Showing 192001 words to 195000 words out of 196754 words
Chapter 65 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL
tana fatan kada dukiyar ta kare kafin a zo kan yaranta.
Haka tana ji tana gani aka canza takardun gidan suka koma mallakin Ahmad kuma aka bashi mota irin ta
Baba Karami.
‘Yan bautar kasa suna fitowa daga camp Abba ya sa aka yi posting din Zulaiha FCE Bichi. Yayi haka ne
don baya son Sa’a tayi masa shigar sauri ta sa a kawota Kano don ta dawo masa gida. Da yake suna
fitowa daga camp Bichin ta wuce sai Abban ya dauki takardun da kansa ya kaiwa Baffanta har Bichi, ya
sanar da shi ta gama karatu saura bautar kasa gashi nan ya sa an kawota kusa da gida. Baffanta ya ji dadi
sosai yana ta godiya, ita kuwa Zulaiha da Sa’a basu so haka ba don sun san yanzu zai fara sakasu a gaba
da zancen auren Zulaihan da bata da miji a hannu.
Shi kuwa Salim da kansa yayi ta fadi tashi ya samu aka kai shi sakateriyar karamar hukuma don baya son
inda zai dinga zuwa kullum saboda yanzu ya ganewa kasuwa sosai.
Kafin su Salim su gama bautar kasa lokacin bikin su Baba ya zo. Nan da nan aka fara shirye shirye, gaba
daya gidan saida Abba ya sake fenti ya canza musu labulayen aka gyara tsakar gida sosai.
Ranar Asabar da safe aka daura auren Baba karami da Fathiyya a nan Kano sannan aka dunguma zuwa
Dukku inda aka daura Ahmad da Zahra. Zahra amarya da kuma Baraka duk suna dukkun, nan da nan aka
hau hidima da ‘yan daurin aure. Nama ake ta gasawa ana dama fura ana fito da ita saboda kakan Zahra
cewa yayi ‘yan binni ne zasu zo don haka a yanka sa daya na Zahra shima a hada da nashi san guda daya,
da kanta Zahra ta sa aka siyo disposable plates da cups aka dinga rabawa angwaye nama da fura. Kaf
mutanen gidan su Zahran da da suke tsangwamar uwarta duk sun sauko suna ta hidima. Bayan an gama
daurin aure Baraka ta dauki waya ta kirawo Ahmad tace ya shigo ya gaisa da iyayen Zahra don haka su
uku suka shiga shi da abokansa, nan da nan matan gidan suka hau zarya ana gaisawa ana kare masa
kallo. Daga baya suka yi sallama suka kama hanyar Kano. Baraka da Zahra kuma da su Ummi duk a nan
suka kwana saboda daga nana za a dauki Zahra a wuce Kano.
Ranar daurin aure da daddare Baraka ta kirawo Madu a waya, bayan sun gaisa tace
‘Da kai za a zo Dukku daukan amarya?’
‘A’a anti ina Kano.’
‘Amma ai kana nan za su taho ko?’
‘Ina nan Anti ni zanyi musu lodi.’
Tace
‘Yauwa, kada uwarka Sa’a tazo min nan duk yanda za ayi kada ta biyo ‘yan daukar amarya.’
Ya kyalkyale da dariya
‘An gama Hajiya Anti, a nan za a manta da ita.’
‘Yauwa.’
‘Anti to zata je Abujan?’
‘Kai gaskiya ba zata je ba.’
Ya ce
‘To, dama Abba yace a sayi ticket din mutum shida sai a cireta kenan.’
‘Yauwa, Amma Abba ya kyauta mana don na zata a mota zamu je. To Babu ita a ciki ka ka tambayi
Mommy wadanda zaka saka Kuma ko tace harda Sa’a ka cire min ita, gidan Ahmad din ma ba zata ba.’
‘An gama Anti.’
‘Ka turo min account number dinka na turo maka kudin nawa ticket din ita ma Yaya Shafa zan gaya mata
ta turo maka nata don duk mu samu mu hau jirgi daya.’
‘Shike nan Anti.’
Sukayi sallama suka ajiye waya Madu yana ta kyalkyala dariya.
