Showing 6001 words to 9000 words out of 196754 words

Chapter 3 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15352

ma kuma Rabin sai ta fi jin dadin haka don dama tana ganin kamar dole yayiwa
amaryar.

Ita dai ta fi so ya barsu kada ya matsa musu, a hankali ai za su saba.

Yaranta ma duk wani Jan kunne ta yi musu. Ta kuma umarcesu da duk wanda amarya ta aika ko ta sa wani
aiki toh ya yi batare da musu ba.

Toh tun daga wancan lokacin bai sake yin gaba da ita ba sai yanzu bayan wajen wata shida, shi ma kuma
duk a dalilin amarya, saboda kawai ta ce ba za tayi tuwo ba.

“Lallai Abban Baba. Har ka auro yarinyar da za ta sa ka yi min wulakanci. Ai shike nan.” Ta fada a fili kamar
mai zance da wani.

Duk da bai fita da abincinshi na rana ba haka ta dage ta dafa na dare. Yana son wainar shinkafa don haka
wainar tayi da miyar taushe, ga kuma zobo mai sanyi.

Da ya dawo daga kasuwa ya shigo wajenta amma bai kulata ba kamar yanda ta zata, kuma bai ci abincin
ba.

Sai kawai ta ganshi ya fito da kayanshi daga daki, ta zata ma bayarwa zai yi ko ya kai wanki duk da dai a
goge ma suke. Madu ne kawai a falon yana karatu.

Ya mike ya karbi kayan ya ce:

“Abba kawo na kai maka, mota za a kai.?”

“A’a can wajen antinku za ka kai ka ajiye min a falo.”

Ya karba ya fice shi kuma Abban ya koma ciki inda ya kwaso wasu kayan ya zo huce ta.

Tayi tunanin kamar zai dawo ya sake diban wasu kayan don haka ta bar falon ta koma daki. Tunani daban
daban ne suke yawo a kanta. Tunda amarya ta tare bai kwashi komai daga dakinsa wanda yake nan
wajenta ba. Ya dai gaya mata daki uku ne a can din; daya na shi, daya na amaryar daya kuma na baki.
Amma duk da haka kayan sawarshi suna nan, ko wanki ya Kai sai dai ya dawo da su nan ta shirya masa a
wardrobe. Sai dai kawai wata rana idan ya shigo musu sai da safe ya kwashi abun da zai saka gobe ya fita
dasu.

Don haka ganin cewa ga wannan fushi da yake da ita Kuma gashi ya zo yana kwashe kayanshi ta yankewa
zuciyarta lallai baya ma son ganinta. Sai da tayi kuka saboda takaichi.
Ita dai bata san haka kishiya take ba. Lokaci guda ta sa mutumin da kayi shekaru da shi ya sauya maka,
lallai sai ta dage da addu’a idan ba haka ba zuciyarta za ta iya bugawa ta mutu.

Ta tabbatar yau kwanan ma ba za’a bata ba. Don haka abincin daren ma bata dafa ba. Ita ta dafa indomie
ta ci tace wa Khalifa idan yayyanshi sun shigo ya ce musu ga ragowar waina nan a flask kowa ya ci; don
itama yanda bai ci wainar nan ba takaici ba zai barta ta ci ba. Tunda ta shirya idan ya zauna cin abincin ne
zata yi amfani da wannan damar ta bashi hakuri, kuma ta nuna masa ita dai ya daina saka ta hidimar
matarsa don su zauna lafiya, amma duk wani shirinta ya rusa.

Yanda ta zata ba haka ne ya faru ba, don kuwa a nan dakinshi ya kwana. Wajen 10:30 na dare ta fito falon
don ta dubo yara kuma ta rufe gidan sai ta gano fitilar dakin nashi a kunne ta kasan kofar don haka ta nufi
dakin.

A hankali ta murda hannun kofar domin ta san idan dai shi kadai ne a dakin baya saka mukulli, sai dai idan
tana ciki.

Ga mamakinta sai ta ji kofar a kulle.

“Wa ye?” ya tambaya daga ciki.

Kamar ta share shi ai kuma ta daure ta amsa.

