Showing 123001 words to 126000 words out of 363280 words

Chapter 42 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1435

ajiya" Yakai qarshen maganar yana tura cheque na kudi daya rubuta masa masu yawan gaske. Kai ya girgiza

"Nop sir.....bazan amshi komai ba,aikina ne nakeyi kuma dole mutum irinka a masa aikin daya dace saboda alfanunsa ga al'umma". Wani abu dake gefansa ya dannan wata qaramar ma'ajiya ta fito,ya jefa cheque din yana cewa

"Ba bribing naka nakeyi ba.......wannan din kyauta ne na baka,na jima da sanin wanene kai......inda baka cancanata ba ko qwandalata ba zata shiga hannunka ba.....kana daya daga cikin mutane masu aiki tuquru da qoqarin kamanta gaskiya duk da yadda qasarmu ta lalace.....so you deserve it,xan baka koda bakamin aikin komai ba"

"Thank you sir.....thank you so much" S.nuhu ya fada yana jin dadin gwaggwabar kyautar da me jadda din ya bashi.

Tunda wuri taqi zaman parlor din don batason ma ya dawo shi ya gansu ko ita ta ganshi,ta zame tayi zamanta a daki dole amna ma ta biyo ta can.

Tana saman sofa din dake gefe daya a dakin,amna na zaune saman tattausan carpet din tana assignment. Idanunta kan takardun tana jin sha'awar amna din,tana jin inama ace itace ta samu dama irinta amna?,inama ace ta samu daman zuzzurfan karatu kaman amna?,wadda gata ya sanya tace bazatayi karatu wata qasar ba tsabar samun dama.

Maida bangon littafin tayi tana duban sabreen cikin murmushi

"Done......sai yanzu hankalina ya kwanta...lecturer dinnan mugu ne adda.....any mistake game over" Murmushi ta tayata dashi,ta jawo jakarta tana qoqarin maida litattafan

"Adda......kin taba jin labarin labarin uwar data watsar da yaranta tun suna qananu ba tare data damu da waye zai kula dasu ba?,waye zai zama gatansu?" Takai qarshen maganar tana zuba idonta akan fuskar sabreen. Maganar sai tayi ma sabreen wani iri,a hankali ta girgiza kanta

"Aah amna"

"Kin taba jin labari,bayan wasu shekaru ta dawo garesu,amma kinsan me yasanya ta dawo garesu?" Kai sabreen ta sake girgizawa

"Kudi......arziqi da rufin asirin da suka samu tazo ci,ba yadda suka rayu bane damuwarta......ba lafiyarsu ko akasinta ba". Idanu sabreen ta zubawa amna tana jin labarin ya kasa kama hankalinta,tsahon wasu mintina ba wanda yace da kowa komai,har sai da sabreen ta fara magana

"Wanne irin cukurkudadden labari ne wannan amna?,a ina kika jiyoshi." Qaramar dariya amna ta saki tana janye jakarta gefe

"Labarin mijinki kenan.....hamma na....." Bata qarasa ba shigowar saqo wayarta ya katse sauran maganar dake bakinta. Wani irin shuru sabreen tayi lokacin da hankalin amna yayi kan wayarta

"Maamah?,mariya?....." Abinda kawai sabreen ke iya juyawa cikin ranta kenan

"Bai rayu da ita ba?......batasan komai nasu ba?......batasan wahalarsu ba?,dukiyarsu tasa ta dawo??,dukiya???" Tarin tambayoyin da suka jujjuyawa cikin kwanyarta kenan. Maganganun amna gaba daya sai suka kasance mata kamar ta jefeta da wata cukurkudaddiyar sarqa,ta kasa hada daya da daya ya bata biyu.

