Showing 225001 words to 228000 words out of 363280 words

Chapter 76 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1367

baccinta kaman ba abinda ke damunta,ya sunkuya yayi kissing dinta sannan ya fara takowa yana fitowa.

Tun bai qaraso parlor din ba yaji muryar farouq dana likitan,yana tsaye sanye da farar lab coat dinsa suna hira sama sama da farouq din. Fuskarsa sake ya miqawa fuad hannu cikin sanin darajar dan adam da iya aiki,shima ya bashi suka gaisa,sannan ya fara bude takardun hannunsa.

"After conducting the necessary tests,I'm pleased to inform you that your wife is pregnant...." Likitan ya fada da murmushi a fuskarsa.

Karon farko da yaji ya koma kaman dan koyo a fannin turanci,kaman ma baya gane komai. Ya zubawa likitan idanu yana buqatar qarin bayani,muryar farouq ta dawo dashi hayyacinsa.

"Alhamdulillah......ya rabb lakalhamd.....alhamdulillah......muna godiya sosai likita" Farouq daya kasa zama ya fada yana kama hannun likitan da kyau ya riqe cikin nasa.

"Allah ya inganta......ya bata lafiya me dorewa.....ina tayaku murna" Abinda likitan ya fada kenan yana murmushi,sannan ya miqawa farouq takardan gwajin yana masa bayani.

"Idan ta tashi a bacci za'a qarasa bata duk wani treatment daya kamata"

"Mun gode" Farouq ya sake maimaitawa yana karbar takardan likitan ya juya ya fice.

Ganin gaba daya fuad din ya zama wani statue ya sanya farouq kai masa duka

"Dude......kayi nasara.....ka jefa qwallonka a raga daidai" Sai a sannan ya tattaro kalaman bakinsa da qyar

"Am going to be a father?" Ya tambayi farouq cikin neman bayani gamsashe.

"Yes dude.....bakai kadai ba,harda ni,anni zata zama grandma for the first time......zamuyi yaro ko yarinya dukanmu......" Bai jira farouq ya kammala ba yayi masa wata wawiyar runguma hawaye suna kubce masa.

"Ya rabba.....antal kareemul lazi ya yaraddu sa'eelan,la'ilaha llla antar rahmanir raheem......shukran ya Allah,shukran" Sai muryarsa ta karye,ya dora fuskarsa saman kafadar farouq kuka nason qwace masa.

"Bansan wannan jarumin muhammadun da saurin kuka ba.....duk da na lura sabreen ta maidashi baby da gaske" Farouq ya fada shima zuciyarsa tana raunana amma yana qoqarin bawa kansa qwarin gwiwa. Kansa y a daga yana riqe farouq da kyau,yanata qoqarin masa magana amma ya kasa,sai kawai ya jijjigashi yana kada kai sannan ya taka da sassarfa yana komawa dakin.

Baccinta take kaman yadda ya fita ya barta,ya sake sumbatarta a goshi da labbanta,a hankali ya furta

"Kece duniyata.....na gode,na gode" Sai ya rufe mata qofar yana komawa parlor din da sauri.

"Zanje nayi sallah masallaci......zan kuma aiwatar da wani abu,idan zakaje mu hadu a hanya" Ya fada yana saka hannu ya kwashe takardun ya zubasu a aljihunsa sannan ya fita da sassarfa bayan ya sanar musu su aika me kula da ita zaije juma'a ya dawo.

Ba inda yakejin ya kamata yaje ya juye farincikinsa da godiyarsa ga Allah irin cikin rauda.....ya godewa Allah daya samu wannan labarin a irin wannan wajen,banda haka ya tabbatar sai yayi qaramin hauka saboda farincikin yayi masa girman da zuciya ba zata iya daukarsa ba ita kadai.


*_BAYAN AWA DAYA DA RABI_*


*_B A Z A T A_*


Anni,amna,musaddiq,saddiq dukkaninsu suna zaune a parlor din dakin asibitin bayan sun shiga sun dubata tana bacci sun fito.

