Showing 270001 words to 273000 words out of 363280 words

Chapter 91 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

6468

Mamaki sosai malam yayi sanda yake zama saman dayan kujerun dake wajen. Ta zame tana gaidashi kaman yadda fu'ad yayi.

"Ashe da gaske rumaisa take?,sanda take gayamin ke kike auren muhammadu ba dauka shirmenta ne kawai.....muhammadu kayi sa'ar mata da gasken gaske" Malam ya fada yana maida dubansa ga fu'ad. Sabreen fu'ad din ya kalla sannan ya maida dubansa ga malam.

"Tana da tausayi da taimako......tana da yawan sadaka da kuma kyauta,bata wata batayi sadaka ga mabuqata ba......marainiya ce muhammadu......nasan halinka kai dinma.....muna da kyakkyawan zaton nagarta daga gareka......ka riqeta hannu bibbiyu,lada biyu gareka,ladan riqon maraya,ga kuma ladan kula da iyali".

"In sha Allah malam" Ya fada yana sadda kansa qasa. Inama ace malam yazo a sanda yake tsaka da fara cusgunawa rayuwarta?,inama ace malam yazo a sannan ya ceceshi daga feeling guilty da yakeyi a duk sanda ya tuna yadda ya mu'amalanceta a baya?.

Duk da cewa ba laifinsa bane.......yayi dukkanin binciken da zai yi a matsayinsa na dan adam.....kuma abinda ya samu kenan. Da gaske ga a inda kudaden da duk take diba sukafi tafiya kenan fiye da jikin 'yan uwanta,sai yakejin wannan din dama ce ta sake samun wasu labaran a kanta ta wajen malam din.

Hira kadan tayi da malam tana tambayarsa inna ta bada saqon gaisuwa ga rumaisa da shaida mata sun dawo sannan ta koma ciki.

Da kanta ta shirya abun motsa baki ta kawowa malam din,duk da ma'u tace ta barshi amma tace sam malam yafi gaban haka.

Qarfe tara tayi shirin bacci,don tunda ya fita ba sake jin motsinsa ba,ta tabbatar zai wahala idan ba baqin bane suka sha masa kai. Ta dawo parlor din farko da nufin daukan madarar shanu ma'u na fitowa a kitchen da alama ta gama komai na yau sai gobe kenan.

Tana mata sallama amma idanunta akan kwalin hannun mau,tsirfa da tsarabe tsarabe irin na musu ciki haka kawai taji yawunta ya tsinke.

"Amma fa ma'u meye wannan?" Kallon farin box din tayi tayi murmushi.

"Wallahi amna ce ta aikomin dashi,wani doughnuts ne da ta taba ban guda daya ta yafi dani,sai tace zata sake sakawa a kawomin".

"Mu gani" Sabreen ta fada tana matsowa,bude mata ma'u tayi take yawun bakinta ya qarasa tsinkewa gaba daya.

"Don Allah ma'u ko guda daya ne" Ta fada tana narke fuska idonta akan doughnuts din da aka yiwa wankan madara.

Dariya ta qwacewa ma'un,tasan halin ciki yafi gaban haka,bataga abinda zata samu ta hana sabreen din ba,bare wannan da nan da nan idan sunason wani za'a sake kawowa.

"Jeki da kwalin gaba daya" Ta fadi tana tura mata kwalin. Har wani dan tsallen murna tayi,ta amshe tana godiya ta haura saman dashi.

Gudu gudu ta gama shiryawa,ta ware gashinta saman bayanta ta haye sofa tana bude kwalin. Lashe baki tayi tana jin kaman ya mata nisa ta tsaya bude ledar a daidai kawai saita farke.

"Uhmmmnnnnn" Ta fadi saboda yadda wata lafiyayyar madara ta hade da doughnuts din a bakinta

"Ya salammmm" Ta sake fada sanda tayi gutsira ta uku,kawai saita kasa daurewa ta juya bayan kwalin ta kuwa dace da sunan mamallakiyar abun.

*_Maman ummies delight_*+234 803 049 9555

A fili ta karanta komai tana lumshe ido,saita rasa wanne zata fara kira a tsakaninsu?.

Landline kawai ta nufa ta soma kiran amna.

"Addarmu"

"Ba wani addarmu......yanzu amna harki samo abun arziqi irin haka amma ki kasa tunawa dani?". Tsam amna tayi tanaso ta tuna meye,ita ta dauka ma complain zatayi akan sun sauka bata nemeta ba

" Adda mene?"