"Unbleavable!......oh my god!" Amna ta furta da wani irin qaraji,abinda ya yanke zaren tunanin sabreen kenan,ko kafin ta farga har amna ta fado jikinta ta cukuikuyeta

"From nigeria to Maldives........wedding bells adda.......wedding bells" Ta fada tana dariyar dake cakude da farinciki zalla a muryarta. Qoqarin dagata sabreen takeyi cikin murmushi da mamakin abinda ya sanyata tsananin farinciki irin haka

"Zaki karyani auta" Ta fada a dan shagwabe tana riqe amna din. Da sauri ta dagata tana fadin

"Am sorry adda.....wani irin mamaki uncle BB ya bani......yayi surprising dina irin wanda ya jima baimin ba......adda hutunmu na wannan shekarar zai fara daga Maldives......kinsan mafarkaina akan wajen kuwa?,kowanne year idan anzo zaben wanne qasa za'a je idan na kawo sai BB da saddiq sun kushemin.......yaa musaddiq kawai ke goyon baya na" Ta qarasa maganar muryarta a narke,da alama tana jin haushin yadda abun yake kasancewa. Dan murmushi sabreen ta saki,don ita inda take maganar ma batasan ina bane ballantana tasan muhimmancin da yake dashi ba da za'a dokanta aje.

"Your dream have come true"

"Really adda.......adda wannan shine tafiyan da zatafimin kowacce dadi da alama......ina da sister like you nima wannan karan.......ha saddiq ya daina yimin gori idan za'a fita......i don't know yadda zan miki bayanin Maldives......but gani ya kori ji" Dan qaramin murmushi ta aje mata kawai don ita bataga wani abun doki ba a nan.

"Labari na biyu adda.....muna da biki,borno zatayi kira......bikin BB farouq date din yayi daidai da dawowarmu da sati biyu kacal".

"Ma sha Allah.....Allah ya sanya alkhairi"

"Wannan qarshen shekaran bame sauqi bace adda......can't wait......bari na bawa besty labari" Ta fadi tana laluben number wayar aminiyarta guda daya da take da ita.

"Adda......anya ba honeymoon BB farouq ya hada muku keda hamma ba?" Amna ta dakata daga qoqarin kiran besty din nata da take tana duban sabreen. Bata jira ma sabreen ta bata amsa ba ta saki dan qaramin ihu tana tsalle gefe

"It makes sense=?L?.....that's my big bro farouq" Amna ta fada tana dariya nishadi kaman zai kasheta. Baki kawai sabreen ta kama tana kallon amna

"Amna......nace miki binku zanyi?". Tana dariya ta bata amsa

" It's for the whole family adda........kowa ma yana tafiya hutu a wannan lokacin,indai kai under jadda family kake......hatta ma'aikatan dake aiki cikin gida lokacin hutunsu ne.....kawai dai,nayi mamakin rage date din da aka saba tafiyan" Ta fada tana duba wayarta.

Rasa abinda sabreen zata fada tayi,maganan gaskiya ita sam bata shirya zuwa ko ina dasu ba,don bata jin tana cikin family dinsu,hasalima tazara take son bayarwa tsakaninsu.

Duk sanda amna ke waya da qawarta ita tayi nisa wajen juya maganganun amnan. Wani irin mamaki ke tsarga mata,wai dama haka matar take tun usul?,ta yaya zata samu gaskiyan abinda amna ta gaya mata?,tun tale tale gurbataccen hali gareta?,indai haka ne mene yaran sukayi me muni da zata cutar dasu?. Kwanyarta ta sake harbawa,da qarfi da yaji ta soma qoqarin hada daya da biyu ko zata bata daidai




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

67


_Manzan Allah S A W yace "idan dayanku zaiyi fada/zai daki dan uwansa,to ya guji fuska/kada ya mari fuskarsa_

>???


"Biri yayi kama da mutum,tsananin qaunarta da duniya da kuma dukiya,shine silar qoqarin mallakar d'anta ta qarfi da yaji?,wannan shine daliinta?". Numfashi ta fitar me nauyi tana saka hannuwanta saman fuskarta

" Adda......maamah keson magana dake" Amna da sunan maamah din ya fito ta true call din ya gaya mata wace ta fada kai tsaye,duk da bata da tabbacin da sabreen takeson magana.

Hannu kawai ta bawa amna,tana maida wayar kunnenta.

"Har yanzu kina kan bakanki?,kinci gaba da lamuntar jefa rayuwarki cikin hatsari maimakon tseratar da rayuwar taki?,a naki tsammanin kin tsira kin tseratar da yan uwanki?"

"Idan kura tana maganin zawo ta yiwa kanta mana?". Dif maamah tayi,batayi gaggawar amsa mata ba,don maganar ta jefeta da wani qudundunanniyar ma'ana.

