Showing 177001 words to 180000 words out of 363280 words

Chapter 60 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1455

Raba jikinsa yayi da qofar ya fara takawa a nutse yana dosarta.

Dukan hankalinta yayi nisa wajen killace plates din data wanke. Kwata kwata bata kawowa ranta wai dawowarsa ba ballantana shigowarsa kitchen din ba. Ta gama jerawa tayi taku biyu baya don matsawa daga wajen,santsin man daya diga a qasan tiles din ya kwasheta,tayi baya zata fadi a matuqar tsorace. Hannayensa ya sanya duka biyun ya tarota,take ta samu masauki a faffadan qirijinsa.

Gam ta sanya hannu tana riqeshi ba tare data fahimci a jikin wanda take ba,tunaninta duka ta samu wani abunne ta kama.

Fadowarta jikinsa ya bashi daman qarewa kyakkyawar fuskarta kallo. Karon farko da wannan tsiwatacciyar fuskar ta fito a matsayin matsoraciyar fuska. Sauke idanunsa yayi saman qirjinta dake sama da qasa alamun tsoro muraran da kuma yawan adadin bugun da zuciyarta ta qara. Cikin qasa da second ashirin hankalinta ya fara dawowa jikinta bayan ta tabbatar batasha qasa ba,ta zuqi numfashi sosai wanda hakan ya taimaka mata wajen isar lallausan qamshinsa qofofin hancinta ya kuma isar da saqon waye me turaren cikin kwanyarta.

Idanunta ta ware da sauri,take suka fada saman fuskarsa dake dab da tata,sukayi wani zuzzurfan musayar numfashi daya hautsina masa tunani karon farko. Kyakkyawar fuskar nan tasa dake shimfide da wani irin kyau da ba kowacce fuskar d'a namiji ke da baiwar irinsa ba.....wani irin kyau me cakude da kwarjini musamman cikin narkakkun idanunsa da kallon cikinsu yasha banban da idanun kowacce d'a namiji data taba kalla.

Cikin sauri ta tura qirjinsa baya tana zamewa daga jikinsa,saidai ya gwada mata halittar sam ba daya bane ta hanyar miqa hannunsa ya damqota. Wata kyakkyawar runguma yayi mata ta baya gana matseta cikin jikinsa,ya aza fuskarsa saman kafadarta,sannan ya motsa labbansa da wani irin nannauyan numfashi.

"Am back.....am home.......but......" Ya fada yana dagata gami da juyo da ita gaba daya tana fuskantarsa sosai. Raina kanta tayi sosai ganin yadda ta koma 'yar qarama a gabansa,ya kuma ritsata da wannan kallon nasa yana duban duka qwayoyin idanunta kafin ya jefa mata tambayarsa.

"You break my rules hajjaju.....don't blame me indai na tashi hukuntaki" Yayi maganar cikin nuna mata da gaske yake yana miqa hannunsa zai shafi gefan fuskarta. Baya taja da sauri,abinda ya sanya ya tsaya ya zuba mata ido. Da gaske take batason koda yatsarta ya taba.....ko yaya ya kusanta kanshi da ita saitayi wani abu da zai nuna bataso.

"Ya kamata kabar kitchen din nan kafin wani ya shigo ya ganka" Ta fadi masa tana qoqarin maida hijabinta. Taku uku ya isa gabanta,ya sanya hannu ya fusge hijabin yana kuma jawo kujera dab da ita ya zauna ranshi a hade yana fadin.

"Wace irin mace ce ke?.....bakiyi kewata ba?" Yayi tambayar da gasken gaske tun daga qasan zuciyarsa,yana fatan ko sau daya yaji tace tayi kewarsa.

Wani kallo ta watsa masa sannan ta janye idanunta,ta taka tana kashe gas din sannan ta soma tafiya a nutse zuwa bakin qofa. Iya hakan ya bashi tabbacin ficewa zatayi,ba kuma zaka kulashi ba kenan. A zafafe ya miqe yana wurgi da hijabin nata,ya sake shan gabanta yana mata wani duba nakai tsaye. Ko ba'a gaya mata ba zuwa yanzu tana saurin gane abinda ya taba zuciyarsa. Sauyawar yanayinsa wani abu ne da yake saurin razanata.