"Doughnuts mana.....doughnuts din maman ummi". Dariya sosai ta zowa amna,duk yadda taso tareta kuwa sai data fito,karon farko data fara yarda masu cikin ajinsu da zasuga sun fiya fi'ili da neman fitina da gaske sukeyi bawai iya shege bane,yadda ta fadi doughnuts din maman ummin tar a bakinta saika rantse ta santa farin sani,kaman ba yaune cin farko ba.

"To adda mu fara da bismillah mana.....dama anni ta gayamin triplets ne,suna sauka albishir din data fara yimin kenan da alama da abun take kwana tana tashi.....Allah ya bawa hamma juriya,ni dama guduwa zanyi na barku". Baki sabreen ta kama

"Iyeeee,au gayamin kike aure zakiyi kenan" Kunya ta kama amna kaman sabreen tana gurin.

"Ni na isa adda...."

"Yanzu mu ajiye wannan maganar.....ina za'a samu doughnuts dinnan?,na kusa cinye wannan" Ido amna ta zaro.

"Tana kaduna fa?,amma saga kaduna zuwa kano kawo doughnuts dinta kaman kina garinsu ne,sharp sharp ne.....idan ta kama sai asa hamma ya tashi jet a karbo miki" Dariya sosai maganan ta bawa sabreen,saidai da gaske dadin doughnuts din har cikin tsokokinta take jinsa.

"Seriously amna.....am addicted to it......zan samu nayi breakfast dashi?"

"Lemme call her......zaki samu koda wajen 10 ne haka in sha Allah.....ko duba flight din safe sai ayi idan akwai a sako miki.....amma indai shi zaki koma ci hamma yana kwale kwale" Amna ta fada tana qyaqyata dariya tayi kuma saurin katse kiran.

"Kada fa haka ta kasance" Ta fada tana raba ido bayan ta lamushe taji bata gamsu ba. Ledar tabi ta tande madarar tasss ta saka kwalin a gaba har tana fatan inama tana sauran wani a ciki?.

Bata ankara ba bacci yazo yayi awon gaba da ita sassaucin da aka samu kenan.

Qarfe sha daya saura ya qaraso cikin parlor din,idanunsa a kanta,wani soyayyarta yakeji tana sake ratsa dukka qasusuwansa. Bayanan da ya sake ji daga bakin malam sai yakejin kamar ta cancanci sama da soyayyar da yake nuna mata.....kamar ta cancanci sama sa wannan rayuwar da takeyi a yanzu.

Sai daya kammala komai a hankali don kada ya tasheta,ya dawo ya zauna da wayoyinsa. Su anni farouq da musaddiq duka yakeson kira,yanason komai ya kammala da wuri,don kwanaki hudu ne kadai suka rage daurin auren.

Sai sannan idonsa ya sauka kan kwalin,ya jawo ya dudduba yana mamakin yadda aka yiwa ledar tasss,yadan girgiza kai ya kwashe ya zuba dustbin sannan ya dawo ya zauna yana sake duban fuskarta. Wani kyau take qarayi masa kullum,hakanan ba qaramin kyau bacci yakeyi mata ba,murmushi ya subucewa labbansa ya fara kiran farouq.

Kira daya ya daga kaman yana kusa da wayar,muryarsa can qasa yayiwa fu'ad sallama.

"Are you okay?" Fu'ad ya tambaya tana tsayawa cak.

"Am okay dude"

"Ma sha Allah.....ka karba envelope"

"Na karba"

"Ka bude?"

"Na bude dude.....but I'm.....I'm speechless dude.......rubutun jikin invitation card dina da ruwan gold na ainihi?" Murmushi ya subucewa fu'ad.

"Kafi qarfin wannan dude......kada ka sake magana akai.....akwai sadakin fannah a daga envelope din....have you seen it?"

"What?,dowry fa kake magana dude?......wannan gold din ya ninka abinda suke karba a matsayin sadaki......babanta malami ne,kada yaga mun zura da yawa fa".

"Fannah tafi qarfin haka a gurinmu....tunda takeson wannan tsohon tuzurun namu,ta kuma amince zata zauna mana dashi da zuciya daya.....sadakin mace baya yawa a musulunce,ko nawa aka bata yayi,saidai ma yayi kadan,yadda kace babanta malami ne nasan yasan da hakan,sayyadina umar yaso qayyadewa a zamaninsa,wata mata ta tunasar dashi annabi baiyi hakan ba, sai ya qyale shima.... Ka fahimta?"