“Ni ce.” Ta amsa a sanyaye.

“Ki tafi sai da safe, idan akwai wani abun da nake bukata zan nemeki.”

Ya amsa mata daga ciki.

Wani malolo ya tsaya mata a wuya, nan da nan hawaye suka wanke mata fuska.

Yau ita aka rufewa kofa?

Tunda take da shi bai taba hanata kwana dakinshi ba komai fadan da suke yi sai dai kawai idan ta shiga ya
juya mata baya har ta san dabarar da zata yi su yi sulhu. Amma yau saboda ya auro mata yar cikinta ita
yake cewa ta je sai ya nemeta?

Duk da yanda take kokarin kada ta sawa zuciyarta kiyayyar wannan amaryar amman tabbas yau ta ji
tsanarta a rai. Tunda dai wannan fitnar da yake mata bai taba yi ba sai yanzu.

Ta juya tana kwalla ta koma dakinta don kwanciyar bacci, baccin da bata da tabbas din yau zata iya shi.
EPISODE 3



Abinda bata sani ba shine, tun da ta buga kofa Baba karami ya bude kofar dakinsu ya leko don bai saba ji
an buga kofa ba a gidan ba idan dai ba shi da kannensa ne suke buga dakin mommy ko Abba ba. Yanzu
kuma ya ga duk gasu a daki tare da shi sun yi bacci. Don haka ya leko don ya gani. Ko da dai bai san me
aka ce mata ba ya fahimci kofar aka kulle, kuma da ta juya ta nufi dakinta ya tabbatar kuka take yi.

Shima haka ya kwana yana juyi, yana son ya je ya bata hakuri amma kuma yana tsoron kada ta koroshi,
don haka ya hakura.

Sai bayan asuba sannan ta sami bacci, don haka ko kafin ta fito ma ya fice daga wajen nata. Bai tafi kasuwa
ba saboda ranar asabar ce don haka can ya tafi wajen amarya, a can yayi breakfast. Ya riga ya gaya wa
ranshi idan dai shi Rabi zata dinga rainawa hankali toh sai ta gane kurenta, tunda dai yanzu duk abinda
bata yi masa ba ya samu wata wadda za ta yi masa.

Ita kuwa tana tashi da safe ta dau waya ta kira malama Amina; malamarsu ce ta islamiyya wadda duk da
dai ta daina zuwa islamiyya toh duk lokacin da wani abu game da aure ko addini ya shige mata duhu tana
kiranta.

Bayan sun gama gaisawa ta yiwa Malama bayanin abin da ya faru da halin da suke ciki ita da mijinta. Ta
ce:

“Toh malama tambaya ta a nan itace shin hakki ne wanda Allah ya Dora mini na dinga yiwa matarsa girki
ko kuwa akwai inda na sabi Allah a cikin wannan lamarin?”

Malama tayi gyaran murya ta bata amsa:

“Allah Bai dora miki kula da matar da aka auro miki a matsayin kishiya ba. Idan kin sabi Allah a nan sai dai
saboda kin saba umarnin mijinki. Ya baki umarni kiyi tuwo ba kiyi ba. Amma duk da haka ina baki shawara
kiyi hakuri, kada ki bari wannan yar matsalar ta haifar miki da fitna a gidanki. Ki san dabarar da za ki yi ki
ribato mijinki. Maza haka suke, da sun yi aure toh expectations din su a kanki karuwa suke yi, wani lokacin
sai ki ji abun kamar akwai shiga hakki. Amma kiyi hakuri kin ji, kiyi ta tasbihi da istigfaari komai zai zo miki
da sauki in sha Allah. Kina ji na ko Rabi.”

“Eh. Ina jin ki malama, Na gode Allah ya saka da alkhairi.”

Ta bata amsa.

Nan dai suka dan taba hira malama na ta bata baki suka yi sallama sannan ta ajiye wayar.

Sai a lokacin sannan ta fito. Ko kafin ta fito tuni Baba karami ya dafa musu indomie sun ci, Madu shi kuma
ya wanke kwanukan sun gaisheta ya ce:

“Mommy mu munci idomie, ke ma na dafa miki.”

