Showing 84001 words to 87000 words out of 196754 words

Chapter 29 - A-DALILIN-KISHIYA-_Labarin-Rabi_-Complete HAUSA NOVEL

09 Dec 2024

15391

kokari ki ga ya
dawo hannunki gaba daya, da kissa da kisisina da kulawa da tarairaya duk ki kara. Ki nuna masa duk wani
abu da yake jin za ta yi masa kema za iya har ma ki fi ta. Idan ya ji dadi kin ga ba lallai ya dawo da ita ba,
idan kuma ya dawo da ita ma dai ki ga an rage mata matsayi sosai kin kwace komai. Ina yaran nata?”
“Duk suna nan.”

“Toh ki mai da hankali sosai duk kiyi musu saiti, in ba haka ba sai ayi ba’a rabu da bukar ba an haifi habu.
Tsaf gidan nan ya dawo hannunki. Nan ma idan Kaka ta dawo sai na bata abun sadaka ta kaiwa Mallam
ayi miki aiki wanda ba sai an kawo miki komai ba, ko addua ce suyi miki ta samun nasara.”

Tace

“Haka ne.”

Ya Ummu tace

“Sai kin yi da gaske fa in ba haka ba kwabar ki tayi ruwa. Kuma da wuri za ki fara kafin yaje ya dawo da
ita, na san kafin karshen satin za ki ga ya fara nemanta.”

“Hmmn! In Sha Allah ba zan yi wasa ba don nima abun na su ya ishe ni wai su masu uwa a bakin murhu.
Yanzu zan saita gidan in sha Allahu, wanda ya bi ya zauna lafiya wanda bai bi ba kuma ya raina kansa.”

Yaya Ummu tace

“Idan kika dage ma kiga ya aika mata da takardar saki, kin huta.”

Nan ta zauna har sai karfe hudu sannan ta fito ta dauko su Nawwara daga makaranta sannan suka nufo
gidan.
EPISODE 20



Sai wajen karfe biyar da kwata sannan Saudah ta isa gidan, tana goye da Hanan wadda take bacci shi
kuma Baffa karami yana hannunta yayinda Nawwara da Ummi ‘yan makarantar suke biye da ita. A bude
kofar falon take don haka ta shiga da sallama, Abban yana zaune a kan kujerar da take kallon kofar
shigowa ya zuba fuskarshi a tafukan hannunshi. A hankali ya dago ya amsa sallamarsu kamar mai yin
rada, yaran suka karasa da gudu suka fada jikinsa suna murna. Ta yi mamakin ganinsa domin bai fiya
dawowa kafin karfe shida ba, kuma yanayin da ta ganshi ma ya nuna mata akwai wata damuwa. Ta
sauke Baffa da yake hannunta ta karasa kusa da shi ta sauko Hannan wadda ta riga ta tashi daga bacci, ta
ajiyeta ta zauna a kusa da shi tace

“Abba lafiya dai na ganka yanzu a gida? Ko ba ka jin dadi ne.”

Ya daga kanshi a hankali ya kalleta ya girgiza kai yace

“Ba a ga Rabi ba.”

Mamaki ya cika ta, ta ce

“Kamar yaya ba’a ganta ba?”

“Toh duk inda ake sa ran za ta je an duba bata je ba.”

“Subhanallahi, me yake faruwa ne?”

“Shine abinda nake gaya miki, ba’a ga Rabi ba. Amma dai Yayanta ya ce mu bari zuwa da safe za su kara
bincikawa a dangi ko za a sami inda take.”

Mamakinta ya karu, me yake faruwa ne? Ya kamata ace ai gidansu ta tafi ko kuma gidan yayan nata,
kuma mace da girmanta balle ace bata tayi. Ta dube shi tace

“Allah ya sa a sameta cikin koshin lafiya, in sha Allahu ma tana wajen ‘yan uwanta.”

Ya bude baki da kyar yace

“Haka muke fata.”

Suka yi shiru na dan lokaci, ta mike ta nufi dakin domin ta canzo kaya ta zo ta shiga kichin. Har ta kusa
bakin kofar ya juya ya kira sunanta, ta tsaya ta amsa sannan yace

“Ki dafa abincin buda baki da sahur da yaran nan, Madu ma ba lafiya ce da shi ba. Idan kin gama abincin
sai na kirawo su su zo su dauka.”

