Showing 192001 words to 195000 words out of 363280 words

Chapter 65 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

1429

Tsoronta ya sake ninkuwa tana kallon yadda sukeyin qasa ta bangon glass da ginin yake dashi. Jikinta duka ya dauki rawa ganin yadda halittun ruwa ke linqaya a cikinsa suna wucewa abinsu hankali kwance ta bangon glass din.

"Hamm......" Ta motsa bakinta don kiran sunansa amma saita kasa. Ya jita sarai,kuma yana jin tasirin tsoro sosai a muryarta da jikinta duk da bai waiwaya ya kalleta ba. Idonsa ya lumshe yana son sake jin sunan HAMMA a bakinta wanda sau daya tak ya taba ji ta ambata a wancan ranar. Ba inda zai kawota ya boyeta yadda yake so......ya dora mata karatun da yakeso irin nan din. A nan ne kawai yake da tabbacin cire wannan tsiwar tata gaba daya ba tare da yayita cusa kansa zuwa gareta ba. Yaji dadin samun information din tana da tsoro wasu lokutan,wannan ya sake bashi qwarin gwiwar ci gaba da zama a Maldives ko don saboda ita.

"Nidai.....wannan gurin" Ta sake fada muryarta na sake tsinkewa saboda hango wani babban kifi yana matsowa kusa da glass din.

"Wayyo Allah na" Ta fada da qarfi tana ruqunqumeshi cikin jikinta da wani irin tsatsauran riqo daya sakashi sakin wata qatuwar ajiyar zuciya. Wani irin riqo ta masa da ya tabbatar inda a hayyacinta take ba zata masa shi ba,ya ware idonsa yana duban abinda ya tsoratata. Wasu irin kifaye ne guda biyu masu girma da suka matso dab dasu kaman masu sansanasu,sai suka juya abinsu suna wucewa gami da kada jelarsu. Qaramin murmushi ya subuce masa,inda wannan ne a the Muraka ya fara bata tsoro to tabbas wata babban dama ce a wajensa,zasu kuma qulla kyakkyawar abota da tsoro din.

Duk da sun tafi amma bai tadata a jikinsa ba,don yadda ta maqale shi din shi yayi masa,sai yaji wani sashe na nauyi da bacin ran da yakeji yana kwaranyewa.

"Is okay.....sun wuce fa,ba abinda zasuyi miki..... You're safe na gaya miki" Ya fada cikin sauti na rada dab da kunnuwanta,abinda ya sanya tsigar jikinta tayi wani irin yarfawa kenan.

Fuskarta ta daga a narke tana dubansa,duban da yayi kusanci da yawa a tsakaninsu har suna musayar numfashin juna,tadan taka zata ja da baya ya riqo bayanta ta hanyar tarota da tafin hannunsa yana sakar mata wani irin abu cikin idanun nasa.

"Stay close to me" Ya fada can qasan maqoshinsa yana qoqarin danne feeling da yakeji yana taso masa a kanta. Yana gayawa kansa ba yanzu ba......ba yau ba.

Bata taba jin kasala irin na yanzu ba,saita sauke dubanta daga kansa saidai fuskarta da yanayinta gaba daya ya fidda wani quruciya tata sosai,har ya fara contemplating akan ainihin shekarunta.

"Tsoro nakeji......ka maidani wajen anni" Ta fada da wata shagwababbiyar murya da batasan ta yita ba.

Wani qawataccen murmushi ya saki,ya saketa yaja hannunta zuwa wata lafiyyar sofa dake wani corner na dakin zai zaunar da ita,saidai suna zuwa dab da wajen wasu gungun kifaye suna iso zasu wuce. A zabure ta taka tana sake fadawa jikinsa ta riqeshi da kyau,muryarta da zuciyarta suna karyewa.

"Ka gani ko?" Ta fada kaman zata saki kuka. A wannan karon duk yadda yake danne dariyarsa sai da ta fito da wani irin nutsatsen sauti. Riqet yayi da kyau yana qarasawa da ita gefan gadon ya zaunar da ita,ya koma gabanta ya tsugunna a nutse saman qafafunsa. Kanta ta daga sama,still ruwa ne sosai a saman nasu da wasu halittun ruwan suna rayuwa abinsu hankalinsu kwance,fuskarta a kwabe a kuma narke ta kalkeshi,saita nuna gurin da yatsa tana tabe baki kaman qaramin yaro zai saki kuka.