“Ai kuwa da ka taimaka min Baba.”
Nan da nan kuwa ya dafa mata indomie, harda kwai. Ya hada mata shayi ya kawo mata har nan falon.

Ta chi ta koshi sannan ta shiga hidimar gidan ita da yara. Sun gyara ko ina amma ko kallon kofar dakinshi
bata yi ba tunda daman yaran sun saba ita kadai take shiga ta gyara babu wanda ya kawo wani abu, sai
Baba karami kawai.

A haka suka dauki satittika. Kwata kwata ma ta daina bari su hadu, sai dai ya jiyo muryarta ko kuma
motsinta. Da zarar ta ji ya nufo kofarta sai tayi maza ta shige daki. Tun sauran yaran basu fahimci komai
ba har suka gane ba’a kula mahaifiyarsu. Babu dai wanda ya ce mata komai sai dai su yi ta yi a daki a
junansu, tunda sun san bata basu damar shiga lamuranta irin wadannan ba.



A sati na uku ne ya fahimci lallai Rabi da gaske take. Domin dakinshi kadai ma ya isheshi, babu shara ga
bandaki kaca kaca, ko ina kaya. Can din ma kuma wajen amaryar haka yake, domin ita bata iya yin komai
kwanciyarta takeyi ta ce jikinta babu kwari saboda ciki. Abincinma wataran sai dai ya siya don bata iya
girkawa, ko ta girka ma ba ya dadi sai tace ai saboda bata iya dandanawa ne kuma bata son warin abincin.
Ita kanta abun ya ishe ta don cikin duk ya jagwalgwala ta, haka dai suke ta hakuri.

Ta takura shi matuka a kan ya daukar mata mai aiki amma ya ki. Sai dai kullum ya ce mata shi baya son
masu aiki, gidanshi ba a taba dauka ba.

Ta yi kuka har ta godewa Allah. Ga shi ko gidansu ita ce auta don haka babu kannen da za su zo mata. Ita
da a tunaninta idan ta auri mai kudi komai zai yi mata. Amma gashi mai aikin da za a dinga biya dubu biyu
ta zo ta yi mata wanke wanke da shara ta gagara. Kudin ma da kafin ya aureta da ta ce ya bata yake bata
yanzu duk abubuwan sun chanza. Ga shi kuma cikin nan duk ya jagwalgwala ta. Don haka idan ya shigo
gidan kawai sai ta lafke, duk wannan tsaftar da ta saba masa da ita yanzu abun baya yiwuwa.

Don haka ya na so su shirya da Rabi, ko babu komai ya ci ya koshi ba tare da wata damuwa ba sannan
kuma dakinshi fes.

A haka dai ya yanke hukuncin daukar mai aiki, amma zai shawarci Rabi, domin sai dai su dauki mutum
daya idan ta gama da wannan ta shiga tayiwa wannan ta tafi. Baya son mutane da ban da ban suyi ta shiga
suna fita.

Yaran kawai ya tarar a falon don haka ya tambayesu ita.

Ya murda hannun kofar dakin ya shiga da sallama. Chatting take yi da yayarta don haka murmushi ne a
kan fuskarta a dai dai lokacin da ta dago ta amsa sallamar shi.

Sai kuma ta mayar da fuskarta yanda take.

“Ke da wa kike hira ne a wayar kike ta faman yiwa waya murmushi.?” Ya tambaya tare da zama a gefen
gadon ta wajen kafarta, yayinda ita kuma ta dan janye kafar ta domin ya samu wajen zama.

“Yaya Shafa ce.” Ta bashi amsa.

“Toh ma Sha Allah. In ce ko suna lafiya ita da iyalan nata?”

“lafiya kalau suke.”
“Toh ma Sha Allah”

Sai kuma suka danyi shiru na dan lokaci. Kowa da abinda yake ransa. Ita tana mamakin zuwansa shi kuma
yana tunanin ta inda zai fara. Bayan Dan lokaci da ya tabbatar ba za ta ce wani abu sai ya ce:

“Uhm! Maganar mai aikin nan, ina ga ya kamata a samo muku wata yar dattijuwa ko wanke wanke da
shara ne ta rage muku. Tunda kinga ita kanwar taki ma komai bata iyawa.”