A ciki ta daure ta bashi amsa

“Uhmmn, toh.”

Ta tura kofa ta shige dakin. Bata yi zaton zai ce ta dafa abinci da su ba musamman da taga jiya bai yi
zancen ba sai ma tambayar su da yayi sun ci abinci? Ita ba mace ce mai son girki ba tana yi ne kawai don
ya zamar mata dole, ya za ayi kuma ya ce ta yi girki da yaran, kenan sai ta yi abincin mutum takwas ko
tara idan ta hada da kanta da Bala mai gadi. Anya kuwa za ta iya? Sai kuma ta tuna abinda Ummanta ta
gaya mata

‘Gidan da maigidan duka sun dawo hannunki, sai ki mai da hankali.’

“Akwai aiki, Allah ya bani iko.” Ta fada a fili yayin da ta karasa gaban mudubi.

Nan da nan ta canza kaya ta wanke fuska da yake saida tayi sallah a gidan Umma sannan ta fito don haka
sai kawai ta canza kaya ta fito. Inda ta barshi na ta same shi, sai da ta karaso wajen ya mike tsaye yace

“Ga su nan bari na je na dan kwanta.”

Ya tsallake su ya huce dakin ya turo kofa, ta bi kofar dakin da kallo tana daga nan a zaune. Wannan wane
irin abun haushi ne, ta ma yi zaton zai dan zauna ta bar masa yaran ko aikin nata ya fi sauri ya ma wani
tashi ya shige wai kwanciya ma zai yi. Ta gode Allah ma ta riga ta gyara Baffa da Hanan tun a gidan
Umma kafin su kamo hanya, don haka babu mai jin yunwa. Ko kayan makaranta bata tsaya ta cirewa su
Nawwara ba ta barsu da shi a jikinsu ta fada kichin, sai da ta dauki mintuna a tsaye a tsakiyar kichin din
tana tunanin me zata dafa kafin ta yanke shawara. Ruwan zafin ta dora na shayi sannan ta fice ta tafi
store din baya inda duk wasu kayan abincin gidan suke, tana hanyar shiga suka ci karo da Salim a hanya
ya dauko doya guda daya da kwai guda goma a roba. Dauke kai yayi zai huce ta dube shi tace

“Abinci za ku dafa ne?”

Ya dube ta a banzace yace

“A’a wasan kasa za mu yi.”

Ko sauraronta bai yi ba ya huce ya barta tana bin bayanshi da kallo. Duk cikinsu ma shine wanda take
ganin ba shi da rashi kunya ko wani jin kai kamar na sauran yaran, don haka wannan maganar da ya gaya
mata tayi matukar ba ta mamaki. A fili tace

“Hhm uhm! Zan yi maganinku ne daya bayan daya, mukullin store din ma sai na sa an kwace shi na ga
tsiya.”

Ta huce ta bude store din da nata mukullin ta shiga. Akwai freeze babba a cikin store din inda ake ajiye
kifi da duk wani nama na gidan, nan ta bude ta debo kaji itama ta dauko doya ta fito, tana shiga kichin ta
ajiye kayan ta huce dakin Abban. A kwance yake amma ba bacci yakeyi ba domin ba zai iya bacci ba yau
idan ba ji yayi ance an ga Rabi ba. Bayan ya amsa sallama ya juyo ya dube ta yana jiran ta Fadi abinda ta
zo dashi. Tana daga tsaye tace

“Na ga fa Salim ya debo doya da kwai daga store ina ga fa girki za su yi kada su zo su wahalar da ni.”

Cikin yanayi na kosawa ya yi tsaki ya dauki wayarsa ya danna kira ba tare da ya ce mata komai ba, ana
daga wayar yace

“Salim kada kuyi girki antinku za ta dinga dafawa daku.”

Ya ajiye wayar ya dube ta yace

“Ki je ki dafa a nan za su dinga karba.”
Ya juya mata baya kafin tayi magana, ta bi bayanshi da kallo na dan lokaci sannan ta juya ta fice. Ta so
ace ya barsu su dinga dafawa don gaskiya ba zata juri girki ba musamman na mutane da yawa haka.
Haka ta koma kichin ta dora tukwane don ta soya doya kuma ta dafa farfesun kaji, in ya so daga baya ta
dafa ko taliya ce don sahur. Haka ta ci gaba da aikin nan tana yi tana tunanin yanda za ta yi ta rama
wulakancin da Salim yayi mata.

