Showing 297001 words to 300000 words out of 363280 words

Chapter 100 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1362

ya zube a qasa.

"Zakasan kayi mistake........idiot!" Jordan ya fada cikin tsananin fushi yana masa wani mummunan dauri.

Amna ya daga da hannu bibbiyu,ya cire rigar daya dora daga saman rigarsa yana yafa mata saboda yadda take gayarta haka,ba dankwali bare mayafi. Wani irin zafi zuciyarsa takeyi,ya riqe amna da kyau suna takawa kafin ya kalli jordan

"A yau nakeso su fadamin waye ya sanyasu wannan aikin,a yau basai gobe ba!" Ya fada da tsananin zafin zuciya.

Yau din ta koma masa lovey dovey dinsa,ta koma masa amnansa sak ta shekarun baya,ta mance da wani surukuta a tsakaninsu,ta lafe kanta saman kafadarsa tana rera kuka.

Ita kadai tasan ya takeji a zuciyarta da qirjinta,nata duka me sauqi ne,tana tausayin fu'ad ne a sanda sakamakon binciken ya fito sunan MAAMAH ya zama suna na farko cikin wadanda suka assasa dauketa. A baya wani tsoron matar takeji......a yanzun kuwa sai zuciyarta gaba daya ta qeqashe a kanta. Tayita kwanciya ne bayan ta farfado saboda tsoro,saboda tanason ta tsira da mutuncinta. Tana tsoron ta nuna musu ta warke batasan meye next step nasu ba.

Maamah tayi waya dasu har sau ba adadi......taji kuma muryarta ta sake tabbatarwa da cewa tabbas din itace. Abun ya matuqar bata m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????amaki ita kanta,ya kuma girgizata.

"Wacce irin zuciya ce a qirjinta?" Ta tambayi kanta da kanta a mamakance.

Wani abu me zafi da tauri ya dinga hadiyewa,kai tsaye ya bada umarnin wucewa da amna asibiti don a duba lafiyarta.

Kasa zama yayi ko tsaiwa waje daya,yana jin kaman ya sanya kai dakin da likitoci suka rufu a kanta suna checking dinta. Bashi da wani qwarin gwiwar sanarwa kowa an samu amna din har sai ya tabbatar da cikakken lafiyar amnan,har sai ya tabbatar da cewa ta kubuta da mutuncinta da lafiya da kuma cikakken hankalinta.

A qalla sai da suka kwashe awa guda kafin su fito,cikin lallashi Dr aswad yace mishi.

"Karka damu sir.....komai nata lafiya yake,ba wani abu daya sameta,saidai jikinta da yayi weakening saboda hodar cocaine da suka shaqa mata me yawa.......but shima idan tasha ruwa sosai jikinta zai koma normal in sha Allah".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya maimaita yana jin zuciyarsa tana quntata. Cocaine kuma?,abar da yayi imani ko a ido aka ajiyewa amna ita ba zatace gata ba.

Dakin ya koma,tana kwance tana bacci,ruwan da suka saka mata saboda samun qarin kuzari yana shiga jikinta. Wayarsa ya laluba ya fara kiran number abba.

Daidai lokacin yake rufe shafin alqur'anisa,inda yakai qarshen suratu yaseen daya dauki gabarar karantata tunda abun ya faru sau wani adadi. Ya samu wannan sirrin daga bakin malam,wanda fu'ad ya raba kudi sosai aketa addu'a da kuma roqon Allah akai.

Bismillah yayi sanda yaga kiran daga fu'ad ne.

"Abba......an karbo amna,lafiyarta qalau alhamdulillah,amma muna asibitinmu tana dan shan drip saboda jikinta ba qwari"

"Allahu akhbar......alhamdulillah.....tabbas ubangiji yayi gaskiya da yace ku roqeni zan amsa muku,Allah kaine abun godiya,sannu sa qoqari muhammadu.......inajin bazan shaida musu ba sai wannan drip din ya qare tukunna ta farka,ni zan taho,kafin sannan ina sanya ran qila ta farka".

"Hakanma yayi abba" Ya furta yana katse kiran. Farouq ya kira da temporary line din da yake using nashi a kwana biyun. Kalamansa dukka irin na abban ne......saidai ya cika da mamakin abinda ya sanya fu'ad ya tunkari gagarumin aiki irin wannan bai gaya masa ba.