Soma hade tazarar dake tsakanin su yayi yana duban idanunta sosai.

"Na tsani nuna halin ko in kula......na tsani wannan attitude din.....Please behave.....or I'll have to take disciplinary action" Yayi maganar har zuciyarsa yana nufin abinda ya fada din soft lips dinta masu kalan red dake motsawa kadan kadan alamun tsiwa na cinta suna fusgar hankalinsa. Yasha imagination na sanda zata mallaka masa su ba gardama ba tare daya qwata da qarfi ba......bama iya su kadai bama.....dukkaninta yakewa wannan fatan da kuma burin. Lallausan tafin hannunta ya matsa yana sauraren Jin muryarta. Muryar data zame masa abokiyar hirarsa a mafarki tun waccan ranar data amsa wayarsa a garin makka.

Idanunta ta jjanye daga kanshi,har yanzu batajin zata iya kulashi din......duk sanda ta kalli fuskarsa fareeda take gani kwance cikin qirjinsa.....duk sanda ta kalleshi munanan maganganunsa a kanta take tunawa.....muguntarsa da musguna mata da mugayen maganganu,don haka ta taka zuwa side din hagunsa da nufin rabeshi ta fice.

Cak ya dagata ya azata saman kitchen cabinet din ba tare da tunanin tayi kusa da qofa ba,ko kuma jama'ar dake gidan ba. Hannayensa ya sanya ya zagaye bayanta dasu,ya hana mata kowacce dama da zata raba jikinta da nasa,ya kuma yi kane kane a fuskarta ya hanata matsawa ko kadan,da wannan daman ya samu ya riqe lips dinta da suke tsone masa idanu ya fara aike mata da wani irin tattausan kiss. Ba wannan zafin ba kuma wannan hanzarin,wani irin sarrafata yakeyi da wani irin sanyi da salo daya soma zare mata duk wani kuzari da takeji da kuma zafin da takeji a kansa.

Duk wani tunani nata ya tsaya cak tun daga sanda ya wuce cikin kitchen din. Wani abune da yazo mata a bazata wanda bata taba tunanin zai faru ba. Yau fu'ad ne a gabanta ya tsallake yabi mace kitchen da zummar zai samo ruwan dumi?.

Cup din hannunta ta ajiye tunaninta yana komawa baya,ta saita dukkan idanunta da hankalinta akan qofar kitchen din tana lissafin mintuna nawa zaiyi kafin ya fito. Falon yayi shuru saboda wucewar kowa sai ita daya data rage,ta dauke kanta tana duban agogon hannunta bayan shudewar mintuna biyar din data tabbatar ko dafa ruwan za'ayi wadannan mintunan sun wadatar. Kujerar da take kai din sai takejin kamar ta mata nisa da bakin qofar. Miqewa tayi tsam tana canza kujera mafi kusa da bakin kitchen din tana sauke wani zazzafan huci,tanata qoqarin hana zuciyarta ci gaba da hasashen abubuwa daban daban da zuciyarta ke saqa mata.

"Da gaske yarinyar nan 'yar bariki ce.....da gaske bariki takeson gwadamin?.....wai uban me yakeyi a kitchen din?,da gayya ta tsareshi kenan don ta gwada mata iyakarta?" Wadannan tunane tunane su sukaci gaba da kai kawo tsakanin zuciya da kwanyar maamah. Sake matsawa tayi kujera ta gaba tana sake zurfafa jinta da kuma idanunta akan qofar kitchen din,amma bata iya jiyo komai,abinda ya sake assasa baqincikinta. Wai wanne tsautsayi ne ya hanata tsaiwa a nigeria tasa ayiwa fu'ad da sabreen din mummunan farraqu?,irin farraqun da ko me irin sunanta zai tsani ballantana ita da kanta.