Huda haneefa nadra da kuma momma bahijja sune kadai daga cikin dakin,suna taba tasu hirar kadan kadan wadda ke cike da farincki da qaunar juna.

Maamah dake zaune kallon kowa takeyi kawai daya bayan daya,yanayin yadda taga sabreen a yanzu ya soma sauke mata duk wani qwarin gwiwa da takejin tana dashi akan ba ciki bane a marar sabreen din. A shigarsu ta dazu ta gama qare mata kallo da kyau,ba abinda idanunta suka hango mata kuma banda dashewa irin ta me yaron ciki.

Iya wannan abun kawai data gani ya sanya gumi ya fara yanko mata,duk da yadda zuciyarta keta qarfafata tana mata romon bakan cewa ba ciki bane.

A yau din batajin zata matsa daga asibitin nan ba tare da an gwada yarinyar nan ba anga uban abinda yake damunta ba.

Sake jan qaramin tsaki tayi jan qasa qasa tana gyara zamanta. Gaba daya zaman wajen takeji ya gundireta,daidai lokacin fu'ad ya turo qofar dakin da sallama a bakinsa ya shigo.

Sannu da zuwa dukkaninsu suka fara masa banda maamah dake jifansa da wani irin kallo. Saddiq musaddiq da amna dukka suka gaidashi da tambayar me jiki,ya amsa musu cikin kulawa kafin ya qarasa gabansu anni yana gaidasu.

Da qyar maamah ta amsa,ta bishi da kallo sanda yake miqewa zai wuce ciki

"Zo nan muhammadu" Ta kirashi,sai ya dawo ya samu waje yana zama kujerar dake fuskantarta.

"Wannan ciwon da yaqici yaqi cinyewa ina ganin ya kamata a auna yarinyar nan asan me yake damunta,kada mutane suna zamansu lafiya taje tana yawo da ciwo tana yada ma mutane tunda gata ga yadda take a baya". Sosai maganar maamah ta sokeshi,ya kuma fahimci inda ta sanya gaba,anni kuwa sai da tayi da gaske ta iya controlling kanta.

Idonsa ya lumshe kana ya budesu ya gyara zamansa.

"Ba wani ciwo da ameenatu take dauke dashi a jikinta......tunda nine mutum na farko dana fara karbar mutuncinta na 'ya mace......ciwonta na yanzun kuma nine silarsa.....ga bayanin nan a rubuce" Ya fada yana zaro takardar,sai kuma ya dakata yana dubansu.

"Naji dadin ganinku a tare gaba daya" Ya fadi yana sake zura hannunsa a aljihun rigarsa.

Dollars dubu biyu ya fiddo sabbi kar a miqe,ya miqawa maamah takardar ya kuma miqawa anni kudin.

"Abba......alhaji hamza kibiya ta hannuna ya karbawa musaddiq mahmud jadda auren amna......bisa sadakin dala biyu biyu lakadan ba ajalan ba......ta hannun wakilinsa abokinsa alhaji muhyidden kibiya da tarin shaidu cikin masallacin annabi muhammad SAW,bisa yarjewar waliyyansu ni muhammad fu'ad jadda da kuma abba wato alhaji hamza kibiya"......


TURQASHI!......FU'AD.....NACE ME JADDA?,WANNE IRIN MATCH KA TARO HAKA?,KO TAKARDAR DA MAAMAH TA WARWARE BAKA BARI TA GAMA DUBAWA BA?.

TO NIDAI JAMAA WANNAN FADAN YAFI QARFINA
NAYI NAN=??=?? @&? @&? @&? @&? @&?



