wani kwanciyar hankali tana ratsata.

Yanzunma hakan yayi mata,saidai suna fara tafiya tace

"Hamma"

"Na'am adda sabreen" . Yadda ya fada din ya sakata sakin murmushi,muddin zata ce masa hamma,to shima fa zaice mata adda sabreen.

"Umra nakeso nayi......". Kallonta kadan yayi sannna ya maida hankalinsa kan titi.

"Yaushe kenan?".

"Kafin ayimin Cs.....ban sani ba ko itace ta qarsh"

"Ameenatu!" Ya kirata da wani irin sauti kaman kan motar zai subuce masa kafin ya daidaitata.

"Don Allah ki rufan asiri karki qara fada,kinsan tsarki da darajar garin nan kuwa?,kinsan ko ina kayi addu'a indai a cikinsa ne ta musamman ce?,kin sani ko muna tare da mala'iku?" Ya qarasa fada kaman zaiyi kuka. Sanyi itama jikinta yayi,sai tayi qasa da kanta tana fadin.

"Kayi haquri,bazan sake ba in sha Allah" Shuru yayi kaman bazai amsa ba kafin ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya.

"Allah yayi miki albarka,ya rayamu a tare"

"Ameen" Ta amsa tana satar kallonsa tausayinsa yana ratsata.

Hanyar komawa gida taga ya canza sai kuma yace mata.

"Jibi in sha Allah zamuje kiya umra......amma muje in nuna miki wani abu" Kai ta gyada,sai ya qaro sautin qur'anin kadan yaci gaba da tuqin a nutse.

Sosai karatun yake ratsata,qasan zuciyarta kuma tana jaddada godiyarta ga Allah. Haqiqa tasan bata da haufi.....bata kuma da tsoron kalar uban data zabawa 'ya'yanta. Nagartar fu'ad kawai wata baiwa ce me zaman kansa,ballanta zallar tausayinsa da jin qansa akan 'ya'ya mata......especially matarsa. Ita kadai tasan wanne irin kalar miji take aure.....a father...a mentor.....uwa uba Selfless partner ne. Batasan yawan addu'o'i da take sha ba daga wajensa.....ita take dauke da cikin kawai,amma ya fita damuwa da kan kanta. Bai taba barinta ta kw ata ba addu'a ba alwala ba,bai taba barinta tana kallace kallace ko jin kade kade ba,duk da dama ita din ba gwanarsu bace,saidai akance dan adam ajizi. Da yawan lokuta yakance.

"Tun a ciki kana iya koyawa yaranka dabi'a me kyau da maras kyau.....tun a ciki kana iya debewa yaranka albarka kana kuma iya sama musu albarkar.....me ciki kullum so ake ta zama cikin d'a'a da bin Allah.....ta zama very attached to her rabb,yawan sadaka.....yawan kyauta,karatun qur'ani ko sauraronsa,ambaton Allah da istigfari,ta guji gulma zagi mugunta tuggu makirci da qarya......wannan zai sanya ta samu nagartattun yara in sha Allahu". Kai ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login