"Ya ilahi dude.....am speechless seriously"

"Zamuyi fada dakai......ina fata ka riqe data din....kwana hudu......saura kwana hudu dude dina ya angwance" Sautin murmushinsa ya riski fu'ad,hakan kuma ya masa dadi a haka sukayi sallama. A duniya bayajin yana da wani abu da zai iya sakawa farouq dashi koda meye yayi masa.

Musaddiq ya kira wannan karon,shima dai kaman yana kusa da wayar ya daga. Muryarsa da mugun sanyi ya amsa sallamar,still shima tambayarsa yayi lafiya yake?.

"I'm fine hamma"

"Maamah ko?" Shuru musaddiq yayi yana mamakin yadda ya gano haka ta farat daya. Shurunsa ya bawa fu'ad tabbaci,ya sauke numfashi.

"Idan ka dorama kanka daukan damuwoyinta ba inda zakaje a rayuwa,zakayita zamane kamar a inda ta tafi ta barka ba tare da damuwan yadda rayuwa zata kasance maka ba.....na kiraka na gaya maka,kayi magana da musaddiq kai dashi ku duba gidajen nan dana bashi details dinsu ku zaba,za'a hade bikinka sana farouq in sha Allah,so ka ajiye damuwan da bata cancanci damuwarka ba.....ka fuskanci rayuwa da reality dinka.....but kada ka sake ka manta da wannan......ka riqe mana amna sai mutuwa ce zata raba". Mutuwar daya fada ta saukar masa da wani irin matsanancin faduwar gaba......ta kuma tuna masa da maganarsu ta dazu da maamah.

"Mutuwa hamma?".

"Yes.....mutuwa,saboda ita kadaice ta isa ta raba Soyayyar masoya" Shuru ne ya wanzu tsakaninsa da shi,har sai da fu'ad din yace.

"Kana layi?"

"Inaji hamma"

"Good......komai da amna zata buqata ka rubuta ka turamin.....bance ko sisinka ka saka a bikinka ba" Baima jira ya masa godiya ba ya katse,saboda baya buqatarta,yanajin wani wajibinsa ne ya saukeshi.

Anni ce ta qarshe daya kira,amna na kusa da ita ta miqa mata wayar.

Ban gajiya suka yiwa junansu,sannan itama ya buqaci ta bada duk wani abu da take buqata.

"Muhammadu kabar 'yan uwanka suyi wani abun mana?" Murmushi yayi

"Anni sai idan bana raye.....ki fadawa amna ta rubuta komai da take buqata na lefe.....idanma ba zata iya ba tazo nan gidan su hadu ita da duniyat....." Saurin katsewa yayi bai qarasa ba,kunya ta kamashi ya aza hannunsa aka yana sosa sumarsa. Murmushi me sauti ya qwacewa anni

"Ita da duniyarka ameenatu" Murmushi shima ya saki.

"Su rubuta komai,bance ta dauke masa komai ba". Kaman sauran bai jira ta masa wata godiya ba ya katse wayar,ya zubawa sabreen ido wani abu yana yawo cikin ranshi.

Da alama baccin ya mata dadi sosai,amma dole ya tasheta don akwai magana me muhimmanci da zasuyi da bata buqatar takai safiya,yana ganin kaman tayi nisa.

Wayar anni ta ajjiye gefanta,tana jin wani abu yana sauka a ranta. Tabbas fu'ad din wani kyautar Allah ne a garesu,bawai don dukiyar da yake da ita ba.....aah....ta jima da sanin haka tun yana fu'ad dinsa dan makaranta secondary school,fu'ad dan bautar qasa. Wata irin zuciya ce shimfide a qirjinsa,wani irin dattako daya girmi shekarunsa......wani irin halin girma me dumbin yawa.

"Tabbas mariya inda kinsan irin kyauta da alkhairin da Allah yayi miki a rayuwa da baki gudu kin bar muhammad ba.....da baki gudu kinbar musaddiq ba". A tattare dasu gaba daya tana ganin wata irin nagarta ta musamman.

"Hammanki yace ki rubuta ko kije gurin addarki ki.masa list na kayan lefe duka" Anni ta fada tana nazarin amna data fahimci ta yawaita shuru shuru tun daga yammacin yau din.

"Lefe ann?" Amna ta tambaya da wata sassanyar murya

"Wani abun daban kikaji na fada?" Anni ta fada tana nazarinta. Kai amna ta girgiza,haka kawai taji hawaye sun cika idanunta,sai anni ta kasa jurewa.

"Meya kuma?"

"Tsoro nakeji anni......gabana yanata faduwa" Sai hawayen da take maqalewa ya gangaro mata.