Maida idanunta tayi ga agogo tana duba adadin lokutan da aka shafe. To badai dafa ruwan dumi ba....ko dan mutum za'a dafa a wannan gabar yaci ace ya dahu wani irin tsalle zuciyar ta keyi,wani sashe na zuciyar na bata shawarar shiga kitchen din da kanta taga qaryar rashin kunya. Sau uku tana miqewa sai ta koma ta zauna cikin shakka da kokwanto. Batasan ya zataji ba idan taje ta tadda daidai da abinda tunaninta yake bata. Qaqqarfan motsin da taji daga kitchen din ya qarasa tunzura zuciyarta,ta miqe da wani irin gaggawa ta durfafi kitchen din.

Baya fahimtar komai sai sabreen din dake gabansa......kowanne sashe na jikinsa karbar saqo yakeyi iyaka,baisan wanne irin kebantaccen shauqi yakeji haka a kanta ba. A yadda yakejin kansa a lokacin yana jin kamar duniyar ma tayi musu kadan shi da ita. Ya sake zurfafa harshensa cikin bakinta yana sake zare mata duk wani kuzari nata. Qwace masa numfashinsa ya dinga yi yana kamoshi da qyar,a daidai wannan lokacin maamah ta qaraso bakin qofar kitchen din cikin zaton zata samesu tsakiya ko qarshen kitchen din.

Tamkar an juya kwanyarta daga sama zuwa qasa haka taji. Wani irin shock jikinta ya dauka na tsakanin mamaki da kuma tsoro,jikinta da qafafunta gaba daya suka dauki kyarma,saita juya da matsanancin sauri tana jin juwa na shirin kayar da ita. Tana juyawa yana zare bakinsa a nata,baiganta duka ba,amma yaga wani sashe na rigarta. Zazzafan numfashi ya furzar yana cure hannun sabreen dukka cikin kasa hadi da kifi fuskarsa a bayan hannuwan nasu yana qoqarin daidaita numfashinsa.

"Maamah" Ya fada can qasan ranshi,kwata kwata ya manta ya barta a parlor,amma yayi tsammanin yadda anni ta wuce daki itama dakin ta nufa. Daga fuskarsa yayi data sauya launi yana zubesu saman tata fuskar. Fuskarta ta kawar tana qoqarin dauke hawayen dake shirin zubo mata. Ya gansu,don haka ya sanya hannu da nufin dawo da fuskarta saitin nasa,saidai ta rigashi ta hanyar ture hannuwan nasa. A wahalce a kuma kasalance yace.

"Na jima ina baki wannan shawarar......zanci gaba kuma da maimaita miki ita....kada kice zaki gwada raba kanki dani......zaki wahalar da rayukanmu ne kawai......don fu'ad bai shirya rabuwa da duk macen data sanshi a d'a namiji ba......fu'ad bai shirya rabuwa da sabrrrr ba" Yana kaiwa nan ya zame hannuwansa daga nata,yaja baya still idanunshi a kanta yana tunanin maamah na parlor din har yanzu ko tabar wajen.

Har takai qofar dakinta ta fasa shiga,ta samu kujera ta zube tana qoqarin qwato koda abu guda ne cikin tarin abubuwan da suke karakaina a kanta.

Da gaske bariki ne zalla za'a gwada mata?......ta samu nasarar mallakarsa ne?,yaushe ta ingizashi zuwa soyayyarta?,tayi imani a banza fu'ad bazaiso mace irinta ba......matar da karuwanci da bariki suka zama shaida kuma tambarinta na farko koda mutuwa tayi?.

Hannuwansa ya miqa mata bayan ya gama daidaita mode dinsa. Bata ko kalleshi ba bare yasa ran zata bashi hannun nata.

"Musunki da gardamarki zasu iya tunzurani na aikata abinda banyi niyya ba.....karki manta kawaici kawai nakeyi miki.....karki yadda kawaicina ya qare......kika bari hakan ta faru.....to tabbas ki rubuta ki ajjiye zan daukeki na kaiki wata duniya da ba wanda ya isa ya ganki sai muhammad fu'ad shi kadai". Fararen idanunta da suka sake glowing saboda siririn hawayen da yake a ciki ta watsa masa,kai tsaye ya saka hannu yana dafe qirjinsa hadi da lumshe idanunsa kafin ya sauke hannun nasa ya saka hannu ya kamo lallausan tafin hannunta yana sauko da ita.

