Showing 234001 words to 237000 words out of 363280 words

Chapter 79 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1361

amna. Number amna ta fara gani saita kira kawai tana fatan ta samu su daga don su suna motar gabansu. Bugu daya aka daga,anni ce ba amna ba,kai tsaye ta fara magana.

"Anni harbi akeyi cikin airport anni.....kice musu mu juya mu koma,munbar hamma a can,dukkanmu mun taho saura shi kadai". Asalin damuwa anni tana cik???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i,amma ta danne don kada ta kashe mata qwarin gwiwa.

"Kiyi haquri sabreena......in sha Allah yana lafiya,don bamusan me yake faruwa ba,da mutane da yawa a ciki bamusan akan meye harbin ya kasance ba....."

"Anni jikina yana bani wani abu.....anni don Allah ku barni na koma"

"Ameenatu" Anni ta kirata da asalin sunanta.

"Na'am anni".

" Kita karanta lahaula walaquwwata illa billah.......bari mu qarasa gida saimu laluba abinda ya faru kinji?". Ba yadda zata iya ci gaba da musu da annin,don haka tace mata to kawai tana sauke wayar daga kunnenta ba tare data kashe ba.

Hannu momma ta miqa ta dauki wayar suka fara magana da anni.

"Ta shiga damuwa,don Allah bahijja ki bata baki,kinga ba ita daya bace,a irin wannan yanayin bata buqatar tashin hankali".

" In sha Allah anni" Daga haka ta ajiye wayar ta kamo hannun sabreen din.

Duk wani kalar bada baki da bada haquri momma ta yiwa sabreen din,saidai kawai tana jin momma dinne bawai don ta gamsu da dukka abinda suke fada ba,tana ji a jikinta akwai wani abu maras kyau daya taba hammanta,a cikin zuciyarta da ruhinta takejin hakan.

Yadda anni taji muryarta ya sanya tayi ma abdur ra'uf magana dukansu suka wuce zuwa mansion House din alhaji hamza kibiya.

A babban parking lot na gidan motocin dukka suka tsaya. Abdulgafar ya qaraso ya bude mata side dinta,su huda da momma suka fita ta daya side din.

Da qyar ta miqe bayan ta zuro qafafunta waje,jikinta idanunta dama zuciyarta gaba daya takejin sun mata wani irin nauyi. Duba daya zakayi mata ka fahimci hankalinta baya jikinta,daga airport din zuwa gidan kuwa idanunta sun fara tasawa saboda kukan data matsawa kanta dashi. A hankali da wani irin sanyi ta zube idanunta akansu anni wadda ke tsaye ita da musaddiq da saddiq,dukkansu su biyun waya sukeyi,amna kuma da alama tanata qoqarin samun wata number ne amma kiran yaqi shiga.

"Anni na kasa samun wayarsa,a kashe take" Muryar amna kenan data sakata jin wani jiri yana niyyar kayar da ita. Baya ta koma kawai ta jingina da motar data fito a cikinta,tana jin momma sama sama tana riqe hannunta.

"Na samu Jordan" Muryar saddiq kenan daya fada da wani irin kuzari,abinda ya sanya anni da su amna duka dawowa gabansa suka tsaya.

Dif sukayi suna jiran joradan ya daga,amma harta qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba. Idanu sabreen ta mayar ta lumshe,tana jin yadda bayan wucewar kowanne daqiqa zuciyarta ke ninka gudu kaman zata tsaga qirjinta ta fito,tana jin wata sallamawa tana ratsata,tana jin cewa da gaske wani abu ya taba mata hammanta......da gaske wani abu ya faru dashi cikin airport din,sai qafafunta suka fara rauni tana jin suna fara gazawa wajen dauke nauyinta.

A kunnenta kira na uku ya yanke ba tare da jordan ya daga ba.

"Wallahi shine.....Allah wani abun ya faru dashi.....naji a jikina fa" Ta fadi da qarfin muryar da har na nesa saida suka jiyota,wanda kafin su huda sukai ga riqeta ta sulale a wajen tana sakin wani tsumammen kuka tana jin mararta na riqewa gam.

Da wani irin sukunannen gudu anni ta qaraso,suka dagata ita da momma Hankalin annin yana tsananin tashi.

"Karkiyi mana haka sabreen......ba abinda ya faru dashi mana.....ga jordan nan an samu wayarsa dagawa ne baiyi ba". Idanunta fal da kuka wadanda zuwa yanzu sun canza launi zuwa red ta kalli anni.

" Indai da gaske lafiya qalau ne ya daga wayar yayi bayani mana?,ya daga wayar yace ba abinda ya faru mana anni?,me ya hana wayar hamma shiga bayan sanda muka fito a jirgi ma ya amsa kira?". Rudata kawai tambayayoyin sabreen sukayi gami da sage mata gwiwa,saita rasa amsar bata. Duk da haka ta rungumota jikinta tana cewa.