"Kece kike sake tafka kuskure akan kuskure......kuma kwanaki dukka wani sirrinki yana qarewa.......komai yana dab da bakaduwa tamkar yadda iska ke diban lallausan gari tana watsashi cikin mutane........ashe ba kaina kika fara nuna rashin sanin darajar halittar D'A ba......ashe baiwa ce sanin darajar haihuwa a zuciyar iyaye......d'anki bashi da muhalli ko daya a zuciyata ko rayuwata,.....kaman yadda banda sha'awar zaman aure dashi......saidai fita a gidansa da rayuwarsa duka sai sanda naga dama... Kinsan yaushe nake nufi?" Bummm zuciyar maamah ta buga tun bataji qarshen zancen ba

"Zan fita ne a sanda na gama karanta masa ainihin WACCE KALAR UWA yake da ita......ba don ina sonsa ba......sai don alkhairi guda daya tak da yayimin........ya karbo 'yan uwana daga hannunki ya kawominsu......abinda yayi silar takawarsu tudun muntsira......ya sanyasu hayewa duk wasu qananun qullinki.....zan saka masa da iya wannan,don bashi da wata nagarta ko guda daya da zata sanya sabreen sha'awar kasancewa dashi......ki riqe wannan......ki rubuta ki ajiye......sabreen ce zata zame miki silar BANKADA!" Tana kaiwa nan saita kashe wayar ta azata saman cinyarta tana ci gaba da lullube fuskarta

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis" Ta dinga maimaitawa,tsanar uwa da danta duka suna turereniya cikin zuciyarta.

Ko da amna ta dawo abinci kawai taci ta fara list na abubuwan da zasu buqata lokacin tafiyar da abinda zasuje dashi. Ba wani abu data tofawa amna sai idanu da take binta dashi. Ba qaramin jarumta tayi ba da take iya binta da murmushi ba,gaba daya ganin abun take a wani abu maras yuwuwa,ita ba ahalinsu bace,bata kuma tunanin zata zama ahalin nasu.....hasalima gaba daya lissafinta yafi karkata ga qarawarta gaba kafin sukai ga dawowa daga yawon qasashe hudun da suka tsara zasuyi,kowacce qasa zaman sati guda zasuyi,ciki kuwa harda umra data zame musu dole duk lokaci irin wannan.

Dukka maganganun sabreen sukayi mata tsaye a rai,a daren ranar duk inda ta juya furucinta ne ke mata kai kawo a rai.

Tanaso jin rauni game da yarinyar yana sauko mata,amma wannan dakakkiyar zuciyar da shedaninta dake gefe suna gaya mata

_karamar halitta irin ta mace......yarinya qarama me qananun shekaru bai kamata taga rauninki ba.....bai kamata ace itace taci galaba samanki ba_. Abu daya ta kasa samun aminci akan yarinyar shine
'Yiwuwar aikata komai". Ko ba'a fada ba ta sani......sabreen zata iya aikata komai,tana da taurin zuciya da qwarin zuciya dama zarrar da zata iya yin komai.....wannan zarrar tata ita taja hankalinta ta zabota zuwa ga aikin da bata taba kawo komai zai warware da wata irin faduwa da rashin nasara haka ba.

Tunda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba. Ta jira har sanda gari yasha,sannan tayi wanka,ta shirya kaman kullum da qasaitattar shigar nan tata dake qara mata jin izza da jin takai inda ya kamata ace takai din,saidai bata qarasa gabar da take da muradin qarasawa ba.

Wayarta ta fitar ta kira driver dinta,ya tabbatar mata yanzu haka yana cikin mota yana jiranta,kai tsaye ta dauki jakarta tana yafa mayafinta ta fice.

Dab da zata bar falon taji laila na kiranta

"Maamah" Tsaiwa tayi tana jan tsaki,don bata shirya komai ya dakatar da ita ba. Qarasowa lailan tayi,ta kuma zube a gaban maamah din. Sam tun daga waccan ranar bata iya tsaiwa gaban maamah.....magana ce ko gaisuwa zubewa takeyi a gabanta tamkar bawa da uban gidansa.

