Showing 189001 words to 192000 words out of 363280 words

Chapter 64 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1416

kowa ba. Zama da JIB ya qareta abubuwa da yawa,tun sanda tayi noticing canzawar huda awancan lokacin da Naseer yaso bata ta,ta yanke ta sakata,wanda ita ta taimaka mata taga duk wani motsi na huda.....ya kuma sake qarfafa mata zargin da shi yayi sila ta gano komai.

"Wannan kawai zan nuna masa don yasan cewa bani na kawo kaina rayuwarsa.......ba sonshi nake ba.......ban taba kuma sonsa ba.....banajin kuma zan soshi din.......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......" Maganarta ta tsaya a nan sanda lallausan qamshinsa ya marabci hancinta.....kaman giftawar walqiya kuma sai gashi a wanze cikin dakin a wani birkitaccen yanayi.

Wani irin kallo da yake saukar mata shi ya sanyata zare idanunta daga kanshi. Wani irin birkitaccen kallo yake mata zuciyarsa na wani mahaukacin bugawa da kalamanta na qarshe da kunnuwansa sukayi katarin ji

"Ba sonshi nake ba......ban taba kuma sonsa ba,bana jin kuma zan soshi din......rabuwa da zaiyi dani kaman ragemin aiki yayi......". Inda tasan girma da nauyin da kalaman sukayiwa qirjinsa tabbas ba zata fadesu ba.

Janye nasa idanun shima yayi daga kanta da suke sake sauya launi saboda bacin ran da yakeji cikin ransa. Yayin da idanun maamah suke zube a kansa ita kuma.....zuciyarta na quna tare da jaddada mata baqar mallaka sabreen din tayi masa da yake kasa sukuni a duk sanda take waje......yake kasa aza idanunsa akan kowacce halitta idan ba ita ba.

Da confidence dinsa ya shiga cikin dakin,yana jin cewa idanma tazo ta gayawa maamah ne bata sonshi don ta sanya su rabu.....ba shakka ta dauko aikin da bazata iya qareshi ba.....a yanxu a kuma yadda yake jinta a kusa da kowacce jijiya ta jikinsa.....ko mutuwa bayajin xaya lamuncewa ta rabashi da ita.

"Gani" Ya fada yana dosana gefan sofa din dakin.

Idanu maamah ta zuba masa tana jin wani irin abu yana birkitata. Ga qoshi ga kwanan yunwa,gashi a gabanta cikin qasa da mintunan data nema ya isketa......gashi a gabanta cikin neman umarninta ya kuma cikashi.....rijiya ta bada ruwa guga ya hana. Ko sau daya koda a cikin mafarkanta na zahiri da na badini.......bata taba tunanin sabreen din nada kaifin basirar ajiye kowacce hujja data shafi rayuwarta ba.....tunanin hana faruwar hakan ya sanyata bata waya ta musamman da zasu dinga communicating......wadda bata nadar komai....komai din kuma idan ya nadu ma zai goge kanshi da kanshi ne automatically.

"Tashi kaje kawai.......zan sake nemanka a lokacin da ya dace" Ta fada tana zubewa sabreen wani kallo dake nuna zallar gargadi da yiwuwar afkuwar komai a karonsu na gaba.

Sam sam sai yaji hankalinsa ya gaza kama maganar maamah din.......kamar ba ita bace ta kirashi ga waya mintuna kadan da suka shude ba cikin wani irin zazzafan yanayi?,to meye ya sauyata da sauri haka?.

Waiwayawa yayi kai tsaye yana duban sabreen,saidai idanunta kaf baya kansu yana kan wayar hannunta. Sake maido dubansa yayi ga maamah,har yanzu shi take kallo......saidai kuma da alama kalaman bakinta na sallamarsa ba sune a qasan zuciyarta ba.