………
Mafi yawancin ‘yan Bichi a wajen Mommy suka sauka don dakin su Ahmad ma kwashe kayansu suka yi
aka barwa baki duk da haka falon ma a cike aka kwana da mutane saboda ‘yan uwan Mommy ma sun zo
da yawa Sa’a da tawagarta kuwa da yake sai ranar daurin aure suka iso bayan azahar dole sai a wajen
Saudah suka sauka. Banda Zulaiha aka zo don ita kai tsaye ta gayawa Ummanta bazata zo bikin ba Allah
ya sanya alkhairi, ita ma Sa’an bata so zuwa ba ta zo ne saboda bata da wani uzuri da zata bayar don
haka ta shiryo ta taho. Duk dukiyar da aka kashe tana da labari kuma tana bakin ciki musamman da yake
Baba bai auri Zulaiha ba, maganar Mommy ce kawai take mata yawo a kai ‘ko bayan raina Dan da na
haifa ba zai auri jininki ba’. Maganar Mommy ta tabbata kenan tunda ita yanzu bata da wata mace bayan
Zulaiha gashi sa’annin aurenta a gidan su ake biki. Ga shi Atiku yace mata shima Ahmad din Abba ya
bashi gida harda mota, don haka tana so taje taga gidan. Abin dai da take bakin ciki ne ya faru, gaba
daya dukiyar Abba ta kare a kan Rabi da yaranta.
Ana gama karya kumallo a gidan bikin aka fara shirin tafiya Dukku dauko Zahra, mota hudu za ayi uku
babu kowa sai driver saboda amarya da ‘yan rakiyarta mota daya kuma ita ita mata za su shiga a nan.
Motocin da babu kowa guda uku a can bakin titi Madu yace su tsaya don ya san in an gansu sai an shiga.
Anti Aisha ce kanwar Baraka a gaban mota sai kuma Maman Farida a baya da kuma Anti Halima amaryar
Baffa Atiku. Saida suka zauna a motar sannan Khalifa ya shiga wajen Saudah ya gaya mata ita ake jira ta
fito don Mommy tace taje ta dauko amaren ta wakilceta. A shirye suka ganta ta fito daga dakin tana yi
musu sallama
‘Mun tafi dauko amaryar Ahmad.’
Sa’a ta mike tare da wasu mutum biyu ‘yauwansu tana fadin
‘Bari muma mu taho.’
Suka dauki mayafi suka rufa mata baya. Suna fitowa Madu ya bude mata kofa ta shiga bayan motar ya
amayar ya rufe ya leka yacewa direban
‘Allah ya kiyaye hanya.’
Ya juya Sa’a tace
‘Babu wasu motocin ne.’
‘Ai mota daya ce daman.’
Ya wuce ya barsu a nan. Sosai ta so zuwa Dukku tunda an ce mata Zahra diyar Fulani ce, tana so taje ko
zata samo abun kushe Zahra amma gashi an hanata. Ta bi bayan Madu da harara tana kwafa, bata son
Madun nan amma komai na harkar gidan sai an saka shi a ciki duk da ba ma shine babba ba.
Sai da mutanen Dukku suka kusa isowa sannan masu dauko Fathiyya suka tafi, don haka kusan a lokaci
guda suka iso gidan. Aka yiwa amare masauki a falon Mommy gaban Baba Yalwa da Inna Hajara da kuma
Gwaggonnin Mommy da suka zo da ‘yanuwanta, nan da nan mata suka dau guda. Mommy ta kawo
ledoji masu kyau guda biyu iri daya kowacce da dadduma da kur’ani da kuma turare mai kyau a ciki da
kuma sababbin kudi naira dubu biyar aka bawa kowacce daya. Inna Hajara tayi musu nasiha sosai. Masu
kai Zahra dakinta suka mike aka fara shirin tafiya. Da wuri Sa’a ta fito bakin gate don tana son taje taga
gidan Ahmad din, Madune a bakin gate da motoci guda biyar a jere, ta tsani yanda ake dora Madu a kan
duk wata harka ta gidan, sai da ta sha kunu sannan tace
‘Wacce motar za mu shiga?’
Ya nuna mata motar da Lalo yake ja suka shiga ita da tawagarta, ana fitowa da amarya yacewa Lalo suyi
gaba don haka Lalo yaja mota. Salim ya fito da CR-V aka kara aka zuba masu kai Zahra suka tafi. Haka
Lalo yayi ta yawo da su Sa’a a unguwar court road ya shiga wancan layin ya fita wancan daga karshe dai
ya juya yace
‘Hajia na fa kasa gane gidan nan gashi Madu baya daukar waya.’
Tace
‘To ka kirawo Salim mana ko Khalifa.’
‘Wayar Khalifa bata shiga, wayar Salim kuwa gata a hannuna za a kaita gyara. Alhaji kuma wallahi ba zai
ma iya yi miki kwatanceba.