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5? _____________________________
_kin dade kina cizon yatsa kan yadda ake kacalcala suturun yaranki da dinkuna marasa ma'ana?_

_HUGUMA na miki albishir da wajen zazzafan dinki na MS KIDDIES WEARS,irin dinkunan yaran da kike gani a Instagram TikTok suna burgeki kuma bakisan inda zakikai ayi miki ba ko kina tsoron tsada_

_Zafafan dinki na gayu da ado kiga yaranki sun fita dagwas dagwas_
_ready

_MS KIDDIES na nan kano gwammaja_

*TRUSTED AND TRUSTED mun gwada mun gani*

_Maza tuntubeta a nan_

+234 708 865 2858

Ko Instagram account dinta

https://www.instagram.com/ms_kiddies_wers_by_nafs?igsh=MTljZWQwM2FsaXlxaA==
______________________________


115



Dukkanin wani da yake numfashi a wajen saida jinin jikinsa ya daskare na wucin gadi,qwaqwale da yawa suka dakata da aiki na wasu mintuna,yayin da idanuwa sukayi warwaje a kansa. Kowa dubansa yake d wani irin madaukakin mamaki da tarin ba zata,dukkaninsu kowa kwanyarsa ta kasa fahimta ko sarrafa maganarsa.

"Mem.....me kake cewa fu'ad?" Anni mutum qwaya daya da tayi qarfin halin sake tambayarsa tana jin yadda jinin jikinta uske tsinkewa. A nutse ya dubi annin nashi,yana da qwarin gwiwa da zato me yawa a kanta,don haka kansa tsaye yace.

"Na aurar da amna ga musaddiq cikin masjid nabawi bisa shaidu da wakilai da sadaki dala dubu biyu" Sai a sannan kwanyar wasu daga ciki ta harba ta kuma dawo da aiki,ciki harda amna.

Wani tsananin tsoro taji yana shigarta,ta shige jikin anni tana buya a bayanta gami da cukuikuyeta,idanunta kuma suna sauka kan fuskar maamah. Wannan fuskar da take bata wani tsoro haka kawai,fuskar da batason kallonta saboda duk wani yanayi da alamu na rashin wanzuwar alkhairi tattare da ita tana ganinsu......a yau mamallakiyar wannan fuskar itace a mazaunin surukarta?.

Shi kuwa musaddiq kama hannun saddiq yayi ya riqe da kyau yana qoqarin tuna maganganunsa da hamman masa mintuna ashirin baya da suka wuce kafin ya shigo cikin asibitin. Abubuwa biyu ke masa kai kawo suna gwarabkiya cikin zuciyarsa,farinciki da kuma fargaba da wani sofane na tsoro dan kadan. Kalaman bakin maamah wani irin daci da dafi ne dasu wanda ya kasa sabawa da jinsu,baya qaunar komai ya hadashi da ita alkhairi ko sharri,dadi ko akasinsa.

Idanu kawai anni ta zuba ma fu'ad tana jin tsigar jikinta na tashi. Wanne irin tashin hankali ne haka fu'ad din ya rakito mata tana zaman zamanta tana lallaba tsufanta?. Wacce masifar ce ke shirin wanzuwa?,meye kuma zai afku gaba ga amnanta?.

"Allah ya sanya alkhairi......yasa anyi a sa'a" Lafuzzan suka fita daga bakin maamah da tayi qoqarin ware idanunta daga qanqancesu da tayi.

Ba wanda kalamanta basu bawa mamaki ba.......kaman yadda suka janyo hankalinsu ga fuskarta wadda ta maida idanunta kan takardar hannunta tana qoqarin hana zuciyarta tsananin bugun da takeyi,tare da fatan gumin dake yanko mata ya tsane jikin atamfar jikinta ba tare da kowa ya gani ba.

Abu guda daya data sani shine......tabbas fu'ad ya siyawa amna tikitin salwantar rayuwarta......don bataga ta inda zata bari itakam da ranta da lafiyarta ta hada jini da alhj hamza kibiya ba..... Idan fu'ad baiyi wasa ba a wannan karon,zata rufe idanunta tayi hukuncinta kan me uwa da wabi......zata mance da alaqar dake a tsakaninsu tunda har ya iya mancewa da matsayinta a wajensa.

Saddiq musaddiq harma da amna sai lafazin maamah din ya sanya suka fara jin abinda ke ransu yana sassauta,wanda sam ba haka bane a qirjin anni da fu'ad. Wani duba sukaci gaba dayi mata,kowannensu yana son karanto ainihin ma'anar maganarta.