……….

Salim yana ajiye waya ya dubi Madu da yake zaune a kan dining table yace

“Abba ne yace kada muyi abinci wai za ta girka da mu.”

Khalifa da yake cikin kichin din ya leko don ya ji me ake cewa yayinda Madu yace

“Manta da su kawai, wa zai ci abincin wannan yarinyar, ku tafi ku ci gaba da aikin ku kawai.”

Don haka suka ci gaba da aikin, suka dafa shayi sannan suka soya doya da kwai suka bar abincin sahur sai
an tashi sai su dafa indomie.

Bayan an yi kiran sallar magriba Abba ya karya azuminsa ya fito da niyyar tafiya masallaci, a nan kan
barandar Saudah ya tsaya ya kwalawa Khalifa kira. Yana zuwa Abban yace

“Shiga ka karbo muku abinci, in ka kai ka ajiye ku taho masallaci.”

Yace

“Toh.”

Ya shige Abban kuma ya tafi masallaci. Yana shiga tana tsaye a dining table ta nuna masa kwanukan da
zai dauka guda biyu, na farfesu da kuma na soyayyiyar doya ya fice. Ita kuma ta dan tsaya tana hangen
shigarsa wajen ta tagarta, har ta juya za ta bar wajen sai ta hango Madu ya fito ya tare shi da kwanukan.
Daga nan kan baranda ya kwalawa Malam Bala kira, da sauri ya ajiye butar sa da ya gama alwala ya
karaso ya rage tsaho

“Dan Alhajin Allah barka da shan ruwa na wajena.”

Yace

“Barka Malam Bala.”

Ya umarci Khalifa ya mikawa Bala kwanukan ya bude murya yana magana da karfi yace

“Samu wasu masu rangwamen gatan ka basu wannan su sha ruwa Mal Bala.”

“An gama na wajena, Allah ya bada lada Allah ya maimaita mana.”

Ya karba ya na ta murna ya dubi khalifa yace

“Taimaka min da wani dan faranti na juye sai a ajiye wadannan fulasan ba sai an fita da suba.”

Suka juya suka shige ciki suka barshi yana godiya.

A fusace ta saki labulen ta juya ciki ta yi tsaki a fili tace
“Lallai yaran nan ‘yan iska ne, tab. Wallahi ba zai yiwu ba, dole ya dau mataki kuma sai na sa an karbe
mukullin store din za su gane kurensu.”

Ta huce ciki domin yin Sallah.




Haka ya sha ruwa yana yi yana waya, duk wanda yake tunanin yana da alaka da Rabi sai da ya kirawo shi
amma babu wanda yake da labarinta. Bayan ya gama shan ruwa ya taso daga dining table ya dawo ya
zauna a kan kafet ya kunna labarai. Tana kallonsa ta tabbatar hankalinshi baya kan TV din Bai ma San
abinda ake yi ba. Ta Dan yi gyaran murya don ta janyo hankalinshi, ya dubeta tace

“Abba su Khalifa basu ci abincin da na dafa ba fa, Bala mai gadi suka bawa wai ya bayar.”

Da mamaki ya dubeta yace

“Suka bayar muma, ko dai ragowa suka bayar kin san Mommy bata jira sai an cinye saka su take a gaba
kowa ya debi abinda zai iya cinyewa tana cewa a bayar da zafinshi yanda wanda ya samu shima zai ji
dadi.”

“Babu fa abinda suka diba, ko shiga ma da shi basuyi ba fa suka bayar. Ni dai idan baza su dinga ci ba a
daina wahalar da ni kawai.”

Ya dauki waya ya kirawo Ahmad, tana nan zaune tana mita yayi sallama ya shigo ya tsuguna a gaban
Abban yace

“Ga ni Abba.”

“Wai baku ci abincin da antinku ta dafa ba kuka bayar?”

“A’a Abba, diba fa muka yi wanda yayi saura ne muka bawa Bala ya bayar don kar ya huce. Ba ma shi da
yawa fa wanda aka bayar din.”

“Toh shike nan, ina Yusufa?”

“Yana nan.”

“Toh shike nan, je ka.”

Ya tashi ya fice ya barsu. Abban ya dubeta yace

“Kin dai ji ko? Ki dinga yin abinci da kowa kawai, ko bako ne ya shigo gidan nan bai kamata ya fita bai ci
abinci ba balle dan gida.”

