Showing 351001 words to 354000 words out of 363280 words

Chapter 118 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1387

dauki nauyin karatunsu har zuwa degree,har masters ma idan suna buqata har sama da hakan". Kai yake jinjinawa,ya jima yana ayyukan lada dana alkhairi kala daban daban,amma wannan din yafi kowanne yi masa dadi da qara masa walwala da nishadi. Uwa uba kuma wani abu daya lura dashi,tun daya sanda gidan ya fara aiki dukiyarsa kaman amai take,wani irin mahaukacin hauhawa takeyi,wani irin bangajejen budi yake qara samu da shi kansa kai tsaye yanzun bazaice ga adadin abinda ya mallaka ba.

Ci gaba sukayi da tattaunawa shi da ita da wani irin yanayi da zai gaya maka zallar soyayya da tausasawa da jin qaine ke wanzuwa tsakanin ruhi da zukatan wadannan masoyan.

Suna isa ya karbi mamarshi ameenatu iffa,don ta farka a sannan. Ita dinma da gudu ta nufoshi tana fadin.

"Miss you abbee...."

"Mamana.....My incomparable mother.....a mother without equal" Ya dagata yana juyata abinsa,ba ruwansu shi da ita da al'ummar dake farfajiyar gidan,wadanda kusan dukansu sun fito ne saboda tarbar Sabreen din,wanda wasu lokuta suke mata title da THE MISTRESS OF THE VILLA.

K'ananun shekaru gareta amma ta zama babbar qarfi da yaji cikin gidan,duk da ta tasamma shekaru arba'in daidai a duniya......amma tsananin kula da kai da gyara jiki da kuma shan natural abubuwan gyara ga diya mace ya sanya zaka yita daukanta a shakarunta ashirin da biyar ko da takwas take. Bugu da qari idan ka kwatantata da su anni da suka kasance manya a gidan,ba laifi idan ka kirata da yarinya. Kusan duk wani dawainiya da matsaloli da zaa kaiwa annin ta hana isarsu Gareta,ballantana maamah da ba cikakkiyar lafiya gareta ba,yau da lafiya gobe babu.

Girman ya karbeta da kyau,yadda ta tafi dashi kuma cikin adalci da mutuntawa ya sanya kowa yake biye da ita da tarin qauna.

Ko a wajen bata wuce ba sai data duba lafiyar duka ma'aikatan,fuad na biye da ita dauke iffa yanata shan surutu,daya hannun nasa kuma handbag dinta ce. Wannan dabi'ar tasa kowa dake jadda villa ya santa,tun suna kunya har ya zame musu jiki. Ko zaman kwana uku kawai kayi cikin villa din zakasan cewa akwai wata mahaukiyar soyayya irin ta hanta da jini a tsakaninsu.

Tare suka jera cikin gidan bayan gamawa da ma'aikatan yana tsokanarta.

"Hajjaju da kanta......yau masu gidan sun dawo kowa ya shiga saitinsa" Yayi maganar yana maqalewa a bayan fuskar iffa yana mata gwalo. Murmushi ta saki tana mintsinar hannunsa.

"Ka daina mantawa fa da cewa yanxun baban samari ne kai.....in suka ganka kana tsokanar ummensu tabbas xakaji kunya".

"Suma sun jima da sanin cewa ba'a raba hanta da jini......yadda nakeso susan zallar madarar soyayyar dake tsakanin abbeensu da ummeensu alhamdlh sun fahimta" Kai ta gyada,ita kanta tasan da hakan,hakan kuma ya taimaka sosai wajen bawa yaran qwaqwalwa da rayuwa me kyau,hakanan kuma suma sai suka tashi da qaunar junansu sosai.

"Banga kowa ba cikin dukka yaran gidan nan ba.....sauban dai ancemin yana gurin anni".

"Kin rigani fade ne......duk da kaman su nadra sun tafi siyayya dasu sahl samr suhail duka sun bisu". Murmushi ta danyi tana jinjina kai,tana sake jin rayuwarta tayi mata dadi idan ta tuna yau zata aurar da nadra da haneefa gaba daya,ragowar abinda ya rage mata kenan take addu'ar Allah yakai mata ranta.

"Kaman yaushe zaku fara bikin nan?" Fuad ya tambaya sanda suke dab da isa sassan maamah. Umarnin anni ne,duk sanda suka dawo daga wata tafiya ko kuma suka tashi da safe zasu shiga su gaisa ita ta yafe zuwan farko,su fara zuwa wajen maamah tukunna su dubata.