Sun riga da sun sani.........banza bata kai zomo kasuwa......hakanan kowa ya tuba don wuya to tabbas babu lada.......ba haka kawai maamah zata bada amsa ga lamari me girma irin wannan ba......ba haka siddan zata miqa wuya ga al'amarin daya fado bagtatan irin wanna ba.....TABBAS AKWAI WATA A QASA.

Lokacin da idanunta suka kai kan conclusions na gwajin sabreen din sai ta fara qanqance idanunta a hankali,ji tayi kaman debi yaji an watsa mata cikin idanunta kafin a hankali taji kaifin ganinta kaman yana raguwa.

"Ciki?,sati uku?" Tambayar data samu daman motsa labbanta ta yiwa kanta da kanta kenan.

Iskar dakin taji tana mata wahalar shaqa,kamar babu isashiyar oxygen dake wulgawa ta wajen,takai hannunta wuyanta tana janye mayafin data yafa waiko yana cikin abinda ya jawo mata qarancin iska,still sai taji ba abinda ya canza.

Da gaske iska ke neman mata kadan,wannan ya sanya ta soma jan iska da qarfin gaske tana aikawa hunhunta don ta samu taci gaba da numfashi,yayin da ilahirin jikinta ya soma rawa kadan kadan.

Musaddiq ne ya fara ankara da hakan,don fu'ad tuni ya soma takawa xuwa dakin da sabreen take don kaucewa kallon tuhumar da anni ke jifansa dashi. Baida matsala da duk wani tuhuma na maamah ko kuma kalar kowanne qalubale daga gareta,damuwarsa daya yadda annin dama zata karbi abun,ko ita dinma ya shirya mata,don bayajin akwai wani abu guda daya daya dace yayi sama da wannan din.

"Lafiya?.....kaman numfashinta baya kaiwa" Anni data iso gurin ta fada tana duban hannunta wanda takardar gwajin da fu'ad ya bata ta sulale ta fadi a qasa.

Yanayin sautin anni ya sanyashi dawowa da baya,yadan daga qafa yana qarasowa wajen,sai yayi saurin matsawa wayar dake ajiye a dakin don neman daukin likita ko nurses ya soma kira.

Minti guda kacal sai ga mutum biyu tare da likita sun qaraso,saman wheelchair aka dorata sannan suka turata xuwa dakin da yake daura da wannan.

Dukkaninsu suna farfajiyar dakin daga waje,suna jira suji bayanin da likitan zai fito dashi. Duk bayan sakanni sai anni ta daga idanu ta dubi fu'ad,gaba daya ya gama warware mata zaren tunaninta. Wannan wani abune nashi na daban,tsahon zamanka dashi zaku iya qareshi ba tare da ka iya fadin gundarim halayensa ba gaba daya,yakan zo da abubuwan da hankali da tunani basu kawosu ba,yana da bada mamaki irin hakan,saidai bata taba kawowa zai iya aikata qunar baqin wake irin wannan ba.

shima kansa ya sani,duk wani kallo da anni take masa yana cure ne da mamakinsa,saidai ya sakawa kansa wannan dakiyar da juriyar da wani irin basarwa,don haka ko sau daya yaqi kallon anni,saidai yasan shi take kallo ta gefan idanunsa.

Basu wani jima ba suka fito,suka qaraso gaban fu'ad din.

"Ba wani abu bane me tsanani,kawai ta shiga shocked sosai daya sanya jininta hawa lokaci guda......irin wannan case din yana iya jawo mutuwar barin jiki ko bugawar zuciya idan yazo da akasi.....zuwa yanzu dai ita Allah ya tsallakar da ita,saidai kuma jininta yahau sosai,an mata allura ya kuma sauka alhmdlh,nan da awa daya ma zata iya tafiyarta gida.......amma fa sai tana kiyaye saka bacin rai da damuwa a ranta".

"Na gode Dr" Fu'ad ya fadi yana bawa Dr hannu sukayi musabaha ya wuce.