"Ba lokaci dude.....na matsu na dawowa da anni autarta....besides ma waye zaiyi gangancin dauko ango ya sanyashi a hadari irin wannan bayan bai gama tantance ma zaqin duniyar daya shiga ba?" Murmushi ya sanya dole farouq din ya saki,sai ya yanke kiran shima murmushi yana subuce masa.

Saidai kuma cikin qanqanin lokaci murmushin ya tsaya masa cak,yaji gabansa yana faduwa,sai ya sake lalubar number wayar CP.

Dab da zata tsinke ya daga,yayi apologizing na fu'ad.

"Ba komai.....nace zaiyuwu zuwa nan da azahar na zauna da dukka mutanen nan?".

"Yes sir......zai yiwu,a gida ko a nan?".

"If possible akaiminsu gida,zanwa abdulfattah waya ya bude musu masauki.....waccan dayar matar dake wancan gidan....me take da suna ma?"

"Bibo ko.....habiba mu'azu"

"Yes......itama a daukota,a hadamin ita a cikin su".

"Okay in sha Allah" Ya fada suna yanke wayar.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

*_NACE BA......._*>??????
*_Hajjaju a ina kike siyan turare?....._*

*_NACE A INA KIKE SIYAN TURARE?_*

*_Ga wani fa........TASTED AND TRUSTED ne.......mun gwada munga ingancinsa_*

*_Da yardar Allah saikin godemin_*

*_KUNSAN DUK INDA QAMSHI YAKE ZAKA SAMENI A GURIN,MAGANAR GASKIYA KENAN AHTO_*=??=??

Golden oud
Hawi
Sandal balls
Sandal flakes
Cotton bakhoor
Kabbasine mix
Khumra(alba,alsuma,ebony,monarch,musk)
Deep crush (luxury khumra).
Signature oil
Kuleccham
Kabbasine spray

*_YA SUBHANALLAH.....hajiyata dukka wadannan zaki samesu a_*

*_PRIME SCENTS(the scents of royalty_*

*KE DAGA JIN SUNAN KINSAN ZA'A ZUBDA QAMSHI ME AJI DA DAUKAN HANKALI*

*SUNA NAN A*

*_No 3,kabiru sani lawan street,farawa layout,Maiduguri road kano_*

*BA'A KANO KIKE BA?*

*_karki damu,tuntubeta ta nan,TABBAS kayanki zasu iskeki a duk inda kike cikin aminci da yardar Allah,NA BAKI TABBACIN HAKA_*

*DANNA RUBUTUNNAN DON YIN MAGANA DA ITA KAI TSAYE*=?G? wa.me/+2348103155915

KO KI KIRATA TA NAN

08103155915



148


Ba jimawa sai ga abba,shigowarsa kenan farouq shima ya shigo,abinda ya sake zaunar dashi suna tattauna yadda abun ya kasance.

"Amma don Allah me babban suna......zuwa yanzu ya kamata ka daina tunkarar abubuwa haka kai tsaye,bakai kadai bane yanzun kaman baya daka saba abunka gaba gadi,yanzun akwai nauyi akwai iyali da suka dogara dakai".

"In sha Allah abba" Ya fada ne kawai,amma bayajin akwai wani abu da zai hanashi sadaukarwa da iyalinsa ranshi da lafiyarsa muddin yana raye din.

Lokaci ya duba,bayason ya saba magana idan ya yita,don haka ya miqe yana duban abban.

"Abba zanje gida....don sanda na fita tana bacci ne,yanzun haka nasan tana can da tunanin inda naje da kuma inda amna take"

"Maza ka koma kayi mata albishir,ubangiji yayi muku albarka,ya kareku daga dukkan sharrin zamani.....ya tsare gaba"

"Ameen abba" Sai ya juya ga farouq yana bashi hannu,shima bashi yayi sukayi musabaha suna duban juna,a tare a kuma lokaci daya murmushi ya subucewa kowannensu. Farouq ya gode Allah da abba yake a wajen,ya tabbatar da sai fu'ad ya taba masa iya shege komai qanqantarsa.

"Ka gayawa su musaddiq saisu dauko anni tazo ta ganta itama hankalinta ya kwanta"

"In sha Allah oga" Harara yadan balla masa,yasan da biyu ya fadi kalman oga din,sai ya juya yana fita a dakin.