"Don itace me lalura,tafi buqatarku a akaina,ni da lafiyata har yanzu da sauran qarfina.....kuma alhamdulillah zan iya yiwa kaina komai"

"Hamma abubuwa kadan zasuyi fa......zasuyi the day of qur'an da dalibai da malamansu na mu'assas.......then zasuyi bridal shower.......sai waleema da anni ta shirya shikenan,dukkansu suda mazan basason dogon biki". Kai ya jinjina,yana jinjinawa yaran,suna da wani irin hankali da nutsuwa na daban,komai nasu moderate ne,shi yasa ya yuwa rayuwarsu wani tanadi na musamman da ba wanda ya sani sai ranar da aka daurawa kowaccensu aure.

"Ma sha Allah.......Allahumma barik" Ya furta suna sanya qafa makekiyar balcony din da zata sadaka da falon.

Idanunta akan tashar saudi sunnah da suke hasko masallacin ma'aiki tare da karanto hadisansa masu tsarki girma da alfarma,zuciyarta takejin tana tsananin kewa da qishirwan gurin,kaman bata taba zuwa ba tunda take a rayuwarta. Sukanje tana bin jama'ar gidan da suke da kebantattun lokuta da jirgin jadda majesty jet yake jigilar kowacce halitta dake birnin jadda villa din bayan kowanne hutun makaranta da za'ayiwa yaran. Wannan damar suke amfani da ita suke ziyartar fauzan fawad da fawwaz dake karatunsu a madeena king Abdul'azee international School wadda suka kammala kuma za'ayi bikin yayesu sati me zuwa.

Kaman saukar nannauyan dutse daga qirjinta haka taji sanda sukayi sallama a tare,ta motsa bakinta tana amsa musu da sautin da ba'a fahimtar abinda take fada sosai sai wadanda suke da matuqar ganewa kaman sabreen din,don shi kansa fu'ad din sometimes sabreen ce ke gaya masa abinda tace din.

Idanunta ta janye a kansu tana maidawa kan yarinya ta biyu da Allah ya jarabceta da masifar son yarinyar......yarinyar da duk gidan kowa qaunarta yakeyi saboda kasancewarta jika diya mace qwaya daya kaf cikin jikokin gidan ashirin da wani abu. Ameenatu iffa ta sakarwa maamahn murmushi tana zamewa daga jikin fu'ad ta tsallako da gudu tayo wajen maamah.

"Har yanzu baki tashi kin fara tafiya ba?,kikace zaki fara tafiya kafin mu dawo?" Ta fadi cike da quruciya cikin maganarta. Murmushi kawai maamah din ta sake,yarinyar ta tattaka qafafun maamahn ta haye cinyarta tayi dare dare tana bata labarin su hamma fauzan suna gaisheta.

Tayi kewar 'yan ukun sosai,su na dabanne a zuciyarta,duk da gidan cike yake da tagwaye amma nasu qaunar daban yake. Har yanzu suna iya kira video call su dukka ukun su sakata a gaba da hirarraki har sai sun sakata dariya sanna,har zaman jiran kiransu takeyi kulli yaumin,koda basu kira ba zata sanya a kira mata su.

"Barka da warhaka maamah.......ya qarfin jikin?".

" Alhamdulillah " Yau sautin amsa gaisuwar sabreen din ya fita da kyau har sai da sabreen ta daga kai ta kalleta a mamakance.

"Ya taro?" Ta fada da sarqaqqen harshenta.

"Alhamdulillah.....mun kammala cikin nasara"

"Allah ya taimaka" Ta sake fada da qyar tana fuffusgo kalmar.

"Ameen" Sabreen ta amsa tana sadda kanta tana tattalin hawayen farincikin dake son ballewa cikin idanunta.

Kamar yadda maamah ta zata din,sabreen din saidata tabbatar komai yana tafiya daidai a sashen,daga masu kula da ita har kalar abincin da ake bata sannan suka wuce sassan anni.

Suna zaune da mutuminta sauban a courtyard din da ya zamana shuru saboda fitar duka yaran da rashin motsinsu wanda anni batasan me ya kawo hakan ba.

Murmushi ya sakarwa ummeen nasa da abbeen nasa,ya zare headphones din ya ajiye ya tako da nutsuwar nan tasa yana fadin.

"Sannu ummee.....abbee sannu" Ya fada yana kamo iffa wadda tayi tsalle ta daneshi. Akwai sabo sosai tsakaninsu,don wani irin sassanyan kulawa yake bata ta hankali.

"Anata karatun sauban?" Sabreen ta fadi bayan ya gama gaidasu,fu'ad ya dora hannunsa saman kansa. Yana jin yaron sosai a jininsa saboda yadda yake da maitar karatu,yana da buri sosai akanshi,kowanne yaro nashi yana bashi karatu daidai da abinda ya fuskanci yafi karkata akai.....kaman yadda ta fannin neman kudi ma yayi alqawarin zaibar kowa yayi kalar neman kudin da yafi sha'awa muddin bai sabawa addini ba.