Suka yi tsuru-tsuru a bayan mota yayi ta yawo da su har dai ya gaji ya kamo hanya ya dawo da su gida.
Suna fita daga motar ya bar wajen don haka Madu yace masa, sosai ran Sa’a ya baci ko da suka shiga
suka gayawa Mommy hakuri kawai ta basu don ta san aikin Madu ne wanna. Tace su bari in wani ya
dawo a cikin direbobin zai kaisu.
Haka ma da aka zo tafiya Abuja ya lissafa ‘yan kai amarya; Anti Halima amaryar Baba Munzali, Saudah,
Anti Hauwa matar Baba Mubarak da kuma Maijidda matar Baffa Atiku sai Inna Hajara da Baba Yalwa sai
Baba Rakiya wadda yadukkon Mommy ce da kuma tickets biyu na kawayen amarya. Mutane suna
tamabayarsa suma za su je yace a jirgi za a tafi kuma iya ticket din aka bashi kenan don haka dole kowa
ya hakura.
Haka aka gama biki Sa’a bata je gidan amarya ko daya ba domin washegari ma da aka fara shirin zuwa
gidan Baba Karami Abba cewa yayi ba za aje ba kowa ya tafi gida daga baya duk a je. Haka kuwa aka yi ya
sallami ‘yan Bichi suka tafi. Suma ‘yan uwan Mommy sun riga ‘yan Bichin ma tafiya da yake dama su
yawancinsu ‘yan cikin Kano ne.
Bayan kwana biyu da kai amarya Abba ya shiga wajen Mommy da daddare don yayi musu sai da safe; da
yake ba itace da kwana ba. Yaran ya tarar a falo sun hirarrakinsu suna kallon TV, bayan ya amsa sannu da
zuwansu yace
‘Kun fara kewar Amadu ko?’
Madu ya gyara zama yace
‘Haba Abba, ai ba wata kewa da yake ina nan.’
Ya kyalkyale da dariya yace
‘To sarkin gida.’
Duka suka sa dariya.
‘Ina Mommy ne?’
‘Tana daki.’
Ya wucesu ya shige dakin. A gaban mudubi ya sameta tana shafa mai ta fito daga wanka, bayan tayi
masa sannu da zuwa ya karasa ya zauna a bakin gadon daga kusa da inda take zaune. Yace
‘Ya gajiyar biki? Kun yi waya da mutane duk sun isa gida lafiya ko?’
‘Alhamdullilah, kusan kowa na kirawo duk sun isa lafiya.’
‘To Madallah, Allah ya kai mu na ‘yan baya.’
‘Amin amin. Ni da yara muna godiyar abun arziki, Allah ya ja kwana Allah ya kara arziki.’
‘Amin ya Allah. Suma yaran ai kowa yayi kokari sai dai muce Allah ya kara budi.’
Ya zaro takardu guda biyu a envelope ya mika mata yana fadin
‘Jibi za mu tafi Umra in sha Allah, ni da ke sai ki shirya. Kinga in muka gama ibada sai ki fi hutawa sosai.’
Ta karba tana murmushi
‘Ma sha Allahu, Allah ya kara arziki Allah ya nuna mana. Umman Nawwara fa ai da ma kun fara zuwa da
ita.’
Dama ya tsammaci hakan don a tsahon zamansu in dai ya bata mata rai a kan abu to ko yayi daga baya
bata fiya karba ba sai yayi da gaske, ya tsattsareta da ido. Ta fahimci me yake nufi don haka ta kawar da
kanta ta dora takardar a gefen mudubinta
‘To ai dai ka ga itama ta sha hidimar bikin nan kuma itace me jini a jiki ko?’
‘Na gani, sai me kuma? Da ke din za mu je ko da tsiya ko da arziki.’
Tayi dariya
‘Da arzikin ma zamu je in sha Allahu.’
Shima dariyar yayi yace
‘Ai na zata sai dai na daureki a kafata tukunna da kin sha mamaki.’
Ya mike yana fadin
‘Karamar jaka za ki dauka ki hada mana kaya saboda kar mu dauki kaya da yawa.’
‘Toh Allah ya kai mu.’
Ya fice ya wuce wurin Saudah.
Ta ji dadin da ya kawo ticket duk da itama da nata kudaden da ta hada da kudin hayar gidanta take
adanawa zata je Hajji. Yaran ma gaba daya sai da sukayi mamaki musamman Madu da shine ya saba
kama musu jirgi in za ayi tafiya amma wannan Abban da kansa yayi.