"Ina fatan ba wani abu nayi miki ba maamah?" Ta tambaya da tsananin tsoron kada ranta ya baci

"Naga zaki fita baki tasoni ko kisa an gayamin ba" . Wani qaramin tsaki maamah din ta saki,wannan abun ya fara isarta,ba wani motsi da zatayi sai yarinyar ta buwayeta. Irin wannan abun da akan fu'ad ya fada tabbas zata iya cewa tafi kowanne mutum sa'ar zuwa duniya. Ko yaya taga fuskarta ta canza takanyi kaman zata fashe da kuka,komai kuma har abinda bai dace ta sani ba game da lailan lailan saita gaya mata

"Unguwa zanje,kafin na dawo ki gyara falo din,ki hada da bedroom din,duk abinda kika gani ki ajiyeminshi inda kika ganshi,kada kibar kowa ya hauramin sama,akwai underwears dina dana cire ki wankesu ki shanya a backyard ki jira su bushe ki dawo min dasu ciki"

"In sha Allah an gama,Allah ya dawo dake lafiya"

"Amin" Ta amsa tana yin gaba. Sau tari idan taso bautar da laila sama da haka sai wata zuciyar ta gaya mata lailan kome tayi bisa jagorancin mahaifiyarta ne,wannan ya sanya take sassauta mata akan abubuwa da dama.

Tafiyar awa daya da rabi cif suka fara gangarawa mummunan jejin,sai da suka sake kashe wata awar sannan suka isa. Daga nesa ta sanya driver din ya sauketa,sannan ta tattare zanin tsadaddar atamfar jikinta ta fara tsallake qayoyi da busassun tsirrai tana wucewa ciki.

Gurine da zaiyi wahala kaje ka taras d wani duk da tarin al'ummar dake zuwa wajen a kulli yaumin neman duniya,tamkar sun manta da wata rana da zaa shimfidesu babu wannan ruhin daya zama masarrafi na motsinsu da kai kawonsu izuwa gurare daban daban.

Ba wata kafa a jikinta da bata fitar da gumi sanda take zaune a gabansa tana jiran bayanansa na qarshe. Da qyar ta samu ya ganta.....don sharadinsa ne baya aiki biyu akan matsala guda daya.


"ZANGON NASARAKI guda daya ya rage miki......BANKADA zata sameki.....tonon asirinki zai fara daga yanzu zuwa kowanne lokaci.....zangon nasararki zai iya narkewa ya dulmiya sanadin hakan!!!" Ya furta da wata irin murya maras dadin amo.

Dukkanin 'ya'yan hanjinta taji sun tattara sun cure guri daya,idanunta suka qara girma saboda wani sabon kalar tashin hankali da bata taba jin makamancinsa ba

"Kanaso kacemin itace zatayi nasara a kaina?!!!"

"Me muka gaya miki wancan karon?!!!!......" Wasu muryoyi da tafi tsammanin sun kusa guda goma sukayi amsa kuwa a wajen kafin bokan ya karba

"KINYI GANGANCIN ZABOTA......SAIDAI TAURARONSA DA NATA TAURARIN KADAI SUKA DACE......ITACE KADAI MAHADIN AIKINKI........zabi biyu gareki.....ko ki kasheta duk wani burinki ya dulmiya ya koma mafarki......ko ki barta ta rayu kina kallonta kuma naki burin shima yana raye amma babu wata dama ko hanyar cikashi.....zan miki wani aiki guda daya......amma daga kansa!....ina me gargadinki kada ki kuskura ki sake dawomin akan matsalar data shafesu.......aiki yayi kyau ko akasin haka......".

"Na gode da wannan dama daka bani.....na tare dakai su dafa maka" Ta fada jikinta yana rawa da jin qarin dama guda daya,abinda a tarihinsa bai taba ba maimaicen aiki.

"Zaayiwa na tare dani da ma'aikata yanka......zasusha jini wadatacce da zasuyi aikin jinkirtawar tonuwar asirinki........yayin da zangon nasararki ya kama......nan da kwanaki goma sha hudu zuwa ashirin da daya......kiyi duk abinda zakiyi wajen ganin muradinki ya cika......ke zaki yiwa kanki wannan aikin.....mun miki alfarmar samun jinkiri kadai.....amma ki sani tabbas RANAR HASARA DA RANAR TABEWA TANA NAN ZUWA.......DOLE KI FUSKANCETA DA DUKKANIN ZUNUBANKI.........KIYI NESA NESA DA MATSANTAWA TAURARINTA........BA NASARA TA KUSA KO TA NESA......NATA ZANGON NASARAR YANA DAB DA FADOWA HANNUNTA".