"Amma kamar fatan alkhairi ya kamata kiyi ko sabreen da hasashen alkhairi?"

"Na kasa anni.....zuciyata ce taketa gayamin akwai abinda ya faru dashi,ba laifi na bane......DANGANTAKAR ZUCIYA ce tsakanina dashi.....ko meye ya sameshi zuciyata zata gayamin saboda alaqar dake tsakaninmu" . Sosai anni ta lura kaman hankalinta yana neman gushewa ne,don haka ta sake riqeta da kyau tana cewa.

"Shikenan,mu shiga ciki,zan tabbatar miki lafiya qalau yake.....zan kiramiki shi kuyi magana". Tamkar raguwar ciwo ko zugi daga kasu daya cikin dari shine kawai d'an abinda furucin anni ya yiwa sabreen cikin zuciyarta. Anni da momma suka riqeta da kyau kowa cike da fargaba duba da abinda yake jikinta tattali yake buqata kaman yadda tun a madina likita ya gaya musu suka wuce da ita zuwa ainihin babban falon gidan.

Baya kadan anni ta dawo tayi magana da saddiq kan yayi duk yadda zaiyi ya samo ainihin abinda ya faru sannan ta kira musaddiq suka wuce akan yazo ya zauna yayita kiran fu'ad har sai an sameshi ya daga suyi magana ko hankalinta zai kwanta.

Kaman yadda hawaye yaqi tsaiwa a idanunta haka ma kuka yaqi dakatawa. Ruwa me sanyi sanyi anni ta saka aka kawo Mata,ta tsiyaya mata ta miqa mata tana fadin.

"Karbi kisha tukunna ko zuciyarki zatayi sanyi" Kai ta girgiza kawai fuskarta shabe shabe da hawaye,abinda yake taba zukatan su huda kenan har sai da anni ta sanya ma'u ta janyesu zuwa wani falon na daban.

"Ko nasha anni bazai iya wucewa ta wuyana ba.....inaso nasan halin da yake ciki ne kawai". A sanyaye musaddiq daya gaji da kira ana ce masa a kashe take ya dubeta,sai kawai ya ajiye wayar ya miqe tsam.yana duban anni

"Ina zuwa" Ya fada yana fita da sassarfa daga dakin. Kiransa anni takeyi saboda jikinta ya bata abinda zai aikata daga yanayin tashin nasa,amma baiko waiwayo ba bare ya dakata.

"Innalillahi wa inna ilahi raji'un" Anni ta fada tana sadda kanta qasa. Awa guda kenan amma ko daga security dinsa da guards dinsa ba wanda ya samu labarin abinda ya faru. Sun koma airport din amma tun daga tafiya me nisa ma an hana shiga gurin bare su binciki abinda ya faru.....ina yake?,wanne hali yake ciki?. Duk da sun bayyana kansu a mazaunin masu tsaron lafiyarsa amma an dakatar dasu an kuma basu haquri ance su jira,ko meye ake ciki daga baya zasuji.

Zamewa tayi sosai a nan inda tayi sallah tana kukan zuci,tana jin kamar zata hadiye zuciyarta. Batasan ta inda zata fara rayuwa ba idan wani abun ya samu Muhammad........batasan ta yadda zata iya karbar wannnan qaddarar ba.

Me yasa rayuwa zatayi mata haka ne?,me yasa rayuwa zata zo mata da irin wannan yanayin ne?,me yasa rayuwa take wasan kura da ita?,take nesantata da wadanda ta sanya rai da fata me tsanani a kansu?,take nesantata da duk mutumin da zai jibanci lamarinta?,duk mutumin data dora rayuwarta da burinta a kansa?.

A nan tayi la'asar ba tare data ko motsa ba,anni tasa aka shigo mata da abinci amma ko sha'awa baya bata ballantana tayi tunanin ci.

Xuwa qarfe biyar ta koma tamkar ruwa saman abun sallar,zuciyarta na sake yayyankewa da tsananin tsoro da tashin hankali.

Biyar da mintuna anni ta sake shigowa. Duba daya zaka mata itama kasan hankalinta ba'a kwance yake ba. Musaddiq da saddiq da baisan fitarsa ba har yanzu bai dawo ba,hakanan tasa wayar still tana kashe shima tunda ya fita yabar gidan.

A sanyaye ta qaraso gabanta tana qoqarin tattaro dukka dauriyarta waje daya,ta zauna a qasa daidai saitin qafarta tana kallonta.

"Tashi ameenatu" Anni ta fadi cikin jarumta. Kaman ba zata iya tashi ba ta daddafa ta tashi. Amanta uku ba wanda ya sani,abinda ta dauka tayi adabo dashi tunda ta samu kulawa a madeena sai gashi tashin hankali ya sanya ya dawo. A cikin aman nan guda uku ba kalar azabar da 'yan hanjinta basu gani ba,don babu komai a cikin nata.