Shiru tayi saboda takaici ba zai barta tayi magana ba, tana ji tana gani suka bayar da abincin amma kiri
kiri ya ce ba haka bane. Wadanda take wa kallon muminai a cikinsu ma su suke raina mata hankali don
wulakanci.

Sai da ya dawo daga sallar tarawih sannan ya shiga wajen yaran, suma shigowarshi kenan daga
masallaci. Yana shiga Madu ya mike zai huce daki Auta ya bi bayanshi, Abban yayi sauri yace
“Madu, ku zo nan.”

Suka juyo suka dawo dole ta sa suka zauna a kan kafet domin shi Abban ya riga ya zauna a kan kujera, ya
dubi Madu yace

“Muhammadu ya jikin naka?”

“Da sauki.”

“Yaka Auta.” Ya fada yana mika masa hannu, ya taso ya zauna kusa da Abban. Yana zama hawaye ya fara
bin fuskarsa, Abban ya dafa bayanshi yace

“In sha Allahu za a ga Mommy, ni na san babu inda ta shiga, fushi dai ta yi kuma in sha za ta dawo.”

Babu wanda yace masa komai haka suka zauna na dan lokaci. Madu ne ya fara mikewa ya koma daki, a
hankali duk suka watse suka barshi shi kadai da Ahmad wanda yake zaune a kusa da shi. Ya dubi Ahmad
yace

“Kun yi waya da Baba kuwa?”

“Eh muna waya tun jiya.”

Suka sake yin shiru na dan lokaci, Abban ya nisa yace

“Babu inda kuke tunanin kuma Mommy za ta tafi?”

“Uhmmn! Abba muma daman gidan Anti Shafa muka zata za ta je amma bata je ba, toh Baba Munzali
dai yace zai bincika danginsu ko wajen Gwaggonsu ta tafi.”

“Allah dai ya sa can din ta tafi.”

Suka sake yin shiru kowa da abinda yake ransa.

“In Sha Allahu za a ganta, babu inda Rabi za ta shige ace an rasa ta in sha Allahu. Ka dinga kwantarwa
kannenka hankali ka ji, bana son yawan kukan nan da Auta yake yi.”

Abban ya fada yana gyara zama.

“Toh Abba.”

“Zo ka rufe muku kofar Ahmadu, in Sha Allahu komai zai warware zuwa gobe.”

Ya rufe kofar Abban ya fice yana tunani kala kala. Wannan kukan da Auta yake yi ji yake kamar a
kwakwalwarshi yake yi, Yaro mai walwala gaba daya ya shiga damuwa. Sosai yaran suka bashi tausayi, ya
tuno yanda ya shiga tashin hankali da innarshi ta rasu. Toh Rabi da rasuwa tayi ma ai sai su barwa Allah
su roka mata gafara, toh amma fa ‘bata tayi. A wane hali take? Yaushe za ta dawo? Wadannan
tambayoyin su zuciyarshi take ta maimaita masa ya kasa samo amsar su. Ko da ya shiga dakin ma ya
kwanta duk yanda ya so yayi bacci kasawa yayi, don haka sai kawai ya tashi yayi ta Sallah har sai da ya
gaji.

Ko da aka fito sahur ma nan da nan Saudah ta dafa jallofa sphagetti, dole ta debarwa su Madu Abban da
kanshi ya dauka ya kai musu. A kichin suka ajiye abincin suka dafa indomie, sai da safe sa bawa malam
Bala ya bayar.
Daf da Magriba Baba Mubarak kanin Rabi ya iso Kano daga gidanshi dake Kaduna. Yana shigowa ya huce
gidan Yaya Munzali ya ci sa’a kuwa ya same shi ya dawo daga aiki. Suka gaisa sannan suka jajantawa
juna, Mubarak yace

“To ina Rabi za ta shiga ace an nemeta an rasa?”

Munzali ya ce

“Shine abun tambaya, ka san tun safe nake ta waya kaf dangi babu wanda ban kirawo ba har wadanda
nake jin ma bazata wajen nasu ba duk sai da na kirawo su amma babu wanda ya ganta.”

Suka yi shiru na dan lokaci Mubarak yace

“Baraka ma ta ce min gobe za ta shigo da safe.”