Ta dan muskuta ta gyara zama sannan ta ce:

“Toh ita dai sai a samo mata, aikin gidan da ba wani aiki ba. Kuma ma yanzu da bani da kananan yara ma
muna tashi ni da yara nan da nan muke gamawa. Gaskiya bana bukata.”

Sai da yayi murmushi sannan ya bata amsa don ya san wannan kalamansa ne. A duk lokacin da tayi
maganar mai aiki sai ya ce mata aikin gidan da ba wani aiki ba, shi bai yarda a kawo masa mai aiki ba.

“Toh ai na ga ke ma aikin ya fara yi miki yawa, tunda ga daki na nan kwananshi nawa babu gyara kamar
wani juji.”

Ta ce:

“Toh ai kai kace na je idan akwai wani abun za ka neme ni. Kuma da naga ba ka neme ni ba sai na zata
babu wani abu da zan yi a dakin.”

Da yake shiri ya ke nema sai ya kada baki ya ce:

“Toh yanzu na neme ki. Sai yaya kenan?” ya fada yana murmushi.

“Toh in Sha Allah za a gyara dakin.”

Ya girgiza Kai ya ce:

“Rabi kenan. Wai ke yaushe kika fara rigima irin wannan ne?”

Murmushi kawai tayi ta sunkiyar da Kai.

“Toh yanzu dai don Allah gobe ki sa a lalubo mai aikin. In ya so ranar da kike da aiki sai ta yi miki ta shiga
can ma tayi mata.”

“kada ka damu ni bani da wani aiki. Amma idan tana son mai aikin gidan da take zuwa kitso gidan Hajjaju
kace mata idan ta je can ta yi mata magana za ta samo mata mai aiki. Ita ce ma ta samowa maman Farida
ka ga.”

“Toh na ji. Ke me yasa baza ki samo mai aikin ba?” Ya tamabaya yana tsattsare ta da ido.

“Wanda za’a yiwa aiki ai shi ya kamata ya samo mai aiki. Gidan da take zuwa kitso ma idan ta gaya musu
zuwa gobe az ka ga sun samo mata.”

Nan dai ya fahimci tabbas ba za ta samo mai aikin nan ba don haka ya hakura.

Ita kuma tana tunanin babu yanda za ayi ta samowa kishiya mai aiki, salon wani abun ya faru ace ita ta
zuga. Gara ya barta ta samo, damarta ce. Ko ita din ma sai ta fi sakewa akan ace kishiya ce ta kawo maka
mai aiki. Ita din kuma ta hakura saboda abu ne da ba a yi maka shi lokacin bukata ba sai yanzu a dalilin
kishiya, sannan kuma shi ma a shiga nan a shiga can din babu abinda zai haddasa sai fitna.

Har ya tashi zai fita ya tsaya a bakin kofa ya ce:

“A ajiye min abinci na na dare.”

Ta amsa da:

“Toh a dawo lafiya.”

Ya amsa ya fice.

Ta ji dadi da ya kawo kansa, tunda ita ma a takure take da wannan gabar don ita har ji take kamar ta rame,
shine dai ta ga kamar ko a jikinsa. Duk da haka sai da tayi mamaki. Ace mutum ya koma kamar wani yaro,
yau yana gaba, gobe ya nemi shiri.

Nan da nan ta tashi ta gyara masa dakin, ta sa Khalifa ya wanke toilet din. Kafin ta gama an kira magriba.
Tana idar da Sallah ta shiga kichin. Babu lokaci don haka macaroni da miya ta dafa. Ta san yana son shayi
da daddare don haka ta dafa masa mai 0kayan kamshi.

Ai kuwa da ya dawo ya zauna ya ci ya koshi, shayi kuwa sai da sha Kofi biyu don ya jima bai sha shayi irin
wannan ba mai kayan kamshi. Saboda ita amarya ko kanunfari bata iya saka masa a shayi tunda ta fara
wannan laulayin, kamshi indai mai dadi ne bata so, shi abun har mamaki yake bashi. Ko da ya gama cin
abinci ta kwashe kwanukan nan ta barshi ta ce masa sai da safe.Yayi zaton za ta shiryo ne ta same shi a
dakinshi kamar yanda ta saba amma har 11:30 shiru, sai da ya dauki waya ya kirawo ta san nan ta taso ta
same shi a dakin.