"Kinci bashi da yawa na rashin kula da abubuwan da suka ratayi a kanki nawa......duk wani abu nawa daya kamata ace kinyi bakiyi ba ki rubuta ki ajiye ya shiga sahun bashi". Kasa musanta masa tayi sanda yake riqe da hannunta suna fita a kitchen din.

Hannun kujera ta koma ta zauna tana hade hannayenta a qirji zuciyarta tana mata wani irin zafi. Bata jin zata iya daukan wannan abun sam ba zata jura ba.....tana da shakka idan har zata iya barin sabreen a gefen danta har xuwa lokacin data tanadar mata.

Sanda ta daga idanun nata don sake duban kitchen din sai tayi kyakkyawan gani,yana riqe da hannunta gam da taketa qoqarin zamewa.

"Kina qarawa kanki laifi akan laifi......please ki hutar da kanki" Ya fada yana lumshe idonsa gami da jin yadda riqe hannunta kadai ke sakarwa jikinsa wadansu kaifafan makamai.

"Muhammadu" Ta kirashi da wani kaifi da yake nuna zallar bala'i da bacin rai da zuciyarta ke ciki,musamman data lura bai ankara da wanzuwarta a wajen ba.


_ayimin afuwa a karbi wannan ba yawa,mu hadu gobe in sha Allah_



*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?


93


Kiran data masan yaja hankalinsu shida sabreen din,idanunsu suka hadu karon farko ita da sabreen suka sakarwa juna wani kallon kallo kafin sabreen din ta janye idanunta salin alin tana kuma sulale hannuwanta daga cikin nasa. Ta kowanne fanni jikinta ya bata al'amura da dama akan matar daga kallon farko kawai,ta danne zuciyarta tadan ciji labbanta na qasa ta taka a hankali tana qarasawa gabanta.

Abinda bata taba kawowa zai faru ba,sabreen din ta zame a gabanta tana fadin.

"Barka da yamma". Ruwan mamaki ya gama kasheta,ta dauke idanunta daga kanta tana maidawa kan fuad din. Sam idonsa bai kansu,kamar ma bashi a wajen.

"Turqashi.....ni zaki saka cikin kokwanto?" Ta ayyana a ranta. Cikin kwanakinsu dashi a saudiyya ta dinga jeranta masa huduba da qorafin rashin kirkin matarsa da fatan samun wata kafa da zata sake nesantata daga rayuwarsa.......a yanzun kuma sai ga yarinyar da take complain a kanta zube a gabanta tana kwasan gaisuwa.

"Ta yaro kyau take bata qarko......idan kinsan wata bakisan wata ba yarinya".

"Lafiya qalau......sai yau kika iya tunawa da wanzuwata?" Tayi maganar tanason tabbatar da maganarta ta farko a zuciyar fu'ad da ya fara wucewa zuwa dakinsu.

"Aah fa.....wannan d'iyar tamu sai kin mata uzuri.......tunda mukazo Maldives ba lafiya.....yanzun haka jinya take" Muryar anni ta ratsa plan din maamah din ta kuma wargazashi,sannan ta saukar mata wani irin gigitaccen yanayi daya hautsina kwanyar maman.

"Bata da lafiya?,me kuma ya sameta?" Tayi subul da bakan jefa tambayar dake yawo tsakanin zuciya da harshenta.

"Tashi daga tsugonan nan karki wahala da yawa.......jeki watsa ruwa ki huta,Allah yayi albarka" Anni ya fadi tana taya sabreen ta miqe. Ko waiwayen maamah din sabreen bata sake yi ba......zubewarta a gabanta yana da nasaba da musaddiq.......mutum ne cikakke d'aya da d'aya,wanda ke tsananin ganin kimarta da kuma mutuncinta......idan har zata iya wuce mahaifiyarsa saboda wani abu daban da tsakaninsu ne kawai.....to tabbas bata mutunta mutuntawar da yake mata ba. Ya girmeta amma baya iya gaidata a tsaye ba tare daya duqa mata ba.....dame zata biyashi.

