Showing 6001 words to 9000 words out of 363280 words

Chapter 3 - DUNIYATA BOOK 2 COMPLETE

HUGUMA   

11 Nov 2025

6466

fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu.

Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call.

Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro.

Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa.

"Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad

"Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa

"Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan.

Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu

"Am asking you seriously fa.....where are you?"

"Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......."

"Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?.

Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi.

Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar.

Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar.

"Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace

"Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?"

"Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa.

"Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?.

"Jibi din zan shigo in sha Allah anni"

"Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa.

Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?.

"Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji.

"Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya.

"Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka"

"Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah.

Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta.

Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren.

"Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya

"Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe.

"Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata.

"Tana bangaren beauty spa"


5???5?j?5?c?5?^?5?n?5?V? 5?i?5?V? 5?c?5?V? 5?`?5?j?5?Y?5?^? 5?c?5?Z?.
08187255862

5?? 5?? 5?
? 5?? 5?? 5?? 5?? 5??
5?!?5?"?5?'?5?"?5?'?5?"?5?#?5?*?5?:?5?"?5?3?
6B6O6O6K 62

g,D? D? ?

5?K?5?

"Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka.

******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu.

Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima cikin gidan.

Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba.

Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace.

Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a.

"A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude.

"Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi fata>?z?=?
?).

Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta.

Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar daraja.

Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa.

"Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki

"Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba.

"Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha mamaki......har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin.....attajirin matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?" Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya

"Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban ai"

"Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?"

"To alhamdulillah.....haka akeson ji...."

"Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta......kaya ne tace a kawo mata da zata sanya a gobe kenan"

"Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa.

"Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace masu abu da abinsu).

Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa falon da guntuwar fara'arta.

Sunan kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai hakan bai dadata da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata iya rabasu a jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske ko kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen duniya cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da haddaceshi......kusan shi ya zama sila na sauyawar DUNIYARTA.

Hadiyyan ta sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan kusa ba. Bata zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne.

Hadiyya ita ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta. Hidima sosai suke gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me kudi sanin darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba.

"Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja ta fada tana sauke wayarta daga kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi tana sauke fararen idanunta akan fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar ce sam bata da sha'awar wata magana da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata zauna tana gwada mata tata izzar bayan ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba.

Idanu sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda fuskarta daga kallon idanuwan.

Sallamarta kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar sallamar data saukar da duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita amsa mata a nutse matuqa

"Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata bangaren jin sabreen din tayi shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya saukar mata,batasan me yasa a iya waya kawai takejin girma da kwarjininta ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko yaya?.....itadin wacece a wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan tambayoyin da bata da amsa kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani gagarumin abu birne a qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu bane da zai gagari sarrafawarta ba.

"Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade gaisuwar da amsar tambayarta.

"Ma sha Allah"

"Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin ranta takejin bai kyautu ba har sai ta magantu.

"Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu a duk sanda zaki shigo ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna kulawa,kulawar data bayyana kanta sosai cikin sautin muryarta

"In sha Allah" Ta sake amsa mata

"Ina fatan hakan ba takura?"

"Ba komai....in sha Allah"

"To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara dukkan alkhairanku ga junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a tsakaninku". Batasan me yasa ma......amma har tsakiyar qirjinta taji saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan tace kunnuwanta itace mutum ta farko data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji labbanta sunyi nauyi bare su tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya da kawaici suka hanata amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar.

Zuciyarta tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke wakana cikin falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki kaman yadda ta maida hakan dabi'arta.

Bata jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo dauke da wayarta a hannu.

"Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar tace mata ta koma da ita sai ta fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen tana duba me kiran.

Sunan data gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na gaggawa wajen amsa kiran ta sakashi a kunnenta

"Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login