"Kaje nace" Ta sake maimaita masa tana fargabar kada yaci gaba da zama ta kunna video din a gabansa. Kaman bazai miqe ba sai kuma ya miqe din,ya sake duban sabreen da still tayi kaman bata wajen kaman kuma ba kowa cikin dakin. Maganganunta suka dinga tsikarar zuciyarsa da wani irin ciwo. Girman qin da take masa har yakai ta zauna ta fayyacewa duniya?,ta fayyacewa kowa?,shi kam idan bai dasawa sabreen jarababben sonshi ba rako maza yayi duniya kenan,da wannan zafin da fushin ya fice a dakin.

Miqewa tayi sanda ta tabbatar ya fita,tadan kalli maamah din kadan,kaman zatayi magana sai kuma ta shanyeta tana tuna cewa ba sa'arta bace.

"Karki saki jiki kiyi farinciki da tsammanin kin kubuta ko kinci nasara akan mariya.....a'ah....wasa farin girki wannan,hausawa sukace somin tabi ne wannan hatsin gara a buta". Dan waiwayowa tayi,sai ta sake mata murmushi kawai tana sanya qafarta waje.

Bawai kaman jiran fitowarta yake ba......dama jiran fitowartata yake......ba zato ba tsammani taji ya cafke hannunta,bai kuma tsaya sauraren komai ba ya soma tafiya da ita zuwa bakin qofa.

"Ina zaka kaini?.....ina zamuje?.....ka sakarmin hannuna......wannan bai kamata ba,ni ba inda zanje......ka sakeni......wai ina zamuje?" Ta sake tambayarsa da qarfi wanda ko sau daya bai waiwayo ya kalleta ba sai daya tabbatar ya sanyata cikin motar ya kwashe qafafunta ya maida ciki ya rufe ya kuma zagayo ya zauna gefanta.

Wani irin zama da ya bata daman jin irin hucin dake fita daga can cikin zuciyarsa har saman fuskarsa. Ya tsareta da kallo da idanunsa da sukayi kaman kwanciyar jini daga qasansu saboda zallar bacin rai.....farar fatar fuskarsa itama ta canza launi zuwa reddish kaman wanda aka dinga yamutsa fuskar da maruka.

"Zan kaiki na killace......a muhallin da ba wanda ya isa ya ganki......zan kaiki inda zamu rayu daga ni sai ke.....zan kaiki inda ba zaki sake ganin kowa ba sai muhammad fu'ad.....zan kaiki wajen da soyayyar fu'ad ce kadai 'yancinki da zaki samu" Yayi maganar yana sauke don rage radadin da zuciyarsa ke masa. Kafin tace wani abu ta fahimci motar tasu ta fara motsawa tana fita daga gidan.

Hankalinta ya dan tashi,saboda sanin halinsa da tayi,to amma sai tabi shawarar zuciyarta ta hanyar dakewa kaman abinda ya fada din bazai tabbata ba ko bai dameta ba.

Tana iya jin wata irin birkitacciyar ajiyar zuciya da yake saukewa,har tsakiyar kwanyarta takejin fitar ajiyar zuciyar wanda ba zata ce ga dalili ba. Ya maida bayansa yayi relaxing sosai jikin kujerar yana sauke numfashi kaman wanda yaci kuka. A hankali taji ya laluba tafin hannunta ya sanya nashi. Mannewa sukayi guri guda abinda ya sanya tsigar jikinta tashi,tana iya jin yadda dumin tafin hannunsa yake bin kowacce jijiya ta jikinta dake aika saqo,tayi yunqurin zame hannun amma ya hanata,saima ya sanya hannunsa guda daya ya tayar da motar,cikin qwarewa yake sarrafa steering din da hannu daya suna ficewa daga gidan.

Batace masa komai ba.....amma jikinta ya soma sanyi da ganin hanyar da suka dauka. Basu taba bin hanyar ba duk a fice ficensu.