Da wani irin alfahari qauna da soyayya anni ke kallonsu a gabanta,har suka gama gaisawa suka fara taba hira

"Kije ki huta takwara,anjima akwai general dinner a babban dining room na gidan nan,sai a qarasa hirar a can" Murmushi tayi a kunyace sannan ta miqe,fu'ad ya tayata da jakar suka rankaya dukkaninsu wannan karon har sauban suka fice.

Tun kafin sukai ga bude qofar sassan taga kaman parlor din farko yayi duhu da yawa,bangaren sitting room ba ba wani wadataccen haske. Tanata so tayi magana amma kuma Allah bai bata iko ba har sai da suka shiga parlor din.

Duduun ba wani haske,abun da ya basu mamaki kenan daga ita har fu'ad din,ta bude baki zatayi magana fitilan farko ta kama. Harafin H ne tafkeke,mamaki ya cikata,zatayi magana A ta bayyana,da wani irin sauri P ta bayyana a jejjere ragowar suka kama suka bada cikakken sunan HAPPY WEDDING ANNIVERSARY.

Baki sake take kallon harufan,ta juya a hankali da zummar yiwa fu'ad magana ko yaga abinda take gani,sai gaba daya wutar falon ta kunnu hade da wasu abubuwa masu walwali da suka soma bude kansu da kansu daga jikin fitilun suna watsuwa a kansu,lokaci guda kuma muryoyin zuria'ar yara na jadda din ta hadu wajen fadin

"Happy wedding anniversary" Sai a sannan suka ankara da komai da tsananin mamaki. Ameen,Amaan,hilal dan huda na fari,naseem dan amna na fari,sai yaron wajen farouq na farko shima Aleem,sai tagwayen sabreen na biyun masu bin su ameen Aabid da Aadil,sai wasu twins din masu binsu Aadil din,irfan da farhan wadda ameenatu iffa ita ta zama cikon ta gomansu.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862



*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?
*_Domin qulla huldar kasuwanci damu,HUGUMA CLOSET.......,siya ko siyowa wani,reposting ko sari akan farashi me rahusa da babu irinsa,maza yi joining group namu don samun ingantattun kayan da babu ha'inci a ciki da izinin Allah_*
https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX



174



Yara ashirin da daya ne idan ka dauke mutum biyar dasu nadra suka fita siyayya dasu.......sai fannah da huda dake tsaye a bayan yaran da alama su suka tayasu hada wannan surprise din. Inda Allah ya kawo ma sauqin abun amna bata nan,tare suka fita siyayyar dasu nadra tabbas da abun sai yafi haka.

Kasa magana sabreen tayi,harga Allah tana sane da yau dinne suka cika shekara goma sha shida da aurensu,amma bata kawo zatayi wani abu da wani zai gane ba illa tsakaninsu ita dashi,sai gashi yaran sun rigata aiwatar da komai.

"Ku ko?" Sabreen ta fada tana nuna fannah da huda,fanna din da amnar da dukkaninsu zuwa yanzu tana jinsu tamkar uwa daya uba daya suke. Tana nunasun da yatsa tana murmushi sai kuma kukan farinciki ya barke mata,ta aza kanta saman kafadar fu'ad din tana matsar qwalla.

Irin wannan soyayya da suke gwada mata batasan wacce iri bace,bama ita ba.....kusan dukkaninsu ba zaka tantance wane da wane ga daga inda suka fito ba. Rankatakaf jikokin gidan dama iyayensu kallon uwa suke mata,kuma hakan baya rasa nasaba da yadda ta riqesu kaman ciki dayan suma fito.

A cikin yaran ba wanda bata taba rainonsa ba,duk itama tata bataliyar,duk kuma da cewa kusan kowanne yaro yana da nanny dinsa a gidan,sai wanda suka kai shekarun girma irinsu ameen sannan ake barinsu su koyi rayuwa da hidimar rayuwar data zamewa kowa ya koyi yiwa kansa.

Idanun yara kawai ya hana ya rungumeta,amma qasa qasa yake fadin.

"Karki bata fuskarki,karki kashe mana farincikin yau" Ya fada yana dan bubbuga bayanta.

"Kita fatan muci gaba da irga wadannan shekarun tare" Abinda ya rada mata kenan.