Gaba daya yanayinta yaji ya tashi kansa.....dukka quruciyarta da tsoronta sun gama bayyana,abinda bai taba gani ba tattare da ita,hakan ya bashi wani irin farinciki da sai daya sanya fuskarsa cikin tafin hannunta yana boye dariyarsa. Baisan haka muraka zai bashi farinciki ba......tabbas da ya jima da kawosu gurin,wannan tsoron yakeson gani cikin idanunta.

Daidaita mode dinsa yayi yana kallonta.

"Meet my gaze" Ya furta da natsatsiyar muryarsa yana cire wasa a yanayinsa. Kaman yadda ya buqata haka ta tattara hankalinta dama idanunta cikin nasa. Bata taba zaton zata iya dogon kallo cikin qwayar idanunsa ba sai yau. Batasan me ya riqeta ba har ta iya kallonsa na tsahon wannan lokacin,saidai tsakanin mintunan taga abubuwa masu yawa cikin idanun nasa......taga kuma abubuwa masu yawa. Wani irin kyawawan idanu da yau ta fara karantar hakan,tsahon wasu mintuna suna yiwa juna kallon qurilla wanda dukkaninsu da yanayin daya haifarwa da kowa,hannunta ya sake riqewa sosai yana murza a nutse

"You're under my watch....I'll shield you.....i promise to keep you safe.....take my word for it" Ya fada yana bata tabbaci.

"Yaushe zamu koma gida?" Ta fada cikin sanyi da wannan tsoron dake gilmawa cikin idanunta. Dan qaramin murmushi ya sake mata wanda ya sanyata qifta idanunta sau biyu akan fuskarsa.

"Is in your hand......." Idanunta ta fidda waje tana waresu a kanshi

"Ni kuma?" Ta tambaya cikin rashin wayo. Kafadarsa ya dage mata

"Yes......" Ya fadi tare da ajiyar zuciya,muryarsa ta sake zama low sosai,yayi qasa d qwayar idanunsa yana kallonta.

"I crave love and affection in my life,i need someone to talk to,someone who cares......ina da anni ina dasu musaddiq,amma inajin still akwai wani ruhi da nake da buqata daban bayansu cikin rayuwata......Can you fill that role?" Ya jefa mata tambayar yana sake tsareta da kallo.

Karon farko da takejin wani abu daban a kanshi. Yana dasu anni amma yana kewar wani abu.....me yasa dukka zancansa babu maamah a ciki?,me yasa duka wannan qaunar da shaquwa da take gani tsakaninsu da maamah bata ganinsa tsakaninsu dasu?.

"Don't stress yourself" Ya fada yana miqewa gami da zame hannunta cikin nasa.

"Which apartment you prepare?,up or down?" Ya tambayeta yana goye hannunsa a qirji yana son ci gaba da ganin drama dinnan tata.

Idanunta ta dan ware a narke tana dubansa kaman ruwan hawaye na kwanciya>?y?,tana tunanin wanne gurinne zaifi mata,ta zauna a qasan ruwa da kifi ya hallakata?,ko ta zauna a saman shima still ruwan dake kadawa yayita kawo mata farmaki?. Qasa cikin ruwa take tsundum da take ganin kaman glasses din da suka zama katangun dakin kaman zasu tsage ruwan ya shigo.....shi kuma saman nisan ruwan da suke ciki kawai ya isheta firgici.

"Is alright......ki zauna a qasan,zan koma saman" Ya fada yana fara takawa. Ai batasan sanda ta hantsilo ta biyoshi a baya ba,ja yayi ya tsaya yana danne dariyarsa.

"Eheennn" Ya fada yana dubanta da salon tambaya. Kasan masa magana tayi,sai qasa da tayi da kanta tana murza yatsunta,haka kawai yau takejin nauyinsa,ita magana ta Allah daga saman har qasan ba inda zata yarda ta zauna ita daya,gani take kaman zata rasa rayuwarta ne. To amma ta yaya zata gaya masa hakan?,fada masa hakan ma ai daidai yake da ce masa su rayu daki daya,idan kuwa zasu zauna daki daya kenan yana nufin suyi sharing komai?.