Tunda ta farka daga baccin takejin ta samu sassaucin qunci da bacin ran da takeji. Kai tsaye daga gadon kitchen ta wuce saboda yadda yunwar data tasheta a baccin ke neman sabautata. Koda ta duba agogo sai taga ashe ta zarta lokacinta ne. Tana cin abincin tana sake sallamawa lamarin ciki,tayi imanin banda cikin a yanayin da take ciki a yanzun ba abinda zai sanya ta iya sakawa cikinta abinci.

Tsaf ta cinye ma'u na satar kallonta.

"Ko a qara miki?" Kai ta girgiza.

"Doughnuts dina kawai nakeso......ya qare ragowan na cinye yanzu da tea,don Allah ma'u ki sakamin order,kwali sha biyu nakeso" Ta fada tana goge hannunta da towel jikinta sam ba wani kuzari sannan ta juya tana fita a kitchen din ma'u ta bita da kallon mamaki.

Eh dole ace ciki yana saka wasu hauka,batasan ya zatayi da doughnuts kwali goma sha biyu ba,doughnuts din matar da madarar ciki kawai ta isheka ta sanya kaji ka qoshi koda kuwa rabin guda daya kaci,ba qaramin jarumi bane wanda zai iya cinye guda uku ba,komai cinka kuwa idan har kaci ukun nan ba sauran space nacin wani abincin saboda ka gama qoshi.

"Allah ya raba lafiya" Ma'u ta fada tana jawo waya ta soma lalubar number wayar maman ummee kada a samu akasi.

Wata lafiyayyar kasala ta saukar mata,sai kawai ta yada zango saman sofa din falon. Zuciyarta na cike da mamakin yadda bataji motsinsa ba ko kadan......hakanan kuma bataga alamun ma ya nemeta ba.

"Kodai da gaske yana shirin rejecting maganata da kuma qaryatani kaman yadda mamansa tasha shan alwashin hakance zata faru?"

"Ga alama kuwa.....ya fara doubting akan abinda kika fada". Fada ne ya kacame tsakanin sassan zukatanta guda biyu,daga qarshe taja qaramin tsaki,ta jawo landline ta soma neman number gidan anni saboda tata wayar a hannunsa ta barta.

Daya daga cikin masu aikin ce ta daga,cikin girmamawa ta gaida sabreen.

"Hadani da huda ko.nadra ko haneefa"

"Okay maa" Ta amsa mata a ladabce. Dukkaninsu ta kawo mata,suka bata lokaci sosai suna hira kafin suyi sallama.

Daki ta koma donyin wanka,sai a sannan ta lura an kwashe duk wani datti kwanuka data zubar. Mamaki yadan kamata,amma saita samu assurance na shine ya shigo din ya fidda kayan.

Tsaf ta gyare dakin,ta wadatashi da qamshi daya qarawa dakin wani irin sukuni da nutsuwa,sannan saita wuce tayi wanka. Tsaf ta shirya cikin wata chiffon gown maras nauyi,ta lalubo Malaysian hijab ta saka sannan ta fita.

Kaman ba zata haura saman nashi ba amma ta daure. Tasan bai kamata ta barshi haka bata gyara ba,kaman yadda bai kamata ta bari wani ko wata su hau ba.

Tsaiwa tayi tana qarewa parlor din kallo. Komai yana nan a zube inda yayi amfani dashi,da alama ma a nan parlor din ya kwana,saita taka tana tattareshi tsaf,ta kuma sanya vacuum cleaner ta tsaftace saman dukka ta gyare masa toilet din. Sanda ta gama azahar ta kawo jiki,cikinta kamar an mata yasa,dole ta sauko dining din qasa neman abinci.

Tunda lalurar nan ta kamata ma'u ta haddace,bata taba barin dining din wayam ba komai,kaman yadda bata barinta ta dawo sake cin abinci ta samu maimaici.

A nutse ta zauna ta zuba da nufin soma cin abincin amma kuma sai taji ta kasa. Azahar ta sako jiki sosai,ina yaje?,abunda tun fara shaquwarsu bai taba faruwa ba.