"Tsoro?" Anni ta maimaita,kai amna ta gyada mata. Yankewa gaban anni yayi ya fadi,ta sauke numfashi tana ambaton sunan Allah.

"Tashi kije kiyi alawala,ki karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil qafa dubu kafin ki kwanta". Kai amna ta gyada sannan ta miqe a sabule tana fita a dakin zuwa nata.

"Addanmu" Fu'ad dake tsugune gaban sabreen da bacci yaketa danneta ya fada yana leqa fuskarta. Da qyar ta sake bude idon nata a karo na uku.

"Adda sabreen.....tashi don Allah" A cikin baccin taketa mamakin kiranta da adda din da yaketa yi,saita miqe tana daquna fuska.

"Hamma.....bacci"

"Zakiyi,na miki alqawari,amma kafin sannan jeki wanki fuskarki ki dawo". A daddafe ta miqe saboda nauyin bacci,ta lalubi toilet din ta shige.

Ba jimawa ta fito,fuskarta tayi fresh da digo digon ruwa,idanunta sun dan tashi kadan alamun bacci,ta zauna saman sofa tana dubansa.

Ajiye abinda yakeyi yayi ya taso,ya iso gabanta ya tsugunna a hankali. Hannuwansa yakai ya kamo tafukan hannayenta a tausashe.

"Adda sabreen" Ya maimaita fadi yana murmushi. Idanu tadan ware tana dubansa wani malalacin murmushi yana qwace mata. Kai ya jinjina mata.

"Kin bamu daman neman auren sister huda?.....kin bamu izini mu nemawa musaddiq auren sister huda?".




*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_Bgawo's KITCHEN AND APHRODISIAC_*


*_WATA KILLATACCIYAR MASARAUTA CE,WADDA KE QUNSHE DA DUKKAN NAU'IKAN ABINDA KUKESO_*


*_GIRKE GIRKE NA ZAMANI_*

*_KAYAN MAQULASHE DA NAU'IKAN DRINKS KALA KALA_*

*_INGANTATTUN TSUMAMMUN MAGUNGUNAN GYARAN MUTUNCIN 'YA MACE......GYARA IRIN NA IYAYE DA KAKANNI DA INGANTATTUN MAGUNGUNAN DA BABU DUNGUSHE KO KOKWANTO A KANSU_*

*_KALAR MAGUNGUNAN DA SAO WAJEN IYAYENMU NA DAURI.....INGANTATTUN SAUWOYI DA SAQE SAQI DA AKA SARRAFASU ZUWA MAGANIN GYARAN DIYA MACE_*

*_BIKI KUKE DASHI KO SUNA?_*

*_SAUKAR KARATUN QUR'ANI?_*

*_KO KUMA WALIMAR AURE QARIN MATSAYI A GURIN AIKI KO KUMA WANI QWAR QWARYAN TARO?_*

*_KO YAU DIN BAKIJIN SHIGA KITCHEN?,TSAFTATACCE KUMA INGANTACCEN ABINCI KIKE BUQATA A CIKIN WARMERS DINKI KO FOOD FLASK?_*

*_HAIHUWA KIKAYI?_*

*_KO GYARA ZAKIYI KAWAI A MATSAYINKI MA CIKAKKIYAR MACE?_*

*_BGAWO'S KITCHEN SHINE MUHALLIN DAYA DACE DA DUKKA WADANNAN BUQATUN NAKU_*

_Maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number wayar_

08104553105
08127084190

*_zaki godemin qwarai da haduwa da BGAWO'S KITCHEN_*


*_BGAWO'S KITCHEN_*
*MATATTARAR BIYAN BUQATUNKU*




136


Wani saukar ba zata zancen yayi mata,wani irin zuwa ya yiwa kunnuwanta.

"Saddiq kuma?,saddiq dai hamma?" Ta fadi da sautin muryar bacci da har yanzu bata gama warwarewa ba,banda ta zuba ruwa saman fuskarta da sai tace cikin jerin gwanon mafarki kawai wannan maganar take dibanta. Murmushi ya saki me sanyi yana jinjina mata kai.

"Eh......saddiq dinmu addanmu......inaso ya zama mijin huda nan da kwana hudu,kaman yadda farouq zai zama mijin fannah in sha Allah" A hankali ta daga ido tana sake duban fu'ad din,sai takeji kaman wasa yake mata da hankali kawai ko tsokana,saidai kuma ko daya bataga wannan a cikin idanunsa ba.

"Hamma.....huda fa?.....ka manta mudin ba kowa bane hamma.... Mu din ba wasu madaukaka bane,ni din kawai a cikin family dinku ya isa,basai huda ta shigo ba...."