"We can room mate?" Ya tambayeta a tausashe yana lalubar qwayar idanunta. Tambayan ta mata tsauri,a zahirin gaskiya a yanzun ba wata mafitan da tafi wannan,don dai ita ba zata bari ta zauna ita kadai ba......amma kuma t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ana juya yadda hakan zai kasance.

"Let's room together" Ya fada yana wucewa zuwa matakalun da zasu maidashi sama. Wannan karon sai da yayi da gasken gaske sannan ya hana dariyarsa fitowa,don duk inda ya aje qafarsa nan take jefawa,bata yarda ma ya koma saman ya barta a dakin can qasan ruwan ba. Tana tsaye ya dauki wani luggage me kyau da batasan sanda aka kawoshi ba da wani kwali na daban.

"Ranar farko zai zama a dakin sama.....rana na biyu underwater nakeso nayi bacci......hakan yayi?" Ya fada yana daga gira daya gami d qarewa tsoronta kallo a fakaice. Kai kawai ta gyada don nata da wani sauran zabi,tsoron da takeji ma ya isheta.

"Okay.....stay here.....zan duba wani abu zan dawo yanzu" Ya fada yana bata tabbaci da idanunsa. Kai ta daga masa,tana kallo ya bude qofan ya ratsa living room ya fice.

A sanyaye ta sauke idanunta ga ruwan da take kallo gashi gata,wai a haka cikin daki kake kaman ka sanya hannu ka kamoshi. Kujerar da aka aje gaban qofar glass din ta matsa ta zauna tana sake ganin kusancinta da ruwan.

"Subhana man kalaqal kalqa wa'ahsahum adad" Ta fada a ranta tana sake jin girman zatin Allah yana kamata. Ba shakka da yawanmu 'yan adam bamusan waye Allah ba,kawai muna fadinsa ne a bakunanmu ba tare da halasto girmansa a zukatanmu ba. Iya halittar ruwan ya ishi bayinsa sake sallamawa lamarinsa. Ta sauke numfashi tana maida kallonta cikin dakin,idanunta ya sauka kan littafin dake ajiye saman dan qaramin table din dake gabanta. Hannu ta miqa ta dauka,ta fara budewa,cikakken bayani ne akan gurin,taswirar dakin da suka kama inda toilet da restaurant da komai yake.

Idanunta ya tsaya cak kan farashin wajen,adadin kudin da zaka biya duk kwana daya tal,dollar dubu hamsin kimanin million saba'in da wani abu.

Idanu ta fidda waje mamaki yana kasheta,zuciyarta ta kasa gasgata farashin,ko a mafarkinta bata taba tunanin akwai me kudin da zai iya wannan ba daga qasarmu,amma sai take ganin kaman yayi yawa kudaden.....kaman yayi almubazzaranci,sai wani sashe na zuciyarta ke tuna mata hirar da amna ke yawan mata na hamma din. Tabbas ya isa ne yakai.....kudinsa kuma ya zarta yadda take kallonsa,mutumin dake sarrafa diamond da gold ya fitar qasashen qetare......gold ko diamond din kamfaninsa kaman abinci yake a wajensu saboda farinjininsa.


*_DUNIYATA LITTAFIN KUDI NE(PAID BOOK),KAI TSAYE KI TUNTUBI WANNAN NUMBER_*
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
_Zafafabiyar_

6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

99


_Daga abdullahi dan mas'ud R A yace:manzan Allah S A W yace "BAZAI SHIGA ALJANNA BA,DUK WANDA AKWAI KWATANKWACIN KWAYAR ZARRA(MAFI QANQANTAR ABU) NA GIRMAN KAI A ZUCIYARSA_

_muslim ya rawaito_



Ajiyar zuciya ta sauke tana rufe littafin,yayin da a can qasan zuciyarta taji ta raina matsayinta,wacece ita da har zama zai hadasu da mutum me daraja irin muhammad jadda din?,mutumin da iya yau kawai tasan ya tserewa matakin rayuwa da ita.......ya mata nisa fau fau......ya kuma tsere mata irin da mugun nisan tazarar nan..