Duka bayanansa bai wani dameta ba......zangon nasararta da damarta guda daya daya tabbatar mata ita tafi komai yi mata dadi. Kudade masu kaurin da suka haura million hudu ta zube masa,sannan ta fita da baya da takalmanta a hannu ranta fes,tana gayawa kanta dogon zangon tunani ya zame mata dole don samun kyakkyawar mafita.

Tabbas ta kowacce fuska tana da buqatar barin sabreen gidan koda itace murfin nasararta.......gwara tasan yadda zatayi ta maye fareeda da ita a madadin cikar burinta.


&Hadith yana daya daga cikin karatuttukan da suke mata dadi qwarai. Sau tari idan suna karatunsa da rumaisa yafi kowanne littafi daukan musu lokaci.

Ko a yanzun da take zaune tana bita amna na zaune a gefanta,sunata hira da anni wanda rabinta kusan na tafiyarsu ce jibi,lokaci lokaci kuma da tsare tsaren abinda zaa gudanar da bikin farouq.

"Anni....gata karatu take,ki mata magana don Allah" Ta fada a narke. Duk da sabreen batasan akan me amna ke magana ba,amma sai data daga kanta da sauri. Tana balain jin kwarjinin matar da ganin kimarta,daidai nan amnan ta miqo mata wayar tana danne dariyarta hadi da hade hannun alamun am sorry. Da idanu ta nuna mata zan kamaki sannna ta karbi wayar tana sakawa a kunne

"Barka da dare d'iyata.....ina fatan dai bata miki shirme?"

"Barka da dare anni....." Ta fada tana murmushi

"Ya jikin naki?...ina fata dai kinji sauqi?"

"Alhmdlh na warware....anni na gode"

"Ba godiya ai tsakanin uwa da d'iyarta......nace ba,nasan halin yarona sarai,duk sanda tafiya irin haka ta kama saidai a tayashi shirya kayanshi shi kansa,nace idan akwai wani abu da kuke buqata na tafiyar kiyi magana....karki daukeni suruka ameenatu ni mamarki ce,ki rubuta sai a kawo,idan kuma ta amnan zakiyi to saiku fita tare goben,saiki masa magana" Kunya ta sake kamata,bangare daya kuma tana jin wani iri. Ta aza an soke zancan tafiya da ita ne kwata kwata,don tun randa akayi maganar da amnan tace BB farouq yace ta bada details dinta da sauransu bata sakejin komai akai ba.

"In sha Allah anni......Allah ya saka da alkhairi ya qara girma"

"Ameen ameen,a baya magaji ne yake hada masa necessary abubuwan da zai tafiyar dasu.....ina fata yanzun zaki maye gurbin hakan?" "In sha Allah" Ta amsawa annin tana jin wani qaton nauyi ta aza mata akai,daga nan ta miqawa amna wayar ta maida kanta kan karatun.

Amma kuma sai karatun ya gagareta,saboda batasan yadda zata cika maganar anni ba. Batason haduwa dashi kwata kwata,hakanan idan batayi yadda annin tace ba zai zama kaman rainuwa,kuma amna da akayi a gabanta ba zataji dadi ba.

Dabara ce ta fado mata,ta rufe littafin tana duban amna data gama wayar.

"Kina da number magaji din?"

"Eh ina da" Amna ta amsa mata

"Faka faka kiramin shi" Ta furta tana gyara daurin dankwalinta. Sosai abun ya yiwa amna dadi,ta kira magajin ta hadata dashi.

"So nake nasan da meye da meye ake hadama boss idan zaiyi tafiya?". Tayi maganar tana miqawa amna hannu alamun ta bata takarda da abun rubutu.

A ladabce ya dinga zayyano mata tana rubutawa,har ta gama tsaf tayi masa godiya ta yanke kiran,ta miqawa amna bironta ita kuma ta miqe da takardar a hannunta,amna ta bita da kallo tana murmushi. Tasan abinda take shirin yi,zataje ta hada masa jaka tana tunanin baya nan kafin ya dawo,saidai tun daxun taga shigowarsa,kawai bata gaya mata bane tunda ta lura ba hawa saman take ba,itadai adduarta daya Allah yasa adda sabreen din bata cikin sahun shashashun matan nan da basu iya baiwa miji kulawa,duk da itadai a hakanta a halittarta bataga alamun hakan ba.


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login