Wani irin guri ne da zata iya cewa tsahon rayuwarta bata taba ganin gurin makamancinsa ba.....wani tsuburi na musamman dake kewaye da ruwa wanda kafin su qarasa dab da wajen ya ajiye motarsa,tun bai fito ba ma'aikatan gurin suka qaraso. Idanunta ta daga tana duban sunan dake maqale a signboard CONRAD RANGALI ISLAND RESORT. Sanda take dawo da idanunta ya kammala kashe motar ya zare belt din jikinsa,tattausan tafin hannunsa ya miqa mata yana tsareta da fararen idanunsa,a hankali ta kalli hannun sannan ta kalli fararen qwayar idanunsa da suka fara komawa daidai a lokacin.

Yayi wani irin laushi gaba dayansa,tun daga qwayar idanunsa zuwa gangar jikinsa zaka karanci hakan.

"Banaso.....karkimin musu.....na gaji.....na gaji da jin musu,taurin kai,saba maganata.....i beg you koda na awanni kadanne kawai kibi umarnina,koda na iya yau ne" Ya fada da wani sauti me matuqar laushi. Haka kawai taji wani abu me kama da tausayi yanason saukar mata.......duk wani izza da qasaita nashi duka ya zuge tsakanin tafiyarsu zuwa yanzu. Gefe guda halaye da dabi'un matar da take kiran kanta a matsayin mahaifiyarsa yana dawo mata. Wanne irin barazana wannan uwa keyi da rayuwar d'anta?, ta tambayi kanta. Tunawa take da rayuwar da tayi a gidansu,tsakanin kawunta da kishiyoyin mahaifiyarta,dabi'unsu da mu'amalarsu a kanta gaba daya wasu iri ne da basu da dadin ji ballantana gani.....ta fuskanci rashin nutsuwa da barazana me tarin yawa......yau inaga ace mahaifiya da kanta keyi maka haka?.

Tana tsaka da wannan tunanin ta tsinceshi saman kanta,har ya zagayo ya bude mata qofar side dinta,bai gaji ba ya sake saka hannunsa ya kama tafin hannunta yana tayata fita a motar.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


98


_Manzan Allah S A W yace: Bawa zaizo ranar qiyama da tarin ayyuka da kuma tarin lada,yana murna zai shiga aljanna sai Allah ya dakatar dashi,ga tarin mutane da baisan daga ina suke ba.....dukansu masu neman haqqinsu ne a kansu a wajen Allah,yaci dukiyar wancan.....ya zagi wancan.....ya zalunci wannan,ana biyansu da haka da haka sai ya wayi gari bashi da komai cikin ayyukan ladansa,bayan ayyukansa sun qare za'a koma ana diban zunubin mutanen a maimakon biyansu da ladansa ana lafta masa,daga qarshe sai ya tashi baida komai sai tarin zunubai,sai Allah yayi umarni wa mala'iku su jefashi a wuta( Allah ka tsaremu=?O?
_bukhair da muslim_



Sosai ya riqeta yana zagayo da hannunsa zuwa qugunta,sai ta kasa janyewa kaman yadda ta saba saboda idanun mutane,zagaye da ma'aikatan suka taka har zuwa inda wani boat ke ajiye. Kadan kadan zuciyarta ke bugawa saboda shimfidadden ruwan dake zagaye da wajen fari qal da yake bada wani color me kama da sky blue.

"Ina zamuje saman ruwa kuma?" Ta tambayi kanta tana jin tsoro yana shigarta. Tunda take a rayuwarta wanna shine karo na farko da zata taba shiga jirgin ruwa,duk da wannan din wani irin jirgi ne da zai nuna maka tsadar da yake dashi,tsarinsa daban yake da sauran jiragen da take gani,yana da wata fargajiya da kujerun zama masu daukan hankali.