Yadda maamah tabi sabreen da kallo zuciyarta na wani irin duka ya sanya anni sakin gyaran murya. Dawo da dubanta tayi kan annin ita kuma ta basar tana cewa

"Dazun kina tambayar me ya sameta.....lalurarmu ca ta mata......matar aure ai ba'a rabata da qananun lalurori" Anni ta fada tana ajjiye diffuser din da dama ita ta fito da ita ba tare data sake kallon fuskan maamah ba.

Wani dummm taji kunnuwanta har qwaqwalwarta sunayi. Maganan anni maimakon bata haske sai duhu ma data sake sanyata a ciki. Lalura ta mata ciki ko bari?,wanne anni ke nufi a ciki?. Tsaye tayi a wajen kamar sakarya,kafin wani lokaci falon ya sake zama sai ita daya a ciki.

A daren tayi nadamar da batasan adadinta ba na tsananta bincike har kunnuwanta sukaji mata maganar da ta gaza samun amsarta. Magana me harshe damo mafi rudani data taba ji. Idan tace a daren tayi bacci to tabbas me karatu ma yasan tayi qarya,ta qulla ta kuma kwance har batasan adadin sau nawa ba. Tayi rantsuwa ta kuma lashi takobin muddin ciki ne da yarinyar......muddin tayi kuskuren samun juna biyu da muhammadun lallai saita sakata cikin nadama da dana sanin da babu ranar fitarta. Daga qarshe ta yanke shawarar sanya idanu a dukka motsinsu don tasan wanne mizani zata dora mataki na gaba

&Jiyan tunda wuri ta gama shirinta ta kwanta abinta,don haka daga maamah har d'an nata babu wanda yaga gilmawarta sam. Cikin rashin sani maamah din ta tsareshi wajenta da hirarrakinta marasa armashi,a nata tunanin Daki daya suke kwana,duk da tana kokwanton hakan a ranta,amma zargin cikin da takeson tabbatarwa ya kasa bata nutsuwa ko tabbacin taren suke ko ba tare ba.

Duk da akwai cook dinsu ta musamman dake zuwa musu girki tun a wancan gidan,amma sai ta kasa kwanciya bayan gari ya fara haske. Daga amna har anni da bacci ya dauke saman abun sallah tana tsaka da karatun qur'ani basusan da fitar ba.

Haka kawai takejin bai kamata ace ita da amna duka suna kwance ba har sai sun jira cook tazo. Ta san ba wani qwarewa tayi da kalolin girke girke irin nasu na masu hannu da shuni ba,amma ko yaya tana da rawar da zata taka,tana kuma da gudunmawar da zata bayar,zata kuma iya dafawa aci ba qorafi ko mummunan rashin dadi.

Shuru parlor din nasu,kowacce qofar daki kuma a rufe,haka ta ratsa a nutse har ta isa kitchen din. Bata da tabbacin ya tashi,amma still sai taqi fidda hijabin nata,don ma qarami ne bazai hanata kowanne aiki ba,ta fara duba freezer da ma'ajiyar abincin tana tunanin me dame zata fara aiwatarwa kafin matar ta iso?.

Tunda ta idar da sallah tana saman abun sallar,bawai kuma zikiri ko karatun qur'ani takeyi ba.....aah babu ko guda daya. Ta zauna ne kawai tana gadin lokaci,ta zauna ke kawai tana sanya kunne da idanu akan kowanne motsi da zata iya jiyowa daga parlor din.

Tunda yayi sallar asuba shi dinma bai koma ba,wani irin bacci ne mara dadi kwata kwata ya daukeshi. Zuwa lokacin yana jin kamar haqurinsa yana dab da qarewa,cikin sati hudu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login