"Kinyi imani da Allah da ranar lahira?" Kai sabreen ta gyada mata hawaye na fara taruwan mata.

"Kinyi imani da Allah shine me rayawa shine me kashewa?,shike bada kariyarsa akan kowanne abun halitta?". Kai ta sake gyada mata hawayen data riqe suna sauko mata.



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

119


" To inaso ki yarda da Allah ki kama ambatonsa....kibar masa kuma lamarinsa.....karki dauki haqqin abinda ke kwance a mararki ta hanyar hana kanki abinci.....don cin abincinki ko rashin cin ba abinda zai canza saima cutar da yaronki,ki samu wani abu ko ba yawa ki sakawa cikin naki". Hawaye sosai take tana kada kai.

"Ba hanya anni.....bana jin abinci xai samu hanyar wuce kwata kwata".

"To ai akwai abu me ruwa ruwa a ciki,ki duba ko yaya kisha" Ta fada tana buda kwanukan gabanta.

Lafiyayyen kunun gyada ne da yasha madara yayi fari sol,da kanta anni ta zuba mata a mug ta saka sugar dan daidai sannan ta miqa mata.

Karba kawai tayi tana wassafa yadda zata sanya a bakinta,kai.anni ta jinjina mata cikin son bata qwarin gwiwa,wannan ya sakata kai mug din bakinta.

Kurba uku kawai tayi ta dire,annin bata matsanta mata ba ta dauka kawai ta rufe ta bata ruwa. Kurba daya shikam ta ajjiye,saboda batajin zai zauna a cikin ta. Bakinta ya saba da zartsin zartsi na taste din zam zam. Annin ta fahimci haka,don haka ta qwalawa ma'u kira tace ta duba store ta ciro zam zam babban roba. Ba jimawa ta dawo dashi,annin ta bude ta tsiyaya ta bata.

Wannan karon anci sa'a,tas ta shanyeshi ta ajiye cup din,hakan ya yiwa anni dadi,saita matsa ta dauki counter tasbaha ta maqala mata a yatsunta

"Hasbunnallahu wa ni'imal wakil,wallahu galibun ala amrih sau ba adadi" Kai ta gyada a hankali tana jin hankalinta yana karkata ga addu'a maimakon kuka da bala'in tashin hankalin da takeji.

Sai da anni taga ta kama sannan ta miqe a hankali ta nufi qofar ta fita tana rufe mata da nufin dawo dasu huda ciki su tayata zama.

Fitar anni da second talatin kadai wato rabin minti taji kamam muryar musaddiq cikin kunnuwanta. Sakin counter din tayi ta miqe qirjinta na wani irin mahaukacin bugu,cikin sanda kaman barawon daya shirya gagarumar sata ta nufi qofar,ta kamata ta bude a hankali,sai muryar musaddiq din ta fito tas.

"Muje ka gayan me ya faru,koma meye banaso sabreen taji" Taji anni tana fada.

Sakin qofar tayi a hankali ta fara takawa tana biye da bayan annin,duk da cewa akwai ginin hallway daya rabasu basa iya ganinta amma ita tana iya jinsu sosai,cikinta hautsinawa yakeyi sosai,tana cike da tashin hankali da fargabar abinda zataji daga bakin musaddiq din.

Hannun musaddiq kawai anni ta kama kai tsaye ta ajeshi saman kujerun da suke matsakaicin falon,tashin hankali da rudani sunaso suyi galaba a kanta amma tana cinyewa.

"Gayamim musaddiq......ina fu'ad.....ina me babbban suna?" Shuru ya danyi,yana juya yadda zai bata incomplete information,saidai shirunsa zaifi zame mata damuwa sama da amsarsa

"Sun harbeshi" Ya fada a hankali kaman bakinsa bayason fada.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Anni ta shiga maimaitawa. Wani irin bugu maganar ta yiwa sabreen,abu na farko daya fara zuwa kanta shine SUN KASHESHI.

Nutsuwarta da hankalinta ne gaba daya suka fara gushewa,sannu sannu saita fara daina jin abinda musaddiq yaci gaba da fada.....duhu ya fara gilmawa idanuwanta,ta suma sulalewa a wajen ta zube saman rug din.

"Harbin farko ya kauce basu sameshi ba,ya hangi maharbin sai yayi nufin binsa shine ya sameshi a harbi na biyu dana uku......suna tare da yaa farouq,tare ma suka yunqura suka bishin,amma yanxun ba'a ga ya farouq ba,ba'asan ina yayi ba.....shi kansa hamman da jordan dinma ba'asan ina akayi dasu ko yaya akayi dasu ba" Ya qarasa fadawa anni maganar zuciyarsa tana girgiza.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Taci gaba da maimaitawa tana jin zuciyarta na wani irin jijjiga kaman zata ballo daga qirjinta ya fado.