Sai da suka zo kwanciya bacci sannan ya sanar da Saudah tafiyar, yanda yanzu idan tayi masa korafin ita
bai bata wani abu yake gaya mata maganganu marasa dadi yasa tace
‘Allah ya dawo da ku lafiya.’
Yace
‘Amin ya Allah.’
Jimawa kadan bacci ya fara dibansa tace
‘In kunje kwayi mana addu’a muma Allah ya kirawo mu hajjin bana.’
Yayi dariya yace
‘Amin, muma haka.’
………….
Jirgin karfe hudu na yamma za su bi don haka tun safe suka gama shirinsu.
Yana zaune a dakinsa na wajen Saudah ta shigo dakin, bayan ya amsa sallamarta yace
‘Yauwa dama ke nake jira.’
Ta karasa ta zauna a kusa da shi, ya dubeta yace
‘Komai na bukata akwai a gidan, duk kayan abincin yara akwai da duk wani abu ma da ake bukata. Na
bawa mai kanti kudin burodi don haka duk lokacin da kike son burodi ki tura Malam Bala ya karbo miki.
Salim zai dinga kai yara makaranta ya daukosu tunda ke kin gama, ba sai kin fita ba. Idan ana bukatar
wani abun kuma Madu yana nan ki gaya masa.’
Ya bude durowa ya nuna mata bandir din kudi ‘yan dari biya-biyar wadanda za su kai kimanin naira dubu
hamsin yace
‘Ga kudi a nan in an bukaci wani abu na bukata a dauka ayi.’
Ta leka durowar ta gansu, tace
‘To. Allah ya dawo da ku lafiya.’
‘Amin. Ba fa cewa nayi a cinye kudin duka ba, na ajiye su ne kawai saboda kada wani abu ya taso bana
nana. Idan na sayi layi za muyi waya, duk da whatsapp dina a bude yake kullum in da wani abu ki gayawa
Madu ko Salim su tura min ta Whatsapp.’
Ta fita yayinda shi kuma ya karasa shirinsa.
Sai wajen karfe biyu da rabi na rana Salim ya fito zai kaisu. Abba yana wajen Saudah a daki yayinda
kayansa suke wajen Mommy, don haka sai da ya saka kayan a mota Mommy ta fito falo ta zauna sannan
ya yi masa waya. A daki ya sami Saudah tana zaune a gefen gado, ya karasa ya zauna a kusa da ita
‘Mu zamu tafi, ga gidan nan da yaran sai ki yi hakuri da su.’
Ta amsa da ‘To.’
Suka karasa yin sallama ta rakoshi har bakin kofa, har ya saka kai zai fita ta janyo hannunsa don haka ya
koma ya tsaya tana rike da hannunsa da wayarta mai torch light a hannunta, ya kalleta alamar yana jira
yaji me zata ce. Suka hada ido ta sunkuyar da kai sannan tace tana kallon wayarta dake hannunta
‘Ka siyo min waya.’
Yayi dariya ba tare da ya zare hannunsa daga nata ba yace
‘Waya? Ashe kina son waya?’
Ta saki hannunsa tana zumbura baki, ya sake yin dariya
‘Ni da na saya miki waya kika sayar kika zo kika ce min an sace sannan yanzu ki kalli tsabar idona kice na
saya miki waya, kina kallo nace ayi tracking wayar amma baki fadi gaskiya ba kika bari sai da aka je aka
kama yaron mutane a matsayin barawo; ai ni na gama saya miki waya har abada na dai siyo miki wani
abun da ya dace dake.’
Sukayi shiru tana ta faman zumbura baki, ya kula bata da wani abu da zata ce don haka yace
‘Sai mun dawo.’
Ya wuce ya barta a nan.
Bayan Mommy ta fito ta saka jakar hannunta a mota ta dubi Abba tace
‘Bari nayi sallama da Umman Nawwara.’
Ta wuce wajen Saudah, tana zaune a falon ita kadai. Tana shiga ta mike da mamaki don ta dade rabonda
ta ganta a wajen, tun lokacin da Baffa Karami ya kone. Ta kula da yanda take faman cika tana batsewa
amma ta zata saboda zatayi kewar mijinta ne , tace
‘Umman Nawwara.’
Ta dubeta a sanyaye
‘Na’am.’
‘To mu mun tafi sai mun dawo, Allah ya sada mu da alkhairi.’