"Shshshsh" Ya fada yana dora yatsantsa akan lips dinsa. Bayason wannan karayar da take nunawa,bayason wannan raunin da yadda har yanzu ta kasa jinta kaman kowa.....bayason yadda ta kasa daina tuna wacece ita a baya

"Damu daku dukkaninmu abu daya ne yayimu.....jirgi daya ne ya kwaso mu.....ki manta akwai wani lokaci da abinci da sutura suke gagarar muhammad fu'ad?....ki manta akwai wani lokaci daya shude da yunwa take saka musaddiq kwana yana kukan yunwa?,kin manta wani lokaci daya shude fu'ad dan jari bola ne?......kin manta sanda saddiq ke kwana da yunwa saboda ba gatan uwa a gefansa?,duka damu daku ki gayamin meye banbanci a ciki?" Shuru tayi tana tuna komai kaman yadda yake tunasar da ita yanzu.

"Hamma.....amma huda batayi qanqanta ba?.....yanzu zata gama secondary school fa......a haka an sanyata a makaranta da wuri kaman yadda abbanmu yake mana....." Murmushi ya saki yana dan jan kumatunta.

"Qanqanta?.....ke din kanki duka duka shekara nawa kika bata?,banajin yakai biyar,ba gashi muna zaune ba?".

"Hamma karatunta fa?" Hannu ya sanya yana dungure mata kai da sauri

"Lallai dai sai an ja mana aji kafin a bamu auren sister huda.....lallai ko yaya wai sai an wajiga mu?.....me huda zatayi da karatu duniyata?,ba huda ba.....ko wanda ke rayuwa qarqashin inuwar jadda banajin zai buqaci karatu saboda ainihin buqata ta lalura.....saidai duk me sha'awa yayi karatun don dai sunansa ilimi.....ba abinda huda zatayi da takardu.....saidai.idan har tanason karatu saddiq bazai hanata ba.....za'a dauko mata duk kalar malamin da takeso ya koyar da ita matakin ilimi daga na college har zuwa university har PhD ma.......idan kuma makaranta takeso......ta zabi duk makarantar da takeso a fadin duniya cikin jerin qasashe da muke dasu a duniya 195 zuwa 200....kowacce take so zataje in sha Allah......sai me kuma......a shirye muke mu karba duka qorafinki" Ya qarasa fada yana tsareta da ido tare da jiran abinda zata sake fadi.

A hankali ta jinjina kai

"Na amince hamma.....na bada izini bisa sharadi da alqawarin zai bata dukkan wata kulawa data dace koda bayan raina". Wani zazzaro idanu wajen fu'ad yayi yana dubanta.

"Kul.....karki sake zancan bayan ranki my world......waye ya gaya miki fu'ad yana da sauran rayuwa bayan babu taki?". Idonta ta maida ta lumshe a hankali tana murmushi.

" Zamu rayu tar in sha Allah......zamu kula da yaranmu mu kuma basu tarbiyya tare" Ya fada yana sumbatar hannunta a tausashe.

"Na gode sosai duniyata.....na gode sosai da sadaukarmana da daya daga cikin abubuwan da kike matuqar so a duniya.....kika yarda ta zama abokiyar rayuwar saddiq"

"Kafi qarfin komai a wajena duniyata.....kafi gaban haka muffin". Ta fada itama harshenta da sautinta cike da qauna da soyayya.

" Bayan gidan malam......sai ina da ina kike kai taimako?" Ya sake soko Mata tambayar da bata taba kawota ba. Fararen idanunta ta daga ta kalleshi,sai kuma ta sauke idanun nata qasa tana jin nauyinsa. Batason abinda zai sanya ya dauko mata wannan zancan na abinda ya wuce a tsakaninsu.

"Ki bani dama.....inaso ki dore da aikin ladan da kikayi niyya in a halal ways.......inaso na miqar dake kici gaba da abinda kika fara a baya". Sake kallonsa tayi a karo na biyu......tana jin yana sake shiga rayuwarta yadda ya kamata. Soyayyarsa tana sake hudata,wani mafarki ne wannan nata,dasu take kwana dasu take tashi.....hayewar su huda kawai bai sanya zuciyarta ta kwanta d'ari bisa dari ba.....bai sanya zuciyarta ta samu nutsuwar da take yunwar samu ba. A yanzun a kuma wannan lokacin sai gashi ya gama qarasa karanta tunaninta kafffff yana son xike mata ragowar gibin da ya


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login