Ta juya abincin har batasan sau nawa ba amma ta kasa kaiwa bakinta,kaman ahakan ake jira ya faru sallamarsa ya ratso parlor din.

Duk da hautsine yake amma kallo daya tayi masa shigarta taji ta burgeta ta masa mugun kyau. Baqi da baqi a jikin fari,saidai duk da hakan saita wani basar ta dauke kanta tana amsa masa sallamar tan jira taga da wanne irin yanayi ya dawo gidan.

Tsam ta miqe sanda taji alamun takowarsa nan dining din,ta tura kujerar tana nufin wucewa,saiji tayi anyi mata wata Kyakkyawar damqa na tare da bata lokaci ba kuma ya mata wata Kyakkyawar runguma da ta sanya qamshin turarensa mai matuqar sanya nutuswa isa ga hancinta.

Saman wuyanta ya aje fuskar ta,kullum alfahari yake d wannan qamshin nata da yasha banban dana kowacce mace.

"Kina bisa wuyana oum triplets......a yafemin,na leqo kina bacci,banaso kuma na katse wannan daddadan baccin nan.....yaya babies dina" Ya fada yana zamewa ya duqa a gabanta yana yaye rigarta.

Maganganunsa daya saba yi da cikin nata yayi da nufin da yaransa yake magana,ta dauka zai tashi kaman yadda ya saba,sai kawai ya jawota yana tsokanarta ta cibiyarta. Janyewa tayi da sauri ya saki dariya.yana miqewa.

"Anga amna"

"Serious hamma....serous?" Girarshi ya dage mata,saita sauke ajiyar zuciya tana fadin

"Alhamdulillah alhamdulillah.....please hamma"

"Bani hug daya kawai ya isa tukucin yi miki albishir......tausar dare kuma itace tukucin kaiki wajenta"

"Zanyi hamma zanyi wallahi" Ta fada tana dan qaramin tsalle. Riqeta yayi da kyau yana duban tsakiyar idanunta,da wata muryarsa can qasan maqoshi yace.

"Bi a hankali.....yarana" Ya qarasa fada yana dora hannunsa saman cikinta. Kunya ta kamata,ta kuma sanyata janye idanunta da sauri,daidai sanda kira ya shigo masa.

Bai fasa sakata a jikinsa ya matseta ba sannan ya amsa wayar da cp ne ya.kirashi.

"Thank you.....gani nan fitowa" Sai ya katse wayar yana dubanta.

"Zanga baqi my world.....zan dawo shortly in sha Allah....ki kulamin da kanki" Ya fada yana kissing kuncinta duka biyun ya juya yana fita farfajiyar gidan.

Daki ne yalwatacce da aka shimfideshi da lallausan carpet milk color kaman kalan labulayen dakin.

Daga damansa bibo ce ita da zuwaira,sake maida dubansa yayi ga gabansa,mashkur ne shi da dan uwan tasa ta'asar.....mashkur din da gaba daya ya fita a hayyacinsa,tsufa sosai ya kamashi,wani irin tsufa na qarfi da yaji wanda wawulonsa ya sake tsananta munin abun.

Sauran duka ya bisu da kallo,amma kowannensu munin fuskar mashkur ta zarta munin da yake gani a fuskokinsu,bawai muni na fuska kawai ba.....aaah muni na zuciya.

Ma'aikatan gidan jaridar ya fara nunawa.

"Wadannan na gama da case dinsu......aje a hadasu da diyar ambassador......ranar shiga kotu a hadosu tare qarqashin shari'a guda daya,lawyer na zaiji da komai".

"Wayyo Allah.....mun shiga uku,don Allah sir kayi mana afuwa ka yafe mana,wallahi bamusan a kanka tace a buga labarin nan ba". Wani banzan kallo yayi masa.

" Okay,idan wanine bani ba kenan zaku iya tozarta masa iyali,idan wani ne bani ba kenan zaku iya wulaqantashi ku wulaqanta aurensa da shaidar zur.....CP.....bana son sake jin muryarsa a nan wajen" Ya fada yana takawa ya jawo wata kujera.

Kiiiii ya ajiyeta gaban bibo wadda jikinta ketsa tsuma,ya koma ya zauna sosai yana dora qafarsa daya kan daya.

"Nutsu sosai.....labari zan baki sannan na sallameki".