“Da ma tayi zamanta, ko da yake bata jin wahalar tafiya ta riga ta saba.”

Suka sake yin shiru na dan lokaci, can Mubarak ya gyara zama ya fuskanci Munzalin yace

“Toh wai shi Usman din ko ya fara shan ganye ne, in ba haka ba shekara talatin da auren ka tashi da
azumin nan ka cewa mace wai ta bar maka gidanka don wulakanci.”

“Toh wa ya sani ne, ka san zaman auren sai hakuri.”

Ya jijjiga kai yace

“Wallahi Yaya in ba’a ga Rabi ba kotu zan makashi don ubanshi, idan ma da ba don ina yiwa yaranshi
kara ba wallahi sai na sa an rufe shi. Wannan ai cin fuska ne da wulakanci.”

Munzali ya dafa shi yace

“Ni tsiyata da kai saurin fushi, kayi hakuri muga gobe. Ai kwana za ka yi ko?”

“Toh ba dole na kwana ba, ai sai abinda hali yayi.”

“Toh da safe in Sha Allah sai mu je gidan mu same shi.”

“Au Yaya wai baza mu je in an sha ruwa ba?”

Ya sake dafa shi yace

“Ka yi hakuri mu bi komai a hankali, in sha Allah da safen za mu je.”

Duka suna mamakin inda Rabi za ta shiga, shi Mubarak ma ya fi daukar zafi domin gani yake kawai an
yiwa yar uwarsa wulakanci ne, kuma da azumi ka dubi mace ka ce ta tafi, toh ina za ta. Shi dai wallahi
dole a nemo Rabi in ba haka ba za ayi tashin hankali da shi.

Nan suka zauna suka sha ruwa sannan daga baya Mubarak ya tashi ya tafi masaukinshi.

…………………..

Yanda Abba ya kwana yana Sallah haka Baba karami ma ya kwana cikin tashin hankali, Sallah kawai yake
yi yana addua Allah ya sa a sami Mommy cikin koshin lafiya. Tun da daddare yake so ya kirawo Baffa
Hassan don ya san bai san me yake faruwa ba, amma sai ya fasa saboda kar ya hanashi bacci. Gari na
wayewa karfe bakwai ya kasa hakuri don haka bayan ya gama shirin tafiya aiki ya dauki waya ya kirawo
Baffa. Cikin raha da barkwanci suka gaisa kamar yanda yake dabi’ar Baffa. Yace

“Uhmmn, Baffa ko nan wajenku Mommy ta taho?”

“A’ah, bat zo ba babban maigida, akwai matsala ne?”

Cikin rawar murya yace

“Baffa ba a ganta ba fa tun shekaran jiya.”

Baffa ya shiga rudani yace

“Subhanallahi, me yake faruwa ne?”

Nan ya bawa Baffa labarin abinda ya faru, yayi ta salati yana

“Usmanu Bai kyauta min ba, Bai kyauta min ba. Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun. Yanzu kai kana Ina?”

“Ina Abuja Baffa.”

“Kai jama’ah, toh bari na baincika na ji.”

Suka ajiye waya. Baffa ya gigice gaba daya ya ma rasa me zai yi, nan yayi wa Baba Yalwa bayani itama ta
shiga rudani tace

“Malam ai tafiya za ka yi ka sami Usmanun tun bai tafi kasuwa ba.”

“Haka za a yi, daga nan ma in gano yaran.”

Ya dauki waya ya kirawo Tijjani; jikanshi ne na wajen Aliko da yake shi a nan Kanon yake lecturing a
jami’a; yace

“Tija idan baka fita aiki ka zo ka kaini gidan Baffanka Usmanu.”

Yace

“Toh Baffa, ina ma kusa da gidan yanzu zan shigo in sha Allahu.”

Suka ajiye waya.




Da sassafe Baraka ta baro Jigawan don haka kafin karfe takwas tana gidan Yaya Shafa. Suna zaune a falo
suna mayar da zance ta dubi Yaya Shafa tace

“Wai Ya shafa ya za ayi a ce an rasa Bibi a garin nan, wace irin bura uba ce za ta sa da azumi amma
mutum ya dubi mace yace wai ta fice masa daga gida, wannan wane irin hauka ne?”

(Baraka da Mubarak suna kiran Rabi Bibi)

“Nima

24, February 2025
Maryam

Plsss

05, January 2025
Maryam

So good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login