"Amma me yasa duk da wannan tarin matsayin nasa da zai iya auren kowanne nau'in mace a duniya.....duk da wannan dukiyar......kyau da ilimi dake gareshi ya nacewa rayuwarsa sai ni?,me yasa ya kasa rabuwa dani yaje yayi rayuwarsa?" Tambayoyin da suka zo kanta kenan. Ta kalli wayarta dake ajiye gefe,ada tana mamakin yawan kudin wayar,sai gashi a nan din kowacce rana zasu kashe kimanin kudin wayar a kwanan gurin kawai,banda personal cook da taga suna dashi da komai da komai da za'a zo kullum a maka personally.

"Allah me iko" Ta fada bayan data kunna wayarta ta tadda WiFi da cikakken network na wayar,ta maida dubanta kan ruwan,kaman ba'a kan ruwa suke ba?.

Daidai nan ya tura qofan ya sake shigowa,tadan zabura kadan saboda da gaske a tsorace take. Murmushi ya saki dan siriri daya qara masa wani kwarjini da kyau.

"I'll safeguard you....indai kina tare da Jadda kisa a ranki baki da sauran tsoro ko damuwa" Ya fada a tausashe sanda yake qarasowa dakin da wani kyakkyawan tray a hannunsa ya ajiye saman table din gabanta. Haka kawai taji kalamansa suna samun matsugunni a zuciyarta,su huda suka fado mata......indai har hakan ya tabbata hakan na nufin qannenta zasu iya rayuwa da ita?,qannenta zasu samu kowanne kalan rayuwa da take mafarki?" Ta tambayi kanta idanunta zube kan price na wajen ba tare da tasan nan din ta bude ba. To amma meye tabbacin da take dashi a kansa?,kada fa ta rudi kanta........yanzun nan ta sake fahimtar wanne irin tarin dukiya da girman matsayi da yake dashi.......tasan cewa kwata kwata babu hadi tsakaninsu......zaren ba kalar yadin bane......bata da wani assurance.

Baya kadan yaja a hankali,ya sauke gwiwoyinsa qasa yana tsugunnawa a gabanta,hannu ya sanya yana janye littafin yana sauke idanunsa a wajen,saita bishi da kallo haka kawai tanajin kaman yayi almubazzaranci......kaman ya kamata tace wani abu,kaman ya dace ta masa gyara.

"Wannan.......gurin nan kaman yayi tsada da yawa......muna da wajen da zamu kwana fa?". A nutse ya daga idanun nasa yana ajesu a fuskarta,wani abu me kama da murmushi shimfide saman fuskartasa,har tsakiyar zuciyarsa yana jin dadin kusanta kanshi da ita,koda kuwa na qananun sakanni ne sai yaji yana samun nutsuwa.

"Duk tsadarshi baikai ki tsada ba.......You're priceless,no cost is to high......I'd spend my last dime on you,you're worth every penny" Ya qarasa fadi yana duban idanunta......yanajin inama zata bashi dama ya shige jikinta.....ya dora kansa saman kafadarta?,ya sauke ajiyar zuciyar da zata kawo masa sassauci da irin yanayin da yakeji a zuciya da gangar jikinsa". Karon farko da itama ta zuba masa idanu......tanaso ta tabbatar da gaskiyar abinda ya fada ko kuma akasinta......tanaso ta tabbatar har zuciyarsa abinda ya fara ko wani sabon salon yaudarar ne?. Kasa jurar kallonsa tayi kama kullum,ta dauke kanta ta maida still saman ruwan,tana ganin yadda duhun dare ya cakudu da hasken fitilun da aka wadata duka resort din dashi,jifa jifa halittun kifaye nau'i daban daban suna kai kawo. Lissafin kudin take cikin ranta,inda zai rabawa marayu irinta wanne dadi zasuji,saita kasa shuru still,ta buda bakinta a hankali ba tare data kalleshi ba.

"Inda zaka kaishi qasata.......akwai tarin marayu da marasa qarfi da zasu shiga cikin walwala da farinciki sanadin haka.....zasuyita sanya maka albarka.....mutane masu yawan gaske da suke kwana cikin yunwa da ciwo......suke kwana cikin halin babu.....'yammata da yawa sun rasa mutuncinsu sanadin talauci,iyaye da yawa sun rasa 'ya'yansu saboda abinda zasu sanya a bakinsu" Takai qarshen maganar wani abu yana taba ranta,wani abu yana taso mata yana tuna mata abinda ya wuce a baya.