‘Amin. Allah ya dawo daku lafiya.’
Har ta juya zata fita zantukanta suka dawowa Saudan ‘zan cigaba da yi miki addu’a Allah yayi miki abinda
kika yi min.’ Kada fa matarnan taje ka’aba ta yi min muguwar addu’a, kafin kwakwarta ta gama yanke
shawara da sauri tace
‘Mommy.’
Ta juyo tare da amsawa.
Ta sunkuyar da kai tace
‘A yafe mana ko ba za a dawo a samemu ba.’
Tayi ‘yar dariya
‘Kai haba in sha Allahu kalau za mu dawo mu same ku, sai mun ga ‘yayan Baffa Karami da Hanan
tukunna. Allah ya yafe mana baki daya.’
Sukayi sallama ta fice.
Tunda suka sauka a Saudiyya duk wata damuwa tata ta yaye, sosai ta ji dadin tafiyar nan. Haka za su
kwana su wuni suna ibada, bayan sati biyu sun gama duk wata ibada ta Umra har sun dan huta sun zaga
gari. Bai ce su sayi komai ba don haka itama bata ce ba, a yanda ya san ta ya san bazata taba fada ba.
Don haka ranar da zasu tafi da yake jirgin yamma za su hau yace su je sayayya. Wani shago suka fara
shiga na kayan sawa, ya riga ya gaya mata ba zasuyi sayayya da yawa ba don haka abaya ta zaba guda
biyu da kuma material guda daya. Ya dubeta yace
‘Ki zabarwa kanwarki kuma.’
Tayi ‘yar dariya tace
‘Kai da za ayiwa kwalliya ai kai zaka zaba.’
Ta matsa ta bashi waje don haka dole ya zaba da kansa. Haka suka dan zagaya suka sayi kayan kadan, da
yake da yamma za su tafi sai suka koma masaukinsu. Sai da suka koma sannan ya dubeta yace
‘Dubai za mu wuce shi yasa nace kada muyi sayayya da yawa, idan muka je can ma yi.’
Ta kalleshi tana mamaki, yayi dariya yace
‘In da na gaya miki a gida ai sai kin san abinda kika ce shi yasa nayi miki shiru, yanzu ko kinga ai dole ki
bini ko?’
Tayi dariya tace
‘Hmm, nagode Allah ya kara arziki.’
Yace
‘Amin.’
Ya taso daga inda yake ya dawo kusa da ita, ya kalleta yace
‘Kin fi kyau idan ba kya tare da damuwa kamar yanzun nan.’
Tayi murmushi, kafin tayi magana yace
‘Ki daina bari komai yana damunki, Allah yana sonki Rabi, nima ina sonki.’
Tayi dariya tace
‘To a daina damuna sai na daina damuwa.’
Yayi dariya yace
‘An daina matar Usman.’
………..
Suna hanyar airport ya kirawo Saudah, bayan sun gama gaisawa tana jira ta ji yace mata yau ko gobe za
su dawo sai yace
‘Yanzu zamu wuce Dubai sai nan da kwana goma zamu dawo.’
Sukayi sallama ta jefar da wayarta a kan kujera. Yanda ya gaya mata magana a kan waya ya tafi dama ba
wai ta huce bane yanzu kuma yana gaya mata wai za su wuce Dubai suyi kwana goma. Gashi kudin da ya
bar mata a durowa ta riga ta kusan cinyesu don tun suna kwana biyu da tafiya aka fitar da ankon bikin
kawarta naira dubu goma ta dauka ta siya sannan ta dauki dubo goma ta sayi food flask wanda zata
bawa amarya. Sauran kuma duk sayi banza sayi wofi duk ta musu illa.
Tayi tsaki a fili tace
‘Ai dama na san tunda ya dauki wannan tsohuwar matar tasa sai yanda tayi da shi.’
Saida suka kwana goma a Dubai suna yawo suna sayayya, itama da nata kudaden data tafi da su ta sayi
blender, dinner set da kuma tukwane da food flask masu kyau. Canjin kudinta kuma ta sayi zoben gwal
guda biyu masu kyau. Shima ya so ya saya mata sarka amma saboda ba zai sayawa Saudah ba ya kyaleta
ta saya. Tunda ta sayar da wayarta tace masa an sace yake jin cewa ko me zai bata zata iya sayarwa tayi
son zuciyarta ba tare da shawara ba. Suna shirin tafiya Madu
24, February 2025
Maryam
Plsss
05, January 2025
Maryam
So good