Bata fahimci maganar da suke ba don cikin harshen Dhivehi suke magana yaren 'yan qasar. Can qasan ranta tana mamakin yadda ya iya harshen haka,a zamanta dashi taji yana yaruka kala kala da batasan yadda ya iyasu ba. Hannunta ya sanya cikin nasa suka fara yin gaba don shiga boats din,saita tsaya ba tare data motsa qafarta ba tana matse yatsunsa cikin nata ba tare da tasan tayi hakan ba. Zuciyarta ke bugawa kadan kadan cikin tsoron shiga boats din,ta yaya zasuyi tafiya saman ruwa?,ruwan ma shimfidadde irin wannan?.

Kallo daya yayi mata ya karanci tsoron da yake idanunta,yayi qasa qasa da muryarsa duk da bajinsu za'ayi ba yace

"You're safe.......idan kina tare dani you are safe......ki shirya zamu koma rayuwa cikin ruwa,har sai sanda kika koyi soyayyar muhammad jadda.....i can't lose you" Yana kaiwa nan ya sake sanyata a jikinsa sosai yana takawa da ita saman katakon da zai qarasa dasu cikin jirgin.

Dole qanwar naqi tsoron ya ladabtar da ita tayi zaune cikin jikinsa,har zuwa sanda suka qarasa shiga,sai a sannan taga irin qawatar da aka yiwa boats din sosai,banda saman ruwan suke da bazata yarda cikinsa suke ba. Bai barta ba sai daya zaunar da ita saman qawatattun kujerun dake a wajen,ya samu wadda ke fuskantar tata ya zauna yana goye hannayensa a qirjinsa idanunshi a kanta. Har yanzun idan ka masa zuzzurfan kallo zaka karanci ranshi yana bace ne,yana kawai qoqarin dannewa ne. Tana jin nauyin idanunsa a kanta sosai,inda zai mata alfarma da ya rage nauyinsu a kanta. Ma'aikacin jirgin ne ya qaraso yana miqa masa wasu qananun blanket guda biyu masu taushi,ya sanya hannu ya karba ya ajiye a gabansa daidai sanda jirgin ya fara motsawa yana harbawa cikin ruwan.

Ido ta runtse tana curewa waje daya,'ya'yan hanjinta suna kaduwa tana jin kaman zata nutse ne a ruwan,sanda jirgin ya tashi sosai ya fara keta ruwan da gudu sai taji kaman kanta zai juye,wannan ya sanyata bude qafafunta ta cusa kanta a ciki zuciyarta na wani irin bugu.

Batasan sanda ya iso gabanta ba,ta daiji lausasan hannayensa saman tafin qafarta. Ta dago idanunta a hankali tana kallonsa,sai ya miqe ya ware blanket din yana lulluba mata,sannan ya koma ya tsugunna a gabanta yana lalubar tafin hannunta. Bata hanashi ba,don tana buqatar wani a kusa da ita,yadda ruwan keyi takejin kaman zasu fada ne,sai ta maida idanunta ta kulle gam.

Tana jin yadda yake murza tafin hannun nata daga gefe,tamkar me dauke da wani sihiri a nasa a hannun......a hankali sai taji bugun zuciyarta yana daidaita,tsoronta yana raguwa sosai.

Tafiyar mintuna idanunta suka fara hangen wani gini tsakiyar ruwan,mamaki ya cikata har sai data ware idanunta sosai tana duban ginin. Qawataccen gini ne da yake a tsakiyar ruwan,tako ina ruwa ne ba wani qasa a wajen ko wani tsandauri kusa da wajen bare tace ga yadda akayi dabara aka dora ginin.

"The Muraka hotel" Ta fadi sunan data gani an rubuta manya manya sama.

"Hotel?" Ta maimaita sunan qasan ranta,wanne irin hotel ne haka tsakiyar ruwa?,ta sake tambayar kanta a mamakance. Kada dai yace mata nan zasu zauna?,cikin ruwan kaman wasu 'ya'yan aljanu?.