Wannan ya kawo karshen Gabar.



Haka suke zaman na su ba ruwan kowa da kowa. Ita amarya laulayin ya saka ta a gaba, ita kuma Rabi da
yake bata da son hayaniya harkar gabanta kawai take yi.

Tun dare ciwon mara ya takura mata. Nan da nan ta kirawo shi a waya, duk da a wajen Rabi yake ranar
haka ya ce mata:

“Kanwar ki babu lafiya bari na je na gani.”

Ta ce: “Toh Allah ya sauwake. In da wani abu ka yi min waya.”

Ya fito, ita kuma ta biyo shi ta rufe kofar don ta san ba lallai ya dawo ba tunda ba yau aka fara haka ba.

Tana juyowa bayan ta gama rufe kofar taga Baba Karami a bayanta ya fito da yaji bude kofar.

“Antin ku ce bata da lafiya Abban ya je dubota, ba wani abu bane.”

Ya juya ya koma daki itama ta juya ta koma ta kwanta.

Yanzu kam ta saba idan ya fita baccinta take yi, ba kamar da ba da yana fita sai ta shiga damuwa. Cikin
duka watanshi shida amma kullum sai dare ya raba sai a yi masa waya ya fita ba zai dawo ba sai gari ya
waye.
Ya bude kofa ya shiga. A kan gado ya sameta tana ta yatsina fuska tana numfarfashi.

“Sannu Saudah, me ya faru.”

Ta kara yatsina fuska bakinta cike da yawu ta ce:

“Tun dazu ciwon mara ya hana ni bacci, ban taba jin irin wannan ciwon ba.”

Ya zauna a kusa da ita.

“Sannu. Bari gari ya waye sai muje asibiti.”

Ta tashi ta daurayo bakinta a bandaki ta dawo suka kwanta. Nan da nan ta fara jin minsharinsa bacci ya
dauke shi. Takaici ya kamata, wato ita tana fama da ciwo shi yana bacci, duk da dai itama ta saba in dai ta
taso shi toh idan ya zo baccinsa zai yi.Dama wasu lokutan tsoro ne yake saka ta kirawo shi itama ba don
yayi mata komai ba. Ko yaya ta ji wani ciwo a jikinta sai ta ji tsoron kada fa ciwo ya kashe ta ita kadai, nan
da nan sai hankalinta ya tashi. Idan ya shigo sai ta dan sami nutsuwa. Kafin gari ya waye ta ji sauki, don
haka ya shirya ya fice ba tare da sun je asibiti ba.

Wajen karfe 10 na safe mai aikinta ta zo, nan da nan ta kama aiki.Tana zaune a falon tana kallon Arewa 24
ta ji kamar an soki mararta, nan da nan ta mike tsaye ta shige daki ba tare da ta san me za ta yi a dakin ba.
Kafin ta shiga dakin ta ji duk ta jike, tana karasawa ta duba ta ga jini. Nan da nan ta rude, ta dau waya ta
kirawo Baban Halifa.A gaggauce ya shigo gidan, yana shiga ya huce wajenta.

Bayan sun fito ta zauna a mota shi kuma ya shiga wajen Rabi.

“Kanwarki ce bata da lafiya za mu je asibiti.”

“Allah sarki. Toh Allah ya bata lafiya, Sai kun dawo. Idan akwai wani abun kayi min waya ko tahowa sai
nayi.”

Ta bashi amsa.

“In Sha Allah ma baza mu dade ba.”

Ya fice suka kama hanya. Suna tafe yana mata sannu. Yana tunani a zuciyarsa ‘in ba dan wulakancin Rabi
ba wannan yar matsalar da bata fi su je asibitin su dawo ba amma sai da ta sa aka taso shi daga kasuwa.
Gashi ya kira Baba Karami ma ya ce yana lecture. Ita ba ta ma san me yake faruwa

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login