"Musaddiq ina abbanku?" Ta tambaya saboda tana jin duk wata jarumta tata da dabararta ta qare,tana buqatar tallafin abban a kusa.

Kaman yasan shi take nema sai gashi ya sako kai,kai tsaye ta miqe ta nufeshi,bata kuma tsaya bata lokaci ba ta fada qirjinsa hawaye yana sauka daga idanunta,wani abu da bata taba yi ba gaban yaran tsahon shekarun.

"Ya isa ameenatu.....kiyi haquri.....duk inda suke da halin da suke ciki za'a samosu in sha Allah,karki daga hankalinki da yawa,idan hakan ya faru ita kuma sabreen muyi yaya da ita kenan?". Kiran sunan sabreen din ya ankarar da ita,ta janye jikinta daga abban gabanta yana faduwa. Sai sannan ta tuna tayita maimaita innalillahi da qarfi a dazun,wanda zai wahala baikai cikin dakin da sabreen din take ba.

"Bari na dubota abba" Ta fada tana juyawa da sassarfa tana nufar ciki.

Tuntuben da tayi da ita shi ya sakata taja baya da sauri,kasa jurewa abinda idanunta suke gani tayi,sai kawai ta saki qara tana kiran sunan abba a gigice.

Shima ya kadu da jin qararta,wani abu da bai taba ji ameenatu tayi ba komai girman jarrabawa,don haka da sauri yayo hanyar dakin musaddiq yana biye dashi.

"Maza jeka kira mommanta.....kada ka bari yaran su biyoku" Abba yace da musaddiq saboda a yadda anni ta gigice yasan ba zata iya riqe sabreen ba.

Ba shiri momma data tayar da sallar la'asar din da bata samu daman yi ba sai sannan ta sallame tabi bayan musaddiq. A gigice ta duqa gaban sabreen tana dagata,saidai ba wani alamun numfashi a tattare da ita.

"Nutsuwa zakuyi ku taimaketa ta hanyar daukota mu wuce asibiti da ita" Abba yayi qoqarin dawo musu da tunaninsu jikinsu.

Kaman gawa haka suka dagata,suka wuce kuma kai tsaye bakin farfajiyar shigowa gidan,don tuni musaddiq ya sanya an matso da mota gaban ginin.

Makeken private hospital dinnan da babu kamarsa kaf Nigeria suka nufa da ita wato Noor hospital. Idan ka shiga zakayi tsammanin kana qasashen qetare ne bawai a Nigeria ba kuma gida kanon dabo.

Asibiti ne da yake mallakin Muhammed fu'ad jadda.....amma a sirrance mallakar ta kasance,ba kowa bane yasan da hakan. Duk wani kalar kayan aikin da bamu dashi sai a qasashen qetare ya kawosu ya zuba don hana masu kudinmu fita neman magani waje. Donsu din kawai dama yayi asibitin,don babu wani me qaramin qarfi da zaiyi gigin kai kanshi nan. Saidai kuma kusan duka kudaden da ake samu ta asibitin ana tafi dashi ne ta hanyar hidimar al'umma,don baya ci ko karban ko sisi a ciki,saboda baida buqatarsu.

Dr hajar da Dr mubeena ne suka karbeta,don ba wani likita namiji da yayi kuskuren zuwa inda take,duk da dama kusan haka tsarin asibitin yake,mata likitoci mata ke karbarsu,maza kuma likitoci maza.

Cikin qwarewa suka shiga bata taimako don maido numfashinta kan saiti gudun rasa abinda take dauke dashi,sun samu nasara saidai sun mata allurar bacci saboda ta sake samun nutsuwa sosai,don ta shiga shocked ba kadan ba. Sunyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata,harda su scanning da basu tsaya anyi a madeena ba,saidai abinda scan din yaketa nuna musu ya sanyasu a mamaki.

Hankalinta kwance take cikin dakinta tana ninke lace din data siya jiya naira dubu dari tara da tamanin,ta kuma budeshi don ta tabbatar shi dinne. Zuciya cike da saqe saqe da taraddadin cikar mission dinta da tafiyarsa daidai?,ko kuma akasin hakan wato FADUWA wanda ko sunanta bata qaunar taji.

Har yanzu zuciyarta tana mata susa idan ta tuna fattatakar da bokan yayi mata,sam yama qi saurarenta,wanda ita bataga dalilinsa naqin sauraron nata ba bayan tana cika masa aljihu da kudi. Ta dora kyakkyawan zato akan hajja....duk da tasan mutum ne shi da ba'a sakashi ba'a kuma hanashi......amma tana da zato me girma akan hajja din,wannan


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login