A sanyaye ta aza idanunta a kan fuskarsa sanda jirgin ke tsaiwa daidai wata hanya me kama da gada da ta tabbatar ta nan ne zasu qarasa ainihin ginin hotel din. Girarsa duka biyun ya dage mata da wannan miskilar fuskar nashi,sannan ya miqe a nutse yana zare hannunsa daga nata,ya miqa hannun ya cire mata blanket din sannan ya sake kamata ta miqe tsaye suna fita a boat din yana magana da ma'aikatan.

Wata qaramar mota ce me qafa uku me budadden sama ta tsaya a gabansu,ya kama mata hannu tana taka cikin motar sannan shima yabi bayanta,a hankali driver din ya gaidashi ya amsa masa da yarensu sannan ya tashi motar suka fara ratsa gadar.

Tashin hankali.....ta fada a ranta tana ware idanu tana kallon rayuwa a cikin ruwa. Tun basu qarasa ba ta dinga ganin mutane jifa jifa tsakanin hanyar zuwa hotel din suna al'amuransu hankali kwance. Ita kallon ruwanma kawai dake gefe da gefen gadan ta qasansu daga mata hankali yake,a tsorace take har batasan sanda ta cure a kafadunsa ba.

Boyayyen murmushi ya saki batare daya kalleta ba bare ta gane hakan. Yana buqatar wannan tsoronne dama a tattare da ita,samuwar tsoron shine zai sake kusantata dashi......samuwar tsoron shine zai tattaro masa dukka rayuwarta a hannunsa,a inda ba anni ba amna.....ba farouq ba musaddiq ba kuma saddiq ballantana tayi tunanin zata janye jikinta dashi,zata rayu dashi shi kadai......daga shi sai ita a duniyar da ba wanda ya sansu,a duniyar da bazata iya guduwa ko ina ba.

Gajeriyar tafiya ce ta kaisu bakin qofar shiga hotel din. Luxury iya luxury da ko bakasan abinda duniya ke ciki ba idanunka zasu gaya maka. Wani irin gini na alfarma da zata iya cewa bata tsammaci samunsa a haka ba.

Wayarta dake hannunta tadan kada,ta bude tafin hannunta tana kallon fuskar wayar.

"Welcome to the muraka,the first world's under water villa" Idanunta ta janye daga kan wayar tana maidawa fuskarsa,sai ta kasa cewa komai illa tsoro da take sake jin yana mamayarta.

Binsa kawai takeyi har zuwa reception,inda suka karbi komai ya kuma sake riqe hannunta suna takawa a hankali zuwa dakinsu.

Ta kasa tsaida idanunta guri daya,mamakinta yanata qaruwa yadda take taka wajen tamkar a gida. Tana taka tsandauri alhalin tasan tsakiyar ruwa suke tsundum,ta sake riqe yatsunsa da kyau ko tsoron da takeji zai ragu.

Sanda yake bude qofan living room din dake dauke da bedroom dinsa da toilet harda kitchen mutuwar tsaye tayi. Glass doors ne tako ina da zai baka daman ganin kowacce fuska ta shimfidadden ruwan da suke kai. Luxury suite ne dake da bedroom biyu living room biyu duk da daya take gani a yanzun. Baice mata komai ba yana riqe da hannunta har suka shiga bedroom din.

Zare hannunsa yayi daga nata,yaja baya yana zube hannunsa a aljihun wandonsa yana dubanta.

"Ga first bedroom.....muje kiga dayan,saiki zabi wanne zaki zauna a ciki" Yayi maganar idanunsa suna lumshewa yana jin wani abu ya soma fusgarsa a kanta. Fararen idanunta ta aza masa,ita sam batasan ma yadda zata kwana cikin wannan ruwan ba,hannunsa ya miqa ya sake riqo yatsunta yana fita a dakin.

Daga wani sashen daban suka iske stairs da sukayi qasa,ya ware yatsunsa yana zurasu cikin nata ya jawota jikinsa sosai sannan suka fara takawa zuwa qasan.

Idanunta ta fidda sosai zuciyarta na harbawa da mugun gudu ganin suna nutsewa qasan ruwa.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login