"To....to Allah yayi albarka".

" Ameenatu ahmad sabreen takai budurcinta gidan mijinta,wanda ni Muhammed fuad jadda na karbeshi da kaina....kuma mutanen dake rayuwa damu suka shaida hakan a lokacin". Dif wuta ta daukewa bibo duk yadda takeji da tsageranci sai taji maganar ta girmeta.

"Ke din uwace ko?,a kamatance bai dace na gaya miki haka ba ko?,saidai kash.....nidin bana yafiya bana kuma ragayya ga duk wanda yace zai taba rayuwar duniyata.....sabreen,a inda kuma aka samu akasi shine.....tuntuni kika sanya qafa kika take wannan girman daya kamata ki samu......to ina me!miki albishir.....sabreen takai bantenta......ba wani matsiyaci ko lusarin daya samu damar tsallake wannan shingen......yadda kika dinga yada jita jitan mutuniyar banza ce......na baki dama na biyu kisan yadda zaki wanke wannan sunan daga kanta....ki maida gurbinsa da kyakkyawar shaida,idan hakan bata kasance ba kuwa,a karo na biyu idan na daukoki batar dake zanyi bat.....a bude mata ta tafi gida". Bata tsaya tunani ko waiwayen tazarar nisar tafiyar da zatayi a qasa,ba tare da abun hawa ko kudin mota ba ta fice,tunda har ta samu nasarar shaqar iskar 'yanci kuwa......bataga abinda zai hanata hada lecture din wayar da kan al'ummarta kan muhimmancin mutuncin da sabreen ke dashi ba.

Idanunsa ya ware akan mutum uku.....mutum ukun da yakejin laifinsu yafi na kowa girma,ya sake aza idanunsa akan zuwaira wadda daga ita har bibo sunyi wani zuzzurmawa. Duk da ajiya ce kawai akayi musu irin ajiyar da take daidai da aljannar kare.

"Kamata yayi kema a hadaki da wadancan.....sashen manyan laifuka ko?..." Kuka ta fashe dashi tana hurwa tana neman agajinsa.

"Ki rufen baki,don duk yadda raina yakai ga baci bazan iya zabgawa fuskar dakeda furfura mari ba,koda furfurar ta banza ce" Gum ta koma tayi sannna ya bude idonsa yana sake dubanta.

"Kina gidana kina qarqashin inuwata amma kina neman hanyar da zaa shigo a keta haddin iyalina?!.....abu guda ya rage miki ki gayamin......waye ya sanyaki boyesu a dakinki kika fiddosu da dare zuwa sassan matata!!!". Wata bahaguwar tsawa daya sauke mata sai data tattara gudawa me yawa a cikin mashkur,ya rasa wanne.ibtila'i da bala'i ne yake hanashi furta masa sunan.matar kowa ma ya huta?,fatansa daya wannan tsohuwar ta kira sunanta,wataqila ko kwatance da ka yayi akan shima ita ta dauki.nauyinsa duk da akwai nasa shirin.

"Mmm.......maamah ce" Sunan ya saukar masa cikin ba zata. Fuska ya yamutsa yana dubanta.

"Wacce kenan?"

"Hajiya maamah.....mariya mahaifiyarka" Komai ya tsaya masa na wasu daqiqu,sai daya koma daidai kuma kwanyarsa ta cika da wasi wasi.

"Cp.....janye matar nan,a hadata da wadancan mutanen". Kallo daya ya yiwa mummunar fuskar mashkur,wadda ta jima da tashi daga kyakkyawa zuwa asalin mummuna.

"Mariya ce nima!.....maamah ake ce mata" Ya fada da sarqaqqiyar muryarsa da bata fita yanzu tartar saboda fitar haqora sha biyar daga bakinsa.

Kaman ya dauki takobi ya jefeshi dashi haka yaji,duk wani jini dake jikinsa yaji yana neman daskarewa,kwanyarsa kuma tana shirin yi masa formatting da karan kanta irin na kota kwana,saidai kiran wayarsa yaso maida komai muhallinsa,ya daga kiran bawai don yana gane waye ke kiran nasa ba yana komawa kaman wani shashasha.

"Jordan ne sir.......sir an jona musu na'urar fidda bayanai cikin sauqi,sun kuma yi bayanin komai...."

"Me aka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login