Qaramin walima akayi a gurin da kayan maqulashe kala kala,kuma abunda ya bata mamakin shine,koda autar gidan iffa wadda tare suka shigo gidan sun tanadar mata gift din da zata bawa daddy jadda (yadda gidan suke kiransa kenan in general idan ba'a sassansa bane).

Farinciki da walwala ne kawai ya wanzu a gurin,inda daga qarshe dai bata haura samanta ba kota wuce sassanta ta lalace a nan tana tsakiyar family din nata suka zarce da hirarrakin bikin da zaa fara jibi jibi.

Wayarta ta ciro da zummar kiransu nadra taji inda suka dade haka da yawa sai taci karo da tarin miscal din jadda. Ta zaro ido tana mamakin tun yaushe yaketa kira bataji ba?,saiga shigowar wani kiran nasa.

"Sabrrrr" Kawai ya fada a narke,take ta fahimci yana buqatarta a kusa dashi.

"Banda abun hamma.....awa daya kawai ya rage ayi magriba fa?" Ta fada cikin mita tana tura katafariyar qofan master bedroom dinshi.

Bata gama ajiye qafarta taji an ficikota ciki,a zafafe ya manne bakinsu guri daya ba tare daya jira komai ba.

Har kullum har ko yaushe har kuma abada mantawa takeyi da shekarun dake wuyansu idan suna tare da jadda din. Wani irin mutum ne dake da baiwar narkar da zuciyar diya mace ya kuma mantar da ita komai. Abinda yayi imani dashi shine,yadda kowacce diya mace a kullum take fadi tashin neman hanyoyin faranta ran namiji da burgeshi,haka ya kamata kowanne namiji shima ya kasance cikin sanin hanyoyi da salon mallake zuciyar matarsa......wannan dabi'ar tasa ta sanya yayi zarra a zuciyar sabreen din.

Sai data tabbatar ta samar masa da nutsuwa sannan ta baiwa kanta hutu tana aje numfashi,ya birkitota yana maqaleta a jikinsa bayan sunyi alwala sun dawo. Shuru ne ya ratsa tsakaninsu,kafin daga bisani taji saukar numfashinsa a hankali bacci me cike da nutsuwa yayi awon gaba dashi.

Sai bayan sallar isha'i ta samu saukowa daga wajensa,a lokacin ya fita sallar isha'i,da wannan damar ta samu tayi wanka tayi kwalliya kuma cikin atamfa kaman yadda ta saba idan zasuci abinci nasu duka.

D'as d'as take takawa kaman ba wannan jikin bane ya fidda rai goma ba,har ta iso babban parlor din da anan aka gina katafaren dakin cin abinci.

Ta samu kowa yana gurin,kowa kuma yasan mazauninsa yana kai a zaune,sauran wadanda basu hadu ba sai a sannan irin musaddiq saddiq da farouq duka a nan suka gaisa suna tayata murnar ci gaban da aketa samu.

Kowa ya hallara kuma faud din ake jira,shine qarshen shigowa,yana takowa a nutse da wata irin haiba da kwarjinin da ya qara yawa sanadin shekaru da kuma riqo da addini da yake dashi,kwarjinin da yake hana mutum musu dashi ko yin abu ba daidai ba,kwarjinin da hatta sabreen a yawancin lokuta yakan daketa duk kuwa da cewa dazu dazu suka rabu a daki cikin wani sirrintaccen yanayi,amma yanzun data kalleshi kwarjinin nan ya dawo fes saman fuskarsa.

Kusan yara yaran a tare suka gaidashi,su sabreen huda fannah da amna suka fara serving na kowa da kowa a nutse ba wani hayaniya kaman ba taron mutum kusan talatin ba.

Cikin qauna da tsabar sabo da juna suke cin abincin,hirarraki suna gudana a tsakaninsu. Har yau har kuma gobe yana maintaining class dinta a idanunsa,bata duba an dade tare.....an jima da juna ta dinga wasu abubuwa da babu aji sam cikinsa a wajen diya mace( mata yana da kyau ku kula da wannan,stay classy please,karki dinga abu gaban miji wargazaza koda shekara dubu kukayi ki tabbatar masa ajin nan fa akwaisa,idan ba haka ba ya hango wadda bata kaiki ba nata ajin ya dinga dibansa yana burgeshi).

Shi dinma satar kallonta yakeyi,yanason gano meye ya banbantata da sabreen din shekaru goma sha baya?. Ya dade yana against in din maza da yawa akan suna da babban laifi da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen wargajewar matansu,mace 'yar tattali ce.....'yar a bata kulawa ce,mace tamkar fure take,dole idan anaso aci gaba da ganinta sharshar a tsaya mata da ban ruwa,wato cima sutura muhalli abun sha me kyau,a debe mata damuwa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login