Musaddiq ya kalla sai ya taka zuwa cikin dakin saddiq ma ya bishi. Idonsa yaketa qoqarin kawarwa daga annin don kada su hada ido ya soma takawa zai shiga ya duba maamah din amma sai sautin annin ya katseshi.

"Ka kyauta" Ta fada kai tsaye,abinda ya sakashi dakatawa daga tafiyar da yakeyi kenan. Shuru ya ratsa na wasu mintuna,sai kuma ya dawo da baya a nutse ya tsaya gaban annin.

Hannuwanta ya riqe yana zaunar da ita daidai sanda take fadin.

"Kaga irin abinda ka jawo ko?" Zame takalmin qafarsa yayi ya zauna sosai a gabanta ba tare daya damu cewa marbles bane a wajen.

"Ban jawo komai ba anni.....kuma komai bai faru ba,ko ba wannan maganar irin wannan ranar irin wannan lokacin yana dab da faruwa da maamah....... Tunda muka tashi bamu san wani abu farinciki ba sai a sanadinku.......musaddiq ya rasa abubuwa masu yawa tun yana yaro......yanzun kuma a sanadinta sai a haramta masa abinda yake buri yake muradi yake kuma so?,bayan a baya ya rasa abinda yake buri da muradin kuma duka ya haqura?" Tambayar tasa tadan taba annin,saidai duk da haka sai takejin kaman bai kyauta ba abinda ya yiwa maamah,ko ba komai ita ta haifi musaddiq din ta kawoshi duniya.

Ta bude baki zata sake magana yayi caraf ya riqe hannunta sosai,abinda bai taba yi ba. Idanunta ta daga tana duban nasa idanun,wadannan alamun bacin rai mai tsanani din sun bayyana sosai cikin idanunsa,alamun ranshi ya motsu sosai.

"Kina tunanin ga musaddiq......zan bari amna ta auri wani a waje koda baice yana so ba?,wanin da bamu da tabbas a kanshi?,wanin da ban isa na hukuntashi ba idan ya cutatar da ita duk yadda muke sonta kuwa?.........Karki sake cewa komai anni don Allah na roqeki,bakinki kada ya sake furta komai a kansu idan ba fatan alkhairi ba......indai har yanzu kin yarda kina kuma ji a ranki ni da musaddiq 'ya'yanki ne.....amna qanwata ce halak malak kamar yadda musaddiq yake....to karki sake cewa komai sai fatan alkhairi.....ko meye zai faru.....ko menene zai taso anni na roqeki ki saka idanu.....nike da alhakin hakan kuma nine zan dauka". Gaba daya ya gama kashe mata jiki,ya kuma kashe duk wata kalma da yake da yunqurin fadi. Fu'ad din wani mutum ne na daban,ajiyar Allah ne,yana da kaifi wajen komai nasa,kaman yadda nutsuwa da dattako ta mamaye dabi'arsa gaba daya.

"Kai da abba kuka hada baki ko fu'ad?" Anni tayi tambayar a sanyaye. Wani dariya ya tasowa fu'ad,yayi qasa da kansa yana murmusawa kafin ya daga kansa ya sake maidawa ga annin.

"Ba ruruwan abbanmu.....kada ki sashi a ciki anni,aikin Muhammadu ne,ni kadai na kitsa abuna.....saboda asara ce babba ace ba wata dangantaka da alaqa ta dindindin tsakaninmu da ku anni.....kun gama yi mana komai a rayuwa....kun bamu ruhi me tsafta.....ruhi bana rai ba.....ruhi na dabi'a addini tarbiyya da ilimi da kowanne dan adam yake da buqatarsa........ba wata sakayya da zamu iya yi muku sama da wannan" Shuru sukayi dukkaninsu,jinjina kai kawai anni takeyi. Duk duniya ba wanda zai kaita son hada jini da musaddiq......to amma ita fitina ba abar so bace.

"Amma anni......me kike tsoro ne duk da tarin jarumtar da kike da ita?" Ya fada


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login