Sosai.....sosai da sosai maqurar gaske yaji tayi wani bala'in burgeshi......irin burgewar da ya jima baiji wani dan adam ya masa ita ba. A bangaren taimako idan ana maganarsa.....baisan adadin mutanen da suka dogara da rayuwarsa ba......baisan adadin mutanen da suke qarqashin kulawarsa ko kulawar wasu nashi ba,ba'a iya Nigeria kadai ba......bai bari tallafinsa ya tsaya a qasata ba kawai,ya leqa maqwaftan qasashe sosai,saidai kusan komai zaiyi baya bari a fadi sunansa ko a saka sunansa,wani kaso mafi girma na dukiyarsa ya ware ya kuma sadaukarwa al'umma........to amma kuma hirar tasu,yana buqatar tayi tsaho,yana buqatar wannan kusancin a tattare da ita......yana kuma cirar wasu abubuwa daga sautin muryarta da yanayin yadda take maganar daga qasan zuciyarta.....kamar akwai wani abu daya shafeta cikin maganganunta.

A nutse ya miqe yana zama kujerar dake facing nata,yana zube idonsa a kanta tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta.

"Exactly......kin kawo point me girma......me zai hana ki karbi aikin a hannuna?.....a matsayin personal assistant nawa a wannan bangaren?" Maganar tasa taja hankalinta sosai har sai data waiwayo ta dubeshi da raunanan idanunta. Wannan din yana daya daga cikin cikar burin rayuwarta,ta zama sila na shigar da farinciki zukatan wasu,ta zama sanadin yayewar damuwar wasu....amma tana ganin kaman zatayi shishshigi ne ta shiga rayuwar da sam ba tata bace.

Ya fahimci akwai kokwanto sosai cikin kallon da take binsa dashi,sai ya sakar mata murmushi yana dunqule hannunsa guri guda,saboda kallon da take masan kaman tana sakar masa wasu harsasai ne cikin jikinsa.

"Da gaske......ina buqatar irin hakan.....irinki cikin rayuwata.....amma wannan karon ni zan biyaki.....bake zaki biyani ba" Ya qarasa fada yana kallon qwayar idanunta. Murmushi dan siriri ya qwace mata,ta kawar da kanta gefe tana kaucewa ganinsa. Wani irin kyau fuskarta ta sake masa,murmushinta ya tsaya masa a zuciya,ya kasa dauke idonsa a kanta,iya adadin murmushin da ya taba gani akan fuskarta qididdigagge ne,ashe haka murmushi yake mata kyau?.

Yasan me ta tuna,don haka shima boyayyen murmushi ya saki,ya ciri wata farar takarda da abun rubutu da suka samu a gurin ya tura gabanta.

"Zan shiga wanka......kafin na fito ki rubuta adadin salary din da kikeso,daga kan million goma har million dari". Waiwayowa tayi a nutse,ta dafe takardar tana dubansa.

"Ba komai ne akeyinsa saboda kudi ba......kaman yadda ba komai bane kudi ke iya siyansa ba......wasu ladaddakin sunfi duniya da abinda ke cikinta muhimmanci a rayuwar d'an adam" Ta qarasa furucin yana duban labbanta da suke motsawa da wani irin yanayi dake matuqar daukan hankalinsa. Kai ya jinjina yana miqewa gami da matsawa a nutse yana zare socks din qafarsa.

"Na sani....saidai ko Allah daya haliccemu ya sanya ladan kowanne aiki.....kaman yadda idan nayi aiki haqqina ne ka biyani....haka idan akamin haqqi ne akan kowa na biyashi" Ya qarasa fada sanda yake zare rigar jikinsa.

Kanta ta dauke da sauri daga kansa zuciyarta na harbawa,batason kallon wannan ginannen jikin shi wai baisan hakan bane?.

Murmushi kadan ya saki,ya karanci me take daukewa kan sarai,sai ya fara takawa zuwa inda ta maida kan nata,ya saka hannu yana zuge duka curtain din da suka zama hijabi ga idanuwa,suka lullube gilasan suka hana mata kallon ruwan dake gabanta din. Maida idonta tayi ta lumshe,da alama dai taci alwashin ba zata kalleshi din ba. Kai ya jinjina,shi kadai yasan me yake saqawa a zuciyarsa......da sannu zai saita komai kan tsarin da yakeso,a nutse